Free chapter · Read without an account

80

by ZAHRAA · Bayan Murmushi

Ranar ta tashi da wani irin sanyi a Boston. Ina zaune a cikin mota, hannuna yana rawa sanda nake kallon jirgin Cessna 172 dake tsaye a kan kwalta. Yau ce ranar da zan tashi ni kadai, ba tare da Captain Miller yana zaune a gefena ba.na Samu na hada $5k da kyar inda nace Zan biya sauran 7.5k dollars Kafin next solo flight dina 


Naji gabana yana dukan uku-uku. "Maryam, shin kin shirya?" na tambayi kaina. Na tuna kalaman Hamma fahad  bazaki iya ba , na tuna kukan da na yi a dakin Isabella. Amma sanda na kalli zoben dake yatsata, alkawarin Farooq, Wanda Nasan ranar be lura dashi a hannuna ba.sai na ji wani sabon karfi.

Na haura cikin jirgin. Kamshin mai da fatar kujerun jirgin ya bugi hancina. Na fara kunna switch daya bayan daya. "Clear prop!" na fada da karfi. Injin jirgin ya tashi da wata irin ruri mai dadi. A wannan karon, babu Miller dake gyara min zama. Ni ce Captain, ni ce Co-pilot.

"Boston Tower, this is Cessna 172, ready for takeoff," na fada cikin lasifikar dake kunne na. Muryata ba ta yi rawa ba.


Sanda na tura joystick din jirgin gaba, na ji tayoyin sun bar kasa. Wani irin dadi da tsoro suka gauraye a zuciyata. Ina ganin gine-ginen Boston suna kankanta a kasa na. Ni kadai a cikin gajimare! Nayi ihu cikin farin ciki, "Na yi nasara! Diddi, kina gani na? Abbi, gani a sararin samaniya!"

Na zagaye gari sau uku, ina kallon kyawun duniya daga sama. Amma babban kalubalen shi ne sauka. Domin kowane tsuntsu zai iya tashi, amma sauka ita ce fasaha.

Tana sama ita kadai ba kukan sultana  ,ba miss call din abbi,ba scary face din Ak tana ganin motoci Kamar kwanuka .

Farhana ta saita hancin jirgin Cessna dinta a hankali ya taba kwalta. Screech! Tayoyin jirgin suka yi kuka kadan yayin da jirgin ya daidaita a kan titin sauka. Ta ja numfashi mai nauyi, hannunta yana rawa sanda take kashe injin jirgin.

"Alhamdulillah... Alhamdulillah..." ta maimaita sau dubu, hawayen dadi suna zuba a kumatunta.

Tana bude kofofin jirgin, iskar dake kadawa ta shaka mata kamshin 'yanci. Ta sauko kasa da takalman ta na matuka jirgi, tana kokarin daidaita tafiyar ta saboda jiri kadan da take ji. Ta daga kai, sai ta ga mutane tsaye a bakin layin filin jirgin (Hangar).



A kasa kuwa, su Isabella, Hailey, Liam, da yaran Farhana (Lamido da Sultana) suna tsaye suna kallon jirgin sama.

Farooq yana tsaye a bayan wata katuwar mota, sanye da bakin gilashi, yana kallon jirgin da Farhana take ciki. Hawaye ne kokarin zuba a idanunsa. Wannan ita ce Maryam dinsa; macen da ya sani mai buri da jarumta.

"Masha Allah, Maryam," Farooq ya fada a hankali. "Kin zama abin da kike so. Kuma wallahi ba zan bari kudin nan na $12,500 ya zama sanadiyyar dakatar da wannan tashi naki ba."

Farooq ya kalli Isabella, ya gyada mata kai. Ya riga ya shirya yadda zai biya kudin karatun ta ta hanyar "Scholarship" na bogi ta yadda ba za ta gane cewa daga gare shi yake ba, domin kare mutuncinta.

Farhana tana can sama, tana kewayawa, tana jin dadin iskar 'yanci, ba tare da ta san cewa mutumin da ta fi jin kunyar gani jiya, yana can a kasa yana kwalla saboda alfahari da ita ba.


Farhana ta durkusa ta kankame twins dinta , hawaye ya fara zuba a idonta. Isabella ta karaso ta mika mata wani hadadden furare mai launin fari da ja. "Congratulations, Captain Maryam! You did it! Kin keta hazo ke kadai!"

Hailey ita ma ta mika mata nata furaren. "Mun alfahari da ke Maryam. Wahalar waitress ta kusa kare wa 


Farhana tana tsaka da murnar su Isabella, sai ta ga mutane sun ba wa wani wuri. Farooq ya fito daga bayan su, sanye da wata suit mai daukar hankali. A hannunsa, akwai mafi girman furare da Farhana ta taba gani a rayuwarta—Red Roses wadanda suke nuna tsantsar soyayya da girmamawa.

Farhana ta daskare a wurin. Kunyar daren jiya ta restaurant ta dawo mata, amma ganin yadda Farooq yake kallonta cikin alfahari, sai kunyar ta narke.

Farooq ya tsaya a gabanta, idanunsa sun cika da kwalla. "Maryam," ya kira sunanta cikin muryar da take ratsa jini. "Na dade da sanin cewa kina da fikafikai. Amma ban taba tunanin zan ga ranar da zaki tashi sama ba tare da taimakon kowa ba."

Ya mika mata furaren. "Wannan ba na tsohuwar soyayya ba ne. Wannan furaren na girmama jarumtar ki ne. Congratulations, Captain. Kin zama abinda kika dade kina mafarki."

