Free chapter · Read without an account

Lulu

by Fatima Rufa'i Nasidi · IMSAL

It's fatoumspassion IMSAL 
Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM, INTENSE LOVE, EHSAAS and SCARRED.

Chapter 18

Lulu

Da wani irin sauri Mummy ta sha gabansa tana dakatar dashi, ganin kamar faɗan baze yi aiki akansa ba yasa taɗan sassauta murya tana faɗin 
"Mr Farouq asthma ne,
I'll handle it,
just let me, yanzun idan ka fita da ita kafin ka kaita hospital zata iya losing consciousness,"
Mummy ta ƙarasawa a hankali tana kai hannunta saman gashin Imsal data fara fita a hayyacinta cikin faɗa yake fadin 
"then do something,
 why are you still standing here?"
Da sauri Mummy tace 
"Natasha her inhaler,"
 da sauri Natasha tai ɗakin Imsal shi kuma ya juya yana dawowa da ita falon.

ya ajjeta saman kujera yana riƙe hannunta duk da halin da take ciki, ƙoƙari take ta fizge hannunta acikin nasa amman batada wani sauran ƙarfi ta kasa, Mummy shafa bayan ta ta shiga yi tana faɗin 
"calm down baby,
 he won't hurt you, nasan shi kinji he's not here to harm you,
Imsal try and breath kinji,"
A hankali ta sauke idonta akan Mummy kamar maganganun suna shigarta daidai sanda Natasha ta ƙaraso da salbutamol inhaler ɗin nata Mummy ƙarɓa zatai,
da sauri ya riga ta karɓa yana ɗagota zuwa jikin sa ya shiga bata amman tsabar taurin kai Imsal ƙoƙarin takeyi ta fizge daga riƙon sa, tamaƙi yarda ta amsa,
dasauri Mummy tace 
"let me please, kaga kamar batason ka bata ne she's not familiar with you,"
 jinjina wa Mummy kai yayi kamar wani sakarai duk hankalinsa ya tashi,
ya bata,
Mummy ta dawo da ita zuwa nata jikin ƙanƙameta Imsal tayi hawaye na sakkowa daga gefe da gefen kumatun ta ahaka ta bata inhaler ɗin ta ɗaura hannayenta saman na Mummy ta karɓa, 
cikin mintuna ƙalilan numfashinta ya fara dawowa daidai,
Wani irin sauke ajiyar zuciya Farouq yayi ganin ta dena wheezing tayi luf ajikin Mummy tana sauke numfashi.

Kasa rike kansa yayi kawai jitai hannunsa saman lallausan gashinta da hular ta ta riga ta zame yana shafawa ahankali yake faɗin
"I'm sorry Lulu, 
are you okay?"
Ɗagowa Imsal tayi tana jefa masa wani irin mugun kallo da tunda yake a rayuwar sa be taɓa ganin ammasa ba.
da sauri ya janye hannayen nasa daga saman kanta ta fara kokarin miƙewa a jikin Mummy tana neman hularta data faɗi, Mummy riƙota tai tana faɗin 
"Imsal ina kuma zaki, 
koso kike kitashi ciwan ya ƙara tashi eh?"
Girgiza ma Mummy kai tayi tana faɗin 
"I'm fine now, 
kitchen zanje,"
Buɗe baki Mummy tai tana kallonta cikin mamaki tace 
"kitchen kiyi uwarme a kitchen?
 bama na hanaki shiga kitchen ba,"
Natasha ce tai saurin cewa 
"Daddy ne yace fa muyi breakfast amman kinga tunda bata da lafiya bari naje ko scramble egg ne kawai nayi da toasted bread yah Imsal ki huta,"
Imsal babu wanda ta saurara acikinsu ganin hular ta yasa ta miƙe ta ɗauka tana ƙoƙarin barin gurin Farouq ya riƙo hannunta, yana faɗin 
"Stop being stubborn,"
Juyowa tai a fusace tana faɗin 
"Karka ƙara taɓani sakarmin hannunta"
Da sauri Mummy tace 
"saketa Farouq meye haka, banason irin hakafa,"
Aɗan dame ya kalli mummy yana faɗin 
"why?
I just wanna make sure she's fine,
Why can't I hold her hands,"
Da wani irin mamaki daga Imsal har Natasha suke kallonsa da alama wannan ilimin addini be gama ratsa shi ba suka raya acikin ransa,
Mummy anitse tace 
"saketa zanmaka bayani"
 takalli Imsal tana faɗin 
"je ɗakin ki karna sake naga ƙafarki a kitchen ɗinnan"
se alokacin ya saketa da sauri ta nufi dakinta.

Natasha datai fiƙi fiƙi tana kallon su Mummy ta kalla tana faɗin 
"what are you still waiting for?
bazaki wuce kiyi aikin da aka sakaku ba,"
Turo baki tayi tana juyawa ta nufi hanyar kitchen tanayi tana juyowa tana satar kallon Farouq da kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai tanason ta tina inda tasan fuskarshi amman ta kasa.

"Is she always suffering like this?"
Farouq ya tambaya yana tsatstsare Mummy da ido,
Mummy tace 
"kai zan tambaya mekai mata hardata firgita ciwanta yatashi haka, donni lafiya nakwana da ita agidannan"
Taɓe baki yayi kafin yace 
"It doesn't concern you tsakaninmu,"
Da takaici tace 
"okay but kasan ƴata ce ko,"
jinjina kai yayi kafin yace 
"nikuma matana ce,"
Mummy murmushin ta kaici tayi kafin tace masa 
"bata zama ba don haka karna ƙara ganin hannunka ajikinta,
mu anan mace da namiji can't have any physical intimacy koda ko holding hands ne, is Haram our religion and culture doesn't allow that,
inaga abinda kamata yasa ta firgita haka har ciwanta ya tashi da mamaki yake kallon Mummy irin tama raina mishi hankali cikin rainin wayo yace 
"so you mean nobody has ever touched her,"
Jinjina kai Mummy tayi kafin tace 
"yes Farouq"
 murmushi yayi kafin yace
"And you expect me to buy that lie"
Wani irin kallo Mummy take masa jin straight ya karyatata agaban idonta tace 
"Nice nake maka ƙarya Farouq"
Gyara zama yayi kafin yace
"Kinga nifa I don't care about her past or maza nawa tai dating or how many touched her I don't give a damn, 
the only thing I know is that she's now mine and I'm the only one for her, 
if I find anybody near her,
I can kill for that"
ya ƙarasa yana ɗaga t-shirt ɗinsa Mummy ta hangi ƙaramar pistol ɗin daya soke awurin. 
ko ajikinta don ba yau tasan yana yawo da pistol ba,ta jinjina kai tana faɗin 
"and you keep your hands to yourself my daughter is pious don't say you'll do anything until after marriage,"
Murmushi yayi kafin yace
"I'll try but bazan miki ƙarya ba your daughter is very beautiful and attractive, She's very hot, if she tempt me...."
Kallon da Mummy ta mai ne yasa ya fara dariyar iskanci yana faɗin 
"Sorry mums I'm still a virgin too,
I'll wait for her to unwrap me after marriage"
Mummy cikin son canza maganar iskanci da yake mata ko kunya ba yaji tace 
"meyasa kazo yau ba Thursday mukai da kai ba yanzun gashi zaka lalatamin shiri baki ɗaya,"
ɗage mata gira ɗaya yayi kafin yace
"Lulu ce tai daring ɗina awaya,
And na zone nai maganin bakin dayamin rashin kunya,"
Da mamaki tace masa 
"sunyi wayane,"
Jinjina mata kai yayi,
tace
"Me ta maka?"
Girgiza kai yayi kafin yace
"Mummy stop meddling sirrinmu ne bafa komai zaki ringa jiba,"
Mummy miƙewa tai tana faɗin
"Shikenan babanta ya kusa dawowa ka tashi ka tafi,
ranar Thursday ɗin seka dawo kaji
saboda banason ku haɗu baka gama da zuciyarta ba tukunna,"
Inkin tashi Farouq ya tashi, Mummy ganin yaƙi tashi yasa tace 
"Farouq magana fa nake maka,"
Yace 
"now dana ganta I can't stay away Mummy,"
Tace 
"bangane you can't stay away ba"
 yace 
"yes I need a room here,
I want to live near her,"
Mummy batasan sanda ta koma ta zauna ba tana faɗin 
"ance maka agarin arna muke,
 Farouq mufa musulmai ne,
yanmata gareni acikin gidannan kana tinanin mahaifinsu zebar ƙato kamarka ka zauna masa babu dangin iya bare na baba,
beside zamanmu tare dasu is temporary "
Ɗage kafaɗa yayi in I don't care manner kafin yace 
"why not?
 I see nothing wrong in it,
impact I'll stay in her room kinga zamu ƙara samun connection ta haka, 
and I'll be a good boy I promise,
I won't do anything,"
Mummy kallonsa tai tama rasa gane awana garin gaɓa gaɓan ake haka tace "Farouq me kasha kafin kashigo gidannan?"
Murmushi yayi kafin yace mata 
"nothing aina miki alƙawari,
I'll keep it low key,"
Mummy tace 
"i don't trust you"
tana ƙoƙarin sake magana taji ana zuge gate da sauri ta miƙe tana kallon Farouq da yayi ɗai-ɗai saman sofa ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya.
tace 
"please taso muje banason ya ganka like that, look at your hair dolene ma ka aske shi,"
Yace 
"is that my father in law,"
Jinjina kai Mummy tayi Farouq yace 
"let me say hi before going"
girgiza kai Mummy tayi jin an kashe motar tai saurin faɗin 
"come with me dan Allah,"
ganin kamar she's desperate yasa ya miƙe ya bita ƙofar kitchen tai suka shiga kitchen.

Natasha nata aikinta tana mita ita kaɗai ta gansu, ta tsaya tana kallonsu aɗan firgice,
Ta tagar kitchen Mummy ta shiga leƙen Daddy,
Farouq wallet ɗinsa ya ciro daga aljihu yana kallon Natasha da take kallon sa kamar wani TV,
Yace 
"I know I'm very handsome,
but stop staring I'm your sisters man,"
batasan sanda ta fara murmushi ba,
Wani black card yamiƙa mata yana faɗin "spoil yourself and my lulu with this,
Baby sister, year of birth ɗinta ne pin,"
da sauri Natasha ta karɓa tana jinjina masa kai don gayen ya mugun burgeta saboda haɗuwarsa da yadda yake very friendly.

Mummy ganin daddy ya shigo ta main door yasa tai saurin buɗe ƙofar baya tana faɗin "zoka tafi,
Please don't come back until Thursday,"
taɓe baki yayi kafin yace mata,
"Banyi alƙawari ba,
tell my wife to switch on her phone inba hakaba zandawo"
jinjina mishi kawai tayi tana turashi waje, seda taga ya nufi gate sannan taji hankalinta ya kwanta.

Juyowa tai kan Natasha tana faɗin "banason naji mgnr zuwan yaronnan ako ina kinji ko,"
ɗan jinjina mata kai Natasha tayi kafin tace "Mummy ko shine wanda rannan naji kuna magana da yah imsal akansa,"
jinjina mata kai Mummy tayi,
Natasha tai murmushi tana jujjuya katin hannunta tace 
"His very handsome and friendly,
I think I like him,"
Mummy juyowa tai tana murmushi kafin tace 
"his not friendly trust me,
 jininku ne ƙila ya haɗu fitinanne ne kawai ya zonan yasa jinina yahau,"
Murmushi Natasha tai,
Mummy tace 
"bari naje kar Doctor ya fara nemana,"
tana nufar ƙofa,
"Mummy yah Mu'allim fa?"
 ɗan juyowa Mummy tai kafin ta kalleta strictly tace 
"toh ban black card ɗinnan"
da sauri Natasha ta ɓoye abayanta tana faɗin 
"Mummy fa ni yabawa,"
 tace 
"eh jinai kina kiramin Abdullah se kije ai yabaki nasa that is inyana ma dashi kenan,"
Girgiza kai Natasha tai kafin tace 
"sorry Mummy,"
Mummy tace 
"Natasha sekace ba halina kikayo ba,
look at Farouq meye Abdullah ze nuna mishi kyau, ƙira ko arziki"
 girgiza kai natasha tai alamar babu,
Tace 
"toh shine zaɓina shine Imsal zata aura, kinga kuskuren da nai nabi soyayya bazan taɓa bari ɗaya daga cikin ku ta sake making ba,
musamman Imsal saboda tana buƙatar rayuwa cikin daula kodan ciwan da take ɗauke dashi idan ba namiji me arziƙi ba babu wanda ze juri ɗawainiya ds kashe kuɗin da akeyi gurin sama mata lafiya,
Me zatai da wani Abdullah,
Ko ɗan kuɗin gadon da aka bar masa kikeso ya ƙarar akanta"
 jinjina mata kai Natasha kawai tayi 
Mummy ta juya ta fice ta barta ba tareda ta karɓi katin ba.

Natasha jujjuya katin ta shigayi tasha jin labarin meye black card gurin ƙawayenta su Babba, 
amman batama taɓa ganin sa agaske ba inba yanzun ba, 
ayadda taji labari katin is limitless ko nawane zaka cira aciki baze ƙare ba, manyan billionaires petroleum kaɗai suke iya mallakar sa.
murmushi tayi indai hakane kam ita kakarta ta yanke saƙa,
abin nema ne ya samu, yanzun na takeji Imsal tasamu miji wanda yayi daidai da level ɗin kyau da Allah yayi mata, ta ƙarasa tana saka katin a aljihun wandonta quickly tai arranging breakfast ɗin nasu a tray tana murmushi ita kaɗai abinta.

Fitowa tai ta jere kayan saman dining,
tana hango Mummy tana wa Daddy magana ta ƙarasa tana faɗin 
"daddy breakfast is ready,
come and eat,"
Girgiza mata kai yayi yana fadin 
"na samu kunu da ƙosai gurin maama da naje can naci,
cikina kuma ya cika,"
Ɗan ɓata rai Mummy tayi tana faɗin 
"Doctor ya haka,"
murmushi yayi yana jan cheeks ɗinta yace "I'm sorry, koda yake bake zan bawa haƙuri ba Imsal ya kamata na bawa hakuri itada nasa aiki bata jin daɗi,
tana ina?"
Natasha ce tace 
"Daddy tana ɗaki Mummy ce tace taje ta huta kawai,
Ni kaɗai fa nai duka aikin"
ɗan kallon Mummy yayi yace 
"kin kyauta Barrister ni kaina seda na fita naga rashin dacewar sakata girkin safen aida ke natasa daga barcin safennan naki,"
Murmushi tayi tana harɗe kafa tace 
"dako anyi worldwar na biyu,"
Dariya yashiga yi yana tsokanar ta.

Bell ɗin gidan sukaji ana bugawa, Mummy jitai zuciyarta tayi tsalle tana addu'ar Allah yasa ba Farouq ne ya dawo ba,
Natasha ce ta nufi ƙofa tana tambayar "waye?"
jin muryar Mubeena yasa ta buɗe tana kallonta da ɗan mamaki gaisawa suka yi tana tambayar ta 
"ya jikin Imsal?"
tace mata 
"da sauƙi alhmdlh,"
tana bata hanya shigowa tayi hannun ta riƙe da wata haɗaɗɗiyar jaka da rubutun larabci ajiki, tace 
"Daddy yana ciki?"
jinjina kai Natasha tai Mubeena ta ƙarasa ganin su Daddy a falo yasa ta durƙusa har ƙasa tana gaidasu Daddy yace 
"tashi a ƙasa mana Mubeena,
 dawo nan ki zauna"
yana nuna mata gefensa ahankali ta miƙe ta ƙarasa ta zauna,
da mamaki Mummy take kallonta tace "lafiya kika fito da sassafe nan,"
ɗan murmushi tayi kafin ta ajje jakar hannunta gefen Daddy tace 
"saƙone inji yaya,
yace inkawo maka,"
karɓa Daddy yay yana sakin murmushi yace 
"Abdullahi baya gajiya"
ya shiga karanta sunan turaren yace 
"kamar yasani ɗazun nake so na saka Rayyan ya samomin gurin wannan abokin nasu na Abuja,
nasan wurinsa kaɗai zan iya samu, ashe ya shiga zuciya na"
murmushi Mubeena kawai take, Mummy takalli Mubeena tana faɗin 
"kice masa angode,"
Jinjina kai kawai tai, Natasha tace 
"Daddy kabani ƙaramin ciki Please,
yana da daɗi sosai,"
hararar wasa yayi mata yana faɗin 
"ya miki karfi salan ki ringa fesawa kina tafiya duk inda kika gifta akalle ki koh to nahana,"
turo baki tai cikin shagwaɓa take faɗin "Daddy ai agida zanringa sawa,"
Mummy tace 
"sedai idan suna aka sanja miki,"
miƙewa Mubeena tai tana faɗin 
"let me check on Imsal"
bata jira ma wani ya bata izni ba ta nufi ɗakin kanta tsaye.

*IMSAL*
Tana shiga ɗaki ta wani zube akan gado tana rintse ido tana jin hannayensa ajikinta har lokacin,
da sauri ta miƙe jin duk inda ta motsa ƙamshin turarensa ne yake tashi ajikinta ta nufi toilet tana kwaɓe kayan.
sosai take feeling like a sinner ta shiga wanka tana gurje duk inda tasan hannunsa ya kai hatta da gashinta seda ta wanke shi tass sannan ta fito tana jin wani irin kewar Ya Mu'allim da darajarsa da take ƙaruwa a idonta ko sau ɗaya be taɓa attempting taɓa jikinta ba.
ranar daya taɓa ta bisa lalura ne, she's not even conscious kuma he treat her as a doctor amman apart from that tun daga lokacin ko yatsanta be sake yunƙurin taɓawa ba jitai ta kasa jurewa kawai hawaye ya shiga fitowa daga idonta seda tai kuka mai isar ta sannan ta ciro kayan ta ta zira.

Tanajin yan hayaniyar maganganu daga falo kamar basu kaɗai bane sunƙaru,
Jitai ta kasa fita falon duk da yadda takejin wata muguwar yunwa kuwa, 
buɗe ɗakin nata taji anyi ta ɗago kai suka haɗa ido da Mubeena Suhail.
Murmushi Mubeena ta sakar mata tana shigowa ta saka key ta kulle ƙofar tana faɗin 
"kinganni da sassafe koh,
Kofa wanka ban ba"
ta ɗaga hijab ɗinta tana nuna mata kayan jikinta,
yadda tai maganar yasa Imsal sakin murmushin kawai duk da kuncin da take ciki.
Tace 
"keko garin yaya haka?"
Tace 
"tun Asuba yaya yake sintiri waiko natashi daga barci,
akace mai bantashi ba shine fa yana gani takwas tayi ya shigo ya tasheni ya bani turarruka wai na kawowa Daddy,"
Ɗan kallonta tai tana faɗin 
"really"
 tace 
"ashe ashe wayo ne,
ke kawai ya keson wai na duba mai lafiyar ki,
shi kunyar zuwa yake shine ya aikoni inkawo turare,
se kuma nasan yadda zanyi in shigo na ganki in haɗaku,
wai me ya samu wayarki?"
tafaɗa tana ciro wayarta jin tana ringing, ta miƙama Imsal tana faɗin na biyar kenan tun ɗazun yake kirana danma tana silent tunda nashigo gidannan ya maƙi bari muyi gaisawar kirki dasu Mummy shiyasa nayo nan.
"Ungo nan"
taɗaga tana kara wayar akunnen Imsal jitai ƙirjinta yayi nauyi tana tina maganganun Mummy akwakwalwarta yayin data jiyo sassanyar muryar sa akunnuwanta yana sallama 
"Assalamu alaikum ya umri"
Kasa amsa salmar tai ta ɗaura hannunta saman wayar ganin Mubeena ta sakar mata ita.
Ahankali ya sake sallamar jin kamar bata jishi ba,
Itama cikin sanyi tace 
"Ameen Wa Alaikummussalam Yah Mu'allim,"
Wani irin tashi yaji tsigar jikinsa tana yi saboda yadda tai maganar kaɗai yasa ya fahimci she's not fine ahankali yace mata "ya jikin naki ya umri?"
gently tace 
"da sauƙi alhmdlh"
yace 
"I miss you,
saura kaɗan kiji sanarwar bana numfashi babe,"
Cikin damuwa tace 
"meya sameka?"
Gently with slow voice yace 
"bakece kika kashe wayar ki ba,
 I called more than hundred times kinsan cewar I'll be worried,"
 ahankali tace mishi 
"I'm sorry,"
yace 
"ki kunna wayar Please!"
Kasa ce.masa komai tai ya ɗaura da
"inaso na ganki,
nazo babe?"
Da sauri ta girgiza kai kamar yana gabanta,
Ji tai ana murɗa Kofar ɗakinta za'a shigo da sauri ta katse wayar tana miƙawa Mubeena abarta jin kamar ɗakin a rufe yake ya saka Mummy ta shiga bubbugawa tana faɗin 
"Imsal,
Mubeena me kukeyi ne kun shiga ɗaki kun kulle,
kubuɗe ku fito kuyi breakfast,"
jin Mummy ɗince ya saka Imsal ta mike da sauri tana kallon Mubeena,
tace 
"I'll talk to him later,
 let's go"
tana buɗe kofar kasa yarda tai su haɗa ido da Mummy ta ratsa ta gefen ta tai saurin wucewa falo.
Mubeena kallon wayar ta data fara ringing tai alamar ya sake kira ta miƙe tana nufar ƙofa itama tana satar kallon Mummy donta fahimci Imsal kamar atsorace take, 
har tayi gaba Mummy tace 
"Mubeena"
 juyowa tai, hannu kawai ta bata tana faɗin "your phone"
ɗan zaro ido tai tana mata kallon rashin fahimta, Mummy tace 
"nagani,
 indai bawani rashin gaskiyan kuke dashi ba,"
dasauri Mubeena ta miƙa mata zuciyarta ɗaya take faɗin 
"ba abinda mukeyi aciki,
 check Mummy,"
Mummy karɓa tai tana ƙoƙarin buɗewa ta jiyo Muryar Rayyan afalo yana faɗin 
"ke meya samu idonki,
 ciwan kanne har yau be saukaba"
miƙa mata wayar tai kawai ta nufi falo don batason Rayyan ya ɓata mata shiri.
Mubeena bin bayanta tai,
Daddy baya falon ya shiga watsa ruwa tun bayan da suka gama gaisawa da Mubeena ya amshi saƙon nasa.

Daga imsal se Natasha da Rayyan saman dining Natasha na haɗa tea,
Shi kuma Rayyan ya kafe Imsal da ido yana mata tambayoyin data kasa amsa su,
Ganin mummy yasa ya maida kallonsa gare ta yana faɗin 
"Mummy wai ƙuncin me take yi?
Allah wannan ba ciwan kai kaɗai bane nasan Unique ciki da bai she's hiding something, and ina wayar ki tun.jiya nake nemanta akashe,"
Mummy kallonsa tai tana faɗin 
"gaisuwar ka kenan ko?
gwanin na iya,
aika fini sanin ƴayana right,
Kuma ga muguwa ta dawo dole Imsal ta shiga ƙunci da damuwa,"
Rayyan girgiza kai yayi yana jan kujera ya zauna gefen Imsal yana faɗin 
"ai Mummy bahaka bane kawai dai kin san bound din dake tsakanin ku da namu is different, 
ba lallai ta iya faɗa miki abinda zata faɗamin ba,
tell me meke da munki,
ko ciwan ya dawo ne,"
cikin rashin sanin mafita yadda ya tsareta ta jinjina mishi kai.
Yace 
"kinsake samun attack?"
jinjina masa kai tayi tana kallon Mummy,
Yace 
"when?"
Mummy ce ta bashi amsa da faɗin 
"she's fine now,
ko baka gani ba,
I handle everything well,"
Kallon Mubeena yayi da take tsaye agurin har lokacin yana faɗin 
"Bin Suhail yana gida kuwa?"
 ɗan jinjina masa kai tai tana faɗin 
"eh yaya,"
yace 
"Imsal sako hijab ɗinki muje ya sake dubaki koh wani abinne,"
Natasha batasan sanda ta kwashe da dariya ganin yadda yayan nasu ya keso ya raina ma Mummy hankali besan tasan komai ba kar take kallonsa.
Kallonta Rayyan yayi yana kicin kicin da fuska, kafin Mummy tace 
"toh shi baban ku meye amfaninsa kenan, inace shine mentor ɗin abokin naka ma," ɗan sosa ƙeya yayi saboda sam ya manta Daddy na gidan,
 yace 
"ohhh namanta amman kinsan ai Daddy ya ɗan tsufa asabgar,
gara sabon jini ya duba ta ƙilama in yaganta yan koke koken nan dukta bari,
Ya iya rarrashi sosai ko Unique na,"
ya faɗa cikeda rainin wayo yana leka fuskar Imsal da taƙi yarda ta haɗa ido dashi ƙasa ƙasa wanda daga shi se ita zasuji me zatace yace 
"kewarshi kike koh?"
Mummy ce ta katse shi tana faɗin 
"toh ba zataje ba, mema ya kawo ka gidannan da sassafe haka, "
Jawo tea yayi yana faɗin 
"Mummy mutum da gidan su,
se an tambaye shi me yazo yi ku nazo gani mana iyayena,"
Murmushin irin kama rainama kanka hankali tai tana juyawa kan Mubeena tace
"Mubeena zokiyi breakfast,"
da sauri Mubeena ta shiga girgiza kai tana faɗin 
"bari naje gida Mummy,
dama saƙon kawai nakawo zanyi acan,"
Mummy tace 
"okay tohm ki gaida mamanki kice mata anjima zan shigo,"
jinjina mata kai Mubeena tai ganin tayi ƙofa yasa Rayyan miƙewa yana kallon Mummy yace 
"bari na rakata kinsan safiyace hanya ba kyau"
yana fuskewa Mummy tace 
"kaji da gulmar ka dai,"
bece matta komai yabi bayan Mubeena.

Mummy kallon Imsal tayi ganin bata saka komai agabanta ba yasa ta haɗa tea ta miƙa mata tana faɗin 
"zan tambayi alfarmar Umar zanwuce daku Abuja har sanda zaku samu admission, so samu ma kuyi uni acan kawai, inason idan ya tambaye ku,
kunason zuwa,
ku amsa masa da eh,
kunji"
ta ƙarasa tana kallon duk su biyun da sauri Natasha tace 
"dagudu ma Mummy aidama ni nafisan can akan nan"
takalli Imsal tana faɗin 
"kinjini,"
jinjina kai kawai Imsal tayi tana tura shayin jinsa take yi kamar wani maɗaci,
kasa cin toasted bread din tayi bare scrambled egg da natasha ta cika masa seasoning tana gama shan tea ɗin kawai ta miƙe tana kwashe kwanikan da aka ɓata.

Mummy tace 
"kije ɗakina kiɗau wayarki,"
Natasha tace min ansiya maku sababbin wayoyi koh?"
jinjina kai kawai Imsal tayi tace 
"toh hakanma yayi, kiyi transfer din abubuwan ki zuwa ciki, I trust you karnaji karna gani, zan baki sabon sim card wanda kikai jamb registration dashi kikawomin ni zan nemi wayar da zan samiki aciki na ajje miki, ita kuma ɗayar wayar zanmayar wa da Hajiya Nafisa ta bashi abarsa,"
da sauri Natasha da Imsal suka kalleta atare,
Tace 
"meye wani kuka kalleni,
akanki aka fara maida gift," girgiza kai kawai sukai duk su biyun.
Mummy tace 
"Imsal I trust you,
shiyasa zandawo miki da wayarki karnaji karna gani inason maganar Abdullah ta zama past agidannan,
kinga dai mijin da zaki aura baida haƙuri banaso yasan dashi, 
he can do anything for you fitinannen yarone, 
banason yaje yama Abdullahi wani illar kinga koba komai ai ɗana ne shi ba zanso wani abu mara kyau ya same shiba sanadinki"
Imsal jinjina kai kawai tai tana maimaita "wai mijin da zata aura cikin ranta"
 ta nufi hanyar kitchen da plates ahannunta tana ƙoƙarin riƙe hawayenta.
kasawa tai tana shiga ciki ta wani irin fashewa da kuka kamar ranta ze fita tana dire plates ɗin.

Jin motsi kamar za'a shigo yasa tai saurin ƙoƙarin haɗiye kukan ta, muryar Natasha taji tana cemata 
"yah Imsal inkingama ki taho ga Malam garba yazo ze saukemu agurin designer ɗinnan zamu karɓo kayan namu muyo sauran siyayyar,"
Da toh kawai ta amsa mata, 
Natasha ta fice abin ta, wanke wanke ta shiga yi cikin mintina ƙalilan ta kammala ta ajje komai amuhallinsa.
Duk inda Natasha ta ɓata,
 ta samu ta gyara ta koma ɗakinta, 
tana zama Natasha ta shigo tana faɗin "kingama yaya Imsal?
muje"
jinjina mata kai tai ta nufi press ɗinta ta ciro dogon hijab ɗinta har ƙasa da niƙab ta saka ta fito.
Mummy waya takeyi a falo, tana ganin sun fito tai sallama tana faɗin 
"ina zakuje"
Natasha ce ta bata amsa da faɗin 
"Kayanmu zamuje mu anso sannan zamuje musiyo sauran abubuwan amfanin ranar"
Mummy miƙewa tai tana faɗin
"Designer ɗinta anjima zata sauka so theres no need beside batama jin daɗi sosai kije kawai Nats kibar imsal"
Natasha kyaɓe baki tai tana faɗin 
"but Mummy"
Mummy tace 
"Kema I promise zanduba innaga I can afford her zansiya miki dress ko ɗayane wurinta"
Se lokacin Natasha taɗanyi murmushi tajuya takalli Imsal tana faɗin 
"Yah imsal ki zabar min me kyau fa"
Imsal looking confused taɗaga niƙab ɗinta tana faɗin
"Mummy amman ba iri ɗaya zamuyi da nats ba"
Girgiza kai Mummy tayi tana faɗin 
"Change of plan kedai kawai zaki gani zo muje i brought something for you"
 tana kama hannunta,
Natasha tayi gaba tana faɗin 
"toh Mummy ni na tafi se anjima."
Mummy tai hanyar ɗakinta tareda Imsal tana faɗin 
"Sekin dawo nats ayi addu'a kafin afita"
Suna shiga ɗakin ta tareda Imsal,
Kallonta Mummy tai ganin yadda take behaving kamar wata stranger tace 
"Kinga cire hijab ɗinnan kisha iska,
Magana nakeso muyi dake,"
Jinjina mata kai Imsal tayi tana cirewa ta ninke ta ajje gefe Mummy ta miƙe tana ɗakko traveling bag ɗin data zo dashi tana faɗin 
"I know kinajin haushina aranki ko Imsal "
Da sauri Imsal ta girgiza kai irin tayaya ɗinnan,
Murmushin takaici Mummy tayi kafin tace 
"Kinsan ni mahaifiyar kice right, bazan taɓa zaɓa miki abinda yake ze cutar dakeba arayuwa koh"
Jinjina kai Imsal tai alamar eh,
Tace 
" bawai ƙin Abdullah nakeba, dukkanmu munsan shiɗin yaron kirki ne, amman dukkanmu munsan yanada zuciya sosai haƙurinsa kaɗanne"
Shiru Imsal tai,
Mummy tace 
"Imsal nariga nayiwa wani alkawarin bashi dama tare dake kinason inzama ƙaramar mace me saɓa alƙawarin datai,"
A hankali Imsal tace
"A'ah Mummy"
Mummy taɗanyi jim tana ciro wata jewelry box a trolley ɗinta tana buɗewa tace 
"tun kina seventeen yaronnan yake bibiyata yanason ki hatta da mahaifinki munyi magana dashi kuma ya amince ze fara zuwa gurinki abu ɗaya nakeso dake Imsal dan Allah kibashi dama, badanni ba badan halina ba sedam darajata matsayina na mahaifiyar ki Imsal"
tana kama hannunta, da sauri Imsal taɗaura hannayenta saman na Mummy tana girgiza kai tace
"Mummy kidena roƙona dan Allah nasan bazaki taɓa cutar dani ba"
Mummy wata irin murmushin cin nasara tasaki tana faɗin 
"I am trying my best alot of people suna ganina as bad mother amman ku kunsan ina iya ƙoƙorina akanku right,"
Jinjina kai Imsal tai alamar eh,
Tace 
"Imsal duk abinda nasamu kinsan ina hidimta mukune dashi"
Nanma gyaɗa kai tayi alamar tasani,
Mummy ta saki hannayenta tana ciro wata ƙatuwar sarƙar gwal daga cikin box ɗin tana gwadawa awiyan Imsal ganin yadda ta farar ɗaya sarƙar ta amshi wiyan nata yasa Mummy tai murmushi tana cirowa ta ajje saman cinyarta tace 
"wannan zatai sekisa da graduation"
ɗauka Imsal tai tana faɗin 
"Thank you Mummy"
girgiza kai Mummy tai tana faɗin 
"ba saƙona bane na Farouq ne, anjima ma designer ɗinki zata ƙaraso his trying his best to make your day special and memorable"
Imsal jitai tama tsani sarƙar baki ɗaya ambaton Farouq da Mummy tai ganin face ɗinta ya canza yasa Mummy tace
"Imsal am not trying to force you fa, ko marry you up to him, you have a choice kinji you can go for what you want, amman kisani mahaifiyar ki zata zama ƙaramar mace a idon duniya, sannan I'll be very disappointed in you saboda kaf yarana kinsan cewar nafi ƙaunarki sama da kowa,
Ke kaɗai ce kuma nasan inada say acikin rayuwarta saboda nasan kinsan darajata"
Kuka Imsal tafarayi tana faɗin 
"I'm sorry Mummy,
Bazan baki kunya ba in sha Allah"
Rungumeta Mummy tai tana faɗin 
"I know you love him, but kisani love isn't enough and it'll never be enough Imsal, be strong kinji Allah yayi miki albarka try and open your heart kibawa Farouq space shima ze samu shiga in sha Allah"
Jinjina mata kai tai alamar zatayi, daga karshe dai dakyar Mummy ta lallasheta tana binta da duk wani salon manipulation harseda tai mata alƙawarin ba ita babu Abdullah har abada, bayan sun gama tattaunawa ta fito tare suka shiga kitchen.

Yau Mummy dakanta tashiga girka musu lunch ahaka Daddy ya fito ya tarar dasu yaji daɗi sosai ya tambayi ina Natasha Mummy tace mishi taje karɓo ɗinki shima motarsa yashiga ya fice,
Hatta da islamiyya yau Mummy batabar Imsal tajeba duk inda zataje tana jikinta, kamar wata jaririya haka take tattalinta, se bayan la'asar sannan designer ɗin Imsal tazo tareda secretary ɗin Farouq Miss Julia cikin wasu manyan convoys yadda kasan wata yar sarki za'a gwada,
Cikin kankanin lokaci suka gama ɗaukar duk wani measurements nata da suke buƙata Mummy na tsaye akansu tana bada order har suka kammala sukai musu sallama suka tafi, kamar yadda Mummy tayi ma Natasha alƙawari kuwa seda ta latsa service ɗin nata jin uban dollars ɗin datake charging ba shiri Mummy tace mata tafasa zasuyi magana da Mr Farouq kawai,
Designer ɗin ta mata murmushi suka wuce.
 Suna fita Mummy tace Imsal ta saka hijab ɗinta zata rakata gidan Hajiya Nafisa batai mata musuba tasaka hijab ɗinta tafito suka wuce zuwa gidansu Abdullah ɗin suna tafiya tana jin ƙirjinta na bugawa kamar ze fashe ya fito, ahaka suka ƙarasa.

Aunty salma suka samu afalo tai musu lale marhaban tana tambayar Imsal ya jikin nata ta amsa mata da faɗin 
"Da sauƙi alhmdlh"
tace mata
"Allah yaƙara sauƙi"
Kamshin turaren dataji ne yasata zama stiff awuri ɗaya, ta rintse idanuwanta tana addu'ar Allah yasa bashi bane domin har yanzun batada karfin gwiwar fuskantar shi akan maganar da Mummy tazo mata dashi,
Bata gama rufe bakinta ba taji sassanyar muryarsa yana gaisheda Mummy abin mamaki cikeda fara'a taga Mummy tana amsawa tana faɗin
"Lpy lau Doctor alhmdlh, ykk, ya hutu?"
Yace 
"Alhmdllh Mummy barka da shigowa"
tace 
"yauwa"
Shikansa deep down yana mamakin politeness ɗin nata amman dai kawai yamiƙe dayake Imsal tajuya musu baya yasa Mummy faɗin 
"Imsal bakya ganin yayan kine baki gaidashi ba,"
Aɗan rikice ta juyo tana ɓoye rabin face ɗinta a hijab taɗan risina tana faɗin 
"Ina....in...ina wuni ya mu..."
Kasa ƙarasa tai jin kamshin turarensa daf da ita yana kallonta da sauri taɗago idonta yafaɗa cikin nasa dayaga yawani shanye ya faɗa kamar wanda yakwana uku beyi barci ba kana kallonsa kasan da damuwa atareda shi sunkaɗa sunyi jajir.
"Yayaa...yah.. Mu'allim"
Tashiga inda inda saboda yadda ta rikice sanin Mummy na falon, aunty salma ma haka duk suna kallonsu,
Ahankali yace mata
"Yah umri kinaso kiyi kisane?"

Alhamdulillah Masha Allah kamar yadda na faɗa muku tun farko Imsal paid book ne we've done three free books so far, munyi AYSAM, INTENSE LOVE and EHSAAS duk free.
Anan na kawo karshen free pages na Imsal,
Pay 300 naira only into 
Opay
 ***
Fatima Rufa'i Nasidi 
To join Imsal premium lounge inda zamu cigaba da posting daily kamar yadda muka saba.



It's fatoumspassion IMSAL 
Don't forget to 
Like
Share
Comment 
Vote

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol