Free chapter · Read without an account
13
Free Book.
*13*
Hakimi Alhaji Babba zaune akan royal chair ɗin da ke tamfatsetsen parlon da ya gaji da tsaruwa da kayan alatu, duk wani kayan jin daɗi na more rayuwa an zuba a wannan parlon, haka idan har kai farin shiga ne a zuwa gidan, to tabbas zaka iya rantsewa ba'a ƙasar nigeria kake ba. Farin rawani ne akansa, kana masa kallo ɗaya zaka san jinin sarauta ya gama ratsa shi.
Kamar yadda tarihi ya gabatar, an kafa Masarautar Gombe a shekarar 1804 a lokacin jihadin Fulani wanda Buba Yero mabiyin Usman ɗan Fodio ne. Buba Yero ya mai da Gombe (Abba) hedikwatarsa domin yaƙin da ake yi da matsugunan Jukun na Pindiga da Kalam, daga nan kuma yayi ta kai hare-hare har zuwa Adamawa da ke gefen kogin Benue.
A lokacin sarki Alhaji Bukar Dukku shi ke riƙe da sarautar garin gombe, bayan rasuwarsa ne kuma babban ɗansa Hashim Bukar Dukko ya karɓi sauratar, wanda ya riƙe sarautar tsawon shekaru masu yawa.
Sarki Hashim Bukar ya ajiye ƴaƴa a ƙalla guda takwas kuma dukansu maza, kuma duk su takwas ɗin sun fito ne daga tsatson mace guda ɗaya Sarauniya Falmata, wacca a lokacinsu ne aka kafa tarihin sarkin da ya zauna da mace ɗaya tal a karagar mulkinsa har rayuwarsa ta ƙare ba tare da ya mallaki ko da ƙwarƙwara ba.
Cikin ƴaƴa takwas da ya bari sune Adam, Ishaq, Lateef, Harun, Ibrahim, Yusuf, Isma'il, Shu'aib. Akaf cikin yaran babu wanda ya samu kulawa mai girma da gata daga wurin mahaifinsa irin babban ɗansa Adam, kasancewar tun da Sarauniya Falmata ta haife shi sai da ta shafe shekaru goma kafin ta ƙara samun wani cikin, lokacin har sun yanke tsammani da samun wani rabon, kuma daga haihuwar Yarima Ishaq shikenan ta shiga jero haihuwar ƴaƴa har sai da ta jera 8 gaba ɗaya.
Duk da ƙarancin shekaru da Yarima Adam ke da shi a wancan lokacin, hakan bai gaza fahimtar cewar shi wanene ba, ya san daga tsatson da ya fito, domin a ko da yaushe mahaifinsa na faɗa masa cewar gaba da bayansa shi ɗan sarauta ne dan ko mahaifiyarsa ma ƴar sarki ce.
Bayan tarin ƙauna, soyayya, gata da kulawa wadda Yarima Adam ya samu a wurin mahaifinsa da mahaifiyarsa, sai kuma na ɓangaren al'umma. Waɗanda suke ƙasƙan da kansu a gare shi matsayinsa na ɗa ɗaya tilo a wurin Mai Martaba da suke jin ba su da tamkarsa.
Hakan kuma ya haifar da aƙida ta girman kai da gadara a wurin Yarima Adam, har ta kai ga yana nuna ƙasƙanci ga na ƙasansa, hatta ga hadiman dake kewaye da Sarki kuwa.
Tun kamin ayi masa ƙanne ya haddace wani furuci dake fitowa daga bakin al'umma na kirarin da suke yi masa da Yarima Sarkin Gobe, kai ɗaya ne Yariman da akai babu irinsa, bayanka sarauta gabanka sarauta.
Amma tun daga lokacin da mahaifiyarsa ta ƙara haihuwa sai ya ji salon wannan kirarin ya sauya, kuma bai gyaru ba har zuwa lokacin da ta tsaya da haihuwa, kirakiran ya tashi daga kansa shi ɗaya ya koma har ga sauran ƴan'uwansa.
Dalilin da yasa zuciyarsa tayi baƙi kenan akan ƴan'uwansa, dan yana ganin silarsu zai iya rasa wasu tarin nasarori da ya rubuce su a tafin hannunsa. Da tafiya tayi tafiya sai ya zamana sam Yarima Adam ba ya raɓar inda ƴan'uwansa suke, tsakaninsa da su nisantar juna, basa samun fuska a wurinsa matsayinsa na babbansu.
Tun zuciyarsa na raya masa wani abu wai shi ƙiyayya har hakan ta tabbata akan ɗan'uwansa Yarima Lateef, wanda ya ƙwace duk wata fada da yake da ita a wurin mahaifinsu, wannan soyayyar da gata da dukkan komai da ya samu lokacin da yake shi ɗaya daga wurin mahaifinsa gaba ɗaya sai ta koma kan Yarima Lateef, hatta da soyayya da girmamawar da al'umma suke ba shi.
Kuma hakan ya samo wuri ne dalilin banbancin halayya, cikin kaf su takwas ɗin da Mai Martaba ya mallaka babu wanda ya ɗauko kyawun halayyarsa da ɗabi'unsa sai Yarima Lateef, shine yasan darajar mutane, saɓanin sauran da suke nuna ƙasƙsanci ga mutane, haka shine kaɗai mai sauƙin kai amma kaf sauran suna da mummunar ɗabi'a ta girman kai, kuma shi ɗaya ne mai son mutane da yi musu fara'a, gaba ɗaya Yarima Lateef kan manta da cewar shi ɗin jinin sarauta ne kasancewar ba'a gabansa take ba, amma ƴan'uwansa sarautar ita ce abar alfaharinsu da tunƙahonsu, a karan kansu sukan ji tamkar su mutstsuke juna saboda girman izza, kowannensu mulki da muƙami kawai yake wa hari a rayuwarsa amma banda Yarima Lateef.
Shakarun Yarima Lateef 24 a duniya mahaifinsa ya aura masa ƴar gidan wazirinsa mai suna Rumana, itama kuma sai ta samu matsuguni na soyayya a wurin Mai Martaba ta dalilin ɗansa da take aure, dan tun da aka yi auren Mai Martaba da Sarauniya Falmata suke kiranta da gimbiya.
A wannan lokacin Yarima Lateef yayi auren biyayya ne kawai ba don yana son Rumana ba, sai bayan auren kuma ya gane cewar zaɓin mahaifinsa kyakykyawan zaɓi ne a gare shi, kuma dama abin da yasa baya son auren ganin cewar yayyansa Yarima Adam da Yarima Ishaq basu yi aure ba, sai yake ganin kamar babu dacewar ace shi ya riga su yin aure.
Wannan aure na Yarima Lateef shi ya ƙara janyo masa baƙin jini a wurin ƴan'uwansa musamman Yarima Adam.
Kuma auren nasa babu jimawa shima Yarima Adam ɗin ya bijiro da nasa inda ya kawo ƴar gidan gomnan garin gombe a matsayin wacce zai aura, bayan zugo shi da Jakadan Sarki yayi akan cewar muddin yana son kujerar mahaifinsa to yayi aure tun mahaifinsa na raye, idan kuwa ba haka ba wannan burin mulkin nasa na saurauta za su ta shi a tutar babu ne, zai kasance abu me wahala a ba shi saurauta alhalin baida iyali.
Shi kuwa a san da Jakada ke ba shi wannan shawarar ji yake da zai iya kashe Lateef ba tare da kowa ya sani ba da babu abun da zai hana shi, to tsoronsa ɗaya ne, ya riga ya sani abu ne mai sauƙi Mai Martaba yasa shima a kashe shi ko kuma ya kashe shi da hannunsa.
Mai Martaba kan mance da kowa da komai akan Yarima Lateef, kuma ya sha tarasu ya faɗa musu cewar zai iya yin komai akan Lateef.