Farhana ta karbi furaren, ta sanya kanta a cikin ganyen furaren tana kuka mai karfi. Kukan duk wahalar da ta sha a gidan Abdulkadir ne. Kukan yadda dangin Ak suka dinga  wulakanta ta ne. Kukan yadda ta yi aikin waitress don ta sami kudin flight hours ne.

Ta kalli Farooq ta cikin hawaye. "Farooq... me ya kawo ka nan? Na 

Zaka kyamace Bayan ganina a matsayin waitress kuma bazawara.

Farooq ya girgiza kai, ya mika hannu ya goge mata hawayen (duk da bai taba fatar ta ba). "Ba zan taba kyamatar mace mafi daraja a idona ba. Jiya na ga waitress, amma yau na ga Pilot. Kuma Pilot din nan ita ce wadda nake alfahari da ita."

A wannan lokacin, filin jirgin ya cika da sautin tafi da murna. Farhana ta tsaya a tsakiya, rike da furare a hannu daya, Lamido a hannu daya, tana jin cewa yanzu ne aka fara rayuwa.

Abdulkadir ya so ya kashe mata buri, amma Allah ya sanya tsohon masoyinta da kawayen kwarai su zama shaidun nasarar ta.


Farooq ya cika alkawarinsa. Bai sake takura wa Farhana ba, kuma bai sake nuna mata kansa a gidan abinci ko filin jirgi ba. Amma a asirce, ya nufi ofishin lissafin kuɗi na Hanscom Field.

"Ina son biyan ragowar kuɗin karatu na Maryam Farhana," ya faɗawa jami'in asusun. "Amma ina son ku tsara hakan a matsayin 'Excellence Scholarship' (tallafin karatu na bajinta) wanda makarantar ta ba ta saboda nasarar da ta samu a Solo Flight ɗinta na farko. Karku ambaci sunana."

Haka aka yi. Farhana ta sami imel (email) daga makarantar cewa an yafe mata ragowar $7,500 saboda ƙoƙarinta. Farhana ta yi kuka, ta zata addu'ar Diddi ce ta karɓu, ba ta san cewa Farooq ne ya share mata hawaye ba.

Daga ranar ta daina zuwa Aikin Waitress,for now dai Aikin NGO dinta ya ishe ta 

Sati ɗaya kafin Final Solo Flight ɗinta, Farooq ya tura mata saƙon waya:


"Barka da ƙoƙari Captain Maryam. Na san kina cikin shirin karshe. Idan kina da sarari, ko za mu iya shan shayi a daren nan? Akwai wata shawara ta fasaha (IT) da nake son ba ki wadda za ta taimaka miki a tsarin Navigation. Just as friends.


Farhana ta nuna wa su Isabella saƙon, inda suka rinka tsokanarta. "Wai ko Old Love ne ya dawo?" Isabella ta faɗa tana dariya.

Farhana ta girgiza kai, "A'a, kawai dai abokan juna ne. Kuma yanzu Farooq ya riga ya wuce matsayina."


Farhana ta shirya cikin wata doguwar riga ta sanyi, ta fito ƙofar gidan Isabella tana jiran Farooq ya zo daukarta. A daidai lokacin, sai ga motar Abdulkadir ta garzayo, ya zo ɗaukar su Lamido don weekend.

AK ya fito daga motar, fuskarsa a murtuke. , amma kuma har yanzu akwai kishinta a ransa.

"Yaran suna ina?" AK ya tambaya cikin murya mai kaushi, bai ma kalleta ba.

"Suna ciki, Isabella tana fito da su," Farhana ta ba shi amsa a taƙaice.

A daidai wannan sa'ar, wata hadaddiyar mota kirar Tesla ta faka a gabansu. Farooq ya fito, sanye da wata tsadaddiyar rigar sanyi, fuskarsa cike da natsuwa da kamala. Farooq ya nufi wurin Farhana, bai ma lura da AK ba da farko.

"Hi, Maryam. Kin shirya?" Farooq ya faɗa cikin lallausar murya.

AK ya daskare a wurin. Idanunsa suka rine suka yi ja. Ya gane Farooq. Ya gane wannan fuskar da ya raba ta da Farhana shekaru biyar da suka wuce. Ya dube shi daga sama har ƙasa, ya ga yadda Farooq ya zama babban mutum, ya ga nasarar da ke tashi a jikinsa.

"Lallai Maryam..." AK ya faɗa cikin wani irin murmushin mugunta, muryarsa tana rawa saboda kishi. "Ashe wannan yaron  kika fito kike jiran sa? Don haka kika ce kin gama idda? Don ki koma wurin wannan matsiyacin?"

Farooq ya tsaya cak, ya juya ya kalli Abdulkadir. Farooq bai nuna fushi ba, sai dai wani irin kallo na raini da ya jefa wa AK.

"Malam Abdulkadir," Farooq ya kira sunansa cikin natsuwa. "Wanda kake kira matsiyaci, yau shi ne yake tsaye a inda kake takama da shi. Amma ban zo nan don maganarka ba. Na zo ne don na girmama macen da ka gaza ba ta darajarta."

AK ya yi wuf zai nufi Farooq, ransa ya kusa ɓaci ya kai matakin hauka. "Karya kake yi! Maryam tawa ce! Kuma ba za ta taɓa zama taka ba!"

Farhana ta matsa tsakiyar su. "Abdulkadir! Ka daina hauka. Yara suna kallonka ta taga. Ka karɓi yaranka ka wuce, wannan rayuwata ce, ba taka ba."

AK ya kalli Farooq, ya kalli yadda Farooq ya buɗe wa Farhana ƙofar mota cikin girma. Ya ji wani irin zafi a ransa wanda bai taɓa ji ba. Duk dukiyarsa da ikonsa, ya ga yadda Farooq yake nuna wa Farhana soyayyar da shi bai taba bayarwa ba

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol