Free chapter · Read without an account

23

by Halima Zakariyya Haruna · LULLUƁIN BIRI

*23*
Bayan wata huɗu, cikin ƙaton office ɗin da sanyin Ac ke ta busawa yana haɗewa da daddaɗan ƙamshin turaren dake jikinsa yana bada wani irin sanyayyan ƙamshi mai motsa zuciya. 

Turaki ne zaune akan kujera, tana ɗan juyawa da shi gefe zuwa gefe, yatsansa ɗaya akan lips ɗinsa, cikin yanayi na nazari akan wani lissafi nasa na shi ɗaya.
Numfashi ya sauke sannan ya shiga operating laptop ɗin dake kan table a gabansa, ya ɗau lokaci kafin ya ɗauƙi wayarsa a gefe yayi calling lambar Khalil.

Bayan wasu mintuna uku sai ga Khalil ya shigo office ɗin, tun shigowansa Turaki ke kallonsa har ya ƙaraso ya zauna kan kujera. 

"Director". Turaki ya faɗi sunan da yake kiran Khalil da shi a yanzu tun bayan mallakar wannan company ɗin da suka yi. Khalil ɗin shima yana kallonsa ya amsa da nasa sunan da yake kiransa da shi na yanzu. "Yes Excellency".

Anan ne kuma Turaki ya ɓullo da wata magana wadda ta shafi aikin company ɗin na su, sun ɗau tsawon lokaci suna tattaunawa akan issue ɗin, Khalil nata ƙara kawo dabaru da zasu daɗa ɗaga company ɗin zuwa sama, dan sam basa saka kamfanin a matsayin ƙarami saboda kawai yana sabon buɗewa, so suke cikin ƙaramin lokaci ya kai wani babban mataki da ba kowanne company ke samu ba at once.

A lokacin Turaki ya haɗa urgent meeting da staffs, aka shiga aka ƙara tattaunawa kowa na bada POV nasa akan ganin kamfanin ya haɓɓaka. Sai da suka ɗauki tsawon awa guda sannan suka gama. 
Suna kammalawa kuma Turaki ya bar office ɗin, ya tafi airport ɗauko Bello Ƙaraye wanda ya dawo daga sudan ya je wani course.

Akan tinin barin Gombe international airport, cikin motar ƙirar Bugatti, motar da Mai Martaba ya bawa Turaki ita a ranar buɗe company ɗin su, Bello ya kai hannu yayi reducing volume na karatun qur'anin da suke saurare tun barowansu airport, can kuma sai ya kashe gaba ɗaya.

Ya ce,"Kana ciwon baki ne?". 

Turaki yayi masa shiru bai tanka masa ba, idonsa na manne akan titi. 

Bello ya yi tsaki ya ce,"Duk inda ɗan rainin hankali yake, kai ne ubansa. Banda iskanci tun tahowarmu nake magana, but you keep refusing to answer me. Kuma tsabar miskilancinka ya kai intaha, ina kallon bakinka yana motsi, amma ba zaka faɗa min abin da ke zuciyarka ba. I don’t even know what is wrong with you. I noticed some changes in you tun kafin na tafi. To ni fa ba ɗan iska ba ne da zan ta tambayarka kana min banza."

Turaki ya ce,"Ka bani damar magana ne, balle na faɗa maka abin da ke cikin zuciyata? Tun da na ɗaukoka ka ishe ni da Bima Restaurant, sai ka ce baka taɓa cin abinci ba a rayuwarka. Tun saukarka you didn’t even bother to ask about my health… Abinci, Abinci kawai ka sani. Kai idan kana jin yunwa, you see nothing balle ma ka lura da ramewar da mutum ya yi."

Yadda yayi maganar a ƙufule Bello Ƙaraye ya bushe da dariyar ƙeta, shi dai tun da ya fito a jirgi ya kalla kamar idanun Turaki sun faɗa loko, to amma bai lura da muguwar ramewar da yayi ba sai yanzu da yayi maganar. Yunwa yake ji sosai shi yasa idonsa ya rufe da ganin komai.

