Free chapter · Read without an account
Chapter Twenty Two
Bai jira ta gama shiga motar ba yayi mata key, tana zama ya zaburi motar da ƙarfi ya nufi hanyar fita. Bin sa kawai tayi da kallon mamaki, sannan ta sunkuyar da kanta tana faɗaɗa tunaninta.
Suna isa Ammey tayi mata tarba mai kyau, suka zauna a babban parlour gidan sukayi ta hira. Musamman da Zainab wadda Radiya take ganin kirkinta har yaso yayi yawa.
Misalin sha biyu na rana Zainab ta ja hannun Radiya suka nufi kitchen, da kansu suka fara ƙoƙarin shirya abincin rana. Zainab ce ta fara shirya abincin da kowa zai ci, sannan Radiya ta karɓi ragamar girkin da ake yiwa Ammey na musamman.
Haka suka gama girkin tare da taimakon masu aikin gidan, sannan daga bisani suka fara jere su akan babban dinning table ɗin da yake can gefen parlour wanda aka ƙawata wajen kamar na masarauta.
Sai da kowa yayi sallar Azhar sannan suka hallara domin cin abincin rana.
Amma duk wannan abun da yake faruwa Sultan yayi kicin-kicin da ransa, sam yaƙi walwala, duk irin tambayar da Sauban yayi masa ya gaza bashi amsa.
Sai da Ammey ta iso sukayi addu'a sannan aka fara ƙoƙarin zuba abincin. Da sauri Radiya ta miƙe ta fara ƙoƙarin zubawa Ammey biskin da tayi mata da miyar gyaɗa wanda sai tashin ƙamshi yake yi.
Cike da jin daɗi Ammey ta kalle ta tace:
"Ki fara sallamar mijinki tukunna."
Murmushi Radiya tayi ta ci gaba da zuba mata ba tare da tace komai ba.
Sannan ta juya domin sallamar Sultan.
Hannunsa ya saka ya dakatar da ita ta hanyar fara zubawa da kansa.
A sanyaye ta dawo ta zauna jikinta babu ƙwari. Sauban ne kawai ya lura da abinda ya faru, hakan ya saka ya saka ƙafar sa ya zunguri ta Sultan, amma ko a jikinsa ya nuna bai san ma yanayi ba.
Da sauri Ammey ta ƙwalaya mai dafa musu abincin kira. Bayan ta iso ta kalle ta cike da mamaki tace:
"Waye yayi min girki yau?"
A sanyaye ta ɗago ta yi mata nuni da Radiya tare da faɗin:
"Madam ce."
Cike da mamaki Ammey ta kalli Radiya tace:
"Ko da naji, shiyasa Sultan yayi ƙiba, kuma ya rage zuwa gida cin abinci. Ashe haka kika iya girki?"
Murmushi sukayi gabaɗayansu, sannan Sauban ya ci gaba da tsokanar ta.
Ita kuwa kallon yanayin da Sultan yake ciki ya saka dole ta sunkuyar da kanta, saboda ta rasa meyasa take tuhumar kanta da ɓata masa. Hakan ya saka dole ta ƙudurce a ranta cewar a yau zata bashi haƙuri.
To haka suka wuni a gidan suna hira, Radiya ta saki jikinta sosai da Zainab da Ammey da kuma Fawaz, saboda yadda yake murna da ya ganta.
Sai da akayi sallar isha'i sannan suka fara haramar tafiya.
Dab da tafiyar su Sauban ya jawo hannun Sultan suka nufi wani lambu suka zauna, sannan ya kalle shi yace:
"I'm sorry Sultan, na sani kana daurewa, but ka ƙara haƙuri please, yanzu meye actual abinda yake damun ka?"
Ajiyar zuciya yayi, sannan ya lumshe idonsa yace:
"Her feelings."
Shima Sauban ajiyar zuciyar yayi sannan yace:
"I know it's not easy, but don't rush it. Okay?"
Jinjina kansa kawai yayi alamar "To" Sannan Sauban ya dafa kafaɗarsa yace:
"Zan zo gobe sai mu tattauna sosai akan issue ɗin, but, ka ƙara haƙuri please!"
Sake jingina kansa yayi, sannan suka miƙe gabaɗayansu suka nufi motocinsu.
To a hankali Sultan ya fara daidaita yanayinsa, saboda yaji shawarar da Sauban ya bashi. Saboda shima kansa bai san ta yadda zai tunkare ta ba, saboda sam baya son yin abinda zai zubar masa da kimarsa.
Hakan ya saka dole ya daure zuciyarsa ba don yana so ba.
Da wannan tunanin na sa suka isa gida.
Ita kuwa Radiya duk ta tsargu bata jin daɗin yanayinsa, saboda in dai yacigaba da zama a haka to zata rasa fuskar da zata tunkare shi da buƙatarta, hakan ya saka ta yanke shawarar tunkararsa.
Sai dai da mamakinta suna shigowa taga yayi sauri ya nufi ɓangarensa, duk da haka bata sare ba, haka itama ta nufi ɓangarenta.
A sanyaye tayi wanka, sannan ta ɗakko wasu kayan bacci riga da wando jajaye ta saka, sannan ta sake ɗakko wani ƙaramin hijab fari wanda bai fi iya gwiwarta ba ta saka ta nufi ɓangarensa.
Sai da ta fara ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin sannan yayi mata izini da ta shigo. Amma cike da mamaki ya ɗago kansa ganin itace ba masu kawo masa coffee ba.
A sanyaye itama ta shiga tana ƙarewa bedroom ɗin kallo, gaskiya tsarin yayi matuƙar birgeta. A hankali ta ƙarasa inda yake zaune ta nemi kujerar da take fuskantarsa ta zauna.
Tsananin mamakine ya cika shi, hakan ya saka ya sauke laptop ɗin da take kan cinyarsa tare ajiye ta table ɗin da yake gefen sa. Sannan ya mayar da hankalinsa kanta.
Shuru ne ya biyo baya, sannan daga bisani aka sake ƙwanƙwasa ƙofar.
Wani matashi ne ya shigo hannunsa riƙe da plate da kofi ya ƙaraso ya ajiye masa a gabansa sannan ya fice.
Cike da mamaki Radiya tabi bayansa da kallo, saboda bata taɓa ganinsa a gidan ba sai yau, sai sannan ta tuna cewar waɗannan matan daman a iya ɓangaren ta kawai suke aiki.
Gyara zamanta tayi, sannan ta ɗago a hankali ta kalle shi a daidai lokacin da ya kai kofin bakinsa, sannan tace:
"Kayi haƙuri please naga kamar na ɓata maka rai jiya. Nima kaina ba'a son raina hakan take faruwa ba, bana son na samu matsala da Yayana ne shiyasa."
Jim kaɗan yayi, sannan daga bisani ya gano abinda take nufi. Kawar da kansa yayi tare da ɗaukar laptop ɗinsa ya fara danne-danne, sannan daga bisani yace:
"It's OK."
Ba tare da ya kalle ta ba.
A zahiri bazaka taɓa cewa akwai wani abu da yake damunsa ba, amma a baɗini shi kaɗai yasan yaƙin sunƙurun da yake faruwa tsakanin zuciyarsa da gaɓoɓin jikinsa.
Yanayin yadda yayi mata magana sam bai gamsar da ita ba, hakan ya saka ta shiga damuwa, saboda tana tsoron kar shirinta ya lalace. Kuma wannan ita kaɗai ce damar da take da ita.
Sake gyara zamanta tayi, sannan ta ci gaba da magana:
"Naga kamar baka gamsu da maganata ba, kayi haƙuri don Allah."
A raunane ya ɗago da ƙwayar idonsa ya ɗora akan tata ba tare da yace komai ba, ganin hakan ya saka ta sake sunkuyar da kanta, bakinta yana motsi ta kasa magana.
Sake sauke laptop ɗin yayi gefe, sannan ya kalle ta yace:
"Akwai abinda kike buƙata ne?"
Jinjina kanta tayi alamar "eh" ba tare da ta ɗago kanta ba, sannan ya gyara zamansa yace:
"Ina jinki."
Ya faɗa tare da kafe ta da idonsa.
"Daman...zuwan da Yayana yayi kwanaki ashe yana lissafin lokacin da zan koma, kuma kaga matsalar da aka samu daga farko, nayi miscarriage kuma idan aka ce za'a kuma yin wani proceedures ɗin zai ɗauki lokaci sosai gashi lokaci yana tafiya, shine nace...kawai...we can do it naturally."
Ta ƙarasa maganar tare da rintse idonta.
Wani murmushin nasara yayi a sace, tare da godewa Ubangiji a ransa da yake kawo masa komai akan gaɓa, amma duk da hakan sai ya kawar da kansa, sannan ya kalle ta yace:
"Are you sure?"
Jinjina kanta tayi alamar tabbatarwa. Sannan ya kurɓi coffee yace:
"OK, I'll think about it."
Ɗagowa tayi ta kalle shi cike da damuwa, sannan tace:
"Please ka taimaka min lokaci yana tafiya, don Allah, kuma sau ɗaya kawai za'a yi."
Ajiye kofin hannunsa yayi cike da mamaki yace:
"I said I'll think about it. Right?"
Ɓata fuskarta tayi, sannan ta ce:
"Please ba sai kayi tunani ba, ni a shirye nake."
Wani irin abu yaji ya tsarga masa tun daga tsakiyar kansa har tafin ƙafarsa, hakan ya saka cikin dabara ya ɗauki ƙaramin pillow da yake gefensa ya ɗora a tsakanin cinyoyinsa saboda kar asirinsa ya tonu.
"I'm not in the mood. Idan na shirya zan kira ki."
Miƙewa tayi tsaye ranta a ɓace ta fice ta nufi bedroom ɗinta, saboda zafin abinda yayi mata, daman ta sani za'a rina in baiyi hakan ba ai shi ba namiji bane.
Tana isa ta fizge hijab ɗin jikinta ta jefar, ta kasa kwanciya, sai kai kawo take yi abun duniya ya ishe ta, can ta tuna wani abu, aikuwa ta ƙara bazama ta nufi ɓangaren na sa.
Shi kuma tana fita ya ya miƙe, tare da dunƙule hannunsa ya naushi bango cike da nadamar tankwaɓar da wannan damar da yayi da kansa.
Take wannan jin kan na sa ya fara bashi haushi. Sai da yayi kamar ya bi bayanta, amma wata zuciyar ta dakatar dashi dole ya dawo ya zauna.
Wannan karon ko ƙwanƙwasawa ba tayi ba kawai ta faɗo ɗakin, yana hangota yayi sauri ya sake ɗaukar pillow ya ɗora a tsakanin cinyoyinsa.
Sannan ya sake ɗora laptop ɗinsa akai tare da kawar da kansa daga kallonta, saboda kayan baccin da suke jikinta sunyi matuƙar ɗaga masa hankali, sun kwanta luf a jikinta babu abinda ba'a iya gani.
Hakan ya saka ya fara haɗiyar yawu da ƙyar.
A hankali ta ƙaraso ta zauna a kujerar da ta tashi, sannan ta kalle shi tace:
"Ni fa sauri nake yi saboda idan aka gane abinda na aikata a gidanmu wallahi na gama yawo. Ban san ta yadda zan fara yi musu bayani ba."
Ajiyar zuciya yayi saboda wani abu da yaji ya tsikare shi ta ƙarfin tsiya. sannan ya kalle ta yace:
"I said I'm not in the mood."
Durkushewa tayi akan gwiwoyinta tana faɗin:
"Please!"
Juyowa yayi da mamakinsa yace:
"Are you begging for a sex?"
Sunkuyar da kanta tayi cike da jin kunya. Can kuma idonta ya kai kan ƙaramin pillow da yake tsakanin cinyoyinsa.
Ɗagowa tayi ta kalle shi tare da sakin wani lallausan murmushin dashi kansa sai da ta bashi tsoro.
A hankali ta miƙa hannunta domin ta zare pillow.
Doke hannunta yayi tare da faɗin:
"Excuse me?"
Ɗagowa tayi ta kalle shi fuskarta da alamar gajiya tace:
"You said you're not in the mood, so I'm just trying to figure out."
Sake kai hannunta tayi da niyyar zare pillow, amma ya riƙe mata hannu tare da faɗin:
"What's wrong with you? Are you OK?"
Fuskarsa cike da mamakin yadda akai ta gano shi.
Dariya kawai ta saki ta fara ƙoƙarin cirewa ta ƙarfin tsiya, shi kuma yana ƙoƙarin hana ta.
Can shima abun ya bashi dariya bai san lokacin da ya kwashe da dariya ba.
A hankali ta zare hannunta tare da faɗin:
"Ana so ana kaiwa kasuwa."
Want the next chapter?
Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.