Free chapter · Read without an account
42
Hajiya Madina ya gani tana tahowa, da sauri ya tafi wurinta ya karɓi ledan kayan da ke hannunta, a gaban mota ya shigar da manyan ledan kaya kusan guda biyar, da gani kasan ba siyayya ba ce ta jarirai kamar yanda ta faɗa, siyayya ce ta musamman ta yi domin yin kyauta ga Fullo.
Driver ya buɗe mata back seat ta shiga, sai dai tun kafin ya zagayo ɓangarensa, ta buɗe motar ta leƙo kanta tana faɗin,"Ɗan Usaini ina ƴata? Ina Halimatu ta je?".
Ɗan Usaini ya dakata da buɗe motar ya ce,"Hajiya ai ta je kai miki waya, fitar ta ni kuma na je ɗan yin uzuri".
Hajiya Madina ta ce,"Ban gane nufinka ba".
Ya ce,"Ruwa na je kamawa, to ban san ba gaskiya ko ta dawo, na dai barta ta shiga ciki kai miki waya".
Lokaci ɗaya Hajiya Madina ta fito a motar gaba ɗaya,"Ka daina cewa ta kai min waya. Kai wayar tun yaushe ne? Kusan fa minti goma kenan, tana bani ta fito".
Ɗan Usaini na waige yabce,"To ko ta zo ta tarar bana ciki sai ta koma, bari na duba cikin store ɗin".
Ya faɗa yana barin bakin motar. Da sassarfa ya tsallaka side ɗin, ya shiga store ɗin, minti ɗaya zuwa biyar sai ga shi ya dawo da sanarwar bata ciki. Yana maimaita,"Amma dai ciki ta shiga kai miki wayar, ƙila ko wani wurin ta ɗan je."
HYa yi maganar yana ɗan takawa yana dube duben wajen. Hajiya Madina tabi bayansa. Lokacin hankalinta duk bai tashi ba amma dai ta tsorata, ina Fullon zata je? Idan cikin store ɗin ta koma ai tana shigowa za su yi clashing tunda tana daga bakin ƙofa tana biyan kuɗi.
Daga cikin store dai har wajensa babu Fullo, a wannan lokacin hankalin Hajiya Madina ya fara tashi, haka suka dinƙa zagayen arean wajen suna kiran sunanta suna dubawa amma ba ko alamarta.
Ɗan Usaini na tare da security na store ɗin ya ce da Hajiya Madina,"Ƙilan ko da ta shiga kai miki wayar makuwar hanyar fitowa ta yi".
Hajiya Madina dai tana tsaye ta kasa cewa komai, saboda yadda take jin numfashinta na neman yankewa, lissafi da tunani kawai take yi, iska ce a wajen ke ta kaɗawa amma ita zata iya rantsewa hucin zafi take ji a jikinta, zata iya rantsewa kamar ji da ganinta nema ya ke ya ɗauke.
Ƴar mutane ta ɓata a ta sanadinta? Me zata ce da Kakar yarinya? Me zata ce da wanda ke shirin aurenta?.
Lokaci ɗaya kanta ya yi wani mugun sarawa kawai sai ta fashe da kuka.
Mutane dai fa aka haɗu ana ta ƙara lalube, tsawon kusan minti talatin inuwar Fullo ma ba'a gani ba.
Da ƙyar Hajiya Madina ta iya picking call ɗin Baffa, ta faɗa masa halin da take ciki, sai dai kafin ya ce komai Hajiya Madina ta yanke jiki ta faɗi a lokacin, dalilin abin da taji Ɗan Usaini na faɗawa wasu mutane.
"To ni dai bana ce hakan ba ne, zargi kawai na ke da hasashe. Ka ga bakin bishiyar can anan na ga motar ta yi parking, kuma wallahi tun lokacin da zan tafi fitsarin na ji hankalina bai kwanta da motar ba, to kuma sanda na ke dawowa sai na ga motar na barin wajen, sai na bita da kallo har ta ɓacewa ganina, kasan Allah ba wai don saboda ɓatan yarinyar nan ba, jikina kawai na ji bai aminta da motar ba, Ya Rahmanu dai yasa ba ƴan garkuwa bane suka yi gaba da ita".
Nan da nan hankalinta ya gushe gaba ɗaya. Idanunta suka lumshe lokaci ɗaya, jikinta yana neman zamewa ƙasa. Da ƙyar aka iya tare ta kafin ta faɗi, aka yi saurin riƙeta ana kiran sunanta cikin firgici. Cikin ruɗani da tashin hankali aka shiga da ita zuwa mota, aka nufi asibiti da gaggawa.
Tun da suka isa aka karɓe ta cikin hanzari. Nurses suka yi saurin shiga da ita emergency room saboda yanayin da take ciki na suma. Ƙofar ɗakin suka tsaya cirko-cirko, kowanne da irin bugun zuciyar da yake ji a ƙirjinsa, suna jiran fitowar likita domin jin abin da zai ce.
Bai fi mintuna biyu ba aka ga likitan ya fito yana zare gloves ɗin hannunsa a hankali, sannan ya ƙarasa goge hannayensa da hand sanitizer.
A dai-dai lokacin ne kuma Baffa ya iso wajen da saurin taku, numfashinsa na fita da ƙarfi.
Ganinsa ya sa Ɗan Usaini ya yi yunƙurin ƙarasa wajensa, sai dai ko kallonsa Baffa bai tsaya yi ba.
Kai tsaye ya nufi likitan, idanunsa cike da damuwa da tashin hankali.
"Likita… ya jikin matata?" Ya tambaya da murya mai ɗan rawa.
Likitan ya ɗago yana kallonsa kafin ya ce, "Ka biyo ni office."
Da hanzari Baffan ya bishi. Kusan tare suka zauna akan kujera. Likita ya numfasa kafin ya fara magana.
"Ranka ya daɗe, Patient ɗinku BP ɗinta ya hau sosai. Akwai wani abu da ya firgita ta lokaci ɗaya ko ya ɗaga mata hankali fiye da yadda jikinta zai ɗauka, shi ya sa ta suma. Irin wannan tashin hankali ba shi da kyau musamman ga mutum mai shekaru irin nata."
Ya ɗan dakata kafin ya ƙara da,"Yanzu mun saka mata drip kuma mun bata maganin saukar da pressure. Alhamdulillah numfashinta da bugun zuciyarta sun zama stable yanzu, amma ya kamata a kiyaye sosai. Kar a bari tana shiga tashin hankali ko damuwa mai yawa, domin idan BP ya ci gaba da hawa haka yana iya jawo matsala mai girman gaske."
Sai ya dubi Baffa sosai ya ce,"A kula da duk wani abu da zai ɗaga mata hankali don Allah. Tana buƙatar hutu sosai da kwanciyar hankali."
Kalaman likitan suka tsaya wa Baffa a rai fiye da yadda suka fita daga bakin nasa. Wani irin tashin hankali ya ji ya ratsa jikinsa, sai dai a lokaci guda zuciyarsa ta ƙara nauyi, ba ya so yadda ya rasa Ramla a rayuwa, ya rasa Hajiya Madina, domin idan hakan ta kasance, Yaransu za su zama marayu ne, domin shima ba zai zauna a duniyar ba.
Idonsa suka ɗan sauya, yana jin tamkar an ɗora masa laifin halin da Hajiya Madina ta shiga. Ƙofar ɗakin da aka kwantar da ita ya ke haskowa, zuciyarsa na matsewa a hankali. Duk wani ƙarfi da juriyar da yake nunawa tun ɗazu kamar suna neman fara narkewa ne a hankali.
Ya sauke numfashi mai nauyi, sannan ya lumshe idonsa na ɗan wasu sakanni. A karo na farko tun da aka ce an kawo ta asibitin, tsoro ya shiga ransa sosai, irin tsoron rasa mutum da ranka ya saba da kasancewarsa kusa da kai.
Godiya Baffa ya yiwa likitan, kafin ya miƙe su yi musabaha ya fita a office ɗin nasa cikin mutuwar jiki.
Kamar yadda likitan ya faɗa masa ne, za su jira nan da awa guda kafin a bari wani shiga wajenta. Baffa yana tsaye a ƙofar ɗakin kamar ba zai taɓa motsawa ba.
Jinsa ya ke kamar kalaman likitan da ya yi masa bayanin halin da matarsa ke ciki sun ɗaure masa ƙafa a ƙasa ne. Hannunsa na sanye cikin aljihun babban rigarsa, amma duk da haka ana iya hango tashin hankalin da yake ciki daga yadda yatsunsa ke motsi a hankali.
Ya sauke numfashi mai nauyi sannan ya ɗan shafa fuskarsa a karo na babu adadi. Da yana da iko, zai ja lokaci ne, ya saita shi daidai da lokacin da likitan ya ɗiba.
Ta window ɗin ɗakin ya hangota, wani irin sabon tsoro ya shiga zuciyarsa fiye da ɗazu. Tsoron da ba wai saboda ciwon kawai ba, sai saboda tunanin me zai iya faruwa idan har wani abu ya same ta.
Lokaci na cika, bai ko jira cewar wani a tsakanin likita ko nurses ba. Buɗe ƙofar kawai ya yi ya shiga inda take kwance.
Har wannan lokacin kalaman likitan na maimaituwa ne a cikin kansa.
_"Kar a bari ta ƙara shiga halin da ta shiga a yanzu. Komai zai iya faruwa."_
Idonsa suka sauka kanta kai tsaye. Har yanzu bacci take yi, drip a hannunta, fuskarta na shaida tsananin firgicin da ta shiga.
Ya ƙarasa kusa da ita ya ja kujera ya zauna gefenta. A hankali ya kamo hannunta cikin nasa, idanunsa na yawo a kanta cikin wani irin tausayin da ya mamaye zuciyarsa gaba ɗaya.
Tausayinta ya kama shi matuƙa. Ya san ba hawan jini kawai ba, abin da ya fi haka ɗin ma za a faɗa, musamman idan abin ya shafi ƴaƴanta ko wani da take so. Ita mace ce da ba ta iya saka abu a ranta ba, tana da saurin ruɗewa da firgita, musamman idan abin ya shafi waɗanda ke zaune daram a zuciyarta.
Ya san tana matuƙar son Fullo. Domin kusan kullum idan sun zauna sai ta riƙa ba shi labarin yarinyar, tarbiyyarta, hankalinta, natsuwarta da kamun kanta. Har ta kan ce masa ina ma ace yarinyar ta zama rabon ɗaya daga cikin Khalil ko Turaki.
Sau da yawa kuma tana faɗa masa cewa in sha Allah za ta yi iyakar bakin ƙoƙarinta wajen ganin yarinyar ta samu wadataccen ilimi domin rayuwarta ta inganta. A cewarta Fullo ba irin yaran da za a banzatar da rayuwarsu ba ne, aƙi ba su wadataccen ilimi.
Hajiya Madina ba ta farfaɗo ba sai bayan sallar Isha’i. A hankali ta buɗe idanunta, kanta tana jin ya mata nauyi, jikinta kuma a sanyaye. Da ƙyar take iya tantance inda take. Sai idanunta suka sauka kan Baffa, tsaye a gefen window yana waya cikin ƙanƙance murya.
"…Ehh Inspector, ku tabbatar an bi duk route ɗin da aka bi da motar don Allah."
Jin abin da yake faɗa ya sa zuciyarta bugawa da ƙarfi. A dai-dai lokacin ne Baffa ya juya ya haɗa ido da ita. Nan take ya yi saurin ƙar rage muryarsa, sannan ya katse wayar da gaggawa, gudun kada tashin hankalin da take ciki ya sake hawa. Dama ga likita ya gama yi masa bayanin a kiyaye a kula.
Ya ƙaraso kusa da ita yana ƙoƙarin kwantar mata da hankali, amma kafin ya ce komai sai ta cafko hannunsa da sauri, idanunta cike da firgici.
"Baffa… Yarinyar mutane… ƴar mutane ta ɓata a hannuna, Baffa me zan ce wa iyayenta? Me zan faɗa wa mijin da za ta aura?."
Muryarta na rawa kafin ta dafe ƙirjinta tana sake faɗin,"Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un… wallahi banda masaniyar inda ta shiga. Wallahi da na san hakan zai faru da ban fita da ita ba, Baffa ba laifina ba ne, laifin yadda na ke jin Fullo a raina ne…"
Daga yanayin yadda take maganar, kasan gaba ɗaya ba ta cikin hayyacinta. Tunanin inda Fullo take shine kawai ya mamaye mata zuciya.
Sai kuma ta yi shiru na wasu daƙiƙu tana kallon Baffa da idanunta da suka cika da hawaye, kafin cikin sanyayyar murya ta ce,"Baffa… ko an ganta ne? Ɗan Usaini ya nuna motar mutanen?"
Ta ƙarasa maganar tana sakin wani kuka mai taɓa zuciya.
Baffa ya matse hannunta a hankali yana ƙoƙarin kwantar da ita. Cikin murya mai cike da lallashi ya ce,"Please stop crying. In sha’ Allah za a ganta very soon. Ba wai ɓata ta yi kamar yadda muke tunani ba, In sha Allah.”
Ta girgiza kai da sauri tana hawaye.
"Baffa ta ya ya? Ɗan Usaini fa ya ce ya ga motar da bai yarda da ita ba. Kuma ai a lokacin ne ta fito ta kawo min wayata. Baffa… Me kake tunanin ya faru?"
Baffa ya sauke numfashi a hankali. Shi kansa zuciyarsa cike take da fargaba, amma ya san idan ya nuna hakan, Hajiya Madina za ta sake rikicewa.
"Ki daina wannan tunanin Baby. In sha’ Allah cikin daren nan za mu ganta. Na yi report ma police, kuma sun fara aikin nemanta already. Samu nutsuwa kin ji Baby Nah."
Ya ƙarashe maganar yana shafa kanta zuwa bayanta kamar ƙaramar yarinya. Ita kuma tana goge hawayenta wasu na sake zuba. Can kuma sai ta kalle shi, hakan ne yasa ya sauka akan kujerar da yake ya zauna kusa da ita gefen gadon, ta kwanta a jikinsa.
Ya jima yana kwantar mata da hankali da kalamai ma su taushi. Sannan ya ɗauki wayarsa ya sake kiran Inspector Sise. Bayan ya ɗaga Baffa ya ce,"Ta farka yanzu. Wane irin bayani kuke buƙata daga wajenta? Ba ni da buƙatar ace sai kun zo asibitin."
Daga ɓangaren Inspector Sise aka ce,"Ranka ya daɗe ka bata wayar muyi magana da ita".
Baffa ya kalleta, ya ga yadda jikinta ke rawa kaɗan-kaɗan. Sai ya maida wayar kunnensa yana cewa cikin murya mai nuna damuwa,"Tana da saurin rikicewa sosai. Please a kula da irin tambayoyin da za a yi mata."
Tambayoyi daban-daban Inspector Sise ya riƙa yi wa Hajiya Madina, irin kayan da Fullo ta saka, yanayin jikinta, kamanninta, tsawonta, hatta yadda aka yi ta bar wajen. Duk kuwa cikin tashin hankali Hajiya Madina ta riƙa ba shi amsa ɗaya bayan ɗaya.
Sai dai da ya tambayi suna da hotonta, Hajiya Madina ta yi shiru na wasu sakanni kafin ta girgiza kai cikin sanyin murya ta ce,"Gaskiya bana tunanin ma yarinyar tana da hoto. Kuma ni bana so Kakarta ta san da maganar, na fi so a ganta."
Wannan kalmar ta saka Inspector Sise jan numfashi a hankali. Ya ɗan shafa goshinsa kafin ya mayar da maganarsa zuwa ga Baffa, inda yake ce masa.
"Alhaji zan tura za a tafi da driver station. A yanzu duk wanda ya kasance a wajen lokacin da lamarin ya faru suspect ne a gare mu."
Kuma lokaci ba mai tsayi ba sai ga ƴan sanda guda uku sun iso asibitin. Bayan sun gama maganar da za su yi da Baffa, wani a cikinsu yana kallon Ɗan Usaini, wanda tun ɗazu yake zaune a gefe jikinsa a mace.
"Officer, put him in cuffs."
Haka aka sawa Ɗan Usaini handcuff a hannaye. Nan take hankalinsa ya tashi sosai yana faɗin.
"Wallahi ban san komai ba! Wallahi ban san inda yarinyar ta shiga ba!" Haka yake ta faɗa yana ƙoƙarin janye hannunsa.
"Na je kamo ruwa ne kawai! Wallahi ba ni da hannu a ciki! Ku yarda da ni wallahi!"
Sai dai babu wanda ya bi ta kansa. Aka tura shi cikin motar police ɗin aka wuce da shi station.
Daga wannan lokacin ne yanayin lamarin ya fara sauyawa a zuciyar Baffa. Tun farko yana ɗaukar ɓatan kamar abu ne da zai zo ya wuce cikin sauƙi, tamkar yarinya ce kawai ta yi ɓata hanya ko ta tsaya a wani wurin. Amma har ƙarfe goma sha biyu na dare babu labarin Fullo, babu alamar inda take, babu wanda ya gan ta.
A hankali hankalinsa ya fara tashi shima. Yana tsaye kusa da window ɗin ɗakin asibitin, wayarsa a hannu, yana ta kiran numbers daban-daban, zuciyarsa na ƙara cika da wani irin fargaba da bai so ya yarda da ita.
Hajiya Madina kuwa har lokacin banda kuka da ambaton Allah babu abin da take yi. Ta ƙi yarda a tafi gida ko a mayar da ita, duk yadda Baffa ke aikin lallaɓata kuwa.
"Sai an samo yarinyar nan Baffa…" shine kawai take maimaitawa cikin muryar kuka.
Daga ƙarshe Khalil ne kawai ta yarda Baffa ya kira ya sanarwa. Amma tun kafin ya yi magana shima ta ce,"Kar ka bari kowa ya san abin da ya faru."
Don haka Khalil cikin nutsuwa ya shiga ɓangaren Kaka da sunan gaisuwa kawai, kamar yadda Baffa ya umarce shi, yana ƙoƙarin bincika ko Fullo ta koma ne, tun da ai dama yarinyar tana da aljanu, ƙila su suka kaɗata gida.
Kuma har ya gama bincikin nasa ya tabbatar bata koma ba, bai bari su Kaka sun fahimci komai ba.