Free chapter · Read without an account
74
Farhana ta shiga dakin da Isabella ta ware mata ita da yaranta cikin sanyi. Dakin ya yi tsit, sai karar numfashin su Lamido da Sultana dake bacci a gefe daya, basu san irin guguwar dake tashi a zuciyar mahaifiyarsu ba.
Ta ajiye jakar hannunta, ta zaro wadancan takardu da littafin da ta dauko daga gidan AK. Hannunta na rawa, ta fara bude ambulan din dake dauke da Court Order. Kalmomin farko da suka daki idonta sun sanya jikinta yin sanyi:
Asmau sani sambo vs . ABDULKADIR TAHIR TAMBUWAL: ATTEMPTED MURDER.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Farhana ta fada a hankali, tana dafe kirjinta. "Wacece Abdulkadir ya yi yunkurin kashewa? Me hakan yake nufi?"
Ba ta gama fahimtar sarkakiyar shari'ar dake cikin takardar ba, amma ta san wannan babban abu ne da dole ta nuna wa Isabella washegari don ta fassara mata a matsayin tana lauya. Cikin hanzari da son sanin asali, ta bude tsohon Diary din AK, ta fara karantawa daga inda ya fara rubutu game da kuruciyarsa.
KANO, 200X
Rubutun hannun AK ne na lokacin yana dan shekara 19. Layukan sun nuna fargaba da kuma nadama dake boye:
"...Mun zo Najeriya hutu daga USA . Abokina Khalid ya gayyace ni hutun gidansu dake Kano. Wannan ne karon farko da na taba zuwa Kano, ban san kowa ba sai Khalid. Muna jin dadin rayuwa, musamman yadda muke ji da lasisin tuka mota da muka samu tun muna shekara 18 a bara."
"Wata rana, muna cikin jin dadi, muka yanke shawarar zamu yi tsere (Car Race) a cikin gari. Muna cikin gudu ba tare da tunanin komai ba, Khalid yana gefena yana yi min ihu da kirari . Sau uku ina kusan kade mutane amma Khalid sai kara zuga ni yake yi. Muna zuwa daidai titin da zai kaimu gidansu abokin Khalid , ban san yadda aka yi ba, kawai sai na ji na buge mutum da karfi."
"Daga cikin motar, na ga mutum ya yi tsalle ya fadi kasa da karfi. Muma motar tamu ta fa gangara gefen titi. Na fita a guje cikin rude, abinda na gani ya sanya numfashi na tsayawa. Wata mata ce kwance cikin jini, a gefenta wata yarinya ce yar kimanin shekara takwas, ta durkusa a kusa da mahaifiyarta tana wani irin kuka mai cin rai."
"Mutane sun fara taruwa daga ko'ina. Na kalli matar nan a karo na karshe, na san ta mutu. Cikin tsananin tsoro, ban tsaya taimaka musu ba, na shige mota na ja ta a guje. Ina tashi, na ji wani yana ihu yana cewa 'A dauki lambar motar nan!'. Hankalina bai dawo kan Khalid ba sai daga baya, ashe shima ya bugu sosae a hatsarin."
Numfarfashi Khalid keyi cikin jigata
"Kai tsaye na garzaya da Khalid asibiti, sannan na kira yan gidansu. Na kira Mummy na a Abuja ina kuka, nace mata 'Mummy, na kashe mutum a Kano!'. Mummy tace min in yi shiru, in daina kuka, zata taho Kano da asuba. Haka na kwana a asibiti, ina jin kukan yarinyar nan a kunnena, ina ganin jinin matar nan a idona."
"Yan Gidan su Khalid sun cika asibitin, kowa yana kuka. Amma kash, ko kafin asuba ta yi, Khalid ya cika. Abokina daya tilo ya rasu a hannuna, ya bar ni da nauyin ran matar da na kade, da kuma sirrin da nake tsoron ya fito fili..."
Farhana ta rufe littafin, hannunta yana karkarwa. Hawaye suka fara wanke mata fuska. Yanzu ta fahimci dalilin da ya sa AK yake da wani irin daci da kuma tsoro a tare da shi. Ta fahimci cewa duk wannan mulkin da kudin, ashe akwai inuwar kisan kai dake binsa.
"Abdulkadir..." ta fada cikin kuka. "Dama wannan ne abinda kake boyewa duk tsawon shekarun nan?"
Farhana ta ƙara matse littafin a ƙirjinta, numfashinta yana fita da sauri yayin da take karanta yadda aka juya akalar shari'ar a shekarun baya. Rubutun AK na wannan lokacin cike yake da firgici da kuma jin nauyin zunubin da aka tilasta masa ya fito da shi a matsayin gaskiya.
Diary ɗin AK (Cigaba da Karatu)
"Washegari Mummy ta iso Kano da asuba. Lokacin ƙarfe takwas na safe har an kai gawar Khalid gidansu don shirin jana'iza. Muna cikin wannan halin, sai ga 'yan sanda sun zo gidansu Khalid. Sun ce an kai ƙarar wani yaro da ya yi 'Hit and Run' na wata mata. Take anan, ba tare da wani jinkiri ba, dangin su Khalid suka nuna ni da yatsa. Sun harzuka, har suna cewa su ma za su shigar da ƙarar cewa ni ne na kashe musu yaro tunda ni nake tuƙi."
"Gidan ya rude, amma Kakar Khalid, Hajiya Zulaiha, ita ta tsaya ta hana. Ta ce lokacin Khalid ne ya yi, kuma ita ba ta yafe ba idan aka tada maganar burinta kawai shi ne a ci gaba da yi masa addu'ar gafarar Allah. Wannan kalaman nata suka ɗan kwantar da kura, amma fa 'yan sanda ba su bar ni ba."
"Mummy ta tafi da ni ofishin 'yan sanda, ta yi iya yin ta don ganin ba a kulle ni ba, amma abin ya faskara. Ashe dangin matar da na kaɗe su ma masu kuɗi ne da faɗa a gari, tuni suka kai maganar kotu inda aka tuhume ni da laifin Attempted Murder (Yunkurin kisan kai). A lokacin, Daddy yana can ƙasar Turkey yana wani (course), don haka bai san wainar da ake toyawa ba."
"A nan ne na samu labarin cewa ashe matar ba ta mutu ba, amma tana cikin mawuyacin hali (Critical Condition). Muka fara zaman shari'a, kullum zuciyata tana bugawa. Ban san irin shiga da fice da Mummy ta yi ba, sai kawai na ga dangin matar sun janye ƙarar (withdrawing the case). Daga baya na gano ashe akwai wata mace a danginsu matar wadda take da kusanci da Mummy, ita aka bi ta hanyarta aka kashe maganar."
"Koda yake dangin matar (yayyenta maza) ba su yarda ba, sun yi ƙoƙarin yin daukaka ƙara (appealing), amma Mummy ta riga ta shirya komai. Waccan matar da take da alaƙa da Mummy ta tsaya a kotu ta bayar da shaidar cewa: Ba ni ne nake tuƙi ba, Khalid ne, kuma tunda ya rasu babu wanda za a hukunta."
"Mummy ta tura mini takarda, ta ce dole in musanta (deny) cewa ni ne nake kan sitiyari. Na tsaya a gaban alkali, na yi ƙarya, na ce Khalid ne yake tuƙi. A haka aka bar maganar, aka rufe fayil ɗin shari'ar, muka tattara muka dawo Abuja. Amma koda na dawo Abuja, na bar rabi na rayuwata da gaskiyata a Kano. Na san cewa na tafi da haƙƙin matar nan, da haƙƙin Khalid da aka ɓata wa suna, da kuma haƙƙin yarinyar nan da na bari tana kuka.
Farhana ta rufe littafin, hannuwanta suna rawa. Ta kalli inda su Lamido suke bacci, ta ji wani irin tsoro ya ziyarce ta.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un," ta furta. "Ashe Abdulkadir ya yi amfani da mutuwar babban abokinsa ne don ya tsira?
Yanzu komai ya fara bayyana a gare ta. Ta fahimci dalilin da ya sa mummy ta wa Ak text din kashedi Ashe abun da suke boyewa kenan
Farhana ta kara gyara zama, tana goge hawayen dake fita daga idanunta. Rubutun AK a shafukan dake biyo be canza salon ba ; yana nan a rubutu mai cike da fargaba da kuma rashin kwanciyar hankali.
Diary din AK (Cigaba da Karatu)
"Mun dawo Abuja, amma Abuja ta yi min zafi. Kullum idan na rufe idona, sai na ga gawar Khalid, sannan na ga matar nan dake kwance cikin jini. Mummy ta ce min in manta, amma ta yaya zan manta? Na san na yi rantsuwar karya a kotu. Na san na bari a bata wa Khalid suna tunda aka ce shi ne yake tuka motar a high speed ya zanyi da hakkin mamaci ."nine silar mutuwar Khalid .abokina yana da buri ,buri sosai idan mun gama school muyi aure so many things amma Rick less rayuwar sa is cut short .
"Daddy ya dawo daga Turkey, Mummy ba ta fada masa gaskiyar abinda ya faru ba. Ta ce masa hatsari ne kawai, mukayi kuma Khalid ne yake tuka motar. Amma dangin Khalid na bi na da sharri Wai ni ke driving ,inda na Kara wa daddy confirming Khalid ke driving .Daddy ya yi jaje sosae, har ya sa aka yi wa gidan su Khalid kyaututtuka na ban girma don jajen rashin da suka yi. A duk lokacin da Daddy yake yabon jajircewa ta na zama da Khalid har ya rasu, sai na ji kamar in nutse a kasa saboda kunya da nauyin karya."
"Duk inda na sa gaba, kukan yarinyar nan yar shekara takwas yana bi na. Na rinka mafarkin tana nuna ni da yatsa tana cewa, 'Kai ne ka kashe min Mummy!'. Saboda wannan dalilin, na daina son tuka mota sosae a wannan lokacin. Na koma shiru-shiru, fushi ya fara tasiri a rayuwata. Duk sanda wani ya yi kusa da ni, sai in ji kamar ya gano “sirrina ne."
"Wannan takardar ta Court Order da aka bayar na rufe karar, Mummy ta ba ni ita tace, 'Wannan shi ne shaidar cewa ka fita daga matsala, amma kuma shi ne gargadin ka na karshe. Karka taba bari kowa ya san gaskiyar abinda ya faru.' Na boye takardar, amma kullum ina jin ta tamkar wuta a cikin aljihuna. Na yi alkawarin cewa ba zan sake komawa Kano ba, kuma ba zan sake bari wata mace ta yi kusa da zuciyata ba yadda soyayya zai sa na iya fada mata sirrina ba.
Farhana ta rufe littafin ta dade tana kallon bangon dakin. Zuciyarta tana mata wani irin zafi. Yanzu ta fahimci dalilin da ya sa AK yake da wani irin hali na daban. Ta fahimci dalilin da ya sa idan yana bacci yake yawan firgita.
"Ashe duk wannan takamar da kake yi, Abdulkadir, kana dauke da wannan nauyin a zuciyarka?" ta fada a hankali.
Rudanin Farhana
Ta kalli takardar Attempted Murder din nan. Ko da yake an rufe maganar a Najeriya ta hanyar kudi da fada aji Farhana ta sani sarai cewa a dokar Amurka, boye irin wannan bayanin babban laifi ne.
Ta duba sauran shafukan littafin, ta ga har yanzu akwai sauran rubutu a gaba. Zuciyarta tana gaya mata cewa akwai sauran abubuwa da dama da ba ta sani ba. Ta riga ta gano sirrin hatsarin, amma ba ta san takamaiman wacece matar ba, kuma ba ta san abinda ya faru da yarinyar nan ba daga baya.