Free chapter · Read without an account
78
by ZAHRAA · Bayan Murmushi
78
A karkashin hasken rana, Farooq ya yi wani irin kyau na ban mamaki. Fatar sa ta yi sumul, gashin kansa ya yi baki sosae, sannan yanayin sa yana nuna cikar kamala da nasara a matsayinsa na kwararre a fannin Computer Science.
Farooq ya sauke ajiyar zuciya, ya ciro kwamfutar sa (laptop) ya fara dannawa, kafin daga baya ya juya kansa. Idanunsa suka fada kan Farhana.
Farooq ya daskare. Ya kura mata ido, yana kallon yadda sanyi da yanayin Boston suka sa fatarta yin wani irin glowing (kyalli), duk da cewa fuskarta tana nuna alamun gajiya da wahala. Ta kara zama cikakkiyar mace (matured woman),
"Farhana?" Ya fada cikin sanyayyiyar murya, ya rufe kwamfutar tasa. "Ashe kece a gefe na,ya fada cikin wani irin emotional voice
Farhana ta yi kokarin gyara zamanta, tana kokarin boye damuwar dake fuskarta. "Farooq. Me kake a Massachusetts
How dumb of her tambayar da zata masa kenan after all this years da bata ganshi ba ta ayyana a ranta
Aiki ne ya kawo ni wata na daya kenan da zuwa I have 11 months to go
Shiru duka suyi farhana Tana ta so ta dago Ido ta kara kallansa .ya rabbi ,bata taba tunanin ganin farooq a wannan setting din ba in a million years
Shima a nasa gefen yana son kara mata magana it’s killing him from inside amma kuma Ay she’s married probably ma mijinta yana kusa ko yaje ya dawo ne don haka ya kiyaye mutuncinsa.
Suna cikin wannan yanayin, sai su Lamido suka hango mahaifiyarsu daga can nesa, suka taho da gudu suna wasa. Lamido ne ya riga isowa, fuskarsa cike da annuri.
Farooq ya kalli yaron, ya ga kamaninsa ya yi matukar kama da Farhana, amma akwai wasu kwayoyin idanu na wani daban. "Hi, little man," Farooq ya fada yana kokarin daidaita muryarsa. "What's your name?"
Lamido ya gyara tsayuwa, ya mika wa Farooq hannu kamar yadda aka koya masa a makaranta. "My name is Ibrahim Abdulkadir, but you can call me Lamido."ya fada da American accent dinsa
Jikin Farooq ya yi wani irin sanyi. Sunan mahaifin yaron, Abdulkadir, ya doke shi a rai. Ya gane cewa tabbas wannan dan Abdulkadir ne, mutumin da ya kwace masa farin cikinsa shekaru da suka wuce. But then Lamido sunan sa kenan fa ?kallon farhana farooq yayi ,the name is still alive in your heart kenan ?shiru farhana tayi Tana wasa da yatsun ta,thank you for the honor farooq ya kara fada , Lamido ya shiga ransa farat daya; akwai wani irin kwarjini da natsuwa a tare da yaron.
Farhana ta sauke idonta kasa, kunya ta lullube ta. Ba ta san ta yaya za ta bayyana masa cewa duk tsananin rayuwar da ta yi da AK, har yanzu akwai sauran burbushin wannan tsohuwar soyayyar sa a zuciyarta ba.
Sultana ma ta karaso, tana manne da jikin Farhana, tana kallon Farooq da wani irin shakku.
"And you, princess?" Farooq ya tambaya cikin murmushi.
"My name is Rukayya Abdulkadir, call me Sultana," ta fada, sannan ta kara lafewa a jikin Farhana. Ita kam bata saki jiki da shi ba kamar yadda Lamido ya yi.
Farooq ya kalli yaran, sannan ya kalli Farhana. "Masha Allah, Maryam. Yaranki suna da kyau sosae. Ibrahim da Rukayya... sunaye masu albarka."Ashe twins ne Allah ya masu albarka ,ameen ya rabbi Nagode ta amsa a sanyaye
What’s your name uncle ?Lamido ya tambaya farooq
My name is farooq but you can call me Lamido
Baki Lamido ya bude da mamaki
Ammi is that true?we have the same pet name ?
Gyada masa Kai farhana tayi .
Inda yaron ya fara tsalle yana jin dadi yaga mai sunansa cike da yarinta
Farhana ta ga yadda Farooq yake kallonta cikin tausayi da soyayyar da bai iya boyewa ba. Ta ji kunyar halin da take ciki; talaucin dake kokarin cin mata gwiwa. Ta tashi tsaye tana kakkabe rigarta.
"Yamma ta yi Farooq, ya kamata mu koma gida."
"Ina... ina mijin naki, Abdulkadir?" Farooq ya tambaya, yana jiran jin cewa watakila yana ofis ko yana gida tunda gashi har zasu tafi be ganshi ba
Farhana ta hadiye wani abu mai daci a makoshinta. "Yana nan Boston, Farooq. Kawai dai na fito ne don yara su shakata." Ba ta iya gaya masa cewa an sake ta ba; ba ta son ya ganta a matsayin macen da aka kora ko wadda ta gaza a zamantakewar aure.
Farooq ya mika hannu ya shafa kan Lamido dake zaune a tsakiyar su , yana kallon bishiya da yadda iska take karkada gashin kanta. "Kin yi kyau sosae, Maryam. Boston ta karbe ki. Kin zama cikakkiyar mace wadda kallo daya mutum zai mata ya san tana da daraja."
Farhana ta dan yi murmushin mai daci. "Kyawun da kake gani, Farooq, na wahala ne," ta fada a ranta. "Glow din nan da kake gani, fafutukar waitressing ne da flight school suka gina shi."
"Na gode, Farooq. Kai ma ka zama babban mutum. Computer Science dinka ta kai ka matakin da kowa zai yi alfahari da kai am proud of who you become
Su Hailey har Sun isa mota sai horn suke dannawa
. Lamido ya zo ya tsaya kusa da ita, yana kallon Farooq da wani irin so, tamkar ya san akwai alaka tsakanin sa da mahaifiyarsa.
"Zamu tafi, Farooq. Yamma ta yi," Farhana ta kara fada.tun dazu sallama taki kare wa ta ayyana a ranta
Farooq ya tashi shima, tsayinsa ya rufe inuwar Farhana. Ya dade yana kallon fuskarta, tamkar yana son ya haddace kowane fanni na kuncinta. "Maryam ga card dina ,idan akwai abinda kike bukata... karki yi wata-wata. Ko da kuwa Abdulkadir yana nan, ni ma ina nan a matsayin wanda ya taba sanin zuciyarki."
Farhana ta gyada kai, sannan ta ja hannun su Lamido suka tafi. Farooq ya tsaya ya kura musu ido. Zuciyarsa tana gaya masa akwai matsala. Me ya sa Farhana take sanye da kaya masu sauki? Me ya sa take lissafin kudi a takarda tana kuka?yana juyo sultana Tana tambayar farhana Ammi who is he ?
"Ibrahim Abdulkadir..." Ya maimaita sunan. "Amma mahaifiyar ka tana kiran ka da Lamido. Akwai labari a boye, Maryam. Kuma zan gano shi."