Free chapter · Read without an account
18
Free Book.
*18*
Bayan dogon lokaci sai ga Zaytuna ita ma ta shigo ɗakin, har lokacin Khalil yana nan bai tafi ba, yana zaune akan kujerar da Kaka ta ajiye masa.
Yana kallon Zaytuna da mamaki ya ce,"From where?".
Bayan duk ta gaida su Kaka tare da tambayarsu ya mai jiki ta ce da shi,"Bamu jima da shigowa garin ba, muna sauka a airport mu kai waya da Hamma yake ce min yana nan".
Khalil ya ƙara tambayarta,"Ya Granny ɗin?".
Ta ce,"Tana lafiya, duk tana gaishe ku. Da ta saka rigima sai mun zo tare tana so ta ga Hammah".
Ya ce,"Allah sarki Granny, in sha Allahu zan matsa masa akan mu je, sai mu dawo a ranar tun da dai ina da tabbacin ba zai kwana ba".
Zaytuna ta cirewa Fullo drip nata da ya ƙare yanzu, itama tana tambayarta yanda take jin jikin tana faɗa mata komai da sauƙi, ƙafar ce dai har yanzu.
Bayan minti biyar Zaytuna ta yiwa su Kaka sallama saboda kiran da Baffa yake yi mata, tare suka fita da Khalil wanda yake ta mamakin yacca akai har yanzu Turaki bai shigo ba.
Fitar su Maijidda ta da fa shoulders ɗin Fullo ta ce,"Menene damuwar?".
Ta ce,"Me kika gani?".
Maijidda ta ce,"Na san dai ba ki da lafiya amma yanayin fuskarki ya nuna akwai damuwa a ƙasan ranki".
Fullo ta haɗiye yawu tukunna ta ɗago ta kalla Maijidda sannan ta ce,"Mai yake damun Amir?".
Maijidda ta tashi daga kujerar da take zaune ta dawo gefen gadon kusa da ita ta zauna, ta kamo hannunta ta riƙe a cikin nata ta ce,"Me kika gani?".
Fullo ta dake ta hana kuka ƙoƙarin fitowa ta ce,"Sannu fa kawai yace min, ina amsawa yasa kai ya fice".
"Kin yi masa wani laifi ne?".
Ta girgiza kanta,"A'a ni banyi masa komai ba. Kuma ko da ace ma nayi masa ba zai min haka ba tun ma da ya ganni banda lafiya".
Maijidda ta ce,"To kwantar da hankali ba abin da kika masa, kawai yana cikin damuwa ne akan lamarinki. Ya ce ya kasa fahimtar me ke faruwa, yana ganin kamar mutanen ɓoye na so su shafe ki ne tun a wancan ciwon da kika yi, amma wannan karon sai yaga kamar ma sun riga sun shigeki. Baki gani ba wallahi yanda yake ta sadaƙa yana sauke miki alƙur'ani, anan fa yake kwana kullum ba ya tafiya, abinci sai Innarsa tayi da gaske".
Fullo tayi ɗan jim kafin ta ce,"To ai ni banda wasu aljanu, hasashensa ne dai kawai".
Maijidda ta ce,"To aikuwa abin da kowa ke faɗa kenan".
Fullo ta kalli su Kaka da suke can gefe su na maganarsu, hankalinsu ba ya kansu gaba ɗaya. Murya can ƙasa ta ce,"Maijidda ina asirin da na ce miki zan ɗauke a ɗakin Turaki?".
Idanun Maijidda a waje take kallon Fullo da al'ajabi, ai dama tun da hakan ta faru ta fara tunanin da wuya idan ba karambaninta ne ya bata damar ɗauke asirin da ta gaya mata zata ɗauke ba. Ita kam ta fara tsorata da lamarin ƙawarta, ta bakin Amir aljanu sun shigeta domin mutum dai ba zai yi abin da take yi ba.
Fullo ta ja hannun Maijidda, ta ji tayi shiru,"Kina da matsala wallahi, shi yasa wani lokacin da faɗa miki abu gwara shiru".
Bata bawa Maijidda damar magana ba ta ci gaba,"Na ɗauke asirin har ma ya ƙone".
"Shima ke kika ƙona shi?".
Ta girgiza kanta,"A'a wallahi ikon Allah kawai, ba ki gani ba kamar tashin bom haka yayi tushhh, kin ji yadda yake ɗoyi kuwa Allah kika shaƙa kayan cikinki sai sun kusa zubowa. Kuma kin san me?".
Ta faɗa tana muskutawa ta gyara zamanta akan gadon inda ta juyo ta fuskanci Maijiddan.
"Ina ga wannan asirin ne yake hana Turaki Sallah, ai dama na faɗa miki na ji Maama na kokawa da hakan. Kinga nima fa tun sanda na ɗauko shi na ji bana sha'awar yin sallah kwata-kwata. Bari dai mu bar asibiti zan baki labarin komai".
Ita dai Maijidda tsuru tayi tana zubawa sarautar Allah ido, ta ɗan ja baya kamar tana tsoron Fullo ne.
Muryarta itanma a can ƙasa ta ce,"Wani lokacin idan muna magana sai na ga kamar bake ba, shi yasa bakina ba ya rabo da ayatulkursiyu. To Allah dai ya ba ki lafiya ya rabaki da su lafiya. In sha Allah sai anyi galaba akansu...".
Bata ƙarasa ba Fullo ta kai mata duka a kafaɗa ita kuma tayi saurin kaucewa tana dariya.
"Allah ki bar wannan zancen Maijidda bana so, ba wasa bane wannan, wani yaji ai sai ya ɗauka gaske. Ƴar wulƙanci kawai".
Maijidda har sannan fuskarta da dariya ta ce,"Yo daga miki abin arziƙi, addu'a fa Haliman Amir? Ina ga ma wannan dalilin Allah ya duba ya aiko Malam Amir gareki, kinga ai sa dinga cin ƙwal uwarsu a hannunsa, domin ba raga musu zai yi ba da addu'a. Waya sani ma yanzun ko ba ke ba ce".
Wannan maganar tasa Fullo zuro ƙafafunta zata sauko a gadon ta damƙeta, ita kuma tayi wajen su Yami tana ta dariya.
Fullo tayi ƙwafa,"Allah kika ci gaba sai na bugo miki wannan ƙarfen". Ta faɗa tana nuna ƙarfen da ake saƙale drip a jikinsa.
Kaka idonta na kansu tun ɗazun, tana jin zuciyarta na washewa daga damuwar da ke tare da ita, sai yanzu hankalinta ya dawo jikinta. Ko babu komai ta san Fullo ta sami lafiya, abu ɗaya yayi saura, matsalar jinnu da suke tunani sun shafeta.
Fullo ta rafka tagumi tana tunani Kaka ta miƙo mata abincin da bata ci ba ɗazu, ta ɗago tana ɗan yamutsa fuska, murya a narke da shagwaɓa ta ce,"Kaka na ƙoshi fa".
Kaka tayi mata wani kallo ta ce,"Karɓa kafin ranki ya ɓaci, kin farka za ki ɗora daga inda kika tsaya ko. Wadda bata tausayin kanta kawai".
Fullo na turo baki ta karɓi plate ɗin.
"Wallahi ki cinye shi kafin na dawo". Kaka ta faɗa tana kai wa bakin ƙofa.
Yami ta miƙe tabi bayanta suka fita tare.
A bakin ƙofar suka tarar da Turaki wanda jin za su fito yayi saurin matsawa daga jikin windon da yake tsaye a wajen tun ɗazu. Suna ƙoƙarin durƙusawa ƙasa su gaida shi ya dakatar da su.
"Dan Allah Kaka bana son kuke tsuguna min irin haka, ni fa jikanku ne, ku daina kallon wani matsayi da nake da shi, mutum nake kamar kowa".
Yami ta ce,"Ranka ya daɗe kallon matsayi ai ya zama dole kam. Kai ɗin ne dai ka fita daban da sauran da suke da irin matsayinka. Kuma muna godiya a gareka bisa kyautata da mutumtawa, Allah ya haɗaka da mace ta gari".
Kaka ta matsa daga bakin ƙofar tana basa hanya.
"Ka shiga ciki yallaɓai bismilillah, ai tama farka tun ɗazu, jiki da sauƙi kam".
Idonsa na kan handle ya ce,"to ma sha Allahu, Allah ya ƙara lafiya. Ina dai daɗa bada haƙuri Kaka".
Kaka dai bata kallonsa ta ce,"Kai haba ranka ya daɗe wane mutum, ai mu wannan tsautsayin abun farin ciki ne garemu. In banda haka ina ma za'a ganta? Da yanzu muna cikin tashin hankali".
Bai ce komai ba ya kama handle ɗin ya buɗe ƙofar, su Kaka suka wuce bayan sun ce masa zasu je ɗaya ward ɗin ne za su yo dubiyar wata Ƴar Ƙawarsu da aka yiwa aiki ta haihu ɗan ya zo babu rai, yayi musu a dawo lafiya sannan suka wuce shi kuma ya shiga room ɗin.
Maijidda na ta fama da ita kan ta ci abinci amma taƙi, bai maida ƙofar ya rufe ba, kawai ya tsaya yana kallon Fullo kamar ɗazu da ya tsaya. Yana kallonta ta window lokacin da suke abinsu ita da Maijidda. Shi mamaki ta basa sosai bai yi tsammanin ma yarinyar na magana ba, da sakewa irin haka ba, zatonsa a tsorace take ko da yaushe irin yadda ya saba ganinta.
Idanunsa suka nuna masa irin ramewar da ta ƙarayi, ƙasusuwan jikinta tsab za su lissafu, idonta ya faɗa yayi loko kamar yadda ya ga nasa yayi da ya na duba madubi ɗazu.
Ba su san ya shigo ba sai da Maijidda ta miƙe tana faɗin,"Kiran Amir zanyi na faɗa masa kin ƙi cin abincin, shi kya ji maganarsa tun da kin fi sonsa".
Ta harareta ta ce,"Ku da ban ji maganarku ba, bana sonku kenan?".
Maijidda ta ɗaga kafaɗarta,"Ehh mana".
Fullo tayi shiru ta maida ƙafafunta kan gadon ta jingina da pillow, sai lokacin Turaki ya tura ƙofar ya rufe ya ƙarasa shigowa.
Dukansu suka kai idonsu bakin ƙofar, gaban Fullo ya faɗi, ta ji wani tsoro ya kamata. Ta wutsiyar ido yake kallonta, kuma yaga wannan tsoron a idonta wanda bai gani ba a ɗazu da take tare da ƴar'uwarta.
Da sauri Maijidda ta aje abincin da ke hannunta ta durƙusa tana gaishe shi, ya amsa muryarsa bata fitowa sosai. Ta miƙe ta ɗauki kujera daga gefen gadon Fullo ta kai masa, amma sai bai zauna ba.
Fullo dai da bata san ma shi ya kaɗeta ba, ba'a faɗa mata ba. Tana dai cike da mamakin waɗanne irin mutane ne su, ita ba kowan komai ba garesu amma sai zuwa suke suna dubata, ta ji su Kaka sun ce jiya da yau ne kawai Hajiya Madina da Baffa da Boɗejo ba su zo ba, amma hatta Hakimi kansa sai da ya zo, kuma shima Mai Martaba sai da ya aiko iyalinsa suka zo. Ƙwarai kirkinsu ya wuce tunanin mutum, kuma la shakka ba za su taɓa faɗuwa a rayuwa ba sai dai ci gaba. Ba tayi zaton ma Turaki zai iya zuwa dubata ba tun da wanda bai sonka ba ya sonka, no matter what happen to you ba zai nuna tausayinsa akanka ba.
