Free chapter · Read without an account

INUWAR DA BA A GANI BA

by Ayshnur Pyar · INUWAR BAYA (Tale of Haseena)

INUWAR BAYA (TALE OF HASEENA)

Daga Alkalamin Ayshnurpyar (Hameesha)✍🏻

BABI NA BIYU: INUWAR DA BA A GANI BA.

BARRISTER ZAID - THE PROTECTOR

Akwai mutanen da suke magana domin su rinjaya.

Akwai kuma waɗanda suke yin shiru... domin sun riga sun yi nasara.

Barrister Zaid ya saba da zama cikin ɗakin nazarinsa, fitilar teburinsa na haskawa akan tarin takardun Shari'a, alƙalaminsa na motsi cikin nutsuwa.

Duk da shurinsa, ƙaddara ta riga ta tura masa shari'ar da ba ta cikin kundin doka.

A wannan daren, ba zai kare wasu ba kawai... Zai kare wata INUWA. Inuwar da ta fito daga duhu.


5th Jan 2025 1:15am

Ɗakin karatun Barrister Zaid ya kasance tamkar ɗakin ibada; akwai wani irin shiru mai cike da kwarjini, wanda ke gauraye da ƙamshin tsofaffin takardun shari'a, da kuma daddaɗan ƙamshin turarensa mai sanyi.

Zaid na zaune gaban teburinsa, fuskarsa ɗauke da nutsuwar mutumin da ya saba warware sarƙaƙƙiyar shari'a.

Hannunsa na dama riƙe da alƙalami, yana bin layi-layi na shari'ar dake gabansa cikin tsananin natsuwa.

Alƙalamin na tafiya a hankali, baya barin ko layi ɗaya ya kufce masa.

Katsam, wannan natsuwar ta rabe gida biyu lokacin da wayarsa dake gefe ta fara rawa.

Ba ƙara mai tsawo ba, sai dai ya isa ya katse nutsuwarsa.

Ya tsaya na sakan ɗaya, idanunsa suka sauka kan screen ɗin.

"The Big Doc" Sunan yayansa.

Murmushin girnamawa yayi, a hankali yasa hannu ya ɗaga kiran. "Ya Hussain..."

Sai dai maimakon muryar yayansa, numfashi mai rawa da karkarwa ya cika masa kunne.

"Mai... mai wayar ya yi haɗari... ..." Muryar mace ce, tana nishi cikin firgici. Ta bayyana masa wurin da hatsarin ya faru - hanyar daji dake nufar Psychiatric Hospital Barnawa.

"Ku zo da wuri... yana zubar da jini!"

Ba tare da ta jira amsawarsa ba ta katse wayar. Layin ya mutu.

Shiru ya dawo, amma wannan karon shiru ne mai nauyi. Alƙalamin hannunsa ya tsaya cak. Takardar da yake riƙe da ita ta zame ta faɗi.

Numfashinsa ya sauya, amma fuskarsa...Irin ta ƙwararren lauya...Ba ta sauya ba. "Mai wayar...?" ya maimaita a hankali.

'Ba ta ce Hussain ba...Wannan ba kiran wanda ya san su ba ne; wannan kiran wacce ta sami wayar ne.

Kenan...

Da gaske wani abu ya faru.

Hussain ya yi accident.'

Wuf  ya miƙe tsaye cikin izzah yana faɗin, "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun."

Ya sake kira, amma ba a ɗaga ba.

Ba tare da ruɗani ko ihu ba, ya ɗauki mukullin mota da wayarsa.

Ya fizgo suit ɗinsa dake rataye, lokaci guda ya fice yana ƙoƙarin sanya maballan suit ɗin da ya ɗora kan farar rigar dake jikinsa.

Parking lot ya nufa cikin azama.

Ya fito da motarsa ya danna horn.

Maigadi ya buɗe masa gate ya dauki hanya.

Kwanyarsa ta fara aiki kamar na'ura: Wacece me wannan kiran? Me ya sa take tsoro haka? Shin wani mummunan abu ya sami Hussain ne? Tana wurin don ta taimaka, ko kuma ita ce sanadi?

Hasashensa na gaya masa cewa wannan matar ba hatsari kaɗai ta gani ba; akwai wani ɓoyayyen abu dake tsakaninta da wannan duhun daren.

Yana tuki, hannunsa ya matse steering ɗin motar, idanunsa na kan titi yayin da zuciyarsa ke lissafin kowane sakan.

Ya ciro wayarsa, layin yayansa ya lalubo: "K. The Hunter."

Ringing ɗaya. 
Detective Khalid ya ɗaga a take.

"Zaid?"

"An kira ni da wayar Hussain yanzun nan. Ya yi accident a kan hanya..."

"What!?" Ya katse shi da izzar muryarsa irin ta jami'in tsaro.

"A ina? Yana ina yanzu? Waye ya kira wayar?" 

"I don't know, K.

Mace ce ta kira a tsorace. Ta ce suna kusa da Psychiatric Hospital... Ga dukkan alama Ya Hussain yana cikin wani hali mai tsanani don ba a asibiti yake ba..."

Shiru na sakan daya.

"Bari zan kira paramedic yanzun na kusa da asibitinsu. Ka riga ni isa please, zan taho da jami'ai don tabbatar da abinda ya faru..."

Ya ɗan dakata, muryarsa ta ƙara yin nauyi da nuna gargaɗi.

"Kada a taɓa komai har sai na ƙaraso!" Kafin Zaid ya ba da amsa, Khalid ya katse kiran. Halinsa ne; baya ɓata lokaci wurin magana idan aiki ya taso.

Barrister Zaid ya lumshe ido yayin da yake ƙara gudu.

'Idan wannan ba hatsari ba ne... to wani ya fara shari'ar da bai shirya kare kansa daga gare mu ba.'

CRIME SCENE: 1:45AM
THE VEIL SECRET.

Dajin ya cika da duhu mai nauyi. Motoci biyu ne suka kusanto wajen ta mabanbantan kusurwoyi.

Motar Zaid ta fara isowa ta gefen daji.

Daga inda yake yana jiyo jiniyan paramedics dake tahowa ta kan babban titi, alamun sun kusa karasowa.

Wannan tazarar ne ya bashi mintuna kadan masu mahimmanci.

Hasken headlights dinsa ya haskaka akan motar Hussain dake kife, ƙarfen jikinta ya murɗe ta hanyar da ba ta dace da hatsari na yau da kullum ba.

Zaid ya fito da sauri ya nufi inda ya hango Hussain kwance jike cikin jini da yayyafin ruwan sama.

Jini ya bata tun daga goshinsa, wuyansa zuwa gaban rigarsa, numfashinsa na fita sama-sama.

Zaid ya durƙusa kusa da shi, hannunsa dake dan rawa na duba bugun jininsa (pulse).

Ya riko hannun yayansa cikin nashi da karfi "Hussain... Hussain...kana jina? Who did this to you?

Hussain... can you hear me? Stay with me please..." Ya fara kokarin tallabarsa.

A daidai nan, idanun Dr. Hussain suka dan bude da wahala.

Zaid ya zura masa ido, zuciyarsa na tambaya 'Wane ne yayi wa danuwana wannan d'anyen aikin?

Ina wacce ta kira waya?
Ta gudu!?' 

Idanunsa suka sauka kan wani mayafi baƙi (black veil) dake lulluɓe a jikin Hussain. Mayafi ne mai laushi (silk), wanda jini ya taba shi yana fitar da wani scent na daban.

Hannayensu na cikin na juna, Hussain ya sake buɗe ido da ƙyar, ba zai iya magana sosai ba, ya kalli Zaid tare da daga yatsunsa kadan ya nuna mayafin dake jikinsa a hankali ya furta "Khalid."

Lokaci daya Zaid ya fahimci me yake nufi. Hussain ba zai ambaci sunan Khalid haka nan ba, idan yayi to yana nufin abu daya ne a boye....

Yasan halin danuwansa baya bari alama ta wuce ba tare da ya bi sawunta ba.

Ya san cewa idan Khalid ya ga wannan mayafin. 
Mace, 
cikin dare, 
wurin da aka zubar da jini sannan ta gudu.

Tabbas! Bincikensa zai karkata ne kacokan kan gano wacce ta bar shi, kuma hakan zai iya tona asirin da Hussain yake ƙoƙarin rufewa ko da a bakin mutuwarsa.

Ba tare da ɓata lokaci ba, Zaid ya cire mayafin daga jikin yayansa, ba don ya kare Inuwar da ta barshi ba.... Ba don ya hana bincike ba, sai don girmama sirrin yayansa.

Cikin kwarewa da izzah ya ninke shi cike da tunani mai nauyi, ba don tsoro ba.

Ya koma bayan motarsa ya ɓoye shi a seat ɗin baya. Ya dan tsaya na sakan daya...A karo na farko a rayuwarsa ya zabi karya doka ta hanyar boye shaida (evidence) daga idon doka.

Kuma yasan wata rana gaskiya na iya tambayarsa dalili...

Amma a wannan daren, amincin dan'uwa yafi kowace doka a wurinsa.

A hankali ya dawo gun Dr. Hussain, ya cire suit ɗin dake samar farar rigarsa, ya lulluɓe shi cike da kulawa.

Wayar Hussain na kwance kusa da shi. Barrister Zaid ya ɗauke ta, ya kalleta na sakan daya, sannan ya zura a aljihu.

A daidai lokacin, motar asibitin suka karaso.

KIRAN INUWA: THE SECOND RESPONDERS

Paramedics suka sauko cikin hanzari, za su fara aikin ceto rai.

Sautin takun takalman paramedics ɗin ya daki ƙasa da sauri, kowannensu riƙe da akwatin taimakon gaggawa da gadon ɗaukar marasa lafiya (stretcher).

Babban cikinsu ya durƙusa gefen Hussain, idanunsa na yawo a raunukan da jini ya zuba daga jikinsa "Sir, can you hear me? Stay with us!" ya faɗa da ƙarfi yayin da yake duba bugun jininsa.

"Pulse ɗinsa na raguwa! Muna buƙatar C-spine collar yanzu!" ɗayan ya amsa cikin hanzari. Nan take suka ɗaura wa Hussain abin wuya na musamman don kar kashin bayansa ya goce yayin ɗaukarsa.

Zaid na tsaye, suit ɗinsa na jikin Hussain, yana kallon yadda suke yaga saman rigar Hussain da almakashi mai kaifi don duba raunin dake jikinsa. Suka sanya masa oxygen mask, iskar na fita da sauti hiss-hiss yayin da suke ƙoƙarin daidaita numfashinsa.

"Muna buƙatar IV line yanzu, ya rasa jini da yawa!" In ji jagoran nasu. Cikin ƙwarewa suka sanya masa ƙarin ruwa (drip) ta hannunsa, yayin da suka ɗaga shi cikin tsari zuwa kan stretcher ɗin.

Haske ya sake ratsa duhu, motocin jami'ai ya haske dajin tare da jiniya me karfi. Detective Khalid ya bayyana tare da tawagarsa.

Kofa ta bude, Khalid ya sauko.

Akwai masu bincike da suke tambayar mutane.

Akwai kuma waɗanda suke tambayar ƙasa.

Khalid yana daga cikin waɗanda ƙasa ce ke amsa musu.

Ya taka kasa a hankali, ba don yana jin tsoro ba....
Amma don kada ya katse abin da shiru ke faɗa.

Ba ya son hayaniya. Domin hayaniya tana ɓoye gaskiya.

Idanunsa ba sa yawo. Suna tsayawa ne.
Suna zurfafawa.
Kamar wuka da ba ta bukatar ihu domin ta yanke.

Mutane suna ganin jini su kauda kai.

Shi yana ganin jini... ya ga labari.

Ya saba da idanuwan da ke ƙoƙarin ɓoye laifi.

Ya saba da murmushin da ke ɗauke da ƙarya.

Amma abin da bai taɓa saba ba... shi ne shiru kafin gaskiya ta bayyana.

A wajen laifi, Khalid ba ya jin tsoro.

Laifi ne yake jin tsoron sa.

Domin a duk inda ya taka... wani abu yana rushewa.

A wannan daren, ba kawai wani case ya iso hannunsa ba... Farautar inuwa ne ta soma.

Farauta ta fara kafin wanda ake farauta ya sani....

Ya durƙusa. Yatsunsa suka taɓa ƙasa stain na jini, yayyafin ruwa bai gama korewa ba.

Ya ɗan rufe ido na daƙiƙa guda - kamar yana sauraro. Sannan ya buɗe su.

Murmushi ba ya kan fuskarsa. Tsoro ma babu. Sai tabbaci.

Ya miƙe a hankali murya ƙasa-ƙasa ya ce, "Ya yi kuskure."

'Yan sanda suka kalle shi.

"Wane ne, sir?" Idanunsa ba su motsa ba.

"Wanda ya yi tunanin duhu ya fi ni haƙuri."

Shiru ya sake sauka.

"Amma a wannan daren farauta ta fara..."

Pyar✍🏻

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol