Free chapter · Read without an account

SAWUN KEKE...

by Ayeesha Abdulkareem · SAWUN KEKE season 1



Sai da su ka isa wajen Mota sannan Hajiya Laure ta samu confidence ɗin bajewa a ƙasa ta na ƙara sakin wani kukann gami da cewa "Na shiga uku na lalace yau zan biyoka Alhaji Salisu, shi kenan tawa ta ƙare nima yau mutuwar zan yiiiihihihiii"  ta ja ƙarshen maganar gami da gaurayata cikin kukanta.
Hajiya Sauda kuwa haki ta ke famar yi  kamar Zuciyarta za ta yi tsalle ta fito ta baki,  Sautin kukan Hajiya Laure ne ya ƙara faɗaɗa  ta rintse ido kawai faɗi take "Ga su nan sun biyomu  Na mutu na lalace, Salisu gani nan gareka,  na shiga ukuuuuuuhh!!!!!"

Haj Saudah kuwa ta zama tamkar bishiyar da ta yi shekara da shekaru a wajen, hatta idanunta sun ƙame ta zubawa abinda ta ke gani ido da haka ta tafi shuuuu!!!! jikake yiffff!!!  ta faɗi ƙasa a sume.................

Madarasatul-Nurool-Islam
Sheikh Auwal na zaune kan kujerarsa  da ke a Office ɗin Malamai, ya zuba tagumi, gashi dai a zaune amma hankalinsa ya yi balaguro,  tunanin Akhiee wanda ya kwana biyu bai gani ba yake yi, ko ranar da yazo makaranta zuwan ƙarshe sai dai labarin ya zo ya samu amma bai ganshi da idanunsa ba.

Sallama ake rafkawa a bakin Office ɗin amma sam bai ji ba har sai da aka buga ƙofa sannan ya yi zaram ya na rarraba idanu.
Wani Matashi ne da ke a ɗaya daga cikin gidajen Layin  yake ta ƙwalla sallama, sai da ya kuma yin wata sannan Sheikh Auwal ya amsa, gaishe shi ya yi cikin girmamawa sannan ya sanar masa cewar  wasu bayin Allah ne su ka zo neman shugaban makaranta wato dai Sheikh Auwal Ɗin.


Faɗuwar gaba asarar Namiji......... Sheikh Auwal na jin haka  ba tare da ya san dalili ba gabansa ya faɗi kwantsam!!!   amma da yake akwai taurin Zuciya sai ya daddafe ya ce "A sanar musu gani nan fitowa."
Saurayin ya ce "To shi kenan!"  sannan ya juyawa  zuwa waje, bayan ya sanar  wa  Daddy da wanda suke tare ya wuce nashi wuri.
cikin tantama da shakku Sheikh Auwal ya fito, ganin Daddy ne ya sa Zuciyarsa ta ƙara tsinkewa.

Bayan sun Gaisa Mutumin ya ce "Ko za mu iya ganin Muhammad Muhammad?"  Sheikh Auwal ya ce "A'a Kwana biyu ma bai zo Makaranta ba  yau ma bai zo ba,  Lafiya kuwa?" miƙa masa wani ɗan envelope ya yi gami da cewa "Daga Kotu, Iyayen Yarinya sun shigar da Ƙararsa akan Auren Ƴarsu da ya yi ba tare da sun sani ba, in ya dawo gida sai a bashi."  cikin kaɗuwa Sheikh Auwal ya ce "Aure?? kuma Akhiee ɗin??"  Daddy ne ya yi saurin shiga zancen da cewar "Shi kuwa,  na kawo ƴata don ta yi Karatu amma  an ɓuge  ga Aureta,  maganar gaskiya ba zan ɗauka ba dole ne ya saketa."
"Wai Husna?" Sheikh Auwal ya ƙara tambaya don tabbatarwa,  Daddy ya ce "Ita ɗin fa"
Sheikh Auwal kamar ya fashe da kuka, a sanyaye ya shiga basu haƙuri gami da rarrashi,  Shi dai Daddy kawai jinsa ya ke yi don kuwa gani ya ke yi duk da laifinsu don haka  ya ke jin haushinsu.

Har su ka yi sallama su ka tafi ya na ƙara jaddada musu ban haƙuri,  bayan sun tafi ya koma Office ya zauna. duk ya rasa abin yi,    ji ya ke inama ƙasa za ta tsage ya shige sabida tsabar kunya da takaici da baƙin ciki.

Husnee:
kwana biyu da ba ta fita ba sai ta ji tamkar ta shekara  da yake akwaita da son yawo.  Yau dai ta rantse sai ta fita don haka ta dinga kiwon Mommy da Amadu.  Ta na samun dama kuwa ta zumbuɗa Hijab ta fice, kai tsaye  ta nufi Makaranta duk da cewar da ƴar tazara tsakanin yankinsu da yankin makarantar amma yau ba ta buƙatar a kaita a Mota don ta san Direban nata zai hanata fita.
Ta na  cikin tafiya Tankar Yaƙi da Tawagarta su ka sha gabanta.

Ta na sanye da wani mugun ɗamammen wandon  Jeans  blue wanda aka tsatstsaga wajen guiwarsa sabida tsabar gayu,  rigar kuwa  ta ciki fara ce sol  itama ta mugun kama jikinta sai jacket da ta ɗora ita ma ta jeans, sai  farar  bandana wadda iyakacinta goshi, tsefaffen gashinta wanda ke ta zuba ƙyalli ya yi watsa-watsa kowanne ya kama gabansa, hannunta ɗaya a Aljihun riga ɗayan kuma ya na kusa da bakinta ta na zuƙar Wiwi ta na busawa.

Wani irin taku ta ke yi  me cike da izza, zarra, jin kai, ƙasaita,  tamkar ita ce  Queen Elizabeth.

Husnee ta kallesu ɗaya bayan ɗaya  ta ga zaratan ƙarti sai zaro mata na mujiya su ke yi su na huro mata hancika tamkar bujimayen shanu,  Zuciyarta ce ta fara tsallle tsoro da razani da firgici haɗi da tashin hankali su ka kawo mata ziyarar bazata.

JanKai ne ya kalli shugabar ta  shi  cike da ƙagarar  aiwatar da mugun aiki akan Husnee  ya ce "Ya kika ce Zinaru!  mu hau kanta ne ko kuwa??"

Jin haka ya ƙara ɗaga hankalin Husnee idanun nan nata kamar an danne tinkiya za'a yanka sun firfito waje tsuru-tsuru,  Tankar Yaƙi ta busa hayaƙi a ƙasaice ta ce "Saurin me ka ke yi,  ku kawo mini ita nan."
Ta na faɗen haka su ka nufi inda Husnee take dama a tsakiya su ka sata, ba tare da tunanin ita mace ce  su maza ba haka su ka cicciɓeta ta na ihu ta na komai su ka direta a gaban Tankar Yaƙi.

Zabgegiyar wuƙarta me kama da Adda ta karɓa a hannun Jankai ta goge ta sannan ta zubawa Husnee idanunta da su ka koma launin ja,  cikin  murya me ƙunshe da manufofi da dama ta ce.................................

Akhiee,   Ɗan-Bakwai ne  ya miƙo masa wayarsa da take ta tsuwwa, ya karɓa bayan ya  ɗaga kiran ya sa a saman kunnensa,  a ɗaya ɓangaren me kiran ya ce "Ni ne dai Abokin gabarka Inspector Khalil,  ina zarginka da aikata kisan kai na wasu Ƴan Yara guda biyu  bayan ka yi musu Fyaɗe  kai da yaranka,  ba wanda zai aikata hakan sai kai."
Cikin Nutsuwa Akhiee ya ce "Aikin ne ka rasa da za ka biyo ta bayan gida kuma?? Ka san ina yin ɓarna da yawa, ko za ka iya yi mini ƙarin bayani?"
"Sunan Ɗaya Zakiyya Ɗaya kuma Farhana, an tsinci gawarsu kuma bincike ya nuna sai da aka yi lalata da su sannan aka kashe su, ɗaya a ciki ma har da ƙwaƙule mata ido,  Ba wani kwalo-kwalo da za ka yi mini na san kai  ne ka aikata, kuma mu na nan mu na ƙara bincike akanka."

Akhiee ya ja tsaki kafin ya ce "Shashashan banza".
A fusace IP Khalil ya ce "I'm Police fa ni zaka gayawa maganar banza?  wallahi ka guji shigowa hannuna sai ka gane kurenka wallahi, har ni za ka cewa shashasha??  I will arrest you wallahi"

Aunty Indo

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.