Free chapter · Read without an account

KUSKURE 25

by Fatimaoumshaheed55 · KUSKURE

*KUSKURE*




By Mamanshaheed 




Shafi Na Ashirin d biyar







Bayan NAWAL ta koma ɗakin ta d'an taba bacci sanan ta koma chat ,tanata nad'an surutun 'yan Groups din su .



Mama dai saitayi kamar zata tabamyi NAWAL Abu sai Kuma ta shiru ,shiko Abbah ko ajikin shi ya yadda 100% da bayanan 'yar tashi Dan haka ba wani damuwa a tare da shi .



""”"""”""""”""""”""
Huzna dai har yanzu neman inda zataga dogayen rugunan Nan take ,ta kasa gano inda suke ,har kayan su twins sai da tayi bincike aciki batare da kowa ya ganta ba ,bataga Alamar nasu bane .


Noor da haneef,da Janna sunata sauraron tatsuniyar da Indo take musu ,sunata Jin Daɗi ,suna Mata tambaya Tana Basu amsa .


Ammy da su twins sunata sauraron su ,ganin yadda take musu tatsuniyar cikin hikima da ƙwarewa da nuna musu tarbiyar cikin tatsuniyar da yadda take Basu amsa cikin gwanancewa gashi ada Ammy Tana tunanin batayi ilimin zamani ko kadan ba ,sai gashi tunanin Ammy na neman zama ba gaskia ba ,Dan haka tace "Indo" ta kira sunan ta. 

Indo ta tsaida tatsuniyar amsa da "naam Ammy". 

Ammy tace "meye matakin karatunki ne kuwa Aisha Indo?" 


Sunkuyar da kai tayi alamar kunya kafin ta amsa mata da "nayi primary bayan na gama naci gaba da secondary zuwa junior section tunda nayi JSCE banci gaba ba sakamakon wasu dalilai,nayi karatun Addini kadan ya rage ban sauke ba ,Kuma na Dan San wasu litatafai  ,Amman inada burin cigaba in sha Allah Dan Ina Tara kudin Aiki na ma Dan dasu nakeson ci gaba tare da tallafin Inna da sana'ar da zamu Kama nida ita in zanbar Aiki Dan bazan iya hada Aiki da karatu ba shiyisa zamu Kama sana'a da Inna tunda babana ya ɓata "hawaye suka Dan zubo Mata lokacin da muryar ta ta raunana sosai cike d Damuwa. 


Ammy da twins tausayin ta ya kamasu tun basuji tarihin Rayuwar ta ba.

Ganin kuka na Shirin cin karfin ta ,gashi su Noor da haneef da Janna sunata son ganewa ko kuka take yi.

Sai Ammy tace" ku tashi kuje kuyi wasa a ɗakin  da kayan wasa anjima Indo au Aisha daga yau ku dinga kiranta aunty Aishatu shine asalin sunan ta kunji yaran kirki ? "Aiko sukace" toh" noor ce me surutun cewa " dama sunan ta Aishatu ake cemata wata indoooo?" tana turo baki tana neman amsar tabamyar daga  wajen indon?. 

Tayi kokarin hadiye kukan tace, "eh Noor innata ce take kirana Aisha Indo ,daga baya take cewa Indo kawai shine kowa ya d'auka ,Amman sunana Aishatu da mahaifina ya rad'a min". 

Aiko suka sa tsale suna cewa "daga yau Anti Aishatu zamu dinga ce Miki ai kinaso ko?" Ta gyaɗa Kai Alamar eh Tana musu murmushi da nuna godiyar so da suke nuna Mata a wanan gidan .

Ussaina ce tace "maza aje wasa akwai sweet a gefen  wardrobe  kowa ya d'auki 2 kubar min Sauran" da gudu suka tafi suna murna .


Hassana Ce ta "kamo Indo ta dawo da ita cikin su suka zaunar da ita tsakiyan su ,Ammy na kujeranta da ban ,sun manta da ma huzna na gidan tanacan Tana bacin asara bacin gado na rashin zuciya wai ka'ida sai tayi bacin a Rana so biyu ko uku kulin .


Ammy CE tace" Aishatu ,bani tarihin Rayuwar ki Kuma ki yi kokarin gayamin gaskia Kar ki boye min komai ,duk da nasan ƙarya b halayar ki bace a iya ɗan zaman da nayi dake a mu'amalance na Dan fahince ki daidai gwargwado"


Aiko Indo ta nisa, cikin Ranta tace "Ranar wanka ba a ɓoyon cibi" Idon ta  taf da ƙwala ta Fara magana dan ya zama dole yau Ammy ta sani tunda har ta nema. 


Tana cikin Basu labari,sukaji sallamar Yaya safwan ya shigo , Indo tayi nisa cikin labarin Rayuwar ta ko sallamar sa bataji ba balle ta ganshi .

Ammy ce tamai nuni da hannu Akan ya zauna ,Kar yasa indon katse labarin dan Mugun shakka shi take, in ba haka ba dena Basu zatayi  Dan ta gama fahimtar girmamawa da taka tsantsan da yake tsakanin indo da safwan Dan za'a iyacewa Indo nah tsoron sa tsoro irin na uban gida da yaron gida koma ace tsoron girmamawa duk sun San wanan inda yake zaune ma Bata zama Dan girmamashi saidai in Ammy ce tace ta zauna sai Tabi umarnin ta. 

 haka ya bi umarnin Ammy ya zauna yanata Danna waya irin bashi da Abin saurare a Rayuwar indon Dan ya fahimci Kan labarin da take Basu har mamakin nutsuwar su yayi Har Ammy ma. 

Indo ba Abin da ta ɓoye ma su Ammy nadaga Rayuwar ta ,har Wanda Inna ta Bata labari da Wanda ta sani da wayon ta har barin mahaifin ta garin da matakin karatun ta na ilimin Addini Litattafan da ta ɗan sani na Addini da irin kokarin ta a fanni  Boko da Addini yayin da kuka yaci ƙarfin ta da take Gaya musu sun hakura da Abban ta Dan ance musu ma wai ya mutu ,Bata da uwa Bata da uba Dan haka take d'aukan kanta marainiya kuka ƴa sake kubce Mata hassana da ussaina name Bata hak'uri jikin su a sanyaye .


Ba Ammy ko  ussaina ko hassana ba hatta goga SAFWAN labarin ya saukar Mai da wata irin kasala da ya rasa Dame ze kirata gashi bakin sa ko zuciyar sa ko ƙwaƙwalwar sa Basu bashi izinin furta komai akai ba saima korashi da sukayi duniyar masu tunani ,ga waya a hannun sa Amman ya kasa latsa ta ,komai nashi ya tsaya na wucin gadi.



Su twins sunata rarashin ta , ganin baida dama ko ikon sarafa kanshi yasa ya tashi ya fice zuwa resting room Dan dogon nazari, ba tare da sun gaisa da Ammy ba yaga duk suna duniyar tausayi yasan yau indo suka ba Aron lokacin su. 



Indo saida tayi Mai isar ta sanan tayi shiru tare d rarashin su twins.


Ammy ce tayi ta Bata Baki da hakuri gami da nasiha da nuna Mata cewa zasu tayata addu'a indai mahaifin ta na Raye Allah ya bayana shi inkuma ya rasu Allah y gafarta Masa d mahaifiyar Tata. 


Sanan ita Kuma Inna ,Allah ya Cigaba da talafama Rayuwar su ita da indon ,Kuma tace Mata anjima sai suje ita da su twins su dubo Inna Dan ganin lafiyar ta. 

Haka kawai Ammy take jin ƴar ta kwanta mata arai. 


Indo cikin murna da zaƙuwa tace "Amman na gode Ammy,Allah ya Kara girma, Daman inason zuwa na ganta na rasa yadda zan tambaya ne" 


Ammy ta tayi murmushi su na manya kafin tace " saboda me? Keda kakarki ɗaya tilo zaki ki tbamya zuwa dubo lafiyar ta da kin Gaya min da tuni kinje ai" 

"ko acan mmn su noor ɗin hanaki take?" 

Da sauri indo tace "a'a taba bari na sosai" 

Indo tace"kawai dai momyn su Noor Bata barina naje ne sadai idan Inna Bata da lpy ko da wani dalili, Amman ina zuwa"

Ammy tace" saboda  me sai da dalili? "

Indo tace" saboda Aiki "

Ammy tace" wanan ba daidai bane ,kice ba duk sati kike zuwa duba taba ma Ashe?"


Indo tace" eh bantaɓa zuwa na dubata bayan sati Ko sati biyu bama ,Ni da zuwa wajen Inna sadai fa idan Bata da lpy ko Inna d'auki Albashi na, sai na kaimata na ajiye Wanda nake ajiyewa in ba hakaba bana zuwa akai-akai Bata Bari na naje akurkusa"

Aiko Ammy bataji Dadi ba ,Nan ta ƙara tabatar da Abin da su twins suke sheda Mata na azabtar da Indo da  NAWAL take, kawai dai Indon na bata kariya ne, ita kuma NAWAL tana kaskantar da ita da nuna Mata ita ba kowa bace face Yar Aiki wahalaliya Mara 'yan ci *KUSKURE* Ne wanan kowane Dan Adam yanada irin tasa darajar ,ba kasan matsayin sa ba awajen Allah .

Ammy ta ce" gaskia NAWAL Bata kyauta ba ban sani ba tuni da na gyara Al'amarin , hakan ai ba adalci bane .

Ussaina tayi caraf tace , "wlh aikin Aunty NAWAL yafi dahaka ma wlh ai dai ...." 

Ammy ta dakatar da ita da cewa "ke banason surutu matar yayanki ce Akwai girmamawa a tsakanin ki da ita duk d Bata kyauta ba ,Kar na karaji ban baki damar Maganar ta bata nan ba" 

Dole tasa Sukayi shiru ,har hassana da take Shirin ƙara nata bayanin ta hadiye ,Indo ma shiru tayi .

Ammy Ce tace suje su Kamala komai na gidan su shirya suje driver ya kaisu su gaishe da Inna har su Noor ma ashirya su ,sukace too murna fal Ran Indo .


Kitchen suka fada suka shiga Taya iya Aiki ,suna cikin aikin hidaya tazo Indo da hidaya suna murna da ganin juna suka gaisa suka cigaba da aikin .

Indo ta gayama hidaya zasu gidan su da su twins gaishe da Inna ,Aiko hidaya tace wlh da ita za'aje Dan wanan zumuncin da ita za'ayi har take rad'a ma Indo doguwar rigar da zata sa da takalmi, su lndoo har anmanta da wasu dogayen riguna ma sai yanzu da hidaya ta tuna Mata, abinka da wacce bata ɗau duniya da zafi ba. 


Bayan sun kamala komai ,saura Shirin fita zuwa gaishe d Inna .



"""""”"""”""""""
SAFWAN Ko tun komawar shi ɗaki ba a ba kwanyar shi sukuni ba .

A zahiri ya matuk'ar Jin tausayin Indo da Rayuwar ta da duk wani Wanda yake kewaye da Rayuwar ta.

Amman Yana tuhumar kansa danme ze damu d Rayuwar ta haka ga Abin da ya kamata ya dame shi can Rashin  NAWAL. 


Can Kuma yace "hmmmm NAWAL din me , tunda ta zabi Aiki Akan Shi har iyayen ta ma Ashe tunanin su iri daya ne,shima ko ze nuna musu da ɗan halak sukayi" 


Kuma ma me ze dameshi yana tare da farin cikin shi yaranshi ,ga Kuma Mai kula Mai dasu ko uwar da ta haife su Albarka .

Kai ma Ai Dole ya Kuna nutso cikin damuwa da Rayuwar Indo ko Aishatu da yaji Ammy ta furta ,? Dan itace komai na yaran shi tun daga haihuwar su har ka yau , ai Hausawa sunce gaida Mai gaisheka ko baze amsa ba , yaba kyauta kuma tukwici Dan Tana taimakama yaran shi ne kawai dalilin tausaya Mata da yayi bawai dan wani abu ba da ace bata shigo cikin rayuwar yaran shi ba da besan wani hali suke a yanzu ba. 


Ya jima Yana tunani akan Indo da Abin da ya shafi yaran shi ,ganin tunani ya Hana shi sukuni yasa ,ya gayaci baccin Dole ko ya Sami sassauci.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol