Free chapter · Read without an account
81
Farhana ta rintse idonta, sai ta ji tamkar har yanzu tana cikin motarsa, tana jin dumin rungumar da tayi masa a ƙofar gidan Isabella. Ta rinka tuno yadda ya koma—ya yi kyau sosae, ya zama cikakken namiji mai cikar haiba da kwarjini.
"Ya Allah, Farooq ya canza," ta faɗa a fili tana murmushi ita kaɗai a cikin duhu: Ba wancan saurayin siriri da ta sani ba ne a jami'a. Yanzu ya zama well built kafaɗunsa sun faɗaɗa, muryarsa ta yi wani irin kauri mai daɗin sauraro.Akwai wani irin natsuwa da hikima a idanunsa, waɗanda suke nuna cewa ya san duniya, ya kuma san abin da yake nema.Kasancewarsa kwararre a fannin Computer Science ya ba shi wani irin kwarjini na daban. Ba wai kuɗin ba ne kawai, a'a, salon takunsa da yadda yake magana cikin nutsuwa ne suka sake sace mata zuciya.
Farhana ta mirgina a kan gado, tana jin wani irin shauki dake yawo a dukkan sassan jikinta. Tana jin kamar an goge dukkan radadin shekarun da ta yi a gidan Abdulkadir. Soyayyar Farooq ta dawo mata danya, tamkar yanzu suka fara.
"Ashe har yanzu ina son sa haka?" ta tambayi kanta. "Duk tsawon shekarun nan, ashe boye soyayyar sa nake yi a lungun zuciyata?"
Ta dauki wayarta, ta shiga hotunan suka dauka a airport ranar da ta yi Solo Flight. Ta kura wa hoton da Farooq yake tsaye a gefenta ido, yana mika mata furaren nan na Red Roses. Ta shafa fuskar wayar tamkar tana shafar fuskarsa ne.
Amma nan take, sai ta tuno kiran wayar nan. Kalmar "Dear" ta sake dawo mata danyarta. Wani irin kishi ya daki kirjin ta, ya sanya ta jin wani daci.
"Amma yana da wata yanzu a rayuwarsa ... watakila ma matar sa ce. Me ya sa ya yarda na rungume Shi ? Me ya sa zai kira ni 'Baby girl' alhali akwai wata a rayuwar sa?"
Ta ji zuciyarta tana mata zafi. Duk da tsananin son sa da take ji, ba za ta taba amincewa ta zama mace ta biyu ba, ko kuma ta shiga tsakanin sa da iyalinsa. Amma duk da haka, bata gajiya da tunanin sa. Idan ta rintse ido, shi take gani. Idan ta bude, shi take muradin gani.
Farhana ta ja bargo ta rufe fuskarta, tana jin yadda zuciyarta take bugawa da sauri. A daren nan, ta gane cewa ko da ta zama Captain Maryam, zuciyarta tana nan a kulle a hannun Farooq Lamido.
A can ɓangaren Farooq, hankalinsa yana kan farhana Kullum idan ya tashi, hoton Farhana da yadda ta koma jaruma yake yawo a ransa. Saboda haka, kusan kowane dare sai ya kira mahaifiyarsa (Mamma) a waya don ya sauke mata nauyin dake zuciyarsa.
Mamma tana zaune a kan sallaya bayan ta idar da sallar dare, sai ga kiran Farooq ya shigo. Sun dade suna gaisawa kafin ya fara ba ta labarin nasarar da Farhana ta samu a makarantar jirgi.
"Mamma, kin san yadda rayuwar nan take? Maryam da kika sani, yau ita ce take shirin zama kwararriyar Pilot a nan Amurka. Ta sha wahala Mamma, Abdulkadir ya wulakanta ta, amma Allah ya daukaka ta."
Mamma ta gyara zama, ta yi ajiyar zuciya mai nauyi. "Lamido... me kake nufi da wannan labarin Farhana da kake bani kullum a waya? Tun ranar da kace kun hadu, baka da zance sai nata."
Farooq ya yi shiru na dakiku kadan, kafin ya sauke murya cikin girmamawa. "Mamma, kin sani fa. Kin san yadda zuciyata take tun shekaru biyar da suka wuce. Har yanzu ita ce kadai a cikinta."
Mamma, wadda dama can tana son Farhana saboda tarbiyarta da natsuwar ta, sai ta saki murmushin jin dadi. "To Lamido, Allah ya zaba abinda yafi zama alkhairi. Idan har ita ce rabon taka, Allah ya hada kanku cikin aminci."
Suna cikin wayar, ashe yayunsa mata, Safina da Husna, suna jinsu dan a speaker yake , suna kaduna gidan mamma sunzo bikin yar Aminiyar mamman .Safina ta tabe baki, yayin da Husna ta hade rai.
"Mamma," Safina ta karaso gefenta bayan Farooq ya kashe wayar. "Wannan zancen Farhana ya isa haka. Bayan ta yi aure ta haifi yara biyu, sannan Farooq zai ce zai koma gare ta? To kuma Khairiyya fa an mata Adalci kenan ?"
Husna ma ta kara da cewa, "Gaskiya ne Mamma. Farooq ya wuce matsayin bazawara mai yara biyu. Khairiyya ta ishe sa rayuwa,
Mamma ta daka musu tsawa cikin lallausar murya mai dauke da tarbiya. "Safina! Husna! Ku kiyaye harshenku. Shi auren nufi ne na Allah. Idan Allah ya kaddara ita ce matarsa, babu abinda zaku iya yi. Kuma Maryam tana da mutunci da daraja, zawarci ba aibi ba ne. Ku taya dan uwanku da addu'ar alkhairi kawai."
Ganin ran Mamma ya baci, sai Safina da Husna suka sunkuyar da kansu. "Muna neman gafara Mamma. Allah ya zaba abinda yafi alkhairi."
Dayake sun jiku da tarbiya basu kara tada maganar ba .
Ranar ta waye da wani irin haske na musamman a birnin Boston. Farhana ta fito daga gidan Isabella, ta dade tana kallon kanta a madubi. Akwai wani irin natsuwa da ya ziyarci zuciyarta, duk da radadin kishin Farooq dake boye a wani sashi na ranta.
"Yau ce ranar, Maryam," ta fadawa kanta. "Daga yau, babu wanda zai sake ce miki ba zaki iya ba."
A Filin Jirgin Hanscom Field
Sauran daliban makarantar duk sun fito don ganin tashi na karshe na "Maryam the Warrior," yadda suke kiranta saboda jarumtarta. Captain Miller ya mika mata taswirar tafiyar (Flight Plan).
"Maryam, yau zaki yi tafiyar mil dari biyu (200 miles) ke kadai. Zaki tashi daga nan, ki nufi jihar New Hampshire, sannan ki dawo. Wannan shi ne babban kalubalenki na karshe Kafin matakai na gaba
Farhana ta gyada kai. Ta shiga cikin jirgin, ta fara binciken karshe. Ta tuna yadda ta taba zama a kasa tana kuka saboda rashin kudi, amma yau gata a kan kujerar direban jirgi.
Tana shirin kashe wayarta kafin ta tashi, sai saƙo ya shigo. Daga Farooq ne.
"Ina kallon jirgin naki daga nesa, Maryam. Kada kiji tsoron komai. Iska tana tare da ke, kuma addu'ata tana karkashin fikafikan jirgin naki. Fly high, Baby Girl."
Farhana ta ji wani irin dumi ya mamaye mata zuciya. Duk da zargin "Dear" da take yi masa, wannan sakon ya ba ta kwarin gwiwar da ba ta taba tsammani ba. Ta kashe wayar, ta ja hancin jirgin.
Jirgin ya daga. Vroooom! Farhana tana kallon birnin Boston yana kankanta a karkashinta. Tana sama, sai ta fara magana da kanta, hawaye yana wanke mata fuska.
"Abdulkadir, kalle ni! Ka ce ni ba kowa ba ce. Ka ce ba zan taba iya rayuwa ba tare da kai ba. Amma yau gani a saman gajimare, ina kallon duniya daga inda kai ma baka isa ka gani ba!"
Dukkan wadannan abubuwan suka zama mata tamkar tururi dake tura jirgin sama. Ta kewaye jihar New Hampshire, tana kallon duwatsun dake cike da kankara. Ta ji wani irin kusanci da Ubangiji. A wannan lokacin, ta yafewa kanta, ta kuma yafewa dukkan wadanda suka cuce ta, domin daukakar da ta samu ta fi karfin a adana kiyayya.
Bayan kusan sa'o'i uku tana shawagi ita kadai, Farhana ta hango filin jirgin Hanscom. Ta tuntubi Tower cikin murya mai natsuwa.
"Hanscom Tower, Cessna 172 Romeo-Alpha-One, on final approach. Requesting landing."
"Cleared to land, Romeo-Alpha-One. Welcome home, Captain."
Ta sauke jirgin cikin kwarewa wanda ko kwanon ruwa aka dora a jikin jirgin ba zai zubar ba. Tana kashe injin din, ta kifa kanta a kan sateyarin jirgin ta fashe da kuka. Kukan dadi, kukan nasara, da kukan cikar buri.
Alhamduillah solo flight done and dusted .
Captain Miller ya shigo ya zauna a gabanta. "Maryam, kin gama Solo Cross-Country dinki lami lafiya. Yanzu saura abu daya ya rage miki."
Farhana ta dago kai, idanunta cike da gajiya amma akwai azama. "Me ne ne hakan, Captain?"
"The Checkride," Miller ya fada yana mika mata wasu takardu. "Jami'in FAA zai zo ranar Juma'a. Zai gwada ki a kasa (Oral Exam) kan ilimin jirgi, sannan zai shiga jirgin tare da ke don ganin yadda kike tashi da sauka, da kuma yadda kike shawo kan matsalolin gaggawa (Emergency Procedures). Idan kin tsallake wannan, to ke ba daliba ba ce kuma; ke cikakkiyar Pilot ce."
Duk da muhimmancin jarabawar nan, tunanin Farhana yana can wurin Farooq. Ta rasa dalilin da ya sa tun ranar da suka sha shayi bai sake neman ta ba. Saƙonnin sa na "Friends" sun rage yawa.
"Wato dai 'Dear' dinsa ta mamaye masa lokaci," ta fada a ranta cikin kishi.
Wannan kishin ya sanya ta maida dukkan fushinta da bacin ranta kan karatun. Ta rinka haddace kowane sassa na injin jirgin, tana karanta yanayin gajimare (Meteorology) tamkar ranta zai fita. Ta yanke shawarar cewa ko da ta rasa Farooq, ba za ta taba rasa wannan lasisin ba.
Farooq kuwa, baya kiran ta ne saboda yana tsoron kar ya ruda mata lissafi a wannan satin na jarabawa. Amma yana lura da duk wani motsinta ta hanyar Isabella.
Ya riga ya yi oda na musamman na Uniform na Pilot na alfarma, wanda aka rubuta sunanta: CAPT. M I mazatu . Sannan ya riga ya tuntuɓi wani babban kamfanin jirage na alfarma (Private Jet Charter) dake Boston don ya samar mata da aiki nan take bayan ta samu lasisi.
"Mamma," Farooq ya kira mahaifiyarsa a waya. "Yau saura kwanaki uku Maryam ta zama Pilot. Ina so in hada mata babban taya murna wanda kowa zai shaida ."
Mamma ta yi murmushi. "Lamido, na maryam Yau gaba daya satin zancen flight din farhana ake Toh Allah ya bata saa kace mata Ina mata fatan alkairi
A ranar ne kuma farhana ta kasa jurewa ,ta Danna kiran farooq yafi sau 20 amma ta kasa kira daga karshen ta yanke shawara yi masa suprise visit tunda ya dade da bata house address dinsa ,karfe 8:30 tasan by now ya dawo gida daga office samun kanta tayi da sa wata atamfar ta Wanda da kyar ta shige ta Sabida yadda tayi Kiba ,Kayan Sun mata kyau sosai dan rabon ta da atamfa har ta manta ,cab ta dauka zuwa unguwar su farooq .
Door ta Danna inda wata Kamar yar arewa ta bude fuskar cike da murmushi gaban farhana ya fadi
Hey young lady who are you looking for ?kara duba address din farhana tayi to make sure a wrong house take ba .uhmm farooq
Sai gashi ya fito cikin long sweet pants da hoodie
Hey baby girl shigo mana
What a suprise visit farooq ya fada yana fadada Murmushin sa
A sanyaye farhana ta shiga Tana cursing kanta a zuciyarta
Average American home ne farooq ya fara cika wa farhana gaban ta da snacks da tar kace
Farooq bakayi introducing dinmu ba ,gashi ni ko gaisawa bamu da bakuwar taka ba
Oh yeah right farooq yace
This is Maryam farhana my baby girl
And baby girl ga saudat my colleague
Sama sama matan suka gaisa inda saudat ta masu sallama .
Tana fita farhana ta tamke fuska
Meya kawo colleague Dinka gidan nan at this time shiyasa Ka daina kira na kenan ,ta fada Tana shirin fashe wa da kuka
Am sorry baby girl wasu aiki muke son kammala Kafin gobe shine tazo ,duba table din Bayan ki kinga books da laptop din da muke aiki dasu
Ajiyar zuciya ta sauke inda suka cigaba da hirar su ,movie suke Kallo suna nishadi a haka har dare yayi farhana bata Ankara ba ,farooq offers to drop her home ,suna fitowa kafinsu karasa garage aka tsuge da ruwan sama farhana Dama tana gaba farooq yana baya
Tsakiyar ruwan farhana ta shiga ta bude hannayenta sama
I love you so much farooq , I love you, ta fada da karfin da Allah ya hore mata ,tasan karar ruwan bazai bare farooq yaji taba ,da gudu ya karaso ya ja hannunta har cikin mota tare da kunna masu car heater,Yau kuma wasan ruwa kike sonyi ?ya tambaya da alamar zolaya,Kallonsa take cikin shauki ji take Kamar ta cinye farooq Sabida so,baby girl kinyi kyau the atamfa looks good on you ,so breathtaking.sanyi ne ya ratsa zuciyarta ko ba komai dai ta birge farooq ,and she’s determined to go to any length ta mallaki farooq he’s her missing rib