Zuro da ƙafafuwanta tayi daga kan gadon zata sauko ta gaishe shi, ta ji muryarsa kamar a saman kanta ya ce,"Ki sakko ki yi me?".
Bata ɗago ta kalle shi ba ta ce,"Zan gaishe ka ne".
Idonsa har lokacin na kanta ya ce,"Wa ya farlanta miki hakan?".
Bata ce komai ba tayi shiru sai wasa da yatsun hannunta take ta duƙar da kai.
Shi kam kallonta kawai yake, ta wani natsu kamar wadda ta ga mutuwa, kamar ba ita ta gama surutu ɗazu ba har da dukan ƙawarta.
Ɗakin yayi shiru, Maijidda na daga gefe har yanzu a tsugune, ya maida kallonsa kan abincin da Maijiddan ta aje ya ce,"Ki kawo mata abincin".
Maijidda ta ɗauko plate ɗin da ke ɗauke da tuwon semovita da miyar agusi da naman ganda akai, ta miƙa mata, wacca tuni idonta ya cika da ruwa sai aikin ɓata fuska take yi.
Da mamakin Maijidda babu tirjiya balle musu Fullo ta sa hannu ta karɓa, kallon abincin kawai take ba don tana jin zata iya ci ba. Bakinta babu taste ɗin komai hakan ne yasa ba zata iya cin komai ba, kuma bata ma jin yunwar.
Wucewar daƙiƙa biyu Turaki ya ce mata,"Wa kike jira ya zo ya ci miki?".
Ba tsoronsa take ji ba, ita kawai yana yi mata kwarjini ne, ko bata kalle shi ba indai yana waje sai ta ji girman kwarjininsa ya cika wurin.
Ba don tana so ba ta gutsiri tuwon da spoon ta kai baki, ta tauna ta haɗiye da ƙyar kamar mai tauna magani, tana yin spoon huɗu sai ga amai ya yunƙuro.
Turaki yayi saurin ɗauke idonsa daga kanta ya kauda kai gefe yana jin zuciyarsa na tashi, Maijidda ta kamata suka wuce toilet, duka ta amayar da ɗan guntun abin da ta ci, ta wanke baki suka fito har sannan yana tsaye sai dai yanayin fuskarsa ya sauya.
Sauke numfashi take yi tana maida ƙwallar idonta, ta ƙasan ido take ta kallonsa, tana ce sannu ya zo yi mata ko? To shi bai yi ba kuma bai tafi ba ya tsaya mata a saman kai, Allah ya sani ji take kamar akanta yake a tsaye, da zata iya da ta buɗe baki ta ce masa ya tafi kawai.
A bakin gadon ta zauna, kuma tana zama ta ji ya ƙara cewa,"Ki ɗauka ki ƙara ci, sai ki ƙara zuwa ki yi wani aman, ki dawo ki ƙara ci, ki je ki amayar haka har ki cinye shi".
Wannan karon ba ita ta kalle shi ba Maijidda ce, tana masa kallo ɗaya ta ɗauke idonta ta koma can kan ɗaya gadon da ke cikin ɗakin, room ɗin marasa lafiya biyu ake kwantarwa a cikinsa amma ko da Baffa ya zo sai ya biya kuɗin ɗaya gadon dalilin da yasa take zaune ita ɗaya kenan.
Jin an turo ƙofa Turaki ya kai idonsa wajen, Dr Yusuf ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Duk da cewar tun ɗazu da Turaki ya baro masallaci yana office ɗinsa hakan bai hana su daɗa yin musabaha ba. As usual fuskar nan tasa da murmushin da ba ya yankewa.
"Ya mai jikin ranka ya daɗe?". Dr Yusuf ya tambayi Turaki.
"Gata nan maganin gardama ya rage ku bata kafin ku sallameta".
Dr Yusuf yayi ƴar dariya ya ce da Fullo,"Ya kike jin jikin naki?".
Ta ce,"Na ji sauƙi".
Ya ce,"To Allah ya ƙara lafiya. Yanzu cin abinci yayi miki saura shine za ki samu ƙwarin jikinki".
Ta ce,"To".
Ya juya ya karɓi file daga hannun nurse ɗin da ta shigo ɗakin yanzu, yayi rubuce-rubuce sannan ya rufe ya bata.
Ya fuskanci Turaki ya ce,"In sha Allahu by wednesday zamu sallameta. Komai normal babu wata matsala".
Turaki ya kalleta ya kalli tuwon ya ga ko rabin cinsa bata yi ba, ya ce da Dr Yusuf.
"Allah ya kaimu. Amma babu yadda za ayi a farke cikinta a dinƙa zuba mata abinci ta nan? Tun da bakinta nayi mata wahalar cin abincin".
Da murmushi a leɓen Dr Yusuf ya ce,"Babu matsala sai ayi hakan. Bari yanzu sai mu fara shirye shiryen shiga da ita ɗakin tiyata. Sai dai kuma fa idan za ayi irin wannan aikin dole sai an ɗinke bakin mutum gaba ɗaya ya zamana mutum ya dawo ba ya magana, wurin da za'a yanka a cikin nasa shi ne zai koma yagar bakinsa, abinci da ruwa ne kawai za'a dinga zubawa a ciki".
Turaki ya sosa girarsa sannan ya ja kujerar da ke kusa da shi ya zauna.
"Ayi abin da ya dace kawai Dr".
Sai ya kalla agogon hannunsa ya ce,"Nan da minti nawa za'a shiga tiyatar?".
Dr Yusuf ya ce,"In the next 5minutes ma zamu iya shiga, office kawai zan shiga na fito, ita dai yanzu a shiryata".
Turaki ya ce,"Alright a fito lafiya".
Dr Yusuf ya fita Nurse na biye da shi, wacca take ta dariya ƙasa-ƙasa da zancen da aka yi, ta lura sosai maganar ta tsorata Fullo. Maijidda ma na gefe a tsaye, itama dariya take ƙasa-ƙasa farkon da aka yi zancen farka ciki, saboda yadda ta ga Fullo ta tsure tana raba idanuwa, amma daga baya da taga kamar maganar da gaske ne sai tayi jugum tana dai ta kallon Turaki ta gefen ido, tana kuma jin tausayin ƙawarta na tsarga mata.
_"Amma babu yacca za ayi a farke cikinta a dinƙa zuba mata abinci ta nan?"_
Maganar ta Turaki ta daɗa maimaituwa a cikin kanta. Farko da ya faɗa bata razana ba, amma da ta shiga bin fuskokinsu tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya sai ta tsorata ainun, ko ɗigo babu na alamar wasa a yadda fuskokinsu ke nunawa, hakan ya tabbatar mata lallai da gaske su ke, farke mata ciki za ayi sannan kuma a ɗinke bakinta ta daina magana har a abada. Idan da abin da yafi tashin hankali wannan maganar tasa ta shiga, hangota take babu bakin magana kuma cikinta a yage, ta haɗe murfin idanunta da suke neman zazzagowa ƙasa, tun da aka fara maganar suke a waje.
Jikinta rawa yake sosai, ƙatuwar Malmalar tuwon take ta kallo, lissafi take yi, lissafin yadda za ayi ta cinye shi a cikin miniti biyar kafin a shiga da ita tiyatar da suka ce. Ta ɗago ido ta kalli Maijidda da ke kallonta, yadda take a tsorace haka Maijiddan ma. Cikinsu biyun kowa ya kasa cewa komai, tsoron Fullo ɗaya ne! Ta ce zata basa haƙuri ya sakar mata wannan uwar tsawar da bata so, dan taga kamar hakan yake jira, dalilin da ya sa bakinta mutuwa kenan.
Maijidda tayi sum sum ta fice zuwa kiran su Kaka, tana fita Fullo ta sakko a kan gadon ta wuce toilet, Turaki ya bita da kallo har ta dawo. Ta koma gefen gadon ta zauna, ta saka hannunta da ta wanke ta fara cin tuwon tana kai ƙatuwar lomar da ta fi ƙarfin bakinta.
Kana gani kasan tura tuwon kawai take yi, bata ko tsayawa ta gama cinye na bakin zata ƙara saka wani, tun da take bata taɓa cin malmalar tuwo mai girman wannan ba, kai abincin kansa bata cin da yawan hakan, shi yasa Yami kullum ke mata tsiyar taƙi ci tana ta bushewa.
Yana zaune yana shafa wayarsa amma indonsa sam ba akan wayar yake ba akanta yake, tun lomar farko da ta kai baki. Ba ƙaramin ba shi dariya tayi ba ya danne yana cije leɓe, murmushinsa na fita saboda dariyar ba zata dannu duka ba, yadda take ta tura abinci cikin sauri, har yunƙurin amai tayi amma tayi maza ta maida shi, ga jikinta ma gaba ɗaya rawa yake kamar mazari.
Cikin mintunan da ba za su haura uku ba plate ɗin ya zama babu komai, ta cinye tas sai nishi take yi, ta sakko ta je ta wanke hannu ta dawo. Ta kalle shi taga hankalinsa bai kanta, wayarsa kawai yake dannawa, kamar tayi magana ta roƙe shi su yi haƙuri sai dai tayi shiru, ta kama yatsun hannunta sai jansu take kace tana lazimi. Idanuwan nan da suke loko sai ƙifƙiftasu take yi. Turaki duk yana kallonta, har maganar da bakinta ke son yi yana kallon yadda ɗan ƙaramin leɓen ke motsawa. Shi gani yake ma kamar ƙunƙuni take tana zaginsa.
Suna haka aka murɗa ƙofa, tana jin hakan gabanta yayi mugun faɗuwa ta haye kan gadon gaba ɗaya a zabure, ta takure ƙafafuwanta tana shirin sakin kuka.
Muryarta na karkawa ta cewa Turaki,"Tun ɗazu na cinye abincin dan Allah ku yi haƙuri".
Tana rufe bakinta sai taga ashe su Kaka ne ba Dr Yusuf ba kamar yadda ta tsammata. Hakan yasa ta saki ajiyar zuciya tana bin Kaka da ido, ta ga fuskar Kakan a haɗe alamar ɓacin rai.
"Sannu fa mai babban suna".
Turaki ya tashi ya amsawa Kaka. "yauwa Kaka sannunku da dawowa. ya mai jiki?".
Ta ce "Da sauƙi. Kayi zamanka mana".
Ya ce,"A'a Kaka dama ina niyyar tashi ai".
Ta ce,"Ni dai da ka zauna wallahi, bana jin daɗi idan kana ƙin zaman nan saboda mu".
Ya kalli tsohuwar da jin tausayinta a ransa, sosai suke kama da Fullo kawai dan ita ta tsufa ne. Ba ya son musu da babba saboda haka dole ya koma ya zauna.
Bayan ya zauna Kaka ta ce,"Muna daɗa godiya fa mai babban suna, babu abin da zamu ce sai Allah ya saka maka da gidan aljannah. Kai da iyayenka kuna kulawa damu Allah ya biyaku da alkhairansa".
Ya ce,"Amin Kaka na gode".
Ta sake cewa,"Maijidda ce ta je take faɗa mana abin da ke faruwa na za'a shiga da ita tiyata, shi ne muka taho. Na ce ai hakan ma wani gata ne aka yi mata".
Yami ta ce,"Allah yasa dai ayi a sa'a".
Ya sosa girarsa leɓensa na fitar da murmushi ya ce,"Rhh likitan ne dama ya bada shawarar hakan".
Karaf Fullo tayi saurin cewa,"A'a ba shi bane kai ne ka fara faɗa masa. Ni dan girman Allah Kaka kuyi haƙuri in dai abinci ne zanke ci".
Kaka tayi mata banza, Yami ta ce,"To ai magana ta ƙare tun da har likitan ma yayi shirinsa. Ki yi addu'a kawai Allah yasa ayi miki a sa'a, hakan ai gata aka yi miki Fullo kinga yanzu cikinki ga dinƙa samun abincin kirki. Magana kuwa kya dinƙa nuna abund a kike nufi da hannu".
Yami na yin shiru ta fashe da kuka tana kifa kanta a gwiwarta, ta sani babu wanda zai ji tausayinta, kuma babu mai jin kukanta tun da bata da uwa bata da uba a raye.
Turaki ya ɗauke idonsa akanta, zai fita Kaka ta ce,"A'a mai babban suna tunda dai sa hannunka ne a yin aikin nan to ka ɗan jira likitan ya zo a ɗauketa a gabanka. Mu ba jin maganarmu take yi ba".
Tana faɗin haka suka fice su duka suka bar Maijidda a tsaye, itama sai ta fara hawayen. Bayan fitar su Kaka ya jawo kujera sosai gaban gadon sannan ya zauna, ya aje wayarsa akan gadon, sannan ya sarƙe yatsunsa wuri ɗaya.
Ya ce da ita,"Haƙura za ayi da farka cikin ko kukan za ki ci gaba da yi?".
Kalmar farka cikin ita ke ɗaga hankalinta, tayi saurin ɗagowa fuskarta tayi sharkaf.
"Dan girman Allah karka sa a farke min ciki, zan dinga cin abinci kullum, ai kana kallo na cinye na ɗazu. Don son da kake yiwa Maama da Adda Zaytuna ka ce ba za ayi min ba".
Mamaki yasa kawai ya tsareta da ido, ta ya aka yi ta san yana ƙaunar mutanen nan guda biyu? Ta ya ta san zai iya yin komai akansu? Wa ya faɗa mata ana roƙonsa da su ya aikata abin da bai niyya ba?.
Ya sauke numfashi sannan ya ce,"An fasa".
A hankali ta ce,"Na gode, Allah ya kareka daga sharrin maƙiyanka".
Ta faɗa tana goge hawaye da ɗankwalinta da ya zame. Suka haɗa ido tayi saurin ɗauketa nata, idonsa ya maƙale a gashin kanta ya ce,"Ɗaura ɗankwalin ki bani amsar tambayata".
Ta ɗaura ya ƙara cewa,"To ki cire tsoron ki nutsu".
Ta haɗiye wani irin yawu tana saita nutsuwarta.
Ta ji ya ce,"Ɗago idonki ki kalle ni".
Ta yi yunƙurin yin hakan amma sai ta kasa, ya ci gaba da kallon siraran hannunta da suke ta karkarwa, sai kawai ya miƙa hannunsa ya haɗe hannayenta biyu ya riƙesu cikin nasa guda ɗaya, sai dai da mamakinsa duk da hakan ba su bar karkarwar da suke ba kamar ma ƙaruwa abin yayi, cikin ransa ya ayyana duk yadda aka yi wannan rawar da jikin nata yake yi bana lafiya ba ne.
Jin yanda ya riƙe hannuwan nata yasa ta kulle ido wani abu na wucewa ta maƙogoronta. Kuma kafin ta buɗe idon ta ji ya ce,"Mai ya kai ki wannan wurin a wancan ranar?".
Ta buɗe ido ta sauke a saman sumarsa tana jin numfashinta na ƙoƙarin katsewa.