Free chapter · Read without an account

Page 56

by Fatima Yushau adam · KUDURAR ALLAH

Yana gama waya da Safwan ya tashi ya faɗa toilet,wanka yayi ya shirya tsaf,kana yazo ya tsaya akan Bintu da har yanzu take ta shaƙar baccin ta hankali kwance,a hankali ya sunkuya ya kai bakinsa kan ɗan ƙaramin bakinta ya sumbata,wanda hakan ya farkar da ita, zuba masa ido tayi kana kuma ta ɗan tura baki tare da cewa nifa bacci nake ka tasheni!'ɗage mata gira yayi,ba tare da yace"mata komai ba yaja hannunta ya miƙar da ita tsaye, sannan a hankali ya kuma janta har zuwa cikin toilet duk bata ce mashi komai ba,sai da taga yana ƙoƙarin cire mata kaya,kana tayi saurin riƙe hannun damansa cikin tura baki tace"wai mi zakayi ne? cikin haɗe fuska yace"wanka zanyi miki!'zaro manyan idanunta dake matuƙar burgeshi tayi,kana cikin san ya tausaya mata,tace"dan Allah kabari zanyi da kaina!'ba tare da ya tanka mata ba,ya rabu da ita tare da ficewa daga toilet ɗin,wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke kana tashiga tsaftace kanta.

Bata sameshi a dakin ba sai kayanta da ta tarar har da mayafi da alamu dai yanzun ma fita yakeso suyi,a nutse ta shirya duk da yunwar dake sakaɗar ƴan hanjinta,tsaf ta fito da ita cikin doguwar rigar atamfa mai kalar kore da baƙi, sai hakan ya kuma haska kyawunta da ƙuruciyar ta suka kuma bayyana,takalmin ta ta zura bayan ta feshe jikinta da sassanyan turarukan sa,fita tayi cikin wani irin taku tamkar wata ɗawisu.

Zuba mata ido yayi yayin da yake zaune bisa kujerar dinning table,shigarta,da nutsatstsiyar kwalliyarta da babu hayaniya, ƙamshinta da yanayin takunta shi ya fi tafiya dashi,A hankali ya lumshe idanunsa tare da kwantar da kansa jikin kujerar,jinta dafdashi yasa shi ƙara buɗe idanun yana binta da wani irin kallo wanda ita kuma yake karya duk wata laka dake jikin ta,zama tayi tana bin jerin kwanayen abin karin dake kan table ɗin da kallo,zatayi magana ya rigata da cewa,inno da Hajiya Babba ne suka aiko dashi!'ya faɗa idanunsa na kanta bai ko rissuna su wajen kallon nata,ƙasa tayi da kanta tana jan yatsunta,ita kam ta rasa wannan kallon ko na magani da meyene?katse mata zancan zuci yayi da cewa,ki zuba mana ina saurine!'tashi tayi ta fara saven ɗin sa kana ta zuba itama,yunwa take ji dan haka ba ta tsaya nawa ba ta zage ta cika cikinta,shi dama Abdallah ba baya bane wajen bawa ciki haƙƙin sa,sai da suka gama kana suka fita falon inno,azaune suka sameta ita da taufiƙa wanda rabon da Bintu ta ganta har ta manta, Abdallah kuwa baima shaida ta ba,amma ita idanun ta tamkar zasu faɗo wajen kallon sa,har sai da Bintu ta samu kanta da zabga mata harara,gaishe da inno yayi,ya na gyara zaman agogon hannun sa, Bintu kuwa zuwa tayi jikin innon ta kwanta tana zuba mata shagwaɓa,inno tace"nikam zaki ƙarasani ne? jikina ba irin na mijinki bane mai ƙwari!'ta faɗa cikin dariyar farin cikin ganin su cikin walwala,tura baki Bintu tayi ba tare da tace" komai ba sai idanun ta dake kan Abdallah da take ganin kamar yana kallon Taufiƙa,kawai ji tayi idanunta sun kawo ruwa wanda kuma bata san dalilin hakan ba,Muryar Taufiƙa ta tsinkayo tana gaida Abdallah, ai ko da sauri ta kuma maida hankalinta kansa dan taga yadda zai karbi gaisuwar,amsawa yayi yana ƙoƙarin ɗora waya A kunnen sa,duk da taga yadda yayi amma hakan baisa taji nutsuwaba,juyowa yayi yace"da inno zamu fita amma bazamu jima ba!'inno ba ta tsaya tuhumar inda zasu ba,tayi musu fatan nasara,tashi Bintu tayi ta bi bayansa tana jin kamar ta tsinkawa Taufiƙa mari,Wanda ita kuma Taufiƙan fiye da haka take ji akan Bintun,duk sanda zata ga Abdallah to kuwa sai taji ana ƙara iza wutar san sa a zuciyarta,dan ma bata nan kwana biyu ita da Siddiqa da tasan abin sai yafi haka yawa azuciyar ta.

