Free chapter · Read without an account
37
Motar Turaki bata tsaya a ko'ina ba sai a compound na cikin company na su, ƙarfe biyar na yamma a lokacin, and at that time an ma yi closing, bai san exact abin da ya shigo da shi ba, kawai ɓacin ransa ya kaisa.
Ya yi parking yana daɗa tabbatar da duka glasses na motar a rufe suke, ya kunna karatun qur'ani sannan ya buɗe lock. Ya kalli Fullo da har lokacin kanta ke kife a gefen kafaɗarsa, tun da suka taho take masa magiya da roƙon ya yi driving a hankali ta ga baida hankalin dainawa shikenan sai ta yi shiru, kuma tsoron da take ji shi ya hanata ɗagowa a kafaɗar tasa.
Wucewar sakanni ashirin yana kallonta, yana jin yadda numfashinta ke sauka a hankali, a tunaninsa duk bacci ne take yi, nan kuwa tsabagen zuciya ce tasa ta yi luff kamar wadda baccinta ya yi mugun nisa, wani irin zafi take ji a zuciyarta kamar ana rura wuta, in ace ta ɗago a ɗazu da tabbas babu abin da zai hana hannuwanta shaƙe Turaki, in yaso su yi accident ɗin da gasken gasken.
Kafaɗarsa ya janye nan take kanta ya ƙwalu da kujeran, ta buɗe ido a hankali tana kallon inda suke, bata ko motsa ba har ya fice daga motar, tana kallo ya saka lock ya wuce ya barta, ita kuma ta rakasa da ido.
Tana ganin yadda ƴan tsirarrun staffs da ba su wuce ba kowa na gaida shi, shi kuma yana ɗaga musu hannu.
Duk ƙoƙarin da ta yi don ganin lock ɗin motar ya fita ta kasa, kenan rufeta ya yi a motar ya tafi ya barta? Koma mai zai faru da ita ya faru da ita? To me yake nufi da ɗaukota ɗin? Ga shi ya kashe Ac balle ta samu sauƙin zafin gari da na zuciyarta da take ji.
Wani malolon baƙin ciki ya tokare mata zuciya, sai ta kifa kai da gwiwa ta fashe da kuka, kuka take sosai har tana jin kamar zata shiɗe, ga kanta na uban sara mata, ga zufa duk ta wanke mata jiki, sai da ta yi mai isarta tukunna ta ɗago tana goge hawayen, tana jan majinar hancinta ta ƙara trying buɗe motar amma taƙi buɗuwa.
Sai kawai ta jinginar da kanta jikin kujerar ƙirjinta sai bugawa yake, ta cikin glass ɗin ta fahimci magriba ta gabato saboda yanayin yadda garin ya lulluɓe, zuwa lokacin duk staffs sun ɗaɗe sai mai gadi kawai da take iya hangowa ta cikin mirror. Ta rufe idonta tana bin suratul Yusuf da ke tashi cikin ƙira'ar Yousuf Kalo.
Turaki kuwa tunda ya shiga office ɗinsa zama ya yi kawai ya rufe idonsa, ya yi hakan ne kawai saboda temper ɗinsa yay cool, dan in yaci gaba da kasancewa tare da ita a yanda yake mugun jin haushin abin da tayi ba abin da zai hana sa illata ta. Sai da ya ɗauki tsawon awa guda bai motsa a yanda yake ba, yana kallon kira daga different numbers na shigowa wayarsa amma babu ɗaya da yay picking.
Fullo dai har sannan tana zaune sai wurga idanu kawai take yi, Allah ɗaya yasan yadda take ji a cikin ranta, ta ja Allah ya isa tafi kai ashirin, in ace da wani abu da zata iya fasa glass ɗin tuni ta fasa ta fita.
Tana cikin tunani a ranta sai taga Turaki ya fito daga wani building daban da inda ya shiga ɗazu, cikin sauri yake tafiya yana sauke hannun rigarsa da ya tattare, da alamu alwala ya yi zai wuce masallaci tunda ga ruwa nan a fusakarsa.
Bata ɗauke idonta akansa ba har sai da ta daina ganinsa, bayan minti goma sai ta ji lock ɗin motar ya fita, kuma kamin ta kai ga buɗe murfin idonta ta ji ƙofar side ɗin da take ta buɗe.
"Out". Ta ji muryarsa ta shiga kunnenta a lokacin da take buɗe idonta duka.
Kamar ta yi banza da shi sai kuma ta ji tana tsoron yin hakan, Allah shahidi bata tsoron uban kowa a duniyar nan amma tana mugun shakkar Turaki.
Ta tattaro mayafinta tana ƙudundune jikinta sannan ta fito a cikin motar ta tsaya a gefensa, tana fitowa ya rufe ya yi gaba yana cewa da ita,"Follow me".
Tabi bayansa tana ɗan kalle-kalle, sai yaba kyan company ɗin take yi, daga waje ma kenan ina kuma ga an shiga ciki.
Suka shiga cikin office ɗinsa sannan suka wuce cikin wani ƙaton parlo, inda anan ne Turaki ke hutawa.
"Ki yi sallah". Abin da ya ce mata kenan ya wuceta ya zauna kan ƙaton farar cushion.
Fullo ta kalla haɗuwar parlon ta ƙara kallo tana mai jinjina uban yawan dukiyar da aka kashe wajen ginin company ɗin da kuma abin da aka zuba a cikin office ɗin, wato kuɗi dai suna inda suke, talaka da baida su ne yake ganin kamar babu su ko sai an sha wuya za a same su, ko da ike suma ma su kuɗin dai ba ta sauƙi suka samu ba.
Kanta a ƙasa ta fuskanci kujerar da yake zaune, muryanta a hankali ta ce,"Banda alwala".
Yadda ta yi maganar kawai yasa shi ɗago da kansa yana kallonta, ko kurma ya ji sautin murayar nata yasan da ɓacin rai a ciki. Sosai yake kallonta da son gano abin da yasa ta yi uban hasken da yake gani ajikinta, ba haka yasan asalin hasken fatarta ba, to daga ina wannan mugun farin?.
Jin ya yi shiru ta ɗago kanta karaf suka haɗa ido, ta tsuke fuska da baki tana ƙara ɓata rai. Shi kuma ya yi mata nuni da hannu inda hanyar toilet take.
Bata motsa ba kawai ta tsaya, ita ba zata iya shiga toilet yana zaune a wurin nan ba, sai dai in su shekara a haka, in ya so daga baya ta rama sallolin.
Da kansa ya gane manufarta, hakan yasa ya miƙe ya fice bayan yace mata,"Don't waste my time".
Yana fita ta shiga toilet ɗin, cikin toilet ɗin kansa mugun ƙamshi yake kamar ba'a shigarsa. Ta yi alwalan ta fito, mayafinta ta yafa ta tayar da sallah akan darduman da ta gani.
La'asar da magriba tayi a haɗe, bayan ta idar ta duƙar da kanta saboda mugun sarawar da taji yana yi, ga jikinta ya fara zafi alamun fever na son kamata. Ita kanta ta san ma dole tayi zazzaɓi da ciwon kai ko saboda kukan da tasha a yau.
Minti ɗaya, biyu, uku har minti ashirin suka wuce Turaki na zaune office yana jiran fitowarta amma shiru. Cikin ransa ya ayyana duk yadda aka yi jira take ya koma ya ce mata ta fito, tsaki yaja ya tashi ya koma cikin parlon.
Zaune ya ganta har sannan akan darduman kaman mai lazimi, to amma jin motsinsa bai sa ta ɗago ba, alhalin ya santa da shegen tsoro, ya tsaya yana kallonta yaga dai durƙushen kanta kamar ba na lafiya ba tukunna ya ƙarasa ciki ya zauna kan kujerar dake kusa da ita.
Yasa hannu ya ɗago kanta looking at her innocent face da ya yi ja, with the other hand ya taɓa forehead nata yaji zafi rau. Ya rufe idonsa kaɗan ya buɗe yana ganin yadda hawaye ke suntiri akan kumatunta, kallon hawayen yake yana hango lokacin da yake zaune a gaban Hayyo yana faɗa masa cewar,"Ehh kamar uba nake a wurinta amma ni ba mahaifinta ba ne, wannan yarinyar da kake gani ai ƴar zina ce, ƙwarai ƴar gaba da fatiha ce ranka ya daɗe, mahaifiyarta ma mahaukaciya ce, garin haukar nata ne ta gudu shekaru da yawa har yanzu bamu ganta ba. Amma dai saboda a rufawa yarinyar asiri indai da gaske ka ke sonta ranka ya daɗe kawai ka biya sadakinta yanzu a take, batun sauran kayan al'ada da ake yi duk ba sai ka yi mata ba, yo ai rufa mata asiri zaka yi. Kuma kayan al'ada dama ba faɗar addini ba ce, sadakin dai nata kawai ka kawo itama idan an bata babu hankalin riƙe su, nawa Halima take gaba ɗaya. Ni ne maɗaurin aurenta fa, babu wanda ya san danginsu tunda a titi na tsinci uwar na ji tausayinta na aureta. Ita kuma tsohuwar da kake cewa Yarinyar na hannunta gaskiya to ban ma san wace ba, ƙila ma ko irin tsaffin nan ne macuta".