Kuma bayan rasuwar Sarki Hashim Bukar anyi tata ɓurza wajen naɗa magajinsa, don har sai da ta kai ta kawo duka Yaran sun fito da abun da yake zuciyoyinsu ƙiriƙiri, rigima ta ɓarkewa junansu kowa na ganin ya cancanci a basa wannan sarautar. Majaifiyarsu Sarauniya Falmata ta shiga tashin hankali mara misaltuwa akan babban yaƙin da ke shirin ɓarkewa, Lateef shi ɗaya ne mai ƙoƙarin ganin ya kwantar mata da hankali domin har sai da ta kai ga ya ɗauketa daga ƙasar ya fitar da ita da matarsa mai jaririn yaro a lokacin, saboda komai zai iya faruwa hatta ga rasa rayuka.
To amma da yake Allah ya tsara cewar Lateef shi zai hau kujerar mulki, duk irin yanda Adam ya kai ruwa rana wajen ganin ya hana faruwar hakan shi da muqarrabansa Allah bai ba su iko ba. Daga ƙarshe haka dole suka haƙura suka zubawa sarautar Lateef ido wadda yake gudanar da ita cikin gaskiya, tausayi gami da jin ƙan al'umma kamar yadda mahaifinsa ya aiwatar a lokacin nasa mulkin.
Sarki Lateef ya gaji mahaifinsa ne wajen auren mace ɗaya tun auren da mahaifinsa yayi masa na Rumana, kuma lokacin da Sarauniya Rumana ta haifi ɗa na uku Allah ya yiwa Sarauniya Falmata rasuwa.
Bayan rasuwartata ne wannan ɗan guntun haɗin kan dake tsakanin ƴaƴanta wanda yake na dole a gare su saboda ganin idonta sai ya ƙarasa rugujewa, tana rasuwa kowa ya kama gabansa, da yake dai shima Yarima Adam Allah ya rubuta dole zai riƙi sarauta haka ya zuba uban dukiya aka ba shi sarautar yankin Funakaye, yankin da Babban ɗansa ke mulka a yanzu tun bayan rasuwar Sarki Adam.
Sai a wannan lokacin Sarki Lateef ya samu lafiya, aka sarara da bi masa ta ƙarƙashin ƙasa, kwanciyar hankali ta samu a gare shi.
Allah ya azurta Sarki Lateef da yara huɗu, babban ɗansa Abubakar wanda ya ci sunan Kakansa Sarki na biyu a wancan zamanin, suke kiransa da Yarima Babba, sai dai a yanzu Ƴaƴa da Jikoki na kiransa da Alhaji Babba, kuma a yanzu shi ne Hakimin Kaltungo.
Sai ɗansa na biyu da ya ci sunan mahaifinsa Hashim suke kiransa da sarki na uku, kuma Hashim shine wanda ya ga ji sarautar mahaifinsa Sarki Lateef tun bayan rasuwarsa.
A lokacinsu ba ai wannan tashin hankalin ba na nuna son mulki ga kowannensu, hasalima mahaifiyarsu Sarauniya Rumana ita ta bada zaɓin cewar shine zai maye gurbin mahaifinsu, kuma daga wannan maganartata babu wanda yaja balle a tsaya ja'inja aka tsaya akan abin da ta ce.
Sai ɗansu na uku Habib suke masa alkunya da Dikko, wanda yake babban alƙali a cikin ƙasa da wajenta, wanda gwamnatin tarayya ke ji da shi, kuma mahaifiyarsa ke alfahari da shi saboda gaskiyarsa.
Falmata(Faɗima) ita ce autar Sarauniya Rumana(Boɗejo), wacca aka haifeta bayan rasuwar mahaifinsu da ya tafi ya bar Rumana da cikinta. Ya kuma bar wasiyyar cewar indai an haifi mace a saka mata sunan mahaifiyarsa Falmata, kuma kar a ɓoye mata suna a dinga kiranta da wannan sunan. hakan kuma aka yi sai dai Ƴaƴa na sakayawa su ce mata Inna Falmata, mahaifiyarta kuma ta ce mata Sarauniya.
Bayan biyo ɗan shirun da aka samu a falon na Hakimi wato Alhaji Babba, akan faɗan da yake ta yiwa Turaki na batun ƙin amincewarsa akan auren da iyayensa suke so yayi, ya ci gaba da cewa.