Yana kula da yadda Bintun ke ta faman cin magani,saboda duk wani motsinta akan idanun sa ne,shi dai bai ma gane Taufiƙa ba bare ya gane dalilin hararar da Bintu ke antaya mata,shiga mota sukayi duk da yaso yashiga ɓangaren Hajiya Babba da Alhaji Baba Amma hakan bai samu ba sakamakon saurin da yakeyi,Bintu na ƙoƙarin shiga suka haɗa idanu da Anty Nafisa,ɗauke kai tayi tare da rufe ƙofar,tana mai ci gaba da kallon Anty Nafisa ta cikin baƙin glace ɗin window motar,sosai ta hango tashin hankali kwance kan fuskarta da kuma asalin mamakin da ya rufeta wanda Bintu bata san na meye ba,ji tayi ya jiyo da kanta saitin sa,cikin al'adar sa ta dage gira yace"Ni zaki kalla ba itaba!' so tayi ta harareshi saboda haushin sa da tasamu kanta da ji,amma sai taji baza ta iyaba hakan ne yasa ta juya hararar zuwa wani irin kallo na musamman da bata san ta iyashi ba,kuma batasan halin da yasaka wanda aka yiwa kallon ba,kawai dai taga ya koma ya kwanta sosai yana ɗan lum-lumshe idanunsa tamkar wanda yake shirin komawa bacci,A hankali ta tsinkayi Muryar shi yana cewa,me haka Bint?me nayi Makine?ita zaton ta fushin da takeyi yake tambaya,dan haka sai ta kuma tura ƙaramin bakinta tana magana ƙasa ƙasa,ba waccen Taufiƙan ce take ta kallon ka ba!'sam Bint bata fahimci komai akan abinda tayiba hasalima bata san manufar yin hakan ba,buɗe ido yayi sosai yana kallon fuskarta dake a kwaɓe da alama dai har yanzu da haushin abun atare da ita,dogon hannun sa yasa ya jawota jikinsa gaba ɗaya,ya kuma haɗa fuskarshi da tata,ba tare da yace"da ita komaiba,sai numfashinsa da yake saukar mata kan fuskarta,kwantar da kanta tayi sosai tana jin abinda ya tsaya mata na sauka A hankali,sai kuma ta shiga fitar da numfashi mai ɗauke da manufar samun nutsuwa.

Hajiya zulaiha dake tsaye itama ta lumshe idanun ta tare da cewa,insha Allah ka kusa dawowa gareni,inajin haka ajikina,tun sanda na fara ganin Abdallah nake jin wani abu game dashi wanda nake fata ya zama gaskiya!'Rahima dake bayanta tace"Ammi kamar me?kuma dama baki taɓa haɗuwa da Yah Abdallah ba tun tsawon zaman shi agidan?Hajiya zulaihat tace"ban taɓa haɗuwa dashiba ban taɓa ganin sa ba,sai a daren jiya da suka dawo akan idanuna!'Rahima tace"wallahi Ammi nima inajin kwatan kwacin abin da kike ji,to komeye dalilin hakan?kama hannun ta tayi suka shige falon tana cewa,Rahima Allah ne masani shi kaɗai yasan abinda ke ɓoye,sai dai muyi fatan duk abinda zai biyo baya ya zama Alkhairi!'..

Cikin wani irin tashin hankali da sauri mai haɗe da gudu ta koma ɓangaren ta, cikin karkarwar jiki ta zaro wayarta daga jaka har tana neman faduwa,wajen kira ta shiga ta nemo nomber da zata kira,wayar sai ƙoƙarin faɗuwa take saboda yadda jikin ta ke rawa,da ƙyar ta samu nasarar karata a kunnen ta,sai da ta daɗe tana ringin har ta kusa tsinkewa kana aka ɗaga,Ya dai Hajjaju aiki ya samu kenan?cikin wata irin muryar da take nuni da tsananin tausayin kanta tace"wai mai yasa bani da sa'a ne a rayuwata?me yasa duk abinda na saka agaba sai ina murna na kusa cimma shi sai ya kufce daga gareni?me yasa nake haɗuwa da mayaudara ma ha'inta acikin dukkan sabgata?dariya yayi kana ya shiga bata amsar tambayoyinta,da cewa abinda yasa baki da Sa'a saboda waɗan da kike neman sa ar halaka su basu da alhakin cutar da kowa ballan tana ke, sannan kuma abinda yasa duk abin da kika kama yake kufcewa daga gareki,saboda ba dan kyakykyawar manufa kika riƙeshiba,amsar ki ta ƙarshe itace" saboda kema mayaudariya ce kuma maha'inciya maci amana, dan haka babu ta yadda za'ayi kiyi abota da mai gaskiya da amana dole sai irinki!'ya ƙare da cewa, Hajjaju meye aikin ki? cikin wani irin baƙin ciki da ɓacin rai ga kuma damuwa tace"mai kake nufi da waɗan nan maganganun naka?yace"Hajjaju ke nan nifa tambayata kikayi kuma na baki amsa,kuma kema kinsan gaskiya na gaya miki,kawai dai dan mun kauce ne amma ko yau muna fatan shiriya!'babu yadda zatayi da wannan taƙadirin dolene idan tana so ya bata amsar abinda take nema agurinsa sai ta haɗiye fushin ta,dan haka cikin ƙoƙarin maida mugun fushi da haushin sa da takeji tace"aikin da na baku ba kunce kun gama dasu ba?kai Hajiya Nafisa yaza ayi ki dinga dawo mana da aiki baya,bayan har shaida sai da na turo miki,ki daina haufi akan aikina,ko kinga wani kuskurene?a jiyar zuciyar samun ƴar nutsuwa tayi kana tace"yarinyar da kuka turomin hotunan ta na gani yanzu acikin gidan nan,ita me yasa baku kashe ta ba?yace"sai dai idan lokacin da muka gabatar da aikin bata cikin gidan wannan itace amsar ki,kin gama ina da abinyi yanzu?shike nan dama abinda zan tambayeka ke nan!'kashe wayar sa tayi tare da cire layin ya taune shi kana ya haɗiye,yana cewa,bazaki ƙara ganina ba a rayuwarki har abada,ita kuwa Nafisa baƙaramin kwanciya hankalin ta yayi ba,tana ganin Bintu koda bata kasheta ba bazata bata wata matsalaba,tunda babu wanda yasan ko ita wacece,duk da ko ita har yanzu bata tabbar da abinda take zargiba..

Tun daren jiya baiyi bacci ba,duk inda ya juya tashin hankali yake fuskanta,yanzu abinda su shugaba zasuyi masa kenan? duk yadda aka daɗe ana gwagwarmaya tare,amma shine yanzu zasu juya masa baya har da ƙoƙarin razana rayuwarsa,juyawa yayi ya zubawa gurin da yake idanu duk da ba gani yake ba saboda tsananin duhun wajen,yanzu ɗan ɗan uwansa ne ya jefashi cikin wannan halin?abinda zuciyar shi ke ta tambayar shi ke nan,ji yake tamkar yasa hannu aka yayi ta zunduma ihu,abin duniya ya dameshi,zuciyar shi tamkar ana babbakata da wuta haka yakeji,sai dai kuma sam har yanzu babu alamun nadama atare dashi sai hanyar kuɓuta da samun cikar buri.

Zubawa kyakykyawar fuskar ta idanu yayi wanda sam baya gajiya da kalla,A hankali yayi magana cikin miskilar muryar sa,yace"sleeping beauty wake up!'ya faɗa yana ɗan taɓa tattausan kumatunta,buɗe idanun ta tayi wanda suke cike da baccin da Bai isheta ba,ɗage mata gira yayi tare da cewa,yarinyar nan na kula sam bazaki iya kwanan zaune ba!'a hankali ta zame daga jikin sa tana ɗan bin farfajiyar gidan da kallo,dawo da kallon tayi kansa tana shirin tambayar sa,nuni yayi mata da su fita kar tace komai,dole ta haƙora da abin da take son cewa suka fita daga motar,kai tsaye cikin falon suka nufa,bin ko ina takeyi da kallon baƙunta da kuma mutanen da bata san su ba,gaisuwa suke ta miƙa wa ogan su suna haɗawa da gaida Bintu yarinyar da yanzu suka gama gasgata cewar matarsa ce,ɗakin da Abigirl take suka nufa yana rike da hannun Bintu tamkar ance za a kwace masa ita.

