Free chapter · Read without an account
The Predator & The Prey
by ZAHRAA · JANNAH ANDERSON
The Predator & The Prey
Bayan faruwar lamarin daren jiya a bakin (pool side), dakin Jannah Anderson ya koma tamkar filin daga. Jannah ta kasa bacci, sanyi mai ratsa kashi na Switzerland ya kasa kashe mata zafin kunyar da take ji a ranta. Ta yaya ta bari "First Kiss" dinta ya tafi ga Aliyu? Ta yaya ta nuna rauninta a gaban talakan da take biya albashi?
Duk lokacin da ta lumshe idanu, tana jin dumin lips din Aliyu a nata. Ta tashi ta zauna, ta daki katifar dakin ta da kyar. "Jannah, kin gama da kanki! Kin ba shi damar da zai raina ki," ta rada wa kanta cikin bakin ciki.
Washegari da safe, gari ya waye da wani sanyi mai hade da hazo. Jannah ta fito sanye da bakaken kaya tun daga sama har kasa, fuskarta a tamke tamkar bata taba sanin me ake kira murmushi ba. Aliyu yana jiran ta a harabar hotel din, sanye da nasa rigar sanyin, fuskarsa fess babu alamar gajiya.gaishe ta yayi kamar yadda ya saba ,fir tayi kamar bada ita yake ba ta shige mota
Suna isa bankin Credit Suisse, Mr. Schneider ya tarbe su da wani labari mara dadi
"Miss Anderson, mun yi bincike na gaggawa. Macen da muka gani a hoton CCTV ta bar kasar nan jiya da dare, 'yan mintoci kadan bayan kun bar bankin. Ta bi jirgin sirri ne (private jet) zuwa wata kasa da ba mu riga mun tantance ba."
Jannah ta buga teburin da karfi. "Wannan yana nufin akwai wanda yake gaya mata duk takun da muke yi a nan Zurich!"
Cikin sauri aka sake canza dukkan lambobin tsaro (codes) na asusun Anderson Global, aka kara matakan tsaro wadanda sai da "fingerprint" da "retina scan" na Jannah kadai za a iya taba kwabo. Jannah tana yin hakan ne amma zuciyarta tana kan macen nan dake da tabo a hannu. Tana raye, kuma tana kusa da ita.
Suna hanyar komawa hotel , shiru ya ratsa motar. Jannah ta kalli gefe ta ga Aliyu ta madubi. Aliyu yana ta kunshi dariya, yana wani murmushi na mugunta wanda yake nuna cewa har yanzu yana jin dadin abinda ya faru a daren jiya.
Wannan murmushin ya kusa haukata Jannah. Ta juyo da sauri ta watsa masa wani kallo mai ratsa kashi.
"Aliyu!" ta kira sunansa cikin murya mai kauri.
"Na'am, Ma'am," ya amsa yana kara fadada murmushin sa.
"Ina so ka saurare ni da kyau. Abinda ya faru a daren jiya, kuskure ne na yanayi da kuma damuwa. Idan na sake jin wani labari ya fita, ko kuma na fahimci ka fadawa koda mutum daya ne a duniyar nan, to wallahi Aliyu zan yanke maka harshe da hannuna!"
Aliyu ya danyi gyaran murya, ya rage murmushin amma idanunsa har yanzu suna dariya. "Ma'am, ai ni amintaccen PA ne. Sirrinki, sirri na ne. Amma fa... kin san cewa 'kiss' din nan ba zai taba fita a raina ba, ko?"
Jannah ta ji kanta ya sara. Ta juya ta kalli titi, zuciyarta tana bugawa. Ta sani, Aliyu ya riga ya samu kafar da zai shiga rayuwarta, kuma yanzu ne asalin wasan ya fara.
Sanyi mai ratsa kashi na Zurich bai hana zuciyar Jannah Anderson tafasa ba. Bayan sun dawo daga banki, ta kasa samun natsuwa. Duk inda ta duba, hoton Aliyu take gani da wancan murmushin nasa na rainin wayo.
Dare Ya Sake Yi (12:00 AM):
A duk inda Jannah take, ko a katafaren Penthouse dinta na Lamido cresent ko kuma nan Zurich, filin tafkin ninkaya (Pool Side) shi ne matattarar sirrinta. Ta fito sanye da wata riga ta bacci mai sulbi kalar ja (Crimson Red), rigar ta kasance siririya wacce take bayyana surar jikinta a fili. Iskar daren Zurich mai sanyi tana hura rigar, tana kara fito da kyaun surarta yayin da take tafiya cikin takunta na isa.
Ta zauna a bakin ruwan, tana dan taba wayarta, amma tunaninta yana kan macen nan da ta gudu daga banki.
A can nesa, Aliyu yana zaune a kan wata kujerar shakatawa. Ya sanya rigar sanyi mai kauri, yana waya da Naima. Muryar Naima tana ratsa kunnensa cikin shaukin soyayya, tana gaya masa yadda take kewarsa da kuma burin su yi aure.
"Naima, nima ina kewarki..." Aliyu ya fara fada, amma maganar ta makale a makogwaronsa.
Caraf, idanunsa suka sauka akan Jannah dake takowa zuwa inda yake. Hasken wata ya gauraye da hasken pool din, ya mayar da Jannah tamkar wata aljana dake fitowa daga ruwa. Jannah is looking damn sexy—wani irin kyan da Aliyu bai taba gani ba a rayuwarsa.
Take, Aliyu ya daina jin me Naima take cewa a daya bangaren. Zuciyarsa ta buga, "Junior" dinsa dake kasa ya fara amsawa da karfi, ya mike tsaye tamkar soja dake jiran umarni. ya ji numfashinsa ya fara fita da kyar, jikinsa ya dauki zafi duk da sanyin dake wurin.
Jannah ta karasa har inda yake, ta tsaya daf dashi, kamshin turarenta na Vanilla da Rose ya mamaye kowane sako na jikin Aliyu. Ta kalli wayar dake hannunsa, sannan ta kalli yadda yake kallonta da kishirwa.
"Mr. Aliyu, me ya kara kawo ka nan a wannan lokacin?" Jannah ta tambaya, muryarta a sanyaye amma cike da iko. "Kana tunanin zaka sami wani kiss din ne? Idan hakan ne, to kayi kuskure."
Aliyu ya kasa magana, ya mike tsaye da kyar, idanunsa suka rincike cikin nata.
"Waccan ma kuskure ne mafi girma a gare ni," Jannah ta cigaba da fada tana matsowa daf dashi har suna iya jin bugun zuciyar juna. "Kasan na girme ka, kuma ni Boss dinka ce. Matsayinka baya wuce ma'aikaci a wurina."
Take, Jannah ta mayar da idanunsa kasa, tana kallon inda joystick din Aliyu yake ta harbin iska a cikin wandonsa, ya bayyana radam saboda matsewar da wandon yayi yi masa a kasa ta kalle shi cikin kwayar ido, ta yi wani murmushin rainin wayo.
"Learn to be professional, Aliyu," . "Kada ka bari abinda ke tsakanin kafafunka ya lalata maka aikinka na dubban daloli."
Aliyu ya bi inda take kallo, ya ga yadda ya tona asirin kansa a gabanta. Ya ja numfashi, yana jin yadda gumi yake jika masa jiki duk da sanyi. Lallai Janna h Anderson ta wuce duk tunaninsa; mace ce wacce tasan inda raunin namiji yake, kuma tana amfani dashi wajen nuna mulkinta.
Jannah ta juya masa baya, tana girgiza kunkuminta cikin takun isa, ta nufi dakin ta, ta bar Aliyu a tsaye yana faman daidaita numfashinsa, yayin da Naima take ta kiran sunansa a waya ba tare da ya sani ba thank God ma yayi muting wayar