"To mu ba mutanen banza bane ya kamata kasan da hakan Turaki, babu yacca za'ai ace mu ƙyaleka akan ra'ayinka na cewar kai ba zaka yi aure ba, wannan ma zancen banza da wofi ne. Idan ka manta to ka tuna su waye mu, saboda haka wallahi ƙaryarka ka bar mana abin kunya a tarihin sarautarmu. Na san idan ta ra'ayin mahaifinka ne sai dai ya zuba maka ido, to mu ba zamu zuba maka wannan idon ba ka ji ni da kyau".
A wannan lokacin idanuwan Turaki a kulle suke, kansa a duƙe yake, yana zaune ne a gefen ƙafafun macen da duk duniya bai da kamarta Hajiya Madina.
Ita ce ta kawo ƙararsa ba kowa ba, aure take so yayi ya riga yasan da wannan batun ba tun yau ba, ya sa ni shine burinta akansa. To amma me yasa? Me yasa a matsayinta na wadda ta isa da shi bata gindaya masa umarnin hakan kai tsaye ba sai dai ta kawo ƙararsa gaban wanda cin mutumci shine abin yinsa?.
Wani dunƙulallan abu ya ji ya tsaya a maƙoshinsa, zuciyarsa ta katse da raya masa abubuwa a sanda Hakimi ya ƙara yin magana.
"Turaki ko dai baka da lafiya ne? Idan ka san akwai wannan matsalar a tare da kai to ka faɗa tun wuri a maganceta, duk da cewar abu ne da kamar wuya namiji kamarka ace yana da matsala makamancin hakan".
Boɗejo da ke gefe ta ce,"Ah tou dai nima shi na gani. Wannan zance dai na batun ba shi lafiya ma ƙarya ne, ni nafi ga wani algungumin ne ya jefe mana shi, tunda dai ka ga maitar ibadar nan da yake ma yanzu fa duk ya daina, kuma wallahi ko waye Allah ya isa bamu yafe ba. Yanzu duk wani dogon zance ba shi bane, a tashi tsaye a nema masa magani kawai, idan aka biye ta uwar tasa da uban nasa ba za su yi masa wannan abin arziƙin ba".
Turaki ya buɗe idanuwansa ya zube akanta, magana take tana ƙara kambaba zancen asiri ne akansa. Bai san lokacin da bakinsa ya buɗe ya katseta da faɗin,"Boɗejo ke kuma komai ya faru shikenan sai ki ce aikin asiri asiri".
Tayi masa wani kallo ɗaya sannan ta maida kallonta kan Hakimi ta ce,"Me na faɗa maka Yarima Babba tun kamin ayi zaman wannan kotun? Ai sai dai idan ban faɗa ba amma yaron nan sai ya wulaqanta ni, baka ga kallon da yake min bane kamar ma zai tashi ya rufe ni da duka. Haka fa ubansa ya koya masa kuma alhalin ni ba irin rainon da nayi muku ba kenan, wallahi duk irin son da yake ma yaransa bai kama ƙafar wanda Ubanku Allah ya jiƙan rai ya nuna muku ba, amma ku dai baku san wani abu wai shi raina na gaba ba, hasalima wallahi baku san babba na magana ku saka baki ba, amma su dai Ƴaƴan Dukko halinsu kenan Babba na magana su nuna bai kai ba. To Alhamdu Lillahi daɗin abin Turaki bani na kawo ƙararka ba Uwarka ce gata nan a kusa da kai, kuma billahillazi da ace lokacin da nake sarauniya ne sai kasan na faɗa ka saka baki".
Turaki yayi ɗan guntun tsaki, ya ɗago kai ya kalli Hajiya Madina, suka yi ido huɗu da ita. A kallon da yayi mata ya gano expression ɗin dake tare da ita. Sai yayi saurin kai hannu wuyansa ya shafo shi, ɗabi'arsa ce hakan. Yawanci Boɗejo kan ce wani ƙullin yake shafowa.
Ya sauke numfashi, muryarsa ta fito a hankali, cikin girmamawa da biyayya ya ce da Hajiya Madina.
"Maama ba sai kin kai ƙarata wani wurin ba. Kin isa da ni, kin isa ki bani umarni na bi ko ina so ko bana so, kin isa ki ja layi ki ce kar na shata na haƙura dan dole na, bin zaɓinki dole na, yacca kike so nayi haka zanyi muddin hakan zai faranta ranki...".
Bai ƙarasa ba amon muryarta ya fito da faɗin,"Aurenka nake son gani Mai babban suna, ina so kayi aure tun ina da rai Hammansu, ka sani ina sonka fiye da numfashina, babban burina a yanzu shine naga aurenka, na ga matar da zaka aura, na ga jikana, na ga kalar rayuwar jin daɗi da kwanciyar hankalin da zaka shimfiɗa da iyalinka. Hammansu wannan auren da baka so shine mutumcin mutum, kuma shine ƙarshen jin daɗin rayuwa. Ita rayuwa nan guda ɗaya ce Hammansu, haka ran ɗan adam guda ɗaya ne. Lokaci tafiya yake baya jira, so kayi enjoying rayuwarka tun lokaci bai ƙure ba, ya zamana ka zo baka mori dukkan jin daɗin rayuwar ba. Babu wanda aka yiwa alƙawarin kaiwa gobe a wannan duniyar, tsari kawai muke da hange, kuma zata iya yiwuwa mu matu a lokacin da muke ta shirin tsare-tsaren gobenmu, and that will be the end of us, ni kuma ina so mu tafi ne a lokacin da muka bar masu tuna mu a kowacce daƙiƙa. Da zarar an ce babu kai shikenan duk wasu memories daka bari suma sun tafi, amma ɗa fa? Shi ɗaya ne memory da zaka tafi ka bari a kasa mancewa da kai, hakan yasa nake so kayi aure tun da sauran lokaci, auren nan daga zuriya mai ƙarfi irin zuriyarmu, *SARAUTA*, ta yadda zaka bar bayanka, wannan kawai shine burina akanka Hammansu".
Idanuwan Turaki a ƙasan carpet suke, amma ƙwayar idonsa wasu yatsu take hangowa sirara da suke karkarwa kamar waɗanda ake girgiza su. Ya haɗiye wannan yawun dake saman harshensa zuwa cikinsa, sannan ya rufe idonsa ya buɗe a lokaci ɗaya. Laɓensa na sama da na ƙasa suka tale, harufan bakinsa suka fito da faɗin.
"Aure! Zanyi aure Maama, zanyi yanda kike so, kuma in sha Allahu sai na cika miki dukkan burinki akaina, kuma in sha Allahu ba za'a wayi wata rana da za ace kin riga ni tafiya ba, ni nake so na rigaki tafiya Maama, ni nake so, bana so ki tafi ki barni, rayuwar zata yi min tsanani, zan daina jin daɗinta kwata-kwata, zan dinga jinta ne kamar ana min feshi da ruwan dalma, dan Allah Maamaaaa".
Maganar yake da kakkaryewar kowanne harafi, kuma maganar tasa ta katse gaba ɗaya lokacin da ya ja sunanta wajen faɗi. Lokaci ɗaya ya nemi ya fita hayyacinsa.
Sautin kuka kawai yake ji acikin kansa, wannan sautin kukan na yarinta da na jarirai, saboda haka yayi saurin saka duka hannayensa ya toshe kunnuwansa, tare da kifa goshinsa akan ƙafafun Hajiya Madina da ke zaune tana hawaye.
Har zuwa lokacin da ya daina jin ihun kukan acikin kunnensa sannan ya ɗauke hannunsa, ya shiga sauke numfarfashi, gaba ɗaya yanayinsa ya sauya, kamar ma ya burkice ne, hannayensa masu rawa a yanzu suka damƙe zanin Hajiya Madina.
A jikinta take jin irin rawar da jikinsa yake yi, jikinsa na rawa amma ita a wannan lokacin tata zuciyar ce take rawa, so take itama ta taya shi kukan, irin kukan da yake yi, so take ta taya shi ko yaya ne, ko da sau ɗaya ne, irin wannan kukan da Uwa da Ɗa ke yi a lokaci guda.
Zaytuna da ke kusa da Boɗejo ta taso cikin kyarmar jiki, ta dawo gabansa ta durƙusa, sannan ta shige jikinsa gaba ɗaya itama nata kukan na ƙara ƙarfi, Turaki yayi mata wata runguma da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma na riƙe ne da zanin Hajiya Madina da yake jin kamar a lokacin ƙwace musu ita za'ayi.