Zaune take ta haɗa kanta da gwiwa kana kallon ta zaka san cewa cikkakiyar kafura ce,jin motsin da tayi ne yasata ɗagowa da sauri,wata irin zabura tayi ganin Abdallah wanda bata taɓa tsammanin gani a daidai wan nan lokaci ba, cikin rawar harshe ta kira sunan da tafi ƙware wa da faɗarsa, Fatash!'wani irin mummunan kallo ya shiga watsa mata,yayin da Bintu ma ta kuma bude idanun ta jin sunan da aka kira Abdallahn ta dashi, cikin tsanar sunan da wadda ta ƙirƙiri sunan yace"ba tun yauba kuma batun yanzu ba nake miki jan kunne akan kirana da sunan kafirai,yanzu kina cikin tarkona ne,dan haka idan na kuma jin wannan baƙin sunan a bakin ki sai na zubda hakoranki gaba ɗaya!'shuru tayi tana kallon sa babu abinda ya sauya daga halayyar dayake nuna mata tun asali,zama yayi ya turawa Bintu kujera itama dan ta zauna, amma sai ta kasa zama ita kawai so take tasan wani abu akan matar nan da kuma sunan da ta ambacesa dashi,gane hakan da yayi ne yasa yayi mata banza,ba tare da yakuma duban inda take ba,ya juya kan Abigirl wadda tayi tsumu- tsumu da ita,tabbas ta daɗe tana fargabar wannan rana da Abdallah zai zo ya tutsiyeta dan sanin abinda take ta ɓoyewa tsawan shekaru,kallon da yake mata yasa ta kuma rikicewa duk ta rasa wata nutsuwa, zuciyar ta cike take da tsoron Abdallah da irin hukun cin da zai yi mata,dan ta san tunda ya rutsata dole sai ta faɗa masa asalin labarin ko taki ko taso, Abigirl yadda ya kira sunan ma kansa abin firgici ne,dan hatta da Bintu dake tsaye idanun ta kan Abigirl ɗin sai da ta juyo ta dubeshi,fuskar nan babu alamun wasa ko wani annurin dake nuna zaiyi sassauci A al'amarin sa da Abigirl ɗin, cikin ƙara kiɗimata da sautin muryarsa yace"waye yabaki Ni kuma a wane dalilin sannan da wace manufa aka bakini?zatayi magana ya dakatar da ita,da hannun sa tare da cewa ba yanzu nake buƙatar amsarki ko musuntawarki ba,ina miki tambayar ne dan ki shirya amsata agaban dimbin jama'a da kuma wadda ko wanda yasaki aita aikin da zai zamo miki danasi wanda Hausawa suke kira da ƙeya,ina mai tabbatar miki da cewa duk ranar da nazo dan karɓar amsar tambayoyina ki kayi min gardama to wallahi sai kin gane kurenki sai kin gwammaci baki zo duniyar ba,dan haka ki shirya zuwa cikin ESTATE dan fallasa sirrin da kike ta sirrintawa tsawon waɗan nan shekarun!'daga haka ya mike tare da hanƙada kujerar da ya tashi akai zuwa fuskar Abigirl,wanda badan tayi saurin kaucewa ba da tuni ya cire mata wani abun daga sassan fuskarta.

Binsa Bintu tayi ganin ya fita, zuciyar ta cike da tunanin ko ita wannan wacece kuma,tana da tarin tambayoyin da take son yi masa amma yaƙi bata damar hakan,ko meye dalilin sa na hana ta tambayar sa kuma oho?bayan ita duk abinda ya tambayeta tana amsa mashi dai dai da abinda yake son sani,ji tayi wani haushinsa ya kamata tare da kewar fafinta,ko wane hali suke ciki, yace" ta kwantar da hankalin ta zai kawo mata ummin ta da fafi amma har yanzu shuru ko maganar ma bayayi,sai ma can wasu al'amura da yakeyi wanda bata gane musu ba,wani kuka taji yana taho mata wanda hakan yasa ta saka hannun ta ta toshe bakinta,juyowa yayi tare da zuba mata ido sai dai baice komai ba,cikin kallon nata ya fahimci damuwarta da kuma dalilin kukanta,ji yayi jikin shi ya mutu tare da wani irin tausayinta ya kan rasa meke damun shi akan Bint indai lamari akanta ne bashi da wani sukuni ko pawer, hakan yasa ya jawota jikin sa suka ci-gaba da takawa har zuwa bakin motar su,da sauri Yahya ya buɗe musu suka shiga,shi kuma ya zaga ya shiga mazaunin drever,sai da suka fara tafiya kana ya ɗago fuskarta dake kwance kan kafaɗar sa,zaro oily eyes ɗinsa yayi cikin san kawar mata da damuwarta,yace"me yafaru da idanunki haka wannan ai sai ki bani tsoro!'sai ya ɗan rufe idan sa alamun wai baya son gani tana bashi tsoro,sanin tsokanarta yake da kuma yadda yayi da fuskarshi sai hakan ya bata dariya,ga kuma tsananin mamakin yadda yake mata wanda tasan da wannan duk ba halinsa bane,amma yanzu wai duk dan yasata farinciki yake yin abinda bai saba dashi ba,ganin hakoranta sai ya samu kansa da samun nutsuwa har shima ya saki wani ɗan ƙawattacen murmushi da ya ƙawata kyawunshi da kwarjinin shi,wanda har bata san da ta zubawa fuskar tashi idanu ba,ɗan gemunshi dake matuƙar burgeta ta mai da hankali wajen kalla,ji tayi yace"kinaso ne?da sauri ta maida kanta ta ɓoye a ƙirjinshi saboda kunyar da taji ta rufeta, cikin taushin murya yace"Bint kiyi haƙuri Ina sane da abinda nakeyi na kusa cika miki burinki,ki ɗauka tamkar kina tare da Ummi da fafi ne,kinji ko bana son ganin damuwa akan fuskarki!'ya faɗa yana jan lafiyayyan kumatun ta,A hankali tace"to ya Abdallah ka kaini naga Dady mana dan Allah!'zan kaiki shike nan?

Ɗan ƙif-ƙif tayi da idanun ta kana cikin sanyin murya tace"wacece wannan matar da take kiranka da wani suna?kawar da kanshi yayi sam baya san abinda zai dan gantashi da wannan kafurar matar,yace"matar da ta riƙeni ce!'wata irin zabura tayi tana kallon sa cike da mamaki,ganin yaƙi kallonta sai ta ɗan langaɓar da kanta bisa kafadunshi tare da cewa,ayya to meyasa zaka kawota nan?ko itama tasan wani abu game da barinka gida?sai da tayi wannan tambayar ya juyo da fuskarsa inda take,yace"inye kaga yarinya tayi gadon basira,tayi tambaya ta bawa kanta amsa kuma!'dariya tayi wanda saida fararan haƙoran ta suka baiyana,haka nan takejin wani irin nishadi da farinciki duk lokacin da ta kasance da oganta Abdallah, bare yanzu da yake ririta farincikin ta yake gudun damuwar ta yake neman duk wani abun da zai cire kunci a zuciyarta ga shi kuma ta gama fahimtar halayyar sa tsaf sai ɗan abinda ba arasaba,yace"Bint zakisan abinda ya faru dani da kuma irin rayuwar da nayi tare da wannan kafurar matar,amma sai agaban dukkan ahlinmu, acikin falon Alhaji Baba,tare da Dady da Ummi da fafy,da kowa da kowa da yake buƙatar sanin rayuwar da mukayi Abaya!'jinjina masa kai tayi cike da gamsuwa da bayanin sa,daga nan kai tsaye gidan malam suka nufa.

Baƙaramin farinciki sukayi ba ganin yadda aka samu ci gaba a lafiyar Dady Abubakar,sosai yake samun kulawa a gurin malam da sauran ɗaliban sa,duk da dai yana kwance har yanzu bai buɗe ido ba, amma tsaf yake tamkar idanun sa biyu,Bintu ce ta matso kusa dashi tare ɗora hannun ta kan hannun sa ta riƙe a hankali ta shiga karanto addu'oin samun sauƙi gareshi,tanayi tana tofa masa asaman kansa da idanun sa, Abdallah kuma magana suke da malam dan haka sai hankalinsa ya rabu biyu,kamar almara Bintu taga hannun da tarike yana motsawa,nutsuwa tayi tare da zubawa hannun ido dan tana son gasgata abunda idanunta suka gani,ganin bai kuma motsawa ba sai ta dawo da kallon ta kan kyakkyawar fuskarsa wadda asalinta da kwarjinin ta suka bayyana,zubawa fatar idonsa ido tayi saboda ganin kamar tana motsawa,tabbas kuwa ba gizo idanunta kemata ba,kafin tayi wani abu kuwa sai ga idon Dady Abubakar akanta ya buɗe su fes yana kallon ta,wata irin zabura tayi tare da sakin kuka da kabbara duk alokaci ɗaya,wanda hakan yasa malam da Abdallah suka zaburo zuwa inda take, Abdallah jikin sa na rawa yake tambayar ta lafiya?kafin ta bashi amsa ya hango amsar da idanunsa,ɗurƙushewa yayi gaban gadon da Dady yake kai kusa da Bintu,yayin da malam yake ta kabbara tare da hailala, Bintu kuwa cikin wani irin yanayi na tsantsan farinciki take cewa Alhamdulillah masha Allah,Dady kana gani? kayi magana ga Ya Abdallah ga kuma Ni Bintu ɗiyarka ɗiyar ɗan uwanka Abbana Umar!cak taga ya tsaida ƙwayar idanun sa akanta,yana mata wani irin kallo, Abdallah kuwa kwantar da kanshi yayi jikin Dady yana fidda wani sassanyan murmushi wanda yake fitowa tun daga asalin zuciyarsa,A hankali Dady ya shiga jan hannunsa cikin nutsuwa da rashin ƙwarin jiki ya ɗora bisa kan Abdallah yana shafawa wanda hakan ya kuma jefa BINTU cikin wani irin shauƙi jin farin ciki take har ƙoƙon ranta,sai kuma taji wasu hawaye masu ɗumi suna gangarowa kan fuskarta,sha awar Dady da Abdallah taji ta mamaye ta,ina ma itama zata ganta jikin Abbanta yana shafa kanta cikin so da ƙauna,tunanin tane ya katse lokacin da taji Muryar Dady duk da ba fita take sosai ba amma zaka fahimci abinda yake cewa,yace"tashi ka bawa ɗiyata gurin ta ba kanka naso na fara taɓawa ba kanta ne saboda itace bata taɓa jin ɗumina ba bata taɓa zama tare dani ba,ba ta taɓa yin wasa dani ba,kai kuwa ka hau jikina kafin azzalumai su rabamu,kayi wasa dani kafin mu rabu kuma kaci abinci dani,dan haka matsawa ɗiyata ta fara samun nata gatan tun yanzu kafin Allah Ubangiji ya bani ikon miƙewa gaba ɗaya na nuna mata gatan da babu wata diya da ta taɓa samun shi a cikin duniyar mu!'wani irin kuka ne ya ƙwacewa Bintu mai haɗe da wani irin shauƙi da jin ta yau tacika ƴa, ƴar gata,waɗawa jikin sa tayi shi kuma yasa hannu a gadon bayanta yana bubbugawa cike da san rarrashinta,ko Ni tunda nake ban taɓa ganin dariyar Abdallah da hawaye ba sai yau,jarumtar shi ta ƙare ba zai iya jurewa ba,farinciki tare da tausayin su baki ɗaya da kuma kalaman Dady suka saka shi hawaye,malam ma sai da ya share hawayen tausayin waɗan nan bayin Allah,shi tun da yake arayuwar sa bai taɓa cin karo da abin mamaki da tausayi ba kamar labarin bayin Allah nan, Allah ka ƙaremu daga makircin shaidan kayi mana tsari da faɗawa halaka,a hankali Bintu ta ɗago kanta kana tace"Dady na ina son ka,dama haka kasancewa da uba yake? dama haka waɗan da suke tare da iyayensu sukeji? murmushi kawai Dady yakeyi kana yace" fiyema da haka suke ji kema zakiji fiye da haka tukun na dai Allah ya bamu aran lokaci!'amin suka amsa, Abdallah cikin marairaice fuska yace"tunda abun wariyace,nima yanzu zanje na nunawa Abbana ɗan sa da ya daɗe yana bege sai kowa ya riƙe nashi!'dariya sukayi baki daya cikin tsananin farin cikin da ya mamayesu a wannan rana mai ɗinbin tarihi. 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` ***

*_____________________________________*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol