Free chapter · Read without an account

KUSKURE 21

by Fatimaoumshaheed55 · KUSKURE

*KUSKURE*



By maman shaheed 




Shafi Na Ashirin da Ɗaya






NAWAL gidan su ta Fara wucewa  ,mama na ganin ta cikin wani yanayi yasa mama  tambayar ta "ko lpy na ganki haka?" 

  Nan ta ke fad'ama mama duk Abu buwan da ya faru harda k'arin na abin da be faru ba , har Abban ta shima yaji tun kafin ya tabatar da gaskiyar 'yar tasa , a tunanin shi bega laifin ƴar tasa ba Dan ganin ta yi k'ok'arin neman na kanta Dan ta zama wata da duniya dan kare ma kanta mutunci, shine ze dakatar da ita. 

Ita ko mama fad'a ta Fara yi Mata na tsakani d Allah Tana nuna Mata Tabi umarnin mijin ta matuk'ar be sab'a shari'a ba. 


Shiko Abba cewa yayi "indai baza ki taya 'yar ta ƙwaci 'yancinta ba ,to Ki bari a neman Mata akanme ze hanata Aiki,dan night duty ya biyo ta kanta, baya zuwa asibiti ne besan anayi ba? Kuma ai d'orowa takeyi kamawa tayi ,shi inda ba a night duty y samu likitoci a asibitin d yake zuwa yake Kai yaranshi in bukatar hakan tazo,har ke NAWAL da haihu da tazo ai cikin dare kuka tafi asibitin Kuma kwana kikayi ai an  Sami likitoci harda Mata ,inda ba a night ta Ina za'a Sami taimakon gagawa ?har a kular Mai da ke? Oh duk ya manta wanan? "


Ya cigaba da Cewa" toh ashe kinga ko ai night duty shima ya Mai amfani a rayuwa Yana Kan yi Mai Kuma , Koko itace baya son t Sami Lada biyu na Jakarta da na taimakon Al'ummah ?"ya tsatsare mama da ido. 

" toh ko zanyi duk Mai yiwuwa Dan ganin na jagoranci aikin ki ,in ita maman ki bazata dafa Miki ba ,ki kwantar d hankalin ki kinada Ni NAWAL din ta"tayi murmushi Mai cike da so da taɓara gamu sangartaciyar k'aunan mahaifin nata Tana Cewa. 

" Abba na gode da kulawar ka gareni, dan haka nace barin sanar muku dama kar ace nice banda gaskia" 
Mama dai Addu'a shiriya ta musu. 


 haka NAWAL bataje ko inaba ,ta zauna gidan su Tana jira time yayi ta karasa gidan Auntyn ta da tace zataje Dan neman solution. 


************
Safwan yana Isa Gidan Ammy d gudu Janna tazo ta tari su Noor shiko Haneef Yana mak'ale a wajen dadyn sa ,ya ki zuwa duk wajen su ,Dan haka yace su rabu dashi ,suka kyale shi suka wucewar su zuwa main parlour gidan.


Noor ce ta Fara kwad'a sallama tana ganin Ammy ta haye kanta da gudu,itama jannah zama tayi kusa da ammyn, Tana Mata dariya noor Tana tamby Ammy su twins.


Yaya ne dake gefen Ammy yace "Noor karki karyamana farin cikin mu uwa tagari maganin kukan mu" 

Ammy tayi dariya tace "ai wanan k'awar tawa Dena k'awance zanyi d ita Naga karfin ta k'aruwa yakeyi dan takusa Fina ƙarfi" duk suka sa dariya har janna da Indo da  take neman wajen zama a Kan capet. 

Ammy ce tace ta hau kujera ,sanan ta hau Tana gaishe da Ammy cikin girmamawa ,cikin karamci da iya tarban bak'o Ammyn ta amsa Dan awajen ta su twins suka gada girmama kowa. 

Suna cikin gaisawa ,safwan ya shigo shida Haneef bayan sun gama gaisawa da Mai gadin gidan Ammy. 

Janna CE ta Fara gaishe d yaya safwan ,Yana amsawa Yana tsokanar ta wai Ammy Bata ji d ita tunda har t iya barinta taje wani garin Tana Autar Ammy guda .


Yaya ne y kamo hannun Haneef Yana cewa "oyoyo my boy ,Zo mu gaisa gaisuwar ɗa da uba" Haneef y k'arasa gunsa Yana gaishe shi ,ya koma wajen Ammy Yana gaishe ta ,Ammy tace "yauwa me gidan Kai ka gaisheni d Kai nake Auren Amman Noor ko bana k'awance da ita Dan ko gaisheni batayi ba sema turmusheni da Tayi" safwan yasa dariya Yana cewa "zata jika Mana Aiki Tana turmushe Mana farin cikin mu na gidan duniya da kiyama wato   Yaya kana kalon ta, Ko ka shirya ma Ammy ganin likita na musamman ne?" 

Dariya yayan yayi yace "haba, ai bazata turmushe ta ba Ammyn Ca da raki kasan in tsufa ya fara zuwan ma mutum" 

Indo ma kalon Sa ta tsaya yi Dan mamaki kamar Mai magana d kakar sa y lauya zance yanzu,tsarin su na burge Indo wasa d sanyawa junan su farin ciki ta hanyoyi da dama. 

 Ammy magana  tayi "au tanan ka bullo? Kamanta me kace d'azu ko? Indo kinji yayan naku Ko? Kina zaune dai akayi" 

Indo ta d'ago tayi 'yar dariya tace "najishi Ammy" Tana Mai Jin kunyar su dukan su ,safwan ma kalon ta yayi Yana Mai son karanto kunyar me indon takeji atare d Ammy da Yaya Kai harma shi ,duk da kunya gadon ta ce a iya zaman da yayi da ita ya fahimci hakan, Amman Yaya y katse Mai tunaninsa  d cewa "Bari lokaci ya k'arasa mu wuce masalaci ko ?" Yana kallon SAFWAN. 

Haneef cewa yayi  "Nima zani yayan Dady" dake haka suke kiranshi shi d Noor ,Yaya yace "insha Allah ƙafata ƙafarka babban yaron a" 


Noor ce take ta tmby Ammy inda su aunty twins suke, Ammy tace suna gidan "su hameeda sunje barka ne hamrah  ce ta haihu shine sukaje ganin babyn yanzu zasu dawo lNaga sun Jima in Basu shigo ba sai kije ki kirasu Ai kinsan Gidan Ko?" 

tace" eh gidan su ƙawata toh Ammyn Dady"


Sallama Sukaji ta Aunty Amaryar Yaya d su twins d'in d gudu Noor ta Isa wajen su kowannen su sai d tamai oyoyo , suka k'araso suka zauna sunama Indo magana ,cikin Jin dad'in dawowan nasu take gaishe su suna amsawa cikin sakin fuska itama taji dad'i har ta saki jikin ta da Ammy ta tashi ta bar musu wajen .

Yaya da SAFWAN ko sun tafi d'auro Alwala Don tafiya masalaci yin sallah juma'a .

Suko Hira suka Fara suna sako Indo cikin hiran ,sanan Ammy ta Kira twins tace Mata su Taya iya aikin girki Dan ayi Mai kyau da dad'i Kuma Dan ta Kamala d wuri ,tunda Akwai Baƙi a gidan ,Kuma huzna ma ta kirata a waya wai zatazo hutu. 


Twins d tanata murna ,jin ance huzna na zuwa ta d'anji wani irin tasan sarkin matsala da Shan ƙamshi zata Zo ,ita halinta ne yake had'ata dasu twins ,Sam halin su ba ɗaya bane ,Ammy ce tace "lpy dai hassana? Naga kinyi saroro" 

  Ta k'ak'alo murmushin Dole tace "lpy lau Ammy" sanan ta wuce tana Kiran ussaina su nufi kitchen.

Ko da ta gayama ussaina sak'on momy cewa sukayi indo da aunty sufaya tare za'ayi aikin da su ,ba yadda hassana batayi dasu ba Dan su hak'ura Amman sukace Inna Sam ,haka suka nufi kitchen d'in tare. 


Suna shiga kitchen d'in Indo ta Fara gaishe da iya ,cikin fara'a ta amsa har Indo take tambayata hidaya ,iya tace Mata "Tana gida kanta ne yake ciwo Amman zatazo da yamma Dan tayani Aiki" Indo taji dadin ƙawar ta zatazo sun kwana biyu Basu had'u ba ,time to time Indo na lulawa tunanin Hali da Abin da ya faru tsakanin ta da momyn su Noor ,Amman da ta Fara tunanin su twins ko Aunty sufaya zasu dakatar da ita ta hanyar jeho Mata Hira Dole take rabuwa da tunanin ta shiga hirar nasu da haka da haka har tunanin ya bar zuciyar ta n wani lokaci .

Sunata Aiki ,sun ma ce iya taje ta gama gyara ko Ina inda Ba'a gyara ba ta barmusu aikin girkin ,Dan haka ta tafi gyare-gyaren inda ba'a rasa ba. 

Suko sun zage aikin su suketa yi Mai cike da tsafta Indo ma ta dage aikin take sosai Tama fisu dagewa Akan aikin .

Aiko kowa na kawo idea shi har suka Kamala girkin pride rice dayaji hata da kayan lambu coslow da yaji su kwai da madara, bama ,ga dambun shinkafa da yaji zogale ga kunun Aya d zobo d yaji abarba d  cocumber da kayan kamshi ,ga soyayiyar kaza da kwai da Tasha garnishing ,Abin dai gwanin birgewa sun gama jerewa a dining ,sun tafi gabatar da sallar su Suma .


Su Yaya na dawo wa Ammy ta ce musu" food is ready" safwan ne ya doshi wajen ya fara bude-buɗe  kazar da Tasha garnishing atake kamshin ya dakeshi ya shige har kwanyar sa ,atake ya fara yaba Wanda yayi wanna girkin  tunanin sa ya fara sanar Mai wanan ai irin girkin Indo ne dan ya Saba d girkin ya Kamata ace yana gane ƙamshi da d'and'anon harma kalar girkin ta don mugun sabon da yayi dashi ,ganin kwanyar SA zata kaishi inda be Kai kanshi ba na santi, ya samu ya juya akalar tunanin sa zuwa yima Yaya magana Yana Kiran shi y taso suyi lunch.

Shi da Haneef suka taso sai ga SUFAYYA ta fito ,sanan Yaya yace "my heart Zo ki zuba Mana girkin naku ku cika ladan ku" 

 Tana murmushi ta taho. 

Shima safuwan murmushin yayi Yana kalon yayan nashi ta gefen idon shi ,yayan ne yace" kanamin gulma ko ,kaima b kana d dear ka  ba ? Dan nasan gulman da kakeyi Saboda kana nan sai na kasa jiranta da sunan da na saba kitanta dashi a gida? "

safwan  yasa dariya yace" Ni ba dariya nakeyi ba kawai dai Ina jinjina ma so da k'aunan juna ne" sunata dariya har SUFAYYA ma. 


Tana cikin zuba musu ,suka tsinkayo sallama HUZNA bayan ta shigo parlour ,ganin ta ya sa gaba dayan su mamakin zuwanta Kamar Mai gani har hanji. 

Shiko safwan dama yau kwana 3 kenan tanata jera Mai misecall be kirata ba be d'aga ba Dan baya son damuwa yanzun ma ganin ta ya dagulamai lisafi ,yayan sa ma seda ya gano hakan ,SUFAYYA ce ta Fara Mata sannu da zuwa cikin fara'a Dan ta ganeta lokacin bikin su ,sanan Yaya ma ya Mata magana Yana cewa "kece a hanya huzna Amman b waya ba sak'o? Kamar ko rariya" 


 yamutse fuska irin n sangartatun Nan Tayi Tana cewa "wlh munyi waya  da Ammy infact Tama San da zuwa na" 

yace" ok sannu da karasowa"

 safwan ko Loma yake turawa kawai ko kalon ta be sake yiba ,sai d tace "Yaya S bama magana ne?" Tana Mai wani kalon Tana nufo inda yake ganin zata iya sawa ya tsani Abincin yayi saurin dakatar da ita da cewa "a my sis so nake ki huta kafin mu gaisa" jin haka ranta yayi sanyi ta wurga Mai wani kalo Mai salo ta bi bayan SUFAYYA da ta rike Mata handbag d'inta zuwa d'akin su twins.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.