Ya ƙara hasko lokacin da ya sa hannu a aljihunsa domin ɗauko kuɗi, amma sai ya ji babu komai a ciki. Idonsa ya mayar kan Hayyo, mutumin da ya ƙara ganin tsananin kamannin Fullo a tare da shi. Irin kamannin nan da ana gani an san kai jinin wanene ne. Sai dai fuskar Hayyon ita kanta tana ƙaryata duk kalaman da yake faɗa. Kai kana kallonsa ka san ko magana goma zai yi, da ƙyar guda ɗaya za ta zama tsantsar gaskiya. Shi ya sa tun a lokacin babu wata magana da yake faɗa masa ya gasgata; kana ji ka san ƙarya ce tsagwaronta. Gaba ɗaya babu wata alamar nagarta tattare da dattijon. Rashin nagartarsa da yawan ƙaryarsa ma sun riga sun tsofar da shi fiye da shekarunsa.
Ya sauke numfashi a hankali yana jin wani irin abu a ransa. Ya ji Zuciyarsa ta ƙara ƙarfafa masa ya miƙa sadakin Fullo. Ko da ba zai aure ta saboda taimakon da ta yi masa ba, tabbas ta cancanci a aure ta saboda rashin dacewar uban da ta samu. Domin ko kaffara ba zai yi ba, Hayyo ne mahaifinta, kuma Hayyo ba uban ƙwarai ba ne, Kuma Hayyo irin uban da suke jefa rayuwar ƴaƴansu cikin halaka ne, ko a yanzu ya san son abin duniya ne ke ta walagigi da shi, shine dalilinsa na ƙaguwa ya ga ya bayar da sadakin. Shi kuma lura da hakan yasa ya ƙara jin zai bayar, ko da bata taɓa taimakonsa ba, balle kuma ta taimake shi.
To amma da me zai bayar da sadakin nata? Ya yi shiru yana tunani cikin ransa, ko kaɗan ba ya so ya miƙe daga kan tabarmar nan ba tare da ya mallaki yarinyar da ta dinƙa cusa kanta a haɗari ba saboda kawai ta cece shi, ba don so ko kuma wani abu daban ba, sai don kyakykyawar zuciyarta. Kawai yana son ta, yana jin ta a ransa, kamar yadda ya ga Maama tana sonta, kuma tana jinta a ranta.
Yana iya tuna yadda ya dinga jin kallon da Hayyo ke yi masa, yana tuna furucin da Hayyo ya yi masa kan cewar,"Yaro in har babu sadakin yarinyar nan ka zo a yau, to ina mai tabbatar maka da cewar ba rabonka ba ce, domin kuwa tun tana ƙarama akwai wani tsoho da ya roƙi a ba shi ita, to banda ma dai tasa ƙafa ta gudu da maganar da nake shaida maka yanzu ta yi ƴaƴa da yawa, ka san yaran ƙauye haihuwar kaji suke yi. Don haka kana tafiya zan yi masa magana ya bada sadakinta, in ya so tunda Allah yasa kai kasan inda take, sai ka yi mana jagoranci mu je mu taho da ita".
"Zan bayar da sadaki, kuma za a ɗaura mana aure, amma sai na ga shedu".
Hakan ya san ya faɗa masa, kuma minti guda ba a ƙara ba Hayyo ya yunƙura ya miƙe tsaye. Ya kalli yadda ya gyara jikinsa, ya taka ya shiga cikin gidansa, ya ɗau tsawon minti biyu kafin ya fito kansa sanye da hula, da kuma wata shimfiɗeɗiyar babbar riga da ya saka duk ta ji jiki. Kuma bayan fitowar tasa ne ya ɗan gota shi sannan ya ce masa,"Ta so mu je".
Ya sani ƙarfin gwiwar yau zai mallaketa ne ya ɗaga shi tsaye a lokacin ba tare ma da ya sani ba.
"Tafiyar da ɗan nisa, zaka iya jurewa ko zaka haƙura?."
"Babu damuwa, mu je Baba."
Haka ya dinƙa bin bayan Hayyo, wanda ke tafe yana tangal tangal kamar mashayi. Sakanni kaɗan sai ya tofar da yawun aswakin bakinsa, a haka har dai suka iso bakin masallaci. Hayyo ne ya fara shiga ciki, ya bar shi tsaye a ƙofar masallacin, kuma sai da aka ɗauki kusan mintina goma sha biyar kafin wani mutum ya leƙo ya ce masa "Bismillah, shigo da ga ciki."
Yana iya tunawa a lokacin da ya cire takalman ƙafarsa, a jikinsa ya ke jin tamkar Fullo ce ta riƙe hannunsa gam, ta riƙe shi da wannan hannun da ba ya iya tsayawa daga karkarwa idan tana gabansa. Kuma kallonsa take ido cikin ido, ƙwayar idon nan nata ta cika taf da tarin hawaye, a lokacin zai iya rantsewa ita yake gani a gabansa, ita yake kallo miraran a irin yanayin yadda zuciyarsa ke haska masa hotonta. Kuma wannan kallon innocent face ɗin na ta da yake yi, shi ya cicciɓa shi ya shiga cikin masallacin da sauri cike da ƙwarin gwiwa.
Mutum shida ciki har da Hayyo su ya tarar suna fuskantar Limamin masallacin. Ya gane Limamin domin a ɗazu da ya shigo garin shi ya yi masa jagoranci zuwa babban masallacin anguwar suka yi sallar juma'a. Sai sauran mutum biyar ɗin da ke zaune bayan Hayyo bai san su waye ba, amma daga suffarsu ya san ba mutanen banza bane, akwai dattijantaka ta ƙwarai a tare da su.
Yana tuna sanda Liman ya buɗe baki ya tambayesa ina waliyansa, kuma a lokacin buɗe baki ya yi ya ce,"Ni kaɗai ne, ni ɗaya na zo neman auren nan, ba ni da kowa a garin nan. Ban san wa zai yi min wakilci ba, ya halatta na karɓi auren ni kaɗai Liman?".
Hakan ya faɗa, kuma daga faɗar hakan Liman ya buɗe baki ya shiga koro jawabi, jawabin da duk suka zuba masa ido suna kallonsa da saurarensa da buɗaɗɗiyar zuciya har ya sauke numfashi.
"Kamar yadda ka tambaya ko ya halatta ka karɓawa kanka aure, to a bisa duba na sani da addini, babu wani abin shakka a nan. Shari’ar Musulunci ta ba wa namiji baligi, mai hankali, ƴancin ƙulla yarjejeniyar aure da kansa ba tare da sai ya turo wani ya tsaya masa ba. Domin shi namiji, shi ne waliyyin kansa. Bambancin namiji da mace a wannan gaɓar shi ne, ita mace tana buƙatar waliyyi ne domin kiyaye mutuncinta da kuma tabbatar da cewa an yi mata zaɓi na ƙwarai. Idan har ka amince, ka kuma amshi yarjejeniyar a gaban shaidu adalai, to aurenka ya inganta babu ko tantama. Ganin cewa kai baƙo ne a nan, shari'a ba ta sanya maka takunkumin da zai hana ka mallakar abin da kake so ba muddin dai sauran sharuɗɗan aure sun cika.
Manzon Allah (SAW) ya taɓa ɗaura auren wani bawan Allah a masallaci, inda shi mutumin ya karɓi auren da kansa a gaban Annabi (SAW), kuma aka sanya koyar da Alkur’ani a matsayin sadakinsa. Wannan ya nuna mana cewa aurenka zai inganta muddin aka samu shaidu adalai, amincewar waliyyin mace, da kuma sadaki. Amma duk da haka, shari’a ta ba ka damar naɗa wakili idan ba ka so ka karɓa da kanka."
Ba zai mance da yadda ya sauke wani nannauyan numfashi ba, yana jin yadda kalaman Liman suka ratsa shi, suka kuma share masa duk wata fargaba da yake tafe da ita. Ya ɗaga kai ya kalli Liman cikin girmamawa, sannan ya ce,"Na gode ƙwarai Liman da wannan haske da ka ba ni. Amma tunda ni baƙo ne a nan, kuma ina son komai ya tafi cikin daraja da amana, ina so ka zaɓa min mutum guda daga cikin waɗannan manyan mutanen da suke tare da kai, ya zama wakilina wajen karɓar wannan auren a madadina. Na amince da duk wanda ka zaɓa, domin na san ba za ka zaɓi wanda ba zai tsaya min bisa gaskiya ba."
Wannan furuci nasa ya sa mutum biyar ɗin da ke kusa da Hayyo suka fara kallon-kallo, kowannensu yana jin wani irin nauyi ya ziyarci zuciyarsa. Hayyo kuwa tuni jikinsa ya fara sanyi, domin ya ga yadda yake neman dagewa a ƙulla igiyar da ba za a iya tsinke ta cikin sauƙi ba. Hayyon da yake da wata manufa ta daban a game da auren.
Liman ya yi murmushin jin daɗi, ya nuna ɗaya daga cikin dattijan da ke gefensa, wanda fuskarsa take cike da natsuwa da haiba, ya ce,"Tunda ka buƙaci haka, to Malam Jibril zai zama wakilinka. Shi zai karɓi auren a madadin duk wani dangi naka da babu su a nan, kuma muna fatan Allah ya sanya albarka a cikin wannan auren."
A nan ne kowa ya gyara zama, aka fara shirye-shiryen ɗaura auren da ba a taɓa yin irinsa ba a wannan ƙauyen. Don hatta shi Liman ɗin bai taɓa ɗaura aure irin haka ba.
Daidai lokacin da Malam Jibril ya gyara zama domin karɓar wannan nauyi, sai Turaki ya sauke idanunsa ƙasa, yana jan azurfar da ke yatsansa, azurfar da Maama ce ta saka masa ita a lokacin da yake shekaru takwas a duniya. Amma yanzu da yake ja, ji da kallo yake tamkar Fullo ce ke cirewa da maidawa tana wasa da yatsan nasa. Ya sauke numfashi, kafin ya ɗaga kai ya kalli Liman cikin wata iriyar murya, wadda bai taɓa jin kansa da ita ba, sai dai ya san ba komai yasa ta canjawa ba sai shauƙi jin zai mallaki waccan yarinyar da babu tsoka a jikinta sai ƙasusuwa, ƙasusuwan da ke aikin rawa a duk lokacin da suka gan shi.
Akwai ɗan rauni a muryar tasa lokacin da yake cewa,"Liman sai dai wani hanzari ba gudu ba. Ina son yin wannan auren da dukkan zuciyata, a halin yanzu ba ni da kuɗin sadaki a hannuna. Yanayin da na tsinci kaina ya sa ba zan iya amfani da asusun bankina ba. Shin ya halatta na nemi aron kuɗi a wurin wani na bayar da sadakin, ko kuwa lallai sai kuɗin da yake mallakina ne na ƙashin kaina zan bayar domin auren ya inganta?"
Ba zai taɓa mancewa da yadda tambayar tasa ta sanya ɗakin yin tsit ba, don hatta ƙarar fanka sai da ta ɗauke. Kuma tambayar tasa ce tasa Hayyo saurin ɗagowa ya watsa masa wani banzan kallo, kallon ashe ma baka shirya ba ka tsaya ɓata min lokaci, kallon ashe ba wanda zan tatsi kuɗinsa ba ne talaka ne faƙiri irina.
Liman ya yi gyara murya, ya kalla Turaki da murmushi a fuskarsa, da wani irin tausayi da kuma girmamawa, sannan ya fara koro bayani.
"Game da tambayarka, shari'ar Musulunci ta sauƙaƙa lamarin aure domin kada a bar ƙofa ga alfasha. Sadaki haƙƙi ne na mace, amma ba lallai sai kuɗin da kake da su a aljihunka ba a wannan lokacin. Idan mutum ya ari kuɗi ya biya sadaki, auren ya inganta muddin dai yana da niyyar biya kuma ya amshi aron ne a matsayin mallakinsa."
Liman ya ci gaba da bayani, yana nuna yadda faɗin shari'a yake a wannan gaɓar. "Bugu da ƙari, sadaki ba lallai sai kuɗi ba ne (Cash). Duk abin da yake da daraja a idon shari'a, wanda ake kira 'Mal', za a iya bayar da shi a matsayin sadaki. Idan mutum yana da dukiya kamar gida, fili, dabba, ko ma abun hawa, yana iya sanya shi a matsayin sadaki ko da kuwa ba shi da ko sisi a hannunsa. Ma'ana, dukiyar da kake da ita a yanzu, koda ba kuɗi ba ne, muddin tana da daraja kuma ka mallaka wa matar taka ita, to aurenku ya inganta. Don haka, kar ka damu da batun transfer ko rashin cash; shari'a ta ba ka damar amfani da duk wata dukiya taka da kake da ita a nan don ƙulla wannan yarjejeniya ta aure."
Ya ji wani sanyi ya ziyarci zuciyarsa, ganin cewa lallai duk wanda ya dogara ga Allah, Allah zai samar masa da mafita ta inda ba ya zato. Nan take ya kai hannu cikin aljihunsa, ya zaro maƙullin motarsa, ya ajiye shi a gaban Liman yana mai cewa,"Idan har shari'a ta ba ni damar bayar da abin da na mallaka, to ga motata nan, na bayar da ita a matsayin sadakin Halima."
Wannan matakin nasa ya girgiza kowa a wurin, musamman Hayyo wanda idonsa ya zaro ganin cewa ba kawai sadaki ya bayar ba, ya bayar da dukiyar da ta ninka kuɗin da ya yi tsammanin zai samu daga wajensa. Don kallo ɗaya ba sai ka yi na biyu zaka san kuɗi sun samu wurin zama a tare da Turaki, to bai tsammaci cewar zai iya sadaukar da abin da ya bayar ɗin ba, duk da cewa bai ga kalar abin hawar da ya zo da shi ba.
Ba zai taɓa mance yadda Hayyo ya dinƙa kallon maƙullin motar ba with so much expression, har ƙwayar idonsa irin ta Fullo na yin kamar zata faɗo waje. Kuma da mamakinsa a lokacin, sai Hayyo ya dakatar da Liman, saboda gani yake tamkar motar da Turaki ya ba da kuɗinta ba za su haura sama da dubu hamsin ba, don zai iya yiwuwa kura da fatar akuya ne shi ɗin. Don haka ya ce da Liman a ba shi minti kaɗan, ya kalla Turaki ya ce daga ina motar tasa take, ya faɗa masa cewar tana bayan gidansa. A lokacin Hayyo ya ciro wayarsa, ya kira ɗansa a waya ya basa umarnin ya je waje kaza ya gano masa akwai mota a wajen, idan har akwai to ya ƙarewa motar kallon tsab, sannan ya zo masallaci yanzu yana son ganinsa.
Babu jimawa sai ga Abdulhamid a masallacin, saurayin shima mai tsananin kama da Fullo ka rantse da Allah identical twins ne, idan bai manta ba sunan da Hayyo ya kira saurayin da shi ,"Hamid".
Kuma ko da Hamid ɗin ya shigo masallacin dukkansu ya yi jama'u wurin gaishe da su, Sannan Hayyo yana dubansa ya ce motar da ka ga ni kuɗinta zai kai nawa?
And abin da Hamid ya sanarwa da Hayyo shi ne,"Abba babbar mota ce, irin wadda manyan ƙusoshin ƙasar nan ke hawa, zan iya ƙiyasin kuɗinta ya kai miliyan hamsin, amma ina da tabbacin ta haura hakan".
Kuma ba tare da ƙara yin wani bincike ko bayani ba, Hayyo ya kalli ƙwayar idon Liman ya ce masa,"Ka ɗaura auren nan take ba tare da ɓata lokaci ba".
Ya yi maganar yana wani makirin murmushi. Kuma cikin daƙiƙar da ba ta haura goma ba, aka yi komai aka gama. Aure ya ɗauru, auren da ya tabbata tsakanin Muhammad Turaki Habib, da Halima Hayyo.
Haka ya baro garin Taraba a train zuciyarsa cike da tarikan mamaki iri-iri a game da lamarin Fullo da mahafinta, duk da cewar ya so ya keɓe da Hamid to amma bai samu dama ba. Amma kuma bai taho face da lambar wayar Liman da kuma Malam Jibril da ya yi masa wakilci.
Fullo ta buɗe idonta da ke yi mata zafi tana kallonsa, idonsa a rufe yake, har sannan kuma bai saki kan nata ba.
In a cool voice nata ta ce da shi,"Please ka daina taɓani anyhow babu kyau. kuma don Allah ko kuɗin napep ne ka bani na koma gida, Maama da Boɗejo za su ne me ni, turarenka kuma zan biyaka in sha Allah".
A sannan Turaki ya buɗe idonsa yana ɗauke hannayensa akanta. Yana kallon gefe daban kamar zai yi magana sai ya fasa ya miƙe.
Ya nufi ƙofar fita yana cewa da ita,"Biyo ni". Ta tashi cikin sauri tabi bayansa.
Tunda suka hau titi take ta kallon hanya har suka iso asibitin Miyetti, fita ya yi a motar ya barta ita ɗaya ya shiga pharmacy ya sayo magunguna ya dawo, sannan suka ɗau hanyar gida.
Suna ƙarasawa gida Turaki ya yi parking sai Fullo ta kasa fitowa a motar, ta tsinci ƙafafunta da kasa yin motsi su fita daga motar. Tana kallo ya fice ya barta a ciki, sai ta bisa da ido tana kallo ya wuce side ɗin Boɗejo, gaba ɗaya ta rasa me take ji a tare da ita, tasa hannu zata buɗe motar ta fita sai ga motar Samha ta yi parking kusa da ta Turaki.
Da dukkan alama tun fitar safe da tayi sai yanzu ta dawo, Fullo tayi saurin maida ƙofar tana rufewa a hankali gudun kar ta ji ƙara, kasancewar tend glass ne amotar hakan yasa babu mai hangota a ciki sai dai ita ta ga na waje. Ta yi ɗuff ta ɗauke wuta dan ji take kamar za su iya jiyo numfashinta.
Sameer ta ga ya fito daga driver seat sannan Samha ta fito ta ɗayan seat ɗin, ta zagayo ta side ɗin Sameer ta karɓi roban Maltina a hannun Sameer, sun ɗauka a ƙalla minti uku suna magana kamin su saki murmushi, tukunna suka bar wajen suna wucewa cikin gida.
Fullo ta ji ta wani girgiza, bata san wannan shirin na su kuma na menene ba, bata ji su ba, bata san me suka ce ba. Ta ja numfashi ta ɗauka ledar maganin da Turaki ya saya ta fita daga motar, cikin saurin tafiyarta ta yi side na Boɗejo cikin zuciyarta tana ta fatan kar Allah ya bawa Samha ikon ganin Turaki, haka kawai zuciyarta ke faɗa mata wannan roban malt ɗin ba malt bane kawai a ciki, haka kuma ba don kowa aka shigo da shi ba sai don Turaki, tafiya take tana harɗewa tana ƙara jin tsoron mutum a cikin ranta, idan ba a film ba bata taɓa tunanin za'a iya samun siblings ɗin da za su iya kashe ɗan uwansu a gaske ba, sai ga shi yanzu ta gani a zahiri, abin na faruwa a inda take rayuwa.
Maganar Hajiya Madina ta haska cikin kanta, lokacin da ta ce mata,_"Ba halina ba ne, ba haka zuciyata take ba, tunda Allah ya halicce ni banda mugun nufi akan kowa, zuciyata bata da tsatsa ko kaɗan, kullum roƙon Allah nake kar yasa na cuci wani a rayuwata, amma ban san a ina Samha da Sameer suka ɗauko wannan mugun halin ba, ban sa ni ba, dan ba halin mahaifinsu ba ne..."._ Kasa ƙarasa maganar ta yi a lokacin saboda kukan da ya ƙwace mata.
Kamar wadda ta yi gudun famfalaki haka Fullo ta shiga parlon Boɗejo, gaba ɗaya ma sallamar ta mance da ita. Babu kowa a parlo dan haka kai tsaye bedroom na Boɗejon ta wuce, ta san ba zai wuce can Turaki ya yi ba, ta buɗe ƙofar tana shiga da sallama.
Ilham da ke gefen Turaki a zaune ta amsa sallamar tana faɗin,"Bismillah".
Gaba ɗaya Fillo sai ta ji ƙafafuwanta sun yi matuƙar sanyi, bata san dalili ba amma haka kawai ta ji gabanta ya faɗi da ganin Ilham da tayi da kuma yadda ta ganta zaune manne a jikin Turaki.
Zuciyarta ta ji na faɗa mata cewar kawai ta yi reverse, amma sai ta ji ta kasa gaba ta kasa baya.
Ilham na kallonta sosai ta ce,"Ki shigo mana, ba aiki za ki yi ba?".
Kan Fullo a ƙasa ta ce,"Ehh".
Ilham ta ce,"To bismillah".
Ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta, ta shigo ciki idonta a rufe tana jin kamar jiri ne ke neman ɗibarta ya zubar.
Ilham na riƙe da hannun Turaki ta ce,"To Hammah ba sai mu tafi tare ba, tun fa da na dawo ban ƙara zuwa ko'ina ba, Mami sai ta ce wai a'a, kuma ni ko dubai ina so na je na sha iska, please Hammah zan bika".
Ya kama hancinta yaja ba tare da ya ce komai ba, wucewar adadin wasu sakanni ya miƙe ya fita Ilham tabi bayansa, Fullo kuma da ke tsaye gefe guda ta bisu da kallo.
Suna fita ta jefar da ledar hannunta akan kujera, ta ji kamar tana so tayi kuka, amma ba zata yin ba saboda har yanzu kanta ciwo yake yi mata. Kuma ma bata san dalilin da zai sa ta yi kukan ba, ta rumtse idonta sosai, da ƙyar ta iya gyara abin da zata gyara a ɗakin cikin few minutes ta fice.
Tana fitowa parlon ta tadda Turaki zaune a kan kujera shi ɗaya, da remote hannunsa yana sauya channel. Ta tsaya tana kalle-kalle ko zata ga Ilham, sai dai da dukkan alama bata nan.
Table ɗin gabansa tabi da kallo, fruites ne a cikin plate sai roban malt a gefen plate ɗin.
Tayi tsaye daga inda take sai kallon roban take yi, kamar mai son ganin wani abu aciki.
Ta yiwa Turaki kallo ɗaya ta ɗauke kai, bata san me yasa ba haka kawai ta ji tana mugun jin haushinsa fiye da sauran lokutan baya. Inda yake ta ƙarasa ta aje ledan maganin kusa da shi tana cewa,"Ka manta a mota".
Sannan ta kai hannu kan table ɗin ta ɗauke roban malt ɗin zata bar wajen.
Ya yi saurin riƙo hannunta ya dawo da ita,"Ɗauka ki tafi da su".
Ta waiga ta kalla ledan sannan ta kallesa, ta ce,"Maganin da ka saya ne fa".
Shima ɗin yana kallonta ya ce,"Nayi miki kama da mara lafiya?".
Sai ya galla mata harara ya ce,"Ɗauka ki wuce da shi".
Kamar zata yi kuka ta ce,"Shi maganin dama haka kawai ake shansa? Kawai da ka sami magani sai ka ce dole sai na sha. Ka barni na wuce please Kaka na can na jirana".
Ya janyota da ƙarfi sai gata zaune kan kujerar kusa da shi. Zai ƙwace roban malt ɗin ta damƙe da kyau.
Ya dinƙa kallonta da mamaki kafin ya iya buɗe baki ya ce mata,"Mene matsalar ki ne wai?".
Ɗan ƙaramin bakinta ta tsuke ta turo gaba, idonta da kallon yatsun ƙafarsa da ke burgeta ta ce,"Ni ba ni da matsalar komai. Kai ne mai matsaltsalu, ka dage da azkar, kuma ka daina bari mata na taɓaka anyhow, shawara na ke baka kyauta bana buƙatar sadaƙa."
Shi ɗaya ya ji sautin gajeriyar dariyar da ya saki. Ta wutsiyar ido kawai yake ta kallonta. Kamar ya kai hannu ya matse bakin rashin kunyartata haka yake ji. Sai kawai ya tamke fuska yana cewa,"Aje abin da kika ɗauka".
Ta maƙe kafaɗa ba tare da ta ce komai ba. Ya ƙara ware idonsa yana kallonta da mamaki, ta rufe ido ta cije fuska tana son janyewa a kusa da shi ta tashi.
Jin ba zai saketa ba ta buɗe ido ta kallesa ta ce,"Ni wannan nake son sha ba magani ba, don Allah ka bar min".
Bai san time ɗin da ya saki baki ba yana kallonta galala, in bai manta ba lokacin da aka kwantar da ita a asibiti uban malts ɗin da aka ajiye ai duk ƴan dubiya aka dinƙa bawa saboda bata sha, hasalima ko anyi forcing nata tasha sai ta yi amansa, amma yanzu shi take ce ma malt take son sha.
Sai ya sassauta riƙon da ya yi mata yana ƙara tamke fuskarsa ya ce,"Aje na ce, ko ni sa'an wasanki ne wai".
Ta kallesa taga yadda idonsa ya kaɗa ya yi jawur, kuma ya ƙanƙance. Kawai ta kifa goshinta akan ƙafarsa ta fashe da kuka.
Kuma a hankali ya ji kamar mintsininsa fa take yi a cinya.
Ya waiga ya ga har yanzu Ilham bata fito a kitchen ba, kuma babu kowa da zai iya shigowa, don haka da azama ya miƙe ya ɗau ledan drugs ɗin, sannan ya kama hannun Fullo suka fice daga parlon, tana ta tirjewa yaƙi sakinta har sai da suka shiga ɗakinsa, ya wurgata kan gado yana saka key a jikin ƙofar, sai dai abin da ya matuƙar ba shi mamaki yana waigowa yaga ta buɗe roban malt ɗin tana zubar da shi a ƙasan tiles.