Ya ce, "To ka bani damar ganin ramar da ka yi ne, balle na ce Muhammad Turaki ba ka da lafiya? Tun da ka ɗauko ni, fuskarka take a ɗaure. Sannu wannan ba ta haɗa ni da kai ba; to ta ina zan ga wata rama? Motsin bakinka kawai na lura da shi. Anyway, what’s wrong with you? Did you even go to the hospital?"

Turaki yayi masa wani kallo ya ce, "Ciwon uban me na ce maka ina yi da zan je asibiti? Ni lafiyata ƙalau". 

Bello ya ce,"Ikon Allah, to na ji lafiyarka lau. What is the problem?".

Turaki yayi masa shiru yana kallon titin gabansa, cikin ransa yana tunanin ta inda zai fara yi masa maganar, sarai ya san rainin hankalin Bello, yanzu sai ya faɗa masa kuma ya ɗauki maganar a gantale. Ba zai nutsu ya fahimci maganar ba balle ya basa damar fayyace masa komai.
Bello dai na gefe yana kallonsa, ganin bai da niyyar cewa komai ya ɗaga kafaɗa ya maida hankalinsa kan wayarsa, ko mene idan tayi tsami zai ji, ba zai iya da wannan miskilancin ba, yunwar da ke rarakar cikinsa ma ta ishe shi.

Shiru ya ratsa cikin motar. Sai can Turaki ya ce, "Just give me your full attention, let’s talk." Ya yi maganar a hankali, with a serious tone.

Bello ya kallesa ya ga Seriousness ɗin dake kan fuskarsa, sai ya kifa wayarsa a kan cinyarsa ya ce,"Na baka duka attention ɗina, idan ma so kake na cirosa na miƙo maka gaba ɗaya sai na yi hakan".

Turaki ya waigo, ya yi masa kallo ɗaya sannan ya ɗauke kai. Ya dinga motsa bakinsa kamar bebe. Ya san halin rainin hankalin Bello, shi ya sa yake shakkar faɗa masa, he never takes things seriously when it matters.

Bello ya katse tunaninsa,"Mu tafi Restaurant ɗin kawai, ba zan iya isa gida ban ci komai ba". Sai a sannan Turaki ya buɗe baki yayi maganar da tasa Bello ya zabura, har yana ƙoƙarin miƙewa akan kujera.

Da wani mugun shock Bello ke kallonsa yana ganin kamar ba Turakin da ya sani ba ne, wannan wani Turaki ne na daban da zai iya aikata abin da yake faɗa, amma na sa Turakin ko da ace giyar wake yasha ba zai iya aikata abin da wannan ya faɗa ba.

"What! Ka ce mene? Na kasa fahimtar me kake son cewa". 

Bello ya tambaya har sannan idanuwansa a warwaje. 
Turaki ya ce,"Abin da ka ji na faɗa".

Bello Ƙaraye ya cire hular kansa yana goge wani uban gumi da ya fara keto masa, ya koma kamar wanda yayi wa sarki ƙarya. 

"Wait Turaki! Wait!, Abar zancen wasa dan wannan maganan naka ba magana ba ne da za'a ɗauka matsayin wasa...".

Bai ƙarasa abin da yake son faɗa ba Turaki ya katse shi,"Ni dama na taɓa faɗa maka abu a wasa ne? Balle ka ɗau maganar nawa a shashance".

Bello ya ce,"To idan ba wasa kake ba Hauka ka yi? Don maganar da kayi bata masu hankali ba ce kuma ba magana ba ce da hankalina zai ɗauka. Kasan kuwa me ka faɗa? Turaki are you in your sense? Yaushe lissafinka ya fara kwancewa?".

Danger ta tsayar da motar su, fuskar Turaki a ɗaure ya juyo ya kalli Bello ya ce,"Ka ga Malam, ban faɗa maka personal issue na ba dan ka dinga min ihu aka ba, idan ka gane fine, idan ba gane ba just keep quite". 

Bello ya ce,"Ba zanyi shirun ba, mahaukacin banza kawai".

Yayi ɗan jim yana maimaita furucin Turankin a cikin kansa, anya kuwa bai sha wani abu ba kafin ya ɗauko sa?. Ya ɗaga kai ya ƙara kallon Turaki, gaskiyar furucinsa ɓaro ɓaro a saman fuskarsa. Kuma da tsananin mamakin da yaƙi barinsa yake ta kallonsa, da ƙyar ya iya buɗe baki ya ce masa,"Da sanin wa kuma da izinin wa aka yi hakan Muhammad?".

Turaki ya ce,"Da sanin kaina da izinin kaina ni ɗaya, sai kuma me? Sai aka yi ya ya?". 

Da wani mugun jin haushinsa Bello ya ce,"Sai ka yi ba dai-dai ba, kuma tun wuri ka je ka warware kwaɓar da ka aikata kai ɗaya, kar ma akai gaba na ji kana ambatar sunana".

Murya a sanyaye, Turaki ya ce, "Abin da na ga ya dace na yi, shi na yi Bello. Sakayyar da ya kamata na yi kenan. Kai kanka ka sani, komai da lissafi nake yi; bana abin da bai dace ba, ka sani. And I know there’s no one who would support me, shi ya sa na yi komai ni kaɗai. Even if it were you, na tabbata haka za ka yi. Ba za ka gane komai ba sai na yi maka cikakken bayani Bello. Wannan hargagin naka ba shi ne abin yi ba. Ka fara ɗaukar maganar da na yi maka da muhimmanci, sannan sai na yi maka bayani dalla-dalla. Ina buƙatar wanda zai saurare ni a kan wannan issue ɗin Bello.”

"Bayanin banza, Turaki! Wanne bayani za ka yi min dalla-dalla har na fahimce ka? Wait! Kana tsammanin ma zan ɗauki maganar da ka zo min da ita ne? To ba ni kaɗai ba, babu wanda zai ɗauki wannan zancen banzan naka. Tun wuri ma kwaɓar da ka je ka aikata, ka je ka warware ta kawai Malam".

A fusace ya yi maganar, shima kuma Turaki cikin fusata ya ce,"Bello Tukur Ƙaraye kar ka ƙara yi min ihu a cikin mota, kar ka ƙara ɗaga min murya".

Shi ma Bello ya ƙara fusata ya ce, "Muhammad Turaki Habib, ba zan daina ɗaga maka murya ba. Ka yi duk abin da kake ganin za ka yi, ta yaya za ka aikata abin da bai dace ba ka ce ba zan faɗa maka gaskiya ba? Who the hell do you think you are? Ai dama saboda ka san ba zan goyi bayan haukarka ba ne ya sa ka ƙi yin shawara da ni, ka je ka aikata abin da kake ganin ba zai zame maka matsala ba. Ni har yanzu na kasa gane abin da ke cikin kanka, balle na fahimci maganarka. Anya ba ka fara shaye-shaye ba? Ka kalle ni ka yi min bayani da kyau Malami."

Turaki yayi masa banza, Bello ya dinga kallonsa da bala'in mamaki, ko a mafarki bai taɓa zaton Turaki zai iya aikata abin da ya faɗa ba balle kuma a zahiri. 
Shi ya san waye Turaki, tun suna yara suke tare, ya san sarai abin da zai aikata da wanda ba zai aikata ba, and ya san ba zai taɓa aikata abu ba tare da ya nemi shawararsa ba ko kuma ya faɗa masa ba. Turaki baya gaban kansa sai da sanin mutum huɗu, dole Maama ce mutum ta farko da Turaki zai sanarwa abin da zai aikata, sannan shi ya biyo bayanta, sannan Baffa, sannan Zaytuna, dole mutum huɗun nan sai san abu kafin ya aiwatar. 

Amma wannan lokacin baya zaton cikin su huɗun akwai wanda yasan da wannan batun, sai a yanzu da shi ɗin ya sani, ya san abin da ba zai iya ƙaryatawa ba tun da yaga gaskiyar lamarin akan Fuskarsa da kuma furucinsa. Wai har yana faɗa masa abin da ya dace shi na yi Bello? Tukunna ma!

Bello ya sauke numfashi ya ce,"Maama ta sani? Ni ne da ka mayar da ni banza yanzu ka je kai gaban kanka baka faɗa min ba?".

Har yanzu murayar Turaki da sanyi ya ce,"Itama bata sani ba. Ina tsoron faɗa mata, kuma ina tsoron ta sani". 

Bello ya zaro ido,"What!". 

Ya ce masa,"Yes, bata san komai ba akai. Kai ɗin ma na faɗa maka ne saboda na kasa riƙe abin ni kaɗai, ban san wane kalar asiri kayi min ba da bana iya riƙe sirrina sai na sanar maka". 

Fuskarsa a tamke yayi maganar kamar yadda muryarsa ma take a tamke. 

Bello ya yi gajeriyar dariya ya ce,"Allah ka hauka ce ko kuma ka fara shaye-shaye, faɗa min waye ya baka gurguwan shawarar nan na fara shaye-shaye?".

Turaki ya kallesa ta gefen ido ya ce,"Bello ni nake shaye-shaye? Ni kake cewa ina hauka? Just saboda na fita hakkinka tun da na san bama ɓoyewa juna komai".

Bello ya ce,"Ai ko mahaukaci ma ba zai yi abin da kayi ba, abin da ka aikata na ƴan ƙwaya ne, wanda yake cikin hankalinsa ba zai taɓa aikata haka ba wallahi. And imagine, ko kunya baka ji ba kake faɗa min wai Maama bata sani ba. So ko me zaka yi a haukace kake, kana buƙatar ganin likitan ƙwaƙwalwa dole".

Turaki yayi parking motarsa, without looking at Bello yance,"Fitar min a mota". 

Ya ce,"In je ina?". 

Turaki ya ce,"Ka je inda masu hankali suke". 

Bello yayi dariya sosai, dariyar da ke ƙara ƙular da Turaki, ya dinƙa jin wani tuƙwiƙwi a zuciyarsa. 

Bello ya ce,"Don Allah don Annabi ka juyo ka fuskance ni mu yi maganar gaskiya, ka faɗa min cewa ƙarya kake yi, becouse the only Turaki i know ba zai yi wannan haukar ba". 

Turaki ya kallesa yana jin kamar ya bubbuge shi, wani takaicin Bello ya ƙara cunkushe masa a zuciya. Ya ja tsaki kawai ya fice daga motar, Bello na kallonsa ya tsayar da mai napep ya hau suka bar wajen.

Ya tafi ya barsa da tunani kala-kala a cikin ransa, abin da Turaki yayi sam ba na mutane ba ne. Sai kuma yayi shiru yana dogon nazari, to ma...

Sai kuma ya sauke numfashi, da ya sani ya basa damar yi masa bayani dalla-dalla, ƙila ya fahimce shi ɗin, amma duk da haka idan shi ya fahimta ta ya iyaye za su fahimce shi? Da wanne idon ma zai jewa Hakimi?.
Fitowa yayi daga motar ya koma driver seat ya ja motar, yana ta kiran wayar Turaki amma bai picking ba, kuma yasan yana sane, ko da ace ya bisa gida yanzu ba zai taɓa sauraronsa ba, gwara ma ya bari sai gobe sa haɗu, saboda haka kawai sai ya wuce gida da motar tasa.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol