Free chapter · Read without an account

Possessive

by Fatima Rufa'i Nasidi · IMSAL

***


It's fatoumspassion IMSAL 
Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM, INTENSE LOVE, EHSAAS and SCARRED.

Chapter 12

Possessive 

Imsal na tsaye a tsakiyar parlour, 
hannunta har yanzu wani irin rawa yake yi, tana sauke numfashi ahankali, ta riƙe inhaler ɗinta gam ahannu tana rasa dalilin tsoratar datai,
toh mema tayi da take jin tsoro haka ta shiga tambayar kanta
Jin takun sawun sa masu nauyi daga bayan ta yasa jikin ta ya sake tsinkewa kafin ta juya, muryarsa ta sauka a kunnenta yana tambayar ta 
“Wa ya kawo ki gida?”
Cikin wata irin murya dakakkiya wacca bata taɓa jinsa da ita ba, 
Slowly ta juya, idonta aƙasa ta kasa ɗaga ido ta kalleshi kuma akwai yar tazara tsakaninsu don shi yana tsaye ne afarkon falon idonsa jajir, fuskarsa a tsuke,
Hannunsa ɗaya na riƙe da key ɗin mota har jijiyoyin sa sun fito raɗau tsabar ɓacin rai.

 jin bata sake magana ba ya rintse ido yana danne zuciyarsa trying hard to control his anger on her ya sake magana.
“ba tambayarki nake.”
cikin sanyin murya, me ɗauke da gargaɗi aciki,
Wani mugun yawu Imsal ta haɗiye don idan akwai abinda ta tsana arayuwarta faɗa,
da anfara mata faɗa hankalin ta ze tashi, ahankali tace masa
“Na… napep nahau…”
Jin ta kunsa tai da alama ma tsowa yake kusa da ita, ji take duk taku ɗaya na ƙara karfin bugun zuciyar ta,
“Napep?” 
ya maimaita yana kallon gefe yana jin tana harziƙa shi, yace
“Toh me waccan motar fa?”
Da sauri muryarta na harɗewa tace masa 
“Ban… bansan shi ba…”
Idonsa ne yasauka akan fararen hannayenta ta riƙe wani abu aciki gam gam kawai picture ɗin yajja waccan banzan mutumin yake kallon hannun yadawo masa jiyayi ya sake harzuƙa, cikin ɗaga murya yace
“Don’t lie to me, Imsal.”
Haɗiye yawu tai tana sake maimaita masa
“Wallahi bansan shi ba…” 
Shiru yayi ya tsaya yana kallonta closely wannan karan ganin gaba ɗaya ta tsorata se yaji duk ba daɗi kamar be kyauta ba ya ɗan sassauta murya yana faɗin
“Then why was he talking to you?”
Idonta cike da hawaye tace
“Ban sani ba…”
Juyawa yayi yana jin tama gama raina mai hankali ya saka hannunsa a gashinsa yana shafawa trying hard to control his temper
Yace
“Kuma kika tsaya dashi kina magana a gate.”
Nan take ta ɗago kai tana girgiza kai tace
“kawai yace....."
Kafin ta karasa ya ɗaga mata hannu don bama yason yaji abinda ze tarwatsa masa yar nutsuwar sa yace 
“stop Imsal”
Yana kallon hannunta yace
“Meye ya baki?”
Da sauri ta buɗe masa tafin hannunta da har ya fara gumi tsabar yadda ta matse inhaler ɗin da pen tana nuna masa
“Abubuwana ne suka faɗi… ya ɗauko.”
Shiru yayi yana ɗan rintse ido yace 
“Kar ki sake, ”
A hankali ta ɗago kai tana kallonsa da rashin fahimta,
Ya ɗan sunkuyar da kansa kaɗan yana kallonta da wani irin possessive look.
“Kar ki sake tsayawa kina sauraron wani namiji a waje,”
Kamar me raɗa yace
“Kar ki sake bari wani namijin, ya kalli koda fuskar ki ballantana hannunki”
Yadda yake maganar cikin sanyi, 
amman a tsorace take gaba ɗaya ta shiga jinjina mai kai ya ɗan matsa kaɗan yana faɗin 
“Kar ki sake hawa napep daga yau duk inda zakije ki dawo, call me I'll leave everything I'm doing zan kaiki indawo dake”
ɗagowa tai tana kallonsa cikin mamaki wannan karon,
A hankali tace
"Daddy yace....uhmm... Malam garba ne ze ke kaimu, yauma napep ɗinne ya ɓaci shiyasa bezo ba"
ɗan shiru yayi kafin yace
"Whenever irin haka ta sake faruwa call me then, I'll come and pick you"
Jinjina masa kai kawai tai
"And your niƙab ya ringa kasancewa cikin jakar ki whenever kika fito daga school before stepping out of the gate where it"
Sake jinjina masa kai tayi,
Ya ɗanyi shiru kafin yace 
“Because next time…”
Shiru yayi kaɗan yana ja da baya yace 
“…I won’t be this calm.”
A hankali tace 
"Ya mu'allim I'm....."
Bata ƙarasa sorry ɗinba taji muryar Natasha tana faɗin 
"Ya Imsal" 
tana bayan Abdullah don duk conversation ɗinsu akunnenta,
Tsabar takaici yasa tama kasa magana jin zata bashi haƙuri yasa ta dakatar da ita,
"Let's just go upstairs kin dawo naga agajiye kike"
Ta kama hannunta tana  ƙoƙarin janta sama,
"I'm not done talking yet"
yafaɗa ciki kausashshiyar muryar da yasa Imsal cakewa ta kasa bin Natasha, Natasha kasa hakuri tai ƙasa ƙasa take faɗin 
"Wai meye haka bazaki zo muje ba, shi ubanki ne,"
Girgiza kai Imsal ta farayi tana faɗin 
"kije kawai Nats ai nice namai lefi,"
Natasha tsabar takaici sakinta tai aiko ta juya ta koma gabansa ahankali yaɗan tsugunno yana leƙa fuskar ta ganin idanuwanta cike taf da kwalla,
Jiyay gaba ɗaya his feeling guilty amman baƙin kishin dake cinsa ya kasa barinsa yaga gaskiyar dake idonta ahankali yace 
"Inti ʿārifa inni baḥibbik, ṣaḥ"
(Kinsan ina sonki ko)
Jinjina mishi kai tai ahankali ba tareda sanin ta ba hawayenta ya shiga zuba shaaa.
Natasha riƙe ƙugu tai tana kallonsu sama sama takeji a ƙasa ƙasa yake mata maganar, 
hannunsa yasa ya zaro handkerchief daga pocket ɗinsa fari tas ya miƙa mata karɓa tai tashiga goge fuska,
"I'm sorry...."
Shiru ne ya ratsa tsakanin su kafin yace
“I didn't me to shout…I don't know how but sanda na ganshi akusa dake”
Ya cigaba 
“It just… boils inside me.”
Ya ɗan girgiza kai.
“Like I can’t even breathe Babe.”
Shiru Imsal tai tana sauraronsa kamar ba shine yagama masifa yanzun ba, jin batace komai ba yasa yace 
“But that doesn’t mean I don't trust you”
Ya ɗan nuna tsakanin su yana faɗin
"I trust you so much, I trust what we have"
Imsal jinjina kai tayi kaɗan tana cemasa
“Okay…”
Ahankali yace
"Ya umri....ki je ki huta ko we'll talk later”
juya wa tayi a hankali zata wuce yace
“Imsal…”
Tsayawa tai chak tana kallonsa,
Yace
“I love you… so so much.”
Muryarsa very low.
lumshe ido na ɗan second kafin ta sakar mishi murmushi tana ɗaga mishi hannu alamar bye-bye,
shima ɗaga mata hannun yayi kuma bebar falon ba har seda ya dena ganinta.

Natasha dake tsakiya kasa motsawa daga inda take tai kawai don a idonta komai ya wakana jin falon yayi tsit Imsal ta maidata wata timatiri ita da tazo shigar mata har sun shirya tayi tafiyarta yasa ta nufi saman tana faɗin 
"wallahi da sake,"
Ɗakin Imsal taƙarasa directly ta tarar da ita tana cire kaya,
Ta riƙe ƙugu tana faɗin 
"what was that Imsal?"
Imsal bata kulata ba ta cigaba da abinda take,
Natasha tace 
"wai badai uban dokokin daya zuba miki kike shirin bi ba, 
karki sake magana da wani namijin, 
karki sake hawa napep, kullum da niƙab bla bla bla kambalai, 
Imsal he is dictating you fa,
kada so ya rufe miki ido ki bishi blindly yanzun se anyi aure kuma azo ana rigima dashi fa, 
dama ni nasan masifaffe ne ai bansan yana da masifaffen kishi irin haka ba Allah da banbari soyayyar taku takai haka ba, nida ya shigo ma afusace na ɗauka dukan ki zeyi,"
"Natasha please I want to rest, get out of my room,"
tafaɗa tana nufar toilet.

Guri Natasha ta samu tana faɗin 
"wallahi babu inda zanje idan kinga na fita toh kinzo munyi magana,
ni kaɗai ce yar uwarki na fiki experience da maza inban faɗa miki abinda yayi miki just now is not right ba waye ze faɗa miki,
Tsabar ɗan barikine kuma shine ya wani rufe miki baki da tsinannen I love you,"
Bammmmm
taji Imsal tarufo ƙofar toilet alamar ma batajin abinda take cewa wanka ta farayi ta rintse ido sam ita har cikin zuciyarta,
ba taji abinda yayi ya dametan ba don ta fahimce shi sosai kuma ya faɗa mata tuntuni shiɗin mutum ne me kishi, 
so she expect that much from him,
kuma damacan ai ba wai napep ɗin haya suke hawa ba,
so don yace karta ƙara hawa abin baze dameta ba, 
sannan a maganar saka niƙab dama can tana da ɗabi'ar sawa boko ne bata zuwa dashi saboda doka ce amman yanzun ya bata shawara me kyau inta fito seta ringa sakawa kawai don kada irin haka ta sake faruwa.
wani lokacin idan ta fita ba niƙab namiji ya biyota inta dawo gida se taji zuciyarta kamar tana raya mata,
inama itama normal mace ce kamar kowa inama batada irin wannan kyan da ake cewa tana dashi, she wish she can live normally like every other girl ta yadda zatai rayuwar ta without men pestering around her.
ta taɓa having wannan maganar tare da daddy ɗinta har yanzu tana tina maganganun Daddy na cewa 
"ta gode Allah baiwace yayi mata kuma haka yake son ganinta,
shiyasa ya halicceta ahaka, 
sannan Allah baya ɗaurawa bawa kaddarar da baze iya handling ba, 
kuma ta dena ji kamar kyawunta wani naƙasune arayuwarta ta gode wa Allah kartace zata butulce masa da ni'imar kyau da yayi mata cikin dubbannin ni'imomin da ya bata,"
Buɗe idonta tayi tana ƙarasa wanke jikinta tana kammalawa ta ɗauro alwala ta fito da towel ajikin ta ganin Natasha saman gadon ta yasa ta rintse ido tasan maganar zata cigaba da mata,
aiko ilai tana ganinta ta miƙe zaune tana faɗin 
"wai dan girman Allah daba dan na miki magana ba haƙuri zaki bashi?
Yah Imsal naga alamar fa baki biyo halin Mummy ba,
mata zaki rako duniya toh Allah na tuba ai wallahi koni nayi laifin ina mace nasan yadda zanyi manipulating namiji shi yaban haƙurin,"

Imsal gaban mirror ta ƙarasa tana faɗin "laifi namai ya faɗamin yana da kishi tuntuni I shouldn't have talk to the other guy,"
Natasha tace 
"Imsal ayadda naji kuna maganar ainasan bawai zaman hira kikai da gayennan ba nasan fa halinki wama kike saurara banda shi da yayi sa'a na rasa me kika gani a yah mu'allim,
kin liƙe masa ko shegen dogon hancin da gemun da yar farar fatar kike bi eh, 
nagama dai kinfishi kyau da fari da komai,
dani nake da kyan ki da anyi bura'uba wallahi har namiji kamar yah Mu'allim ma zan tsaya in ringa saurara, 
kuma bashida ko sisi likitane ɗan albashi and...."
"Natasha"
Imsal ta faɗa tana juyowa da alama ranta ya ɓaci.

Natasha buɗe baki tai se kuma ta rufe tace "aidole kimin tsawa saboda ni kika raina, 
shi wanda ya gama miki masifa haƙuri ma kika buɗe baki zaki bashi,"
"Natasha you misunderstood him mutumin kirki ne yaya kema kanki kinsani kawai yanada zafin kishi ne,"

"Kawai,
kawai fa kikace"
Natasha ta faɗa tana miƙewa tsaye tace "Imsal wallahi hankali na be kwanta da alaƙarki dashi ba har cikin zuciyata da zaki bi shawarata da kin ɗaga mai visa ya kama gabansa, na tabbata wanda yafishi komai zezo, kuma zama mutumin kirki bashi ke nufin everything kayi aɗauke kaiba anji mutumin kirkine but is he good for you Imsal kinada sanyin hali, Ya Mu'allim nada zafi cutarki ze ringa yi kuma ya dawo yace miki sorry I love you,
ki yanƙare baki hadda mishi bye bye,"
gani tai Imsal ta miƙe ta nufi ƙofa tana gyara ɗaurin towel ɗinta sanin bata fita da towel ko nan da bakin ɗaki yasa tace 
"where are you going yah Imsal I'm not done talking nima, ai shima haka yace miki ga yarsa kuma....."
buɗe ƙofa taga Imsal tayi ta juyo tana faɗin "get out,"
tsayawa tai tai galala tana faɗin 
"korata kike daga ɗakinki donna faɗa miki gaskiya yah Imsal,"
"Out Natasha karna maimaita abinda nace" ahankali natasha ta ƙaraso bakin ƙofa Imsal na tsaye ta haɗe rai rabonta da ta haɗe mata rai irin wannan tama manta a rayuwar ta, don kan kaga Imsal tayi fushi akan abu ana jimawa, tace 
"yah Imsal wai..."
wani kallo data mata yasa ta fito Imsal ta kama ƙofar zata kulle tana jinta tana faɗin 
"In sha Allah bashi zaki aura ba"
Banging ƙofar ta tayi tana lumshe ido ta jingina jikin kofar tabbas da Natasha tasan yadda takejin Ya Mu'allim acikin zuciyarta da bata faɗi waɗannan maganganun akan shi agabanta ba kuma,
she don't know how sweet Ya Mu'allim yake shiyasa take wannan maganar akansa Imsal ta raya aranta.

Komawa tayi ta gama shiryawa tai sallah ta fara shirin islamiyya, tana gamawa ta ɗauki wayarta,
Ganin notification ɗin text tasan shine don da shishi kaɗai suke magana awayar kamar yadda ya buƙata, karantawa ta shiga yi,

"My lady…
I’ll be waiting outside for you.
I owe you an apology… a real one, not just words.
So today, if you’ll allow me, I want the honour of being your driver, willingly, quietly… just to make it up to you.
Let me take you to Islamiyya,
and bring you back safely… the way you deserve."

Tana gama karanta text ɗin ta shiga blushing ta shiga sake karyata maganganun Natasha akansa,
tana wani turo baki kamar yana gabanta cikin shagwaɓa, ta ajje wayar ta ƙarasa wurin window tana leƙawa kuwa taga motarsa na wurin,
da alama tun ɗazun be tafi ba shiga yayi ya zauna kawai cike da excitement ta saka jakar awaya ta fito fuskar ta cikeda nishaɗi ta ƙarasa ɗakin Hajiya,
barci ta tarar da ita tana yi, bata tasheta ba kawai ta zagaya ta tafi ɗakin Mama Zuhra tace mata tatafi makaranta l,
seta dawo Allah ya kiyaye hanya tayi mata, harta nufi waje se kuma ta kalli stairs ganin Natasha bata sakko ba har lokacin yasa ta koma.
Ɗakinta ta nufa ta shiga kwankwasawa 
"Come in*
Natasha ta faɗa daga ciki buɗewa tai ta tsaya daga bakin ƙofa tace 
"kizo mu tafi makaranta,"
Natasha dake shafa powder gaban mirror already tasa uniform juyowa tayi tana faɗin "Malam Garba yace min yana hanya ya taho daga gurin gyaran aibe ƙaraso ba tukunna yanzun mukai waya,"
 Imsal bata kalleta ba tace 
"bashine ze kaimu ba Ya Mu'allim yana waje yana jiranmu kar muyi latti, "
Natasha cikeda mamaki take faɗin 
"kice dokar har zata fara aiki yau kenan
 toh wallahi inzeyi dictating ɗinki,
count me out,
bani ashiga motarsa kije abinki zanbi Malam Garba kawai,"
se alokacin Imsal ta shigo ɗakin tana faɗin 
"Baki fahimce shi bane, 
tun ɗazun fa be tafi ba jirana yake,
Look"
taciro wayarta ajaka tana nuna mata text ɗin karantawa Natasha ta shiga yi kafin ta taɓe baki tana faɗin 
"his just insecure tinani yake inya tafi wanine ze ɗauke ki, nifa duk abinda zaki cemin sedai kice amman bazan shiga motarsa ba Allah kuwa,
kuyi tafiyar ku na taho daga baya,"
Imsal juyawa tai a zuciye tai ƙofa da niyar tafiya se kuma takasa ta juyo tana kallonta tace 
"just this once kinsan zeyi magana inbe ganki ba Nats please his a very nice guy stop hating him,"
Tace 
"ni ban tsane shi ba,
Yah Imsal kinsan da haka,
amman ni abinda yayi yau duk ya fice min arai kuma in halin sane nasan ze sake," ta ƙarasa tana zira hijab ɗinta ta sakko ƙasa imsal biyo bayanta tai tana kiran sunanta seda sukai rabin benan ta juya tana faɗin "yah Imsal ki dena ɓata yawun bakin ki kitafi gurin saurayinki karki sake wani lefin fa,"
Tace 
"Nats..."
 tana ɗan marairaicewa 
"haba mana Please,"
tace 
"ai sanda kika koroni aɗakinki bakisan da wannan ba,
kai bama dole naji bana yinsaba,
his changing you, faɗamin yaushe rabon da ki koreni aɗakinki kora kaca kaca kamar wata mara galihu irin ɗazun, kinnuna min yafini gurinki"
Natasha ta faɗa da karyayyiyar murya cikin manipulation just saboda tanason Imsal ta fahimce ta tasa lagon yat uwar tata tako ina.
Imsal ta shiga girgiza kai tana faɗin 
"kinsan har abada ba nida kamar ki Natasha kefa yar uwata ce,
jininmu ɗaya, Please kiyi haƙuri in abinda na miki ya ɓata miki rai,"
ɗan kallonta natasha tai saboda tausayi take bata sam she's not expose to this world balle halin mutane na asali, yanzun ji ɗan wannan manipulation din datai mata har yayi aiki akanta.
girgiza kai kawai ta cigaba da sauka imsal na bayanta, tace 
"kice masa nayi gaba kawai tunda na rantse"
 Imsal ta turo baki tana faɗin
"yana waje fa tuntuni tayaya ze yarda,"
Natasha tace 
"ba lallai tunda ba gate yake sawa ido ba, nidai bazaki sa na karya rantsuwa taba," Imsal tace 
"amman fa karya kenan Nats"
tace 
"toh karkiyi,
 kije kice masa nace bazan shiga motarsa ba koh ana dolene,"
Juyawa Imsal tai batasan ta ƙarayin faɗa da Natasha kawai ta fito waje ta nufi inda yayi parking motar.
tun kafin ta ƙaraso da yake idonsa na ƙofar entrance ɗin ya fito daga front sit yana kallonta yana murmushi kamar ba shine idonsa kamar garwashi ɗazun ba.

tana ƙarasowa ya ƙarasa gefen me zaman banzan shima buɗe mata ƙofa yayi yana faɗin 
"my lady"
yana ɗan bowing alamar girmamawa murmushi tai tace 
"thank you,"
Ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya buɗe tasa ƙofar ya shiga ɗan wai wayawa yayi yana kallon kofar main entrance kamar yana jiran fitowar Natasha, 
ganin haka yasa Imsal tace "uhmmm...uhmm ya Mu'allim uhmmm ta..ta..fi"
Murmushi yayi yana kwantar da kansa saman steering wheel ɗin, kallonta ya keyi da sauri tasa hannayenta ta rufe fuska tana faɗin 
"Please stop staring at me that way,"
Yace 
"kicema Natasha karta ɓatamin umri ta koya mata ƙarya I know she's still inside,"
girgiza kai Imsal ta farayi alamar a'ah yayi murmushi kawai yana miƙewa yayi ma motar key ya tuƙa.

Malam Haruna ya buɗe musu suka fita a gidan baki ɗaya ahankali yake tuƙa motar yanayi yana juyowa yana kallonta idonta agefe tana kallon titi,
ƙur'ani ya kunna as usual, ya fara bi cikin zazzaƙar ƙira'arsa da yasa ta lumshe ido ta juyo tana ta lafe a kujerar motar dake wani irin kamshi mai sanyaya zuciya, 
yanayi yana juyowa yana kallon ta, zara- zaran gashin idonta gwanin birgewa kamar me barci amman ba barci take ba tana jinsa har suka ƙaraso ƙofar islamiyyar har ciki ya shigar da motarsa.
sunkai minti goma ba ƙarasowa amman bata buɗe idonta ba,
shi kuma be dena kallonta yana karatun shi ba, don sosai kallonta tare da karatun yake bashi wani irin nutsuwa da be taɓa samun irinsa ba akaf rayuwarsa.
 jin tsit yabar karatun yasa ta buɗe idonta shima gani tayi ya juyo dukanshi bangarenta ya lafe saman kujerar yana kallon kawai wata irin kunyace ta kamata tasa hannu ta rufe fuskar tana faɗin "yayaaaa,"
Shima hannu yasa yana rufe tasa fuskar irin yaji kunyar nan yace 
"my babyyyy,"
Turo baki tayi gaba cikin shagwaɓa tace mishi 
"I'm not a babyyyyy"
 ciki ciki sarai ya jita amman se yace
"me kikace"
 girgiza kai ta shigayi ta ɗau jakarta ta sauke niƙab ɗinta tana ƙoƙarin buɗe ƙofa tace bakomai bance komai ba.
jin ƙofar arufe yasa ta ɗan kalleshi murmushi yayi yana faɗin 
"kinmanta ni driver ne,
nizan buɗe miki"
ɗan waro ido tai tana kallon compound ɗin yadda student ke shigowa tako ina don yanzun ake zuwa makarantar ta maƙe masa wiya alamar itadai a'ah be saurari me zatace ba kawai ya fito yana zagayawa ya buɗe mata ƙofar kunyace ta rufeta gaba ɗaya tai ƙasa da kanta yace 
"we are here my lady ko mukoma ciki baki gama kallona ba,"
yafaɗa cikin tsokana yana murmushi da sauri ta fito daidai motar Latifa na shigowa makarantar, 
Ganin ta fara tafiya yasa yace 
"bakiji ba"
 ɗan juyowa tai ahankali ya ƙarasa har inda take be damu ba kawai yay leaning close to here ears yace mata 
"Bin Suhail yana ƙaunar Imsal sosai, ta kula mishi da kanta da kyau,"
jinjina mishi kai kawai tai don gaba ɗaya ya bata kunya gani take kamar duk ɗaliban gurin suna jin me yake cewa,
da sauri ta wuce ƙafafunta har suna harɗewa tai ɓangaren classes shi kuma yana tsaye har Malam sani ya ƙaraso inda yake seda ya dena ganinta ya juyo suna gaisawa.
Malam Sani ya ɗan sosa ƙeya yana faɗin "yau tareda kanwarmu kake Allah yatemaki ya Sheikh"
ɗan jinjina mai kai yayi kawai face ɗinshi na dawowa normal kamar ba shine ya gama ware haƙora agabanta ba, excusing kansa yayi yaja motarsa ya fice amakarantar don yanama the program ɗin daze gabatar 4-5 live.

Latifa jitai kamar ta bishi ta tambayeshi ita meye aibunta daya kasa iya ganin kalar son da take masa da kuma kalar nata kyan se wannan yar mitsitsiyar ya yarinyar.
huci ta shigayi ita kaɗai tana jin inama zata iya data bi ta kanta da mota ta kashe sanda ta nufi hanyar classes ɗinnan yana kallon ta.
wayarta sabuwa dal ta ciro 16pro ta shiga latsawa tana kiran jalila ringing biyu ta ɗaga tana faɗin 
"uwargida kuma amarya agidan Dr kuma Sheikh Abdullah Bin Suhail,"
wani irin murmushi Latifa tai tana faɗin 
"lila har kin kwantar min da hankali kinsan yanzun na ganshi da aljanar yarinyar nan shine ma ya kawota fa da alama,"
Lila tace 
"kice Allah kenan dai maganar Malam ta kusa tabbata, zamusha bikin"
Tace 
"ke ai tunda malamin nan ya faɗamin maganar nan na saki layinsu wallahi bazan taɓa bari karairakin yan tsubbu da boka su hanani kwanciyar hankali ba,
aidama kincemin makaryatane"
 Jalila dake ɗaya bangaren ji take kamar ta tuntsure da dariya jin kalar san zuciyar Latifa saboda taje taji abinda ranta be mata ba shine ta dawo take cewa ma karyatane cikeda ƙeta Jalila tace 
"yanzun kuma,"
Tace 
"lila danabi shawarar ki tuntuni da banyi asarar kudin ticket ɗina ba balle kuɗin dana bawa shegen baya hudannan ya gaya min ƙarya,"
Lila cikeda tsokana tace 
"kefa kikace aikinsa kamar yankan wuƙa kuma kawarki data haɗaku laila tace baya duba wanda baya tabbata,"
 tace 
"ke saki layinsa arnene,
ɗan iska ni idan naga nasamu kuɗima india zanje don bokayean Africa makaryata ne wana irin mutum ne asiri wai baze tasiri ƙaramar yarinya ta gagaresu, wai kinga yadda ya rikice kuwa waita ƙonamai sheɗanun da yake jidasu shi baze ƙara ɗaukar riski ba ko wace kallar ibada takeyi oho,"
Lila tace 
"toh ai Latifa ko azkar ɗinnan da mutane suke wofantar dashi mutum ya riƙe yanayi safe da yammaci kinsan cewa babu abinda ze sameshi kin karanta kuma kinsan da hakan bare ma ita naga basawa ba fitarwa kamar zatai ibada,"
Tsaki Latifa tayi tana faɗin 
"karki ɓatamin rai, aida ta cika kamila me kamun kaida shegiya bata ringa shiga motar saurayi yana yawo da gantali da ita atiti ba, 
waya san ma me sukeyi acikin motar kefa ba'a banza ya haukace yayi mana rashin mutunci akanta ba ƙila dai da abinda take bashi shiyasa kullum yana kusa da ita yayi ta yanƙare baki kenan kamar wani mumu,"
Lila jan numfashi tai kafin tace
"Not everyone is you"
Latifa tace me kikace da sauri ta bagarar tan fadin cewa nai
"zato dai zunubi ne koda ya kasance gaskiya, beauty kinsan yah sheikh mutumin kirkine and kuma har yanzun soyayyar gaskiya fa akwaita tatsakani da Allah..."
"Ke dalla dakata min"
 Latifa ta daka mata tsawa tana buɗe motarta ta fito wayar akunnenta tace 
"se anjima"
 
tana katsewa ta jefa ajaka tafito tana taku ɗaiɗai se tashin wani jahilin kamshi take yi, ta ƙarasa aji gaggaisawa tai da few people ɗin da suke gaisawa ta samu guri ta zauna tana kallon Imsal da Mubeena Suhail sunata ƙus-ƙus jitake kamar taje ta shaƙeta yadda taga Mubeena na dariya rayawa tai aranta ƙilama bata labarinsa take.
tanajin ranta na sake ɓaci, ahaka malamar da zata ɗaukesu first period ta shigo kusan tare suka shigo da Natasha wacca kallo ɗaya taima beauty ɗin ta koma baya sit ɗin da yake na Jalila ada ta zauna tana dakko littafin ta.
Latifa dama taga take taken Natasha tunda ta dawo avoiding ɗinta takeyi kamar wata dodo da alama Imsal ta hure mata kunne akanta ta shiga rayawa aranta.
Ta hura hanci tana faɗin 
"wallahi baki isa ki rabu dani yanzun da ya zama ke kaɗaice ladder na da zan cimma burin da nake dashi akan yar uwarki" malamar tana fita ta juya tana kallon Natasha data dauke kai kamar ma bata ganta ba tace 
"Nats Umar how far?
 baki ganni bane,"
 tabe baki Natasha tayi tace 
"na ganki Latifa se akai yaya?"
murmushi Latifa tayi tana faɗin 
"wai duk fushinne akan abinda akaiwa Imsal,
 nagadai an hukunta mu duka kuma ita wacca akayi mawa ɗin ta hakura,
amman naga kamar kinfita ɗaukar zafi, kumama naga jalila ce tayi ba niba kuma ankoreta,"
Tsaki Natasha tayi tana faɗin 
"sedai ki faɗawa wani bani ba,
 jalilan dake kike juya ta kamar waina, ni gaskiya beauty kawai a cigaba da mutunci ƙawance dai nafasa saboda duk wanda ze iya cutar da Imsal nima ze iya cutar dani yar uwatace, uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya don kinga farko bamu faɗi identity ɗinmu ba, i have my reasons kuma nafaɗa miki badon saboda bana sonta bane ba,"
Latifa jinjina audacity ɗin Natasha take yarinyar da har dar ɗar takeyi inzata mata magana wato Imsal duk abinda take dashi seta rabata dashi hatta da mutuncinta da dayawa daga cikin ajinnan suke gani tunda ya sheikh yaci zarafinsu yayi suspension harda ita shikenan ake mata wani gani gani miƙewa tayi kawai aranta tana faɗin
"I won't let this happen,"
Sit ɗin su Imsal ta nufa daidai ana kiran Sallah, 
Sallama tai musu tana faɗin 
"sannunku!
 Imsal yakike 
sannu Mubeena,"
Mubeena ƙanƙantar da idonta tai tana kallonta da mamaki don tunda ta dawo bataiwa ɗaya daga cikin su magana ba, Imsal ce ta amsa mata sallamar tana cemata sannunta itama,
Latifa tace
"Imsal na zone in ƙara baki haƙuri da abinda ya faru don Allah komai ya wuce afara gaisawa ana mutunci da juna naga kamar baki hakura ba shiyasa ma nake tsoron yi miki magana, "
Imsal girgiza kai tayi tana faɗin 
"Na hakura Allah,
ai tun ranar na faɗa miki,"
Mubeena tai saurin tarar numfashin Imsal tana faɗin 
"ta hakura mutunci kuma babu maganarsa tsakanin mu dake Latifa, gadai ƙawarki can" ta nuna Natasha da tajuyo tana kallonsu tace 
"kuje can ku cigaba da ƙawancen shirmen ku munan ba mates ɗinku bane"
Ta kalli cikin idon Latifa tafaɗa duk kuwa ba wacca Latifa ɗin bata girma cikinsu ba,
Latifa wani irin sad face tayi tana kallon Imsal tace 
"itama Natasha ta dena kulani,
kuma Imsal kinsan wallahi Jalila ce duk ta shirya abinnan da sharrin shaidan dan Allah ko bazaku kulani ba ku,
ki shiryamu nida Natasha inason ƙawance da ita tanada kirki sosai ga hankali ko mamanmu dana bata labarin ki,da abinda ya faru da halayenki tace ke mutuniyar kirkice kuma ƙawance da mutanen kirki ya kesa kazama na kirki,
kuma tunda Natasha kanwarki ce koda bata ɗakko duka halinki ba zata dau wani abun dan Allah kimata magana mudawo yadda muke adacan ta yafemin kuskurene," jinjina kai Imsal tai tanajin duk wani iri ganin babba kamar Latifa wacca ta girmesu tanata bata hakuri tace 
"in sha Allah zanyi mata magana kuma muma komai ya wuce za'a ringa gaisawa in sha Allah,"
Latifa miƙa mata hannunta tai alama suyi musabaha, itama ta ciro nata hannuwan da bata saka safa ba farare tas tana ƙoƙarin miƙa mata da sauri Mubeena ta janyo hannun tana riƙe gamgam tana faɗin 
"Imsal..."
 murmushi Imsal tayi ta kalli Mubeena tace "Allah ma muna laifi ya yafe mana, 
kuma muma yana so mu kasance masu yafiya atsakanin junanmu kuma ita musabaha sunnah ce"
 ta karɓe hannunta cikin na Mubeena tana miƙawa Latifa da sauri ta karɓa suna gaisawa wani iri daskarewa ta kusan yi a gurin tsabar baƙinciki don wani irin laushine da taushi fatar Imsal ɗin take da shi,
da kina taɓawa kinsan koda bata wani aikin wahalar da halitta, don haka duka jikinta yake kamar wata jaririya.
seda Imsal ta karɓe hannunta tana murmushi ahankali ganin Latifa taƙi cikata sannan Latifa ta basar tana faɗin 
"dan Allah kimata magana"
 tace 
"in sha Allah zanyi mata, bari muje Sallah"
miƙewa tayi mubeena ta fice fuuu tana barinta alamar tayi fushi Natasha bin bayansu tai, ta tadda Imsal don Mubeena tayi gaba already tace 
"yah Imsal me beauty take cemiki eh, 
naga tanata wani shishshige miki kardai kisake mata saurayinki take so wallahi," wani irin dammm Imsal taji ƙirjinta ya buga, Natasha ta shiga dariya tana faɗin 
"eh fah rabin rankin dai shi, duk wani makirci da zatazo miki dashi fall for it,
 Allah sedai kiji ana shafa musu Fatiha da ita ki kula,"
 tana gama faɗar hakan tai gaba ganin Imsal kamar bata sauraron ta batasan tana jiba ta kasa digesting maganar ne, har aka idar da sallah Mubeena bata kula Imsal ba seda aka fito za'a koma aji ta riƙota ta faɗin
"Kiyi haƙuri mana kefa matsalata dake zuciya,
 yanzun daga ɗan wannan abin seki share ni,"Mubeena tace 
"ba dole na share ki ba,
ina nuna miki gabas kina yamma,
Latifa fa munafuka ce ba abar yarda bace" atoh nasan akwai abinda take ƙulla wa, Imsal tace 
"wai mena mata ne dazata ƙulla abu akaina eh, kuma naga Natasha takeso na shiryasu kuma nace mata zan shiryasu so kike na karya alƙawari kuma babu kyau ko mutum yana abu mara kyau in ya tuba acigaba da tsangwamarsa ana kyararsa hakan zesa ya koma ya cigaba da aikata ba daidai ba Mubeena kinsani"
jinjina kai Mubeena tayi kafin tace 
"i just don't trust him ne,
 kawai.... imsal da tasan ma keda yaya kuna tare ne da se nace ƙila don tana sonsa take so ta shigo jikin ki tamiki wani muguntar"
Kmsal tsayawa tai chak tana kallonta Mubeena juyowa tai ganin bata binta tace "lafiya Imsal"
ahankali Imsal tace 
"ɗazun ma natasha tace tana sonshi da gaske sonshin takeyi wai,"
Mubeena ganin kamar hankalin Imsal na ƙoƙarin tashi yasa ta wani riƙo ta tana faɗin "ke karwani ki ɗaga hankalinki,
toh se meye don tana sonshi mata nawane suke sonsa the important thing shine ke ya keso Imsal, kece yazaɓa kuma he can die for you ina faɗa miki, so don't trust Latifa easily,"
Numfashi kawai Imsal taja tana rasa me takeji dangane da Latifa aranta amman har lokacin bataji wai ta tsaneta ko makamancin hakaba, kawai dai taji she's confused don ita batasan ma meye ƙiyayya arayuwarta ba, batasan yadda ake jin ƙi ba.

"Muje aji, kada Malama iklima ta shiga ta fara bala'i mun makara"
ahaka suka ƙarasa aji yau karatu kawai ake don ko rarar period ba'a samunba haka 5:30 nayi aka tashesu.

Natasha karasowa tai gurinsu Imsal da suka miƙe kowacce ta rataya jakarta suna shirin fitowa tace 
"toh ya?
 yah Imsal zaki bini ne ko sabon driver ɗinkine zezo ya maidake eh?
Wani kallo Imsal tai mata kafin tace 
"Nats banson irin wasannan?"
Natasha dariya tayi tace 
"bafa nice nace mai driver ba shine ya rubuta ba,"
 da sauri Mubeena tace 
"wait
 wait 
what am I missing?"
Daidai Latifa na yowa gurin da niyyar yi musu se gobe, taji Natasha na faɗawa Mubeena
"yayanki mana waishi Romeo,
 haka yace wai yazama personal driver ɗinta bla bla bla zancensu dai na masoya waishine zena kaita ya ɗakkota ko ina"
tana sane tafaɗa saboda taji kamshin turaren Latifa daf dasu, 
Mubeena Suhail wata shewa tai yadda kikasan ba'a islamiyya suke ba ta zauna saman desk tana faɗin 
"wai yayan ke dan Allah, love wan tintin"
Natasha tace 
"wallahi ke bakiga text ba, ɗazun ni da aka kusa makantar dani da sukai faɗansu na masoya kinga yadda yake lallashinta ana wani canza ya rirrika from hausa to English to arab yana cemata ana sonta,"
Mubeena cikeda excitement take faɗin 
"don Allah Imsal nunamin text ɗin Please" Imsal maƙalƙale jakarta tai tana faɗin "bazan ƙara nuna miki komai ba Natasha tunda bakida sirri,"
 Natasha dariya ta shiga yi da gayya take faɗin 
"ai Mubeena ce ba bare bace,
daman can balle yanzu da zamu zama in laws yan uwan juna tie by marriage kinsan kuwa shine strongest bond"
taƙarasa tana karɓe jakar Imsal da duk tabata kunya donma dai yan ajin duk sun fice tace 
"bari kiga"
ƙoƙarin karɓe jakar Imsal ta farayi tace 
"akwai dai ƙur'ani aciki maza,jani da kokawa yafaɗi,
alhaki akanki"
da sauri Imsal ta sakar mata ta ɗan yi gaba ta buɗe tana ciro sabuwar wayar imsal tace "kingani 16 pro ɗinnan ma shine ya siya mata, yah Imsal tasamu majnun ɗinta sauramu Mubeena,"
Tanajin takun Latifa yadda ta juya tafice a ajin.

juyawa tai tana sakin wani murmushi irin na satisfaction se yau taji ta ramawa yar uwarta abinda sukai mata har ranta, Imsal karɓe wayarta tai don hankalin Natasha ya koma kan ƙofa, tasa ajaka itama ta juya don facing wall sukeyi shiyasa ma su basu ganta ba tace 
"nidai natafi se anjimanku,"
Mubeena tace
" akwai gobe Imsal wato kinga masoyi shine ni yar rakiyar ki har gaban napep ɗin Malam garba kika tafi kika gujeni koh," Imsal har takai bakin ƙofa ta ɗan leko ajin tace mata 
"eh ɗin kuma sena faɗa mishi duk abinda kukaimin"
 ta ƙarasa tana dariya tayi gaba abinta feeling very happy ganin kamar Natasha tasakko daga fushin datai da Abdullah.

Mubeena cikeda farin ciki ta kalli Natasha tana faɗin 
"she looks so happy, 
na daɗe banga imsal tana dariya haka ba that means yayana is very lucky she really love him,"
Jinjina kai natasha tai kafin ta juyo taci serious tace 
"but she's not lucky Mubeena,
 his too hard,"
Mubeena jan numfashi tai kafin tace 
"he love her,"
Natasha tace 
"i know and bance bayayi ba he's just hard, jikina yana bani kawai their relationship will not work yayanki will ruin it,"
Da sauri Mubeena ta shiga kallonta tana faɗin 
"he won't you have no idea how much Imsal mean to him nasan yana da faɗa and all that amman his very soft from inside Natasha nasan yayana he will never hurt her,"
Natasha murmushi tayi tana faɗin "physically yes he won't,
but emotionally a yadda na ganshi ɗazun..."
 ta ƙarasa tana tafiya da baya da baya 
"He will definitely fuck up,
one way or the other,
 mata masu irin kyan Imsal se ana musu uzuri dole maza su kallesu,
Kuma basu da power ɗin controlling wannan kuma shi baze taɓa gane hakan ba"
tana ƙarasawa ta fice a ajin baki ɗaya tana bari Mubeena da tinani me take nufi da abinda tace.

Imsal na fita motarsa na shigowa harabar makarantar, ta tsaya,
har gabanta motar ta ƙaraso ya fito as usual not minding bunch of Students dake ta kai kawo ya buɗe mata ƙofar gaba ta shiga tana ce masa 
"thank you"
 ya zagaya ya shiga motar ta lura ba kayan ɗazun bane ajikinsa da alama kafin ya fita yaje gida yayi wanka ya sauyasu don manyan kayane jikinsa wannan karon taga ma kamar hadda babbar riga abayan motar da hula wanda da alama cire su yayi,
Jan motar yayi suka fara tafiya,
Ahankali muryarsa aƙasa ya shiga tambayarta 
"ya karatu,"
"Alhmdllh"
tace masa tana kallon titi,
Yace 
"Masha Allah me dame aka biya mana yau, akoyama yaya"
ɗan kallonsa tayi tana faɗin 
"Kai..."
da alamar mamaki yace 
"eh mana Ya Mu'allimati na,
ya kamata nima nafara ɗaukar darasi agurin ki"
girgiza kai tayi kafin tace
"aiduk ka iya,"
Murmushi yayi yana faɗin 
"nidai ban iyaba se kin biyamin,"
Turo baki tai kafin tace 
"nima fa ban iyaba,"
Yace 
"oh rowar ilimin za aima yayan kenan,"
Gyaɗa kai tayi alamar eh idonta aƙasa dariya yayi yana faɗin 
"eh fa kikace Imsal bakyau fa"
murmushi tayi tace 
"aikaima bakyau mutum ya iya abu kuma yace asake koya mishi"
yace
"inji wa,"
Ɗan jim tayi kafin ta nuna kanta yace "enyeeeeee inji Imsal"
 jinjina masa kai tai cikeda kuruciya yace "ɗan yimin Please"
 yana juyowa yana kallonta tace
" toh kadena kallona se nayi"
yace 
"ba laifina bane, idonane baya iya jure second ɗaya in kina kusa seya kalle ki, it can't resist your beauty"
 hannu tasa tana rufe fuskarta tana murmushi ƙasa ƙasa shima murmushin yake yi yace 
"inajin ki,
amin karatunnan inji, hadisi ne farko ko?
wanne kuka karanta yau lamba na nawa?"
Ahankali tace 
"Muwaɗɗa Maleek mukeyi,
Riwayat Yahya al-Laythi, kuma muna Kitabbuzzakah, Babin zakatul fitr, Hadisi mai lamba ɗari da tamanin da ɗaya,"
Jinjina mata kai yayi yana faɗin
"ina jinki karantamin hadisin ki fassaramin" rufe fuskarta tai tana faɗin 
"ya Mu'allim kafa iya"
 turo lips ɗinshi yayi naƙasa cikin kwaikwayon ta yace
" a'ah Ya Mu'allimati ban iyaba faaaa, Please ki karantamin,"
Turo baki tayi tana sauke hannunta idonta aƙasa tace 
أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ ﷺ فَرَضَ زَكَاةَ الْفِطْرِ مِنْ رَمَضَانَ عَلَى كُلِّ حُرٍّ أَوْ عَبْدٍ، ذَكَرٍ أَوْ أُنْثَى مِنَ الْمُسْلِمِينَ، صَاعًا مِنْ تَمْرٍ أَوْ صَاعًا مِنْ شَعِيرٍ

Jinjina kai yayi yana murmushi cikin wani irin jin daɗi da gamsuwa don daidai tayi yace 
"Ya Mu'allimati gashi ɗalibin naki bayajin larabci menene ma'anar hadisin"
ɗan kallonsa tai tana Rolling eyes ɗinta wanda yasa ya tsayar da motar chak gefen hanya ganin tuƙin na ƙoƙarin kwacemai da sauri Imsal ta kalleshi tana faɗin 
"are you okay?"
ɗan jinjina kai yayi ahankali yana faɗin "don't do that again please,"
A mamakance ta ɗan kalleshi tana faɗin "yaya menai?"
Yace 
"your eyes, that roll zasu saka muyi hatsari fa"
wata irin kunyace ta kamata ta wani ja gefe tana cukuikuye fuska cikin hijabinta, murmushi yayi ƙasa ƙasa tanajin ya tada motar yace 
"my babyyyy baza'a fassaramin hadisin ba" shiru tai mishi yace 
"Please ki ƙarasa ladanki ya umri..."
Yanajan riiii ɗin cikin hijabin yaji tace 
"yana nufin,
Lallai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya wajabta zakka ta fidda kai (Zakatul Fitr) a watan Ramadan a kan kowane Musulmi, ƴantacce ko bawa, namiji ko mace, ya bayar da sa’i guda na dabino ko sa’i guda na sha’ir (hatsi irin alkama ko gero)."

Jinjina kai yayi yana jin kamar ya haɗiyeta don soyayya ya huta,
Slowly yace 
"I'm very proud of you,
Imsal ashe har yanzun akwai kaifin haddar nan dama kece ba kisa wasa akanki ba, tun kuna yara duk abinda aka biya kin haddaceshi,
Masha Allah kice yarana sun more uwa ta gari abar alfahari"
 jin abinda yace yasa ta ƙara kunshe fuska, jin shiru sunata tafiya yasa ta ɗago tana kallon titi se alokacin ta lura ba hanyar gida sukai ba sun bauɗe ɗan kallonsa tayi tana faɗin 
"ya Mu'allim ina zamuje nanba hanyar gida bane"
 ɗan murmushi yayi yana fadin 
"zuwa zanyi na saida ƙwaƙwalwarki kinsan kina ja sosai tsada zatai senayi kuɗi," murmushi tai tana maƙale masa wiya tace  "Please ina zamuje, nidai mutafi gida"
daidai suna tsayawa gaban wani babban eatery me haɗe da bakery, kallonta yayi ya nuna mata cikinsa yayi kalar tausayi yana faɗin 
"yunwa 
tun safe banci komaiba basu bani abinci ba,"
"Ayyah sorry...."
 tafaɗa tana kallonsa cikeda tausaya,
Yana mamakin how naive she is, yanzun kalli yadda tai kalar tausayi tana kallonsa kamar itace bataci abincin ba,
Yace 
"Ƙawarki bata iya abinci ba,
aunty salma kuma oppressing ɗina takeyi tabata tayi tasan kuma banaci, shiyasa zanyi aure na huta kinga matata ai zata kula dani koh,"
 jinjina kai tayi tana juya mishi baya murmushi yayi yace
"bazaki barni da yunwa ba ko umri,"
Jinjina mishi kai tayi yace 
"zaki kula dani koh"
 jinjina mishi kai tayi, yace 
"muyi aurenmu koh"
yana dariyar tsokana ƙasa ƙasa jinjina kai tai da sauri kuma ta shiga girgiza, don seda ta gyaɗa ta gane metai murmushi yayi yace "soon babyn yaya,
 nasan dama bani ka ɗaine nakeson muyi aurennan ba,
 Daddy kawai nake jira ya dira ƙasarnan baze koma.ba sai ya ɗauremu da igiya uku" da sauri ta shiga girgiza kai ganin duk ya bata kunya yasa ya buɗe ƙofa yana faɗin "bari nai sauri naje naga maghrib ya gabato karna maidake dare yayi na amsa query ace anfasa bani"
 yafaɗa yana referring to Rayyan ya fice ya wuce cikin eatery ɗin.
kallon titi ta shigayi don ya rufe motar, can ta hango shi da ledoji da yawa ahannunsa ya ƙaraso ya bude gidan baya ya matsar da babbar rigar sa da hula ya ajje ya dawo gaba yana kallonta yace 
"sorry to keep you waiting my lady"
murmushi tayi tana faɗin 
"ba komai,"
jan motar yayi ganin ankusa kiran maghrib a high speed suka ƙarasa.
daidai ana kiran sallar maghrib horn yayima Malam Haruna ya buɗe musu gate yayi parking ƙofar main door.
da sauri ya fito yana buɗe mata ƙofa, fitowa tayi ya buɗe baya ya ciro wasu daga cikin ledojin yana bata yace 
"take it"
ɗan kallonsa tai, 
Girgiza kai zatai ya ɗan ya haɗe fuska yana faɗin 
"Please don't argue ya umri,
sallah karnai missing jam'i"
 jin haka yasa ta karɓa ya rufe ƙofar ya koma cikin motar yaja ya fice agida that means tasan baze dawo ba kenan.

It's fatoumspassion
Don't forget to 
Like 
Share 
Vote
Comment 

SPECIAL ANNOUNCEMENT 
Ina farin cikin sanar muku cewa zan fara posting sabon novel dina IMSAAL a ArewaPen da Wattpad 🤍

But don’t worry… WhatsApp readers are still my priority 🫶🏽
Nothing is changing here, this is still home ❤️
To celebrate this, I have something special for my real supporters 
🎁 The FIRST 20 PEOPLE to:
✔ Follow me on ArewaPen
✔ Follow me on Wattpad
Will get FREE entry into my paid WhatsApp group 💫
🎁 HOW TO QUALIFY 🎁
After following me,
📌 Take a screenshot showing you’re following me on BOTH platforms
Then send it to me on WhatsApp 👇
📩 ***
⚠️ Include your username
⚠️ Only the first 20 valid people will be accepted
⚠️ No screenshot = no entry 👀
ArewaPen @fatoumspassion
Wattpad @fatoumspassion
Hurry… once the 20 slots are gone, that’s all 🔥

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol