Free chapter · Read without an account

Aftermath

by ZAHRAA · JANNAH ANDERSON

Washegari, Jannah ta iso ofis sanye da wata riga kalar maroon da bakin siket. Fuskarta a daure take, babu alamun cewa ita ce macen da ta nuna rauni a daren jiya. Ta wuce ta gaban teburin Aliyu ba tare da ta kalle shi ba.

Aliyu yana tsaye kusa da kofarta, sanye da shirt yaci zanzaro, fuskarsa kamar ba shi ne ya sumbaci wuyanta a daren jiya ba.

"Good morning, Ma'am. Ga rahoton asarar da aka yi jiya da kuma jadawalin ganawar ki da lauyoyi," Aliyu ya fada cikin muryar kwararru, tamkar babu abin da ya taba shiga tsakaninsu.

Jannah ta tsaya, ta kalle shi ta cikin gilashin idonta. "Thank you, Aliyu. Kuma game da maganar jiya a penthouse... na riga na goge shi a raina. Ina fata kaima hakan ne?"

Aliyu ya gyada kansa, idanunsa suka yi sanyi na dakika daya kafin ya maida su kauri. "Kwarai kuwa. Jiya ai ruwa ne kawai ya ruda mu. Ni kaina ina da wadda nake shirin aura nan da watanni kadan, don haka wannan kuskure ne da ba zai sake faruwa ba."

Suna cikin wannan takun-sakar,ne  aka turo kofa da karfi. Sabeer ne ya shigo, ransa a bace, idanunsa har sun yi jawur.

"Jannah! Me kike yi da wannan yaron a kulle a ofis ?" Sabeer ya tambaya yana nuna Aliyu da yatsa. "Jiya kin tafi kin bar ni a taro saboda emergency din da ya kiraki, kuma na kira wayarki a kashe take har asuba. Me kuke boyewa?"

Jannah ta hade rai, "Sabeer, baka da ikon tambayata yadda nake gudanar da kamfani na. In kazo maganar kasuwanci ne, ka zauna. In kuma kishin banza ne ya kawo ka, kofar fita tana nan.kuma kar ka kara banko min kofa haka nan ba wajan wasa ba ne 

Sabeer ya matsa kusa da Aliyu, ya kalle shi sama da kasa, Aliyu ko? Na sanya ana binciken asalin ka. Akwai wani abu game da kai da ban yarda dashi ba I don’t like your vibe . Kuma idan na gano kana kokarin raba ni da Jannah, wallahi sai na sa an garkame ka."

Aliyu ya yi murmushin rainin wayo, ya gyara tsayuwar sa. "Sir, aiki na ne in kare Ma'am. Kuma duk binciken da za ka yi, za ka iske ni ne a matsayin amintaccen mai hidima a gare ta. Watakila kishinka ne yake nuna maka abin da babu shi.

Bayan kace-nacen da aka yi a ofis, Aliyu ya kasa nutsuwa. Kalaman Sabeer na cewa yana binciken sa sun sanya shi jin fargaba, ba don kansa ba, sai don asirin aikin sa dake neman tonuwa.  Excuse ya nema a Wajan jannah Akan cewa bashi da lafiya ,Ya dauki jakarsa ya fice daga ofishin da wuri, yana bukatar ganin mace daya tilo da take sanya shi jin shi mutumin kirki ne 

 ya isa kofar gidan su Naima  . Ta fito tana sanye da doguwar riga ta abaya , fuskarta  tana dauke da wani irin murmushi mai cike da aminci da tsantsar soyayya.

"Yaya tareeq ! Yau kaine kazo da rana  haka?"NAIMA  ta fada yayin da ta karaso kusa da shi.sannu da zuwa yaya tareeq ya aiki ?kwana biyu Ka daina kirana ,Ka daina zuwa Allah yasa ba wani laifi nayi ba ?kuma 

Naga Kamar Ka dan rame ko Akwai abun dake damun Ka kane?wani irin daci  yaji a ransa. Kallon da Naima  take masa na amana ya sanya ya ji tamkar shi ne mafi munin mutum a duniya. Ya tuno da daren jiya, ya tuno da Jannah Anderson, da kuma yadda ya kasa jurewa shaukin zuciyarsa.

"Kiyi hakuri Naima , aiki ne ya sha kaina a ofis. Wayata ma ta samu matsala," Aliyu ya yi karya, idanunsa suna kallon kasa.

, muryarta a sanyaye tace yaya tareeq , na lura kwana biyun nan baka da nutsuwa. Shin wannan sabon aikin naka da kace PA ne akwai wata matsala ne? Idan har aikin nan yana wahalar da kai, gara ka bar shi. Farin cikin ka ya fi min komai."

Aliyu ya kalli Naima , ya ga tsantsar soyayya a idanunta. A lokaci guda, hoton Jannah dake zaune a kan sofa tana kallon sa ya fado masa. "Naima , karki damu. Komai zai wuce. Nan da wattani kadan kuma kin zama amarya ta 

Naima ta rufe fuskarta saboda kunya, tana murmushi. "Insha Allah, yaya tareeq . Amma... akwai wani abu da nake so in gaya maka.Jiya naji abbana yana waya da abbanku Wai an kusa tsayar da rana kuma kamar baza a dauki lokaci ba . 

Aliyu ya gyada kansa, amma a ransa tsoro yake ji. A bangare daya yana son Naima  saboda nutsuwar ta da tarbiyyar ta, amma a daya bangaren kuma, sha'awar da yake ji ga Jannah tana neman ya zama fitila dake cinye dukkan sauran tunaninsa.

Yana barin gidan su Naima , ya sami sako (message) daga babban ofishinsa na jami'an tsaro

"Report to base immediately. Alhaji Bashir has made a move in Zamfara. We found a link to Jannah's past." A haka suka yi sallama da naima 

. Ya zame ya nufi 'Base' domin jin bayanin da aka samu daga Zamfara.

Babban jami'in binciken ya kalle shi ya girgiza kai. "Aliyu, mun bincika bayanan da muka samu daga Zamfara. Mun bi dukkan layukan sirrin  da aka ce Jannah tana dasu a can, amma gaskiya babu wata alaka tsakanin wannan sirrin da Jannah kwata-kwata.".

Wannan bayanin ya sanya Aliyu shiga cikin duhu. Idan har sirrin  Zamfara ba na Jannah bane, to wane ne yake kokarin jefa ta a ciki? Kuma me yasa Alhaji Bashir yake da yakinin cewa can ne tushenta?.kansa ne ya sara wacece jannah Anderson ?

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol