Free chapter · Read without an account
KUSKURE 18
*KUSKURE*
By maman shaheed
shafi na shatakwas
Iyayen nawwara nada Hali ba laifi sunfi karfin komai a gidan su ,sunada rufin Asiri.
Koda sukaje gidan da Indo ,yaune shigan Indo gidan na farko ,suka gaishe da ummah su nawwara ,ta karbi Indo cikin sakin fuska da fara'a Indo ma nata girmamata ,daga Nan d'akin nawwara suka shiga sunata Hira ,yau Dadi y kasheta gata ga Indo acikin gidan su .
Sunata Hira kamar sun shekara ,har nawwara take cemata "Indo sunanki fa Aisha Amman kike amsa Indo"
Indo tayi dariya tace "wlh Nima dai yanzu bana son sunan innace ta ke kirana dashi shikenan 'yan gari suka Kama"
Nawwara tace to "wlh daga yau Aishatu zandinga ce Miki ,Indo tasa dariya"
Sunata Hira ganin yadda nawwara take bala'en son ta yasa ta Bata tarihin Rayuwar ta d Wanda tasani d wayon ta d Wanda inna ta sanar Mata kaf.
Nawwara har kuka Tama Indo ,tace Kuma ta Dena Aiki a gidan su Noor ,Indo tace Sam dashi take taimaka ma Inna.
Nawara ba yadda batayi ba har tace zata dinga koya Mata d'inki sai ta dingayi Dan ta rike kanta ,Indo tace zata koyi dinki Dan tanaso dama can Amman ba yanzu ba.
Itako dama telace dinkuna takeyi na garari .
Haka nawwara ta hak'ura , har indon tace zata tafi , nawwaran ta rakata har gidan Inna .
Nawara tafi Indo sanin wasu abubuwa na rayuwa zata d'an girmi Indo kad'an sanan ta fita wayo da sanin duniya me take cikin Dan kanta awaye yake bakamar Indo ba itama ba irin wayewar Nan ta 'yan duniya bane ,aa ta sanin darasin tafiya da zamani Dan tanada Nutsuwa d hankali g ilimi Dan ta gama secondary school d'in ta tanason cigaba Amman saurayin ta yace sai dai ta Bari in sukayi Aure sai taci gaba a gidan sa.
Bayan Indo t dawo gdn Inna ,yamma tayi lis ,Inna tace tazo ta tafi kartayi dare a hanya tunda da d'an tafiya tsakanin su Dan sai an hau mota ..
Cikin kewar inna ta Ma inna sallama t mik'a Mata ragowan kud'in hannun ta ,Inna nata shi Mata Albarka na mota kawai ta Bari ta d'ebo gyada d Aya zata tafima d Noor d Haneef har d'atar da tasaimusu dazu t d'auko Tama Inna sallama ta tafi.
Tana zuwa bakin layin su ta Sami a daidaita sai gidan su Noor.
Koda ta shiga , Tama Mai gadi sannu d gida , y amsa ta wuce parlour .
Tana sallama Noor da Haneef d gudu suka taso suka Mata oyoyo suna tambayar ta Ina taje sunata nemanta .
Momyn su ko baki sake take kallon su har dadyn su d be Jima d shigowa gidan ba, da gani Dan ko takalmi be cire ba.
Momyn su cewa" tayi wani sabon salo! "Tayi mamakin Dan Bata Saba ganin haka ba.
Noor ce tace" wlh aunty Indo d bakya Nan gidan ba dad'i"
.dadyn sune y bi momyn su d wani irin kallo Mai cike d tuni d nuni agareta Dan duk sunji Abin da Noor ta fada. Shide ya mata kallon in Kinji zafi ki gyara.
Jin haushin kalon d ya Mata yasa ,tace ma noor "dan uwarki da kin sani da binta kikayi kuka tafi marakunyar yarinya magananya"
itako Noor ta turo baki alamun taji haushin zagin d uwar ta Mata Dan basa zagi a gidan Kuma Indo tace musu Mai zagi za a k'onashi a wuta.
Aiko ganin ta turo Mata baki momyn su ta taso d sauri t d'aga hannu zata mareta.
safwan y Kama hannu y wugar gefe yace "ko kusa ko Alama karki sake ko a bayan idona ki dakesu akan rashin dalilin komai yarinya Kuma gaskia ta fad'a ai, in Kinji zafi ki gyara"
Cikin mamaki NAWAL tace " kana ganin Tana turo min baki da rashin kunya Ka hanani hukunta ta ka nuna Mata rashin kunya abunyi ne?"
Yace "to meye acikin turo baki? Nawa ke Kika min a 'yan kwanakin Nan? Kuma me Kika koya Mata zagin yanzu fa da kika mata Ko kinmata zagin d Kika Mata Alhalin kinsan basa zagi na hanesu dashi? Kike karya min dokar gida yanzu? Ke meye hukuncin ki?"
"Kuma karki Kara cema yarana marasa kunya ,Kar ki k'ara zagin su bazan yadda d haka ba ,kema halin zagin d Kika aro kiyi gagawan mayarma duk Wanda y baki Dan be Sami karɓuwa ba ,yarana basa zagi bantaba ji ba sakamakon Basu Sami training d'in shi ba a gidan Nan kema Kuma ba halin ki bane shiyisa nace aro shi kikayi ,Dan haka ki kiyaye ,in ba haka ba zamu samu saɓani nida ke for d first time acikin Rayuwar Auren mu akan yara"
Gargad'in ya shigeta Dan haka ,a hassale tazo ta bangaje Indo saida suka kusa fad'awa jikin safwan d'in Indo d Noor d suke manne da junan su.
Safwan d'in nne y kamo kafad'an indon kafin ta gama fad'a Mai badan ya Ankara ba ,da jikin shi zasu fad'o gaba d'aya , Yana Ankara yayi saurin sake indon , tare d ta'auwizi (A'uzubillahi minashaid'anu la'enun rajim) k'irjin shi na bugawa da sauri da sauri ,a hankali yake sauke numfashin shi.
Ganin Abin ba sauk'i d'akin shi ya wuce Dan samun nutsuwa Mai inganci atare d illahirin jikin shi .
Itama indon ajiyar zuciya tayi Mai nauyi , ahankali ta samu 'yar Nutsuwa bayan ta zauna a kujera ,Tana tunani kala kala daga shigowar ta sai yanzu ta tuna ko gaishe su ma bata sake yi ba, dawowar ta ya dawo da tarzoma ita kam.
Daga zuwan ta gidan ,masifa har ta bud'e Indo agidan daga dawowar ta ?
Noor ko d Haneef suna jikin ta sunyi lif tanata shafa bayansu kamar ta samu kuliya .
Momyn su Noor shiri ma takamayi ,wato anma Bata Mata Rai a gidan Bari ta tafi aikin ta tabar musu gidan.
Bayan ta gama ta fito lokacin dadyn su Noor shima y fito zuwa masalaci ,suka had'u a parlour Indo t basu ayyar da ta taho musu dashi sunata ci suna Santi d k'aramin bakin SU.
Koda Noor taga dadyn ta ,cewa "tayi Dady bisimillah zakaci ayya?"
Cikin kulawa yace" Ina Kika samu Aya?"da ƙaramin bakin ta Tace" aunty indo ce ta kawo Mana Kuma da dad'i ci kaji"
Da sauri yace "yi hak'uri ci kayan ki sallah zani ,sai tayi fushi (kunsan yaro ba ko yaushe yakeson inyama tayin abinsa kaki karba ba ,sai yaji haushi ,zaman lpy kawai ka karba kaci ko bakaso ko da dabara ne ka nuna Mai kaci ka gode kawai)
Ganin tayi fushi yasa yace" sorry Noor d'ita ki ajiye min Inna dawo sallah zanci kinji "sanan ta saki ranta tace" toh Dady kuma fa sai kaci"shima Haneef yace "Nima zan ragema gyad'a ta Dady"
yace" to my Haneef Kai gyaɗa, Noor Kuma Aya a ajiye min sai na dawo" batare d ya Kali inda Indo take ba bare NAWAL.
Itako momyn su bayan ta gama yafa gyalen ta a saman after dress ɗin ta da ta gama sa Tom's d'in ta a k'afan ta ,tace ma Indo "kekuma ki kiyayeni wlh ku Kuma zanyi maganin kune tayi ƙwafa tana Shirin fita"
Dadyn su Noor ne yace "kokuma Ni nayi maganin ki ba kafin kiyi maganin su"
da har zata tanka Mai ganin Kar y Cigaba da dizga ta a gaban yaranta d Indo , Dan bacin ranta be wuce fad'an da ya Mata agaban Indo ba shi yafi bak'anta ranta .fuuuu ta fice a gidan ranta a bace da gayya ma Dan yayi magana ta fetse Shi.
Shima ,takalmi ya sa yayi waje da niyar tafia sallah masallaci, ko takanta be bi ba.
Indo suka Bari da lissafi ,ta sak'a ta kwance ,haka dai tunani fal ranta ,ga tunanin me momyn su Noor zata Mata .
Ranar ji tayi dama ba'a gidan zata kwana ba gashi tafi tunanin dare , gashi jiya Abin d y faru na shigowar dadyn su Noor duk d tasan arashin sani hakan ta faru ,Aiko yau Haneef be Isa ta barshi yaje d'akin shi ba bare yayi bacci azo kawo shi(kujimin Indo da k'ok'ari)
Noor ce tace zataci Abinci , bayan indon taje tayi sallah ta dawo ta kunna musu kallo mb3 .
A sanan Indo ta tafi duba kitchen ko momyn su tayi girki Amman bataga Alamar tayi ba ,Dan haka Indo ta dinga Al'ajabi Tana cewa "Anya momyn su Noor mace ce kuwa?" Tama iya dafa ruwan zafi kuwa ?" Bare indomei zuwa girki cikake?" afili ta dinga tambayar kanta.
(Hhhhh Indo kunada yawa masu tambayar , harda wasu readers d'in)
Cikin lokaci k'an k'ani ta d'ora musu julof d'in taliya d kifi ta manja dama Akwai ragowan lemun abarba data Bari a fridge.
Tana kitchen ,dadyn su Noor y dawo ,su Noor suka Mai oyoyo sunata shak'ar kamshin girkin Indo .
Cikin Nutsuwa dake d zafi Abincin ta rik'o shi a plate tazo kawo ma su Haneef .
Ganin dadyn su yana cin Aya d gyada yanata Santi Yana tsokanar su Noor yasa tayi turusss .
Ji tayi kamar ta koma , Amman ba Hali Dan y d'ago d kansa sun had'a ido ,jiki ba kwari ta k'araso tace" Noor ga Abincin naku Amman d zafi ku bari ya huce karkuci Abinci d zafi Dan ba kyau"
Haneef yace "to ,Ina na Dady Ni da Dady zanci"
Haneef y k'ular da Indo ,kamar ta dukeshi ,can dai ganin dadyn nasu bece komai ba Kuma Yana binta d Ido ,tayi karfin halin ce mai "in kawo ma yanzu dadyn su Noor ?"
Da Kai y Bata amsa ,be samu bakin magana ba.
Bayan taje ta zubo Mai ta zubo lemun abarba a jug ta kawo Mai ya karba yana ci Yana ba Haneef ,inda sabo ya mugun sabawa d girkin Indo Dan shi yakeci a Koda yaushe,tun Yana kin ci harya Saba yabi jikin shi Kuma daɗin shi yakeji sbd ya yarda da tsaftar ta.
Itako Indo ita d Noor suka rabe a gefe inda dadyn su baya ganin su sosai , sukaci , bayan sun gama Indo t kwashe komai ta gyara wajen .
Ta zauna t Fara kalo taga bazata iya ba , ji tayi duk ta takura Dan haka ta tashi ta tafi d'akin ta ta kwanta Tana ta tunanin rayuwa .
Jin shiru Bata fito ba ,ya fahimci nauyin sa takeji , Dan haka yace baze takurata ba Bari y barsu d su Noor shi y shiga daki Dan ayanzu itace farin cikin yaransa tunda uwar su ta zabi aikinta akansu .
Sawa yayi Noor ta kirata ,
Bayan ta kirata tazo ya ke tambayar ta "har kin kwanta ne?"
Tama rasa amsar da zata bashi dan Jin nauyin maganar tasa , tayi da kyar tace "aa gyara d'akin nakeyi"
Murmushi yayi yasan fad'a kawai tayi Dan haka yace "barinje kizo ki zauna dasu kafin ku kwanta" ,sanan tazo ta d'an d'ofana a Kan kujera kamar za Ace ket ta keta da gudu.
Koda ta zauna ganin yanata Hira d yaran shi yaki tafiya ,ita Kuma Taki sakin jiki ,
yasa tace" dadyn su Noor Dan Allah in su twins sun Sami hutu suzo su dinga tayamu kwana ,Naga an kusa jarabawa"
Shiru yayi na wani sakanni ,Yana nazarin inda maganar ta dosa.
Can ya nisa yace "zan duba na gani" ya tashi Yana ma su Noor sai da safe .
Haneef ne yace zai bishi ,Aiko Indo t gwalalo Ido Tana jira taga yadda zata Kaya ..
Dadyn su Noor ne yace "kayi hak'uri ka kwanta anan ko akaika daki ka kwanta ,Amman ka tabata kayi fitsari d Addu'a kafin kwanciya kaji my good boy?"
Sanan Indo ta samu sasauci ,Haneef yace "to Dady nice sleep bye"
Dadyn su shima yace "sleep more my kuratul ayni"
Y wuce d'akin shi Abin shi .