Wani tausayi ya ratsa zuciyoyin duk wanda yake zaune a parlon banda zuciyar mutum ɗaya da ke ƙissima tarin abubuwa acikinta.
Lissafi take, lissafin yanda komai zai tafi, lissafin yanda komai zai warware, lissafin yanda ba ya ba zata taɓa gogewa ba, lissafin yadda komai zai tafi akan nata tsarin lissafin.
****
Komai na ɗakin abin kallo ne, ko da ace baka san kuɗin kaya ba, kallo ɗaya da za kai ma ɗakin da kayan da suke cikinsa zaka san cewa tabbas an narka dukiya wajen siyan kaya da kuma tsara ɗakin.
ko da ace za'a ɗauki tsawon shekara goma zuwa sama ba ai renovating ɗakin ba, ba za'a gane cewar komai da yake ciki ya jima ba.
Lokacin da Fullo ta buɗe ɗakin zata gyara shi, tsayawa kawai tayi tana mamakin abin da za'a gyara, ina ƙurar da Hajiya Madina take faɗi? Babu! Irin ƙamshin dake tashi a ɗakin ko ɗakin da ake gyarawa kullum albarka, saboda haka ne tama rasa ta inda zata fara, gani take sai dai ta ɓata ba dai ta gyara ba, dan komai tsaf tsaf, ɗakin yafi ƙarfin basirar gyaranta.
Amma a hakan dai ta gyara dole, tun da umarni aka bata, kuma sai bayan da ta gyara ne ta fahimci ashe da gasken yana biɗar gyaran. Komai ya ƙara zama fes-fes, adon ɗakin dark blue and silver ne, kalar da ta burgeta kuma tasan ta dace da mamallakin ɗakin.
Lokacin da ta gama gyara komai, sai ta shiga binciken abin da ta daɗe tana roƙon Allah yayi sanadiyar shigowarta ɗakin, wannan asirin da aka ce an saka shi a ɗakinsa, ba ɗakin da yake kwana ba, wannan ɗakin da zai koma da kwana bada jimawa ba, yes taga asirin, ta ganshi a inda ta ji sun ce sun ajiye, ƙasan gadon, a mulmule yake kamar yanda ta ji sun faɗa, sam ba wari yake ba, wani irin daddaɗan ƙamshi yake yi, irin ƙamshin nan da ba zaka so ka daina shaƙarsa ba, irin ƙamshin nan dake motsa zuciya ta faɗa cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa.
Hasalima da ta ɗauko sai ƙamshinsa ya gauraye duka ɗakin, ya kore ƙamshin air freshner da turaren wutan da ta yiwa ɗakin.
Tunaninta guda ɗaya ne a lokacin asirin na menene? Dama asiri yana ƙamshi? Ai tayi zaton asiri wari yake yi? Anya wani bai ganta ba a lokacin da ta laɓe yasa suka faɗi wannan maganar domin a ɗana mata tarkon ɓera?.
Ta tsorata da wannan tunanin, amma ko menene dai ba zata taɓa barin wannan dunƙulallan abin ya ƙara zama a ɗakin ba balle har Turaki ya kwana tare da shi.
Saboda haka cikin hanzari ta yunƙura ta miƙe zata fice, kwatsam idanuwanta suka sauka akan takardun da suka faɗo ɗazu da zata shiga ƙarƙashin gadon, take cewa sai ta fito za ta mayar da su.
Ta kama gefen zanenta ta ƙulle wannan abin da har yanzu zuciyarta taƙi yarda da cewar asiri ne, babu ko ɗigon tsoron zai iya cutar da ita, ta durƙusa ta kwashe takardun ta buɗe drower ta zuba su, sai dai cikin rashin sa'a wata takarda mai duhu ta faɗo.
Daga tsayen da take kawai ta tsaya tana kallon takardar, baƙa ce, duk da duhunta hakan bai hana hoton abin da ke jikin takardar bayyana ba.
Dai-dai take gani ko kuwa gizo ne idanuwanta ke yi mata? Kalmar Tashin hankali dai tayi kaɗan wajen kwatance da halin da ta shiga a lokaci ɗaya.
Ƙafafuwanta suka tafi a hankali gwiwoyinta na zubewa a ƙasa gaban takardar, waɗannan siraran yatsun nata na rawa ta ɗauko takardar, sai bayan ta ɗauko ne taga ashe har da wata ƙaramar takarda anyi stapling ɗinta ajiki.
Ƙwayar idonta ta manne akan ƙaramar takardar dake ɗauke da sunan asibitin *As-Salam International Hospital*, Assalam ɗin kawai zuciyarta ta iya karanta mata banda international Hospital ɗin.
*Nile Corniche, Athar an Nabi, Old Cairo, Cairo Governorate 4220501, Egypt.*
Kamar haka address ya biyo bayan sunan asibitin, bin kowanne rubutu take da ido ba don zata iya karantawa ba, har ta zo inda takke da ilimin karantawar, karatun da ta samu daga wajen Amir, *NAME* zuciyarta ta faɗa, sannan ta ƙara faɗar sunan da ya ke rubuce akan siririn dogon layin da aka zana dan rubuta sunan majinyaci, *MUHAMMAD TURAKI HABIB*.
Ƙasan sunan kuma wani dogon layin ne da aka rubuta *Chronic kidney disease (CKD)* wanda yayi mata walqiya da yadda ta ga irin kalmar a wancan shekarun, *KIDNEY FAILURE*. A duk cikin tarin rubutukan da takardar ke ƙunshe da su, suna uku zuciyarta ta iya karantawa, As-Salam, Name da kuma Muhammad Turaki Habib.
Kuma take zuciyartata tayi wani girgiza da karanta sunan nasa, ba kamar ranar farko ba da bata ji komai ba sanda ta karanta sunan nasa.
Sai kuma ta maida idonta ga haƙiƙanin hoton dake jikin baƙar takardar, ta taɓa riƙe irin takardar nan, wasu shekaru baya da suka wuce, kamar haka ne ba zata manta ba, likita ya ba su takardar dake ɗauke da hoton ƙodar da akayi.
_"Ƙodarta ta daina aiki yadda ya kamata. Za mu fara wankin ƙoda nan ba da jimawa ba… ko kuma a fara neman mai bada ƙoda."
Ba zata manta ba haka likita yayi musu bayani a wancan lokacin.
Allon ƙirjinta ya girgiza lokaci ɗaya, me hakan ke nufi kenan? Shima wanda sunansa ke rubuce ajikin wannan takardar yana ɗauke da irin ciwon da ya kashe mata Adda?.
Bata san lokacin da ta shiga girgiza kai da sauri ba, ai bata manta ba ta faɗa a baya, anyi an gama, ba zata ƙara rasa wani mutum da ya samu gurbin motsi a zuciyarta ba, kuma wannan alƙawari ne ta ɗaukarwa kanta.
Kuma shikenan sai ta shiga rera kuka, zaman durƙushen da bata tashi daga shi ba kenan har zuwa yanzu, tun da ta tuna irin baƙar wuyar da Addanta tasha kafin ta mutu, bayan sun gama sa rai da cewar ta sami lafiya, a wankin ƙoda na arba'in da huɗu da akayi mata, ashe tsawon lokacin da ta ɗauka tana fama ciwon ajali ne.
Hawayen dake bin idanunta ya gangaro ya sauka akan takardar dake riƙe a hannunta, wadda ta tsirawa ido babu ko ƙifce. _"Mutuwa zai yi shima"._ Wani ɓangare na zuciyarta ya faɗa mata hakan.
A lokacin idan ka ga Fullo zaka iya rantsewa hankalinta ya gushe gaba ɗaya daga jikinta, dalilin ambatar kalmar mutuwa da zuciyarta tayi mata, allon ƙirjinta ya ƙara yin wani duka a karo na babu adadi, wata tsawa ta ziyarci cikin kanta, tsawar da ta haɗe da kiran da ya shigo ta cikin wayar ɗakin wadda ke manne a jikin bango.
*Halima.hz✍🏻*
***