Free chapter · Read without an account

PAGE 71 - 75

by SultyWrites · MATAR SADAM




Su najwa sun shiga rudu dan a kullum abin Kara daure masu Kai yake saisa suka yanke shawarar samun daddy akan hakan sai dai daga reaction din sa kawai yasa sukayi loosing courage   .

damuwar da seenah tasa a ranta ya janyo mata rama sosai dama ba wani auki bane da ita sai wani fari data Kara kamar wadda tayi rashin lpy.

A haka ta samu suka gama exams suka karbi results saidai wanna Karin saboda damuwar da ta sawa kanta ita ta dauko third  najwa kuma second , bata wani damu ba kawai ta ajje results din domin damuwar ta yanzu tafi Mata ta results din.

Umma kuwa ba haka taso ba domin so tayi seenan ta koma kauye tare da red card dinta a hannu amma tasan ana daf dayin hakan tunda taga yadda suke treating nata.

Abubuwa sai Kara gaba suke har takai yanzu fitowa parlour ma ya fara gagarar ta kullum tana daki saidai taci kukan ta ta koshi ta roki Allah daya kawo Mata mafita ya fidda ita cikin wanna halin ya kareta daga tuggun umma domin ita yanzu kuma hankalin ta ya koma Kanta ganin yadda take nuna mata tsana Kiri² hade da jifanta da bakaken maganganu wadda yasa ta dasa ayar tambaya akan hakan , ganin bata da wata shaida ya sata jan bakin ta ta tsuke.

Yau tun safe seenah bata fita ko parlourn sama ba tana daki ko breakfast da lunch ma najwa ce ta kai Mata sai can dare ta dai daici lokacin tashin su daga hira sannan ta fito saidai Mai tana sauka taga sadam da Adnan zaune sai najwa data fito daga kitchen juyawa tayi zata koma kawai taji an fisgo ta tagal² tayi zata fadi kafin tayi sa'ar dafe bango tare da Kallon sadam dake tsaye Yana huci kamar namijin zaki , Introduction ya fara Mata da wasu tagwayen maruka da saida taji gaba daya jikin ta ya dauka sannan ya dora da

"sau nawa zan fada miki idan ina waje Karki sake naga wanna kafafun naki a wurin ko inuwar ki bana kaunar gani bare wanna mummunar fuskar taki na tsaneki na tsaneki amma ke kullum naiman matso da kanki kike kina neman cusa kai wajena ni ban taba ganin marar zuciya irinki ba ance ba'a sonki ba'a son ganin ki amma baki ji ba to kici gaba zan baki mamaki kuwa wawuya kawai marar zuciya"
Yana gama fadar haka ya juya ya bar parlourn gaba daya.

Da gudu najwa ta jefar da robar ruwan dake hannun ta tayi kanta ganin yadda take sauke numfashi kamar wata mai asthma da sauri Adnan daya daskare a wajen shima ya nufe su yana fadin najwa miko Mata ruwa da sauri , sakin ta tayi ta wuce dan daukan ruwan data yasar a parlourn .

Tana sakin ta ta sulale a wajen ta rasa a duniya take ko a lahira hawaye take so ya zubo amma yaki wanna wani irin tashin hankali ne ta fado cikin sa addu a kawai take ba tare da tasan mai take fada ba har najwa ta dawo riqe da ruwa ta riqo hannun ta ta tashe ta zaune tana Mai  rungumeta ta saki kuka , cikin kuka ta kalli Adnan da yake shima a dan rikice tace "ya adnan Ka Kira su nina muje asibiti I'm scared baka ji yadda zuciyar ta ke bugawa da sauri² ba kar wani abu ya sameta .

gaban su ya dawo yana fadin seena ! Seenah kalle ni nan "kisani seenah kowani bawa da irin tasa jarabawar a rayuwa sai dai ta wani tafi ta wani kiyi hakuri ki karbi taki da hannu bibbiyu kisa hakuri a zuciyar ki ki ci gaba da addu a in sha allah Allah zai kawo maki mafita, nasan kina hakuri amma ki kara ki daure nothing is permanent wata rana komai zai wuce sai labari .

sai a lokacin taji wani kuka yazo Mata nan ta fara rairashi kamar ranta zai fita najwa na taya ta , tashi yayi ya koma Kan kujera ya dafe Kansa yanajin duk ba dadi dan yanzu gidan nasu gaba daya ba wata walwala irin ta da
" allahumma ajirni fi musibati ya allah kasan halin da wanna baiwar taka take ciki Allah Ka kawo Mana mafita Ka kawo karshen wanna matsalar.

sun dade a wajen har saida ta daina kukan ta koma ajiyar zuciya tukun na yace da najwa " tashi ki kamata ku tafi daki .

Sai da ya raka su har dakin sannan ya nufi part din su zuciyar sa cike da tausayin seena shi dai a iya sanin sa baisan wani laifi mai girma da seena ta yiwa su daddy ba balle kuma shi sadam , a parlourn ya ganshi yayi shuru TV na aiki shi kuma yana kallon wani wuri daban cike da jin haushin sa ya wuce ba tare daya masa magana ba .

Kwana biyu tsakani sadam ya bar kasar, haka rayuwar gidan ta ci gaba da tafiya ba wani walwala irin na da.

A haka suka fara shirye shiryen komawa makaranta .

zaune suke itada najwa a balcony suna yar hira afnan ta iso wajen najwa ce tace Affy daga ina kike hakan nan yau kwata² ban ganki ba? 

" ummm whl yau ban tashi da wuri bane sai yanzu na fito dama daddy ne yace in kiraku keda seenah , " okay Thom kice gamu nan zuwa .

Afnan na barin wajen najwa ta dawo da duban ta ga seenah wadda har ta tafi duniyar tunani saida ta tabo ta sannan ta juyo tana fadin " magana kike ne naj ? " Hmmmmm ki tashi muje daddy na Kira ganin tayi shuru ta tsaya kallon ta yasa ta cewa odahalf !!! , tashi tayi ba tare da tayi magana ba tayi ciki itama najwan tabi bayan ta jiki a sabule.

A part dinsa suka same shi shida Adnan karasawa sukayi cikin parlourn suka zauna yayin da seenah ta koma gefe ta rakube can nesa dan yanzu taka tsantsan take da su , cikin kulawa Adnan yace seena dawo daga nan mana kya koma can ki zauna, murmushi tayi tare da fadin " umm ummm ya adnan nan ma yayi .

daddy ne yace Adnan mika musu kayan , wata leda ya dauko mai dan girma ya mikawa najwa dake kusa dashi shi kuma daddy ya daura da fadin " emir ya bukaci a cire ku daga GAAT tun a wancan lokacin amma ganin kuna a third term ne ya sani ce masa ya bari sai zaku shiga SS 2 to yanzu an canja maku wata , uniform din ku da duk abinda zaku bukata na amfani Yana cikin ledar nan ran Monday zaku fara zuwa , kuna iya tafiya.

  Godia sukayi sannan suka tashi suka koma daki cikin zumudi najwa ta fara zazzage kayan ita dai seena gefe ta koma ta zauna tana kallon najwan .

"laaa odahalf kinga wanna uniform din wando ne najwa ta fada tana daga Mata kayan dogon wando ne black sai grey riga long sleeve wacce zata iya kaiwa kusan guiwa mai igiya daga ciki kamar belt sai black half sunnah hijab Wanda ya Kai musu har ciki, murmushi kawai ta Mata ba tare da tace komai ba ajje kayan tayi ta karasa kusa da ita ta zauna tana fadin
" odahalf zamu yi missing GAAT wallahi amma ai nasan nan ma zamuyi new friends nifa har Allah Allah nake Monday ma tayi, murmushin ta sake yi " Allah ya nuna mana naj anjima ma sai Allah ya yadda bare kuma Monday wasu na can suna planning akan abinda zasuyi gobe amma sai kiga gobe tazo basa raye shuru najwa tayi ta zuba Mata ido ba tare da tace komai ba ita kuma ta tashi ta wuce bathroom.

A Haka suka gama first term suka shiga second, kamar yadda ta saba wani lokacin idan dakin ya isheta takan komawa can bayan gidan ko cikin garden ta zauna to yau ma hakan ce ta kasance ganin duk su najwa suna kokarin fita wajen Malam karatu ya sata cewa najwa din kanta na ciwo suje kawai zata dan kwanta dan ta san ko taje ma ba wani abu zata iya ba ko ya kara Mata ma bata iya haddar balle a kara wata saisa ta rage fitar ma .

Zaune take cikin flowers dinda ke wajen ta daga kanta sama tayi shuru tana tunanin yadda abubuwan suka cakude mata lokaci guda.

Umma ta hango ta fito ta kofar baya tana ta dube² , Kara shigewa tayi cikin flowers din yadda in ba kusa da ita kaje ba baza ka taba zaton akwai mutum awajen ba .

Can karshen bangon gidan umma ta nufa Inda bululluka ke ajje na saman ta daga dakyar tana nishi ta leqa ramukan sannan ta maida bulon yadda yake tana waige² ta karkade hannunta ta wuce, da kallo seenah tabi ta har ta shige ajiyar zuciya ta sauke taci gaba da tunane² har kusan lokacin tafiyar malamin su sannan ta tashi dan tasan Idan najwa ta koma daki bata ganta ba saita biyo ta.

Harta fara tafiya sai kuma hankalin ta ya dawo kan mai umma take nema acan komawa tayi da baya ta nufi wajen kokarin daga bulon ta fara amma ta kasa hakan ya sata turashi da karfi ya fadi gefe  ,  leqawa tayi cikin ramin bulon amma ba taga komai ba sai wata leda harta juya zata tafi sai kuma ta dawo ta tattaka ta zura hannunta ciki ta dauko ledar tana kokarin zamo hannunta abunda ta taka ya goce su Kayi gefe da ita da bulullukan.

Tashi tayi da kyar tana karkade jikin ta kamar za tayi kuka ganin yadda taji raunika a hannun ta, ledar ta dauka tana kallo ta yaga bakin dan kullin da aka masa bazai kuntu ba, wasu Yan kananan kusoshine suka zubo kasa a take kuma suka koma bakaken itace cikin firgici tayi baya da sauri , mai Kenan ta yiwa kanta tambayar da bata da amsar ta, wata zuciyar tace aikin umma mana hmmm ganin Kar wani ya shigo wajen yasa ta miqa hannun bakin ta dauke da addu'a da sauri ² ta debe itatuwan tayi wajen su inno Inda suke nasu girkin na masu aiki a boys quarter .

Bata samu kowa ba awajen hakan yasa tayi saurin zuwa gaban murhun ta tsugunna tare da yin bismillah ta cusa itatuwan gaba daya har saida taga sun cinye sannan tabar wurin.

Tana shiga ta wuce toilet tare da yin sama da hannun rigarta ta fara wanke raunikan da taji ta goge da towel sannan ta fito ta dauki farar powder ta fara zazzagawa a wajen najwa ta shigo da sauri ta karasa kusa da ita tana tambayar meya ji mata ciwo ganin yadda duk ta rikice tana mata tambayoyi ya sata riko hannun ta suka koma bakin gado ta zaunar da ita sannan ta karbi al qur'ani da sauran littafan dake hannun ta ta ajje a bed side drawer ta dawo kusa da ita ta zauna tana fadin ni kuwa naj in tambayeki  mana ?

" inajin ki maiya faru ? 
dan shiru tayi kamar mai nazarin abinda zata fada sai kuma tace naj ni akwai wani abune tsakanin Nina da umma ina nufin tun da dadewa, ajiyar zuciya najwa ta sauke sannan tace a gaskiya odahalf ni bansan da wani abu a tsakanin su ba, ni dai kawai na taso naga umma najin haushin nina kuma umma bata da hali whl kwata² she's not that nice kuma ko gaban nina bata shakkar kyarar mu, ni kaina ina karama nasha duka wurin umma amma nina bata taba kula ta ba kuma ko a fuska bata taba nunawa daddy ba bare ta fada masa saboda kwanciyar hankalin sa dukda kuwa ko a gaban idon sa ne umman bata shakkar yaba wa nina magana amma ita ninan saita maida abun Wasa, toh ni dai iya abinda na sani kenan ban kuma sani ba ko kafin a haifeni Ajiyar zuciya seena ta sauke 

najwa tace but why do u asked me this question ? 

" kingane ne naj I'm suspecting something ko kuma ma In ce idona ya nuna min amma kiyi hakuyi bazan iya sanar maki a yanzu ba sai nayi verifying.

"Allah yasa muji alheri .


*********************

Suna sallar Isha nina ta shigo ta zauna tana kallon su har suka sallame seena dai bata motsa ba bata kuma kalli Inda ninan take ba gudun kar tayi laifi sai kawai taci gaba da addu'o'in ta najwa ce ta mike tare da cire hijabin ta tana kallon ninan tace nina wani abu kikeso ne ganin ta zubawa seena Ido ko kyaftawa bata yi .

    baby!! Nina ta fada idonta na cikowa da kwalla dagowa seena tayi tana kallon ta , Mika Mata hannu tayi alamar tazo gareta kallon najwa tayi tai mata alama da taje din mikewa tayi takarasa gaban ninan tana kokarin zama wajen kafar ta ninan ta riqo hannun ta tare da rungume ta wani kuka ne ya taho mata ta kara rungume ninan .

" I'm so sorry my daughter kiyi hakuri kiyafemin kwata ² na rasa dalilin da yasa nake maki abinda nayi nakan zauna inyi tunanin why am I doing all this amma in har zan ganki bansan me sa ba kawai sai naji raina ya baci zuciya ta na zafi kamar kinmin wani babban laifi dan allah kiyi hakuri ba yin kaina bane.

dagowa tayi tare da sharewa nina kwallar tace 
" ninata baki mun komai ba koma kin min na yafe maki tun ma kafin kimin dan Allah ki daina bani hakuri ke uwatace cikin wani irin so da kauna da kuma tausayin yadda taga seenan ta koma tace dota bakida lpy ne murnushi tayi tana share wasu kwalla masu zafi da suka sake zubo mata tace ah ah nina lafiya ta kalau najwa da tayi tsaye cikin farin cikin ganin nina ta dawo kamar yadda take a zuciyar ta take addu'a allah yasa hakan ta kasance a bangaren daddy ma  .

Gaban su ta karasa ta zauna tana fadin "Nina damuwace kawai kullum bata da aiki daga kuka sai tunani ko abinci bata ci sosai mikewa nina tayi tare da fadin " kuzo parlourn daddyn Ku yanzu ta karashe tana barin dakin ,dole ta samu daddy suyi magana akan hakan dan she feels like they made a big mistake duk da ta rasa ya akayi hakan ta faru .

Nina na fita najwa tayi tsalle ta rungume seena tana dariya tace Allah alhamdulilah odahalf in sha allah matsalar ki ta kau dama masu iya magana na fadin maharkurci mawadaci .

"naj daddy fa ? 

" karki damu in sha allah komai zaiyi daidai tunda kika miqa komai naki ga Allah toh in sha allah Allah zai kawo maki mafita, ba kiga yadda nina ta canja lokaci daya ba , kamar wadda ta tuna wani abu tayi zumbur ta mike
" naj Anya kuwa ba abinda nake tunani bane ya tabbata .

" Mai Kenan? 

Komawa tayi ta zauna tare da fara bawa najwa labarin abinda taji umma na fada tun daga farko har zuwa yau saidai ta boye abinda ya faru tsakanin ta da umman ranar data Kira ta dakin ta da kuma dambun data hana sadam ci , zabura najwa tayi ta mike dafe da kirjin ta tace
" yanzu seena  kinsan da wanna zancen kikayi shuru bafa karamar matsala bace ai irin wanna da wuri ya kamata ki fada a dau mataki tun kafin abu ya kwabe.

" naj calm down banida wani evidence akan hakan ko da na fada kunne nane kawai yaji amma yau nagani da idona kuma na tabbatar domin ganin wanna sudden change din ma daga nina ya isa bamu answer amma yanzu ba zamu kara confirming ba sai munga daddy dan haka tashi mu tafi .

Kusan a tare suka shiga part din daddy tare da nina a Kan pray mat suka same shi Yana karatun al qur ani, sallama sukayi hadi da karasawa suka zauna a kasa yayin da nina ta hau kujera.

Saida yakai aya sannan ya dago da murmushin yana kallansu yace yan Albarka akwai abunda kuke so ne? najwa ce tace ah ah  daddy kawai munzo mu tayaka hira ne kallon seena yayi yana fadin mamanah wai haka , murmushi jin dadi tayi tace Nima haka daddy .

" to naji dadi Allah ya muku Albarka da ameen suka answer sai kuma najwa tace daddy dama inaso muyi wata magana Amma ina tsoro da sauri seena ta kalleta tare da mintsinin ta amma ta shareta .

" go ahead my dear hope ba wata matsala bace.

" toh dama daddy rannan ne naje part din umma Zan karbi story book dina wajen Afnan shine naji......... Duk abinda seena ta fada Mata ta kwashe ta fada masu har abinda ya faru yau amma ta boye cewa seenah ce taji kuma tagani .

Nina ce tayi saurin fadin " ke najwa bansan maganar banza kina yar karamarki har kinsan ki hada abu irin haka yaushe kika koyi wanna halin banzan .

" wallahil azeem nina ba karya nake ba duk abinda na fada akan umma haka ne, daddy ne ya tare zancen da fadin kinga tashi kuje najwa amma kar naji maganar nan a bakin kowa ku dai ku cigaba da addu a domin itace makamin mumini .

" in sha allah daddy dama munayi amma zamu Kara dagewa najwa ta fada tana tashi seenah ma tabi bayan ta suka fice .

Suna fita tace  " naj Mai sa zakiyi haka waya ce ki fada masu yanzu ke wai mai sa ba'a sirri dake ne , tsayawa najwa tayi tana kallon ta har tayi shuru sannan tace " we have no other choice so we have to do so kinga boyewar da kikayi a farko ita taja wanna matsalar yanzu kuma in muka sake boyewa kinsan mai zai iya biyo baya a yayin data fahimci aikin ta ya bace kiyi tunani akai saisa wani lokacin ka boye abu ma bayan Ka sanshi illa ne saboda baka san Mai zai iya faruwa ba, bata Kara ce mata komai ba ta wuce ta barta nan tsaye.

Suna fita daddy ya kalli nina tare da fadin "maisa zakiyi saurin yanke hukunci da cewar ba haka bane su najwa basuyi girman dazasu iya shirya magana har haka ba dudu du cikinsu ba wacce takai 16 ina suke da wayon hada kitumurmura irin wanna, kuma na yadda da abinda sukace dari bisa dari domin nima shaida ne dan wasu lokatan idan emir yanamin magana na kanji warin irin wa'annan abubuwan sometimes amma kasancewar babu wata alama dake nuna Yana sha yasa nake watsar da tunanin a zuwan ko a abokan sa ne wani yake sha amma wanna maganar tasa na tabbatar da hakan to amma ita umaimah miye dalilin ta nayin hakan.

" toh ni daddyn emir abin ma da yafi daure min Kai mai seenah ta tare mata a gidan nan da har take so ta barshi , murmushi daddy yayi irin nasu na manya yace
"nabila Kenan har kyayi mamaki bayan ga magana a bayyane karki manta seenah tana a matsayin matar emir and ke baki ga abinda emir ya ringa yiwa seenan ba a gaban mu amma kuma daga ni har ke an rasa mai tsawatar masa ai daganan ma zaki san da wata a kasa , ni kaina ina yiwa seenah wani abun ba tare dana sani ba amma kuma na kasa hana kaina yin hakan , nabila ki gane duk Wanda fa da farko yace baya kaunar ka to ko daga baya yace yana sonka karya ne haka zalika duk Wanda yace Yana sonka daga farko daga baya idan yace baya sonka to ba hakan bane har zuciyar sa umaima zata iyayin komai tunda tace ta tsane ki ta tsani farin cikin ki kinga kuwa duk wanna karamin aiki ne wurin ta.

cikin jimami nina tace hakane Allah ya kyauta yakare mu daga sharrin mutum da aljan.

"ameen ya allah amma ni abinda nakeso dake muyi pretending a yadda muke da kicewa najwa suzo dinning tare akwai abinda nake son tabbatar wa, tashi nina tayi tana fadin to shikenan barin je in fada masu sai Ka fito.

Duk sun hallara a dinning din banda nafisa da yanzu kullum tana gararan ba a titi , kamar yadda Nina tace wa najwa suzo dinning tare da seena haka kuwa akayi tare suka karaso suna zama daddy ya dakawa seenah tsawa akan Mai suna zaune zata zo ta zauna cikin su ko duk cikin salon raini ne .

A rude ta mike tana kokarin barin wajen nina ta fakaici idonsu ta kyafta Mata Ido amma still ta kasa zama hannun ta har rawa yake da Ido nina ta sake Mata alamar tayi wani abu.

  Kwalla ta fara sharewa tare da dukewa a wurin tana fadin dan allah daddy Kayi hakuri nayi kuskure bazan sake ba na tuba in wani laifin nayi kake min irin wanna hukuncin.

tabe baki umma tayi tare da fadin " alhaji ni in banda naci ma irin naka da kauye kamai da yarinyar nan wallahi yarinya sai bakin jini Wanda aka aurawa ma ba so yake ba amma kaika dage saika hada zuminci Karka je dai garin hada zuminci ya warware ma gaba daya ni inaga kasa kawai ya sauwake Mata ta lumana tunda kaika dauro auran shima kaga ya saba da wayayyun Yara tunda kaga ya bar kasar Kar ya dawo kuma yayi abun da za'azo ana dana sani kasan shi namiji fa ba'a masa tilas fa bare yaron irin sadam da idonsa ya bude da duniya , yauwa ni kuwa alhaji Kana ma bincikar yaron nan kuwa kasan turai ba irin nan bace dole sai ana sa Ido kar yaro yaje ya lalace acan ku kuna nan ya maida ku hoto shi Yana can Yana holewar sa ba mafadi karshe ya zo ya jawo maku abun kunya da girman Ka ya zubar ma da mutunci.

sosai maganarta ta sosa masu zuciya ta kuma tabbatar masu da abinda suke zargi Adnan da maganar ta ta ta kular dashi yace mu ba tarbiyyar da iyayen mu suka bamu ba kenan sannan kafin Ka hango na wani ka fara duba naka tukunna kuma emir din ai ba yau ya fara barin kasar nan ba da duk bai lalace ba sai yanzu ya karashe Yana mai juyawa wajen su daddy yace dan allah daddy kuyi hakuri ku sararawa yarinyar nan haka in har son ta ne bakwayi ku maida ta Inda kuka dauko ta mana ai mahaifiyar ta na san ta amma hakan hakki kuke daukarwa kanku na musgunawa marainiya yana gama fadar haka ya mike tare da tattare wayoyin sa ya fice daga dinning din tare da barin gidan ma gaba daya cike dajin haushin su duka .

najwa da Itama jikin ta yayi sanyi tace daddy Kayi hakuri dan Allah .

"it's okay nina ta fada , tashi najwa tayi ta kamo hannun seena dake durkushe a kasa ta zaunar da ita kujerar dake kusa da ita, sosai zuciyar ta ke zafi kan lafuzan umma ji take kamar ta Kai Mata duka.

Tashi tsaye umma tayi tare da fadin "kaga irin tarbiyyar da ake yiwa mutane ikirari an bawa Yara ko ka duba maganganun da wanna yaran ya kalli tsabagen idon na ya mayar min da magana saboda abinda uwarsa ta nuna masa kenan , hmmm ba girin girin ba dai bari mu zuba Ido muga masu tarbiyya .


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol