Free chapter · Read without an account

CHAPTER 31 (Meeting II)

by Khadeejah Bint Ismail · NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)

Kwantar da Yusairahn ta yi itama ta kwanta a gefenta ko kayan jikinta ba ta cire ba, lumshe idanun tayi ta na mai jin zafi a zuciyarta sosai kamar an d'aura mata gaushi a kai. Wani sabon kuka take yi kamar ranta zai ko zai iya rage mata radad'in da take ji a zuciyarta ko yaya ne, amma kamar almara sai dad'uwa yake yi kusan 2 ta kasa bacci kukan nata ya k'i tsayawa. Sauka tayi daga gadon ba ta ko kalli gefen Islaam ba ta wuce gaban closet, kayan jikinta ta cire ta d'aura towel ta shige toilet ruwa ta sakar ma kanta tana cigaba da kukanta ba ta tab'a sanin ana wanka ana kuka ba sai yau.



Sai da ta gaji da tsayuwa kafin ta fito goge jikinta tayi tun a cikin toilet d'in tana fitowa ta nemi jallabiya mai kauri ta zura a jikinta wajen sallarta ta nufa ta zura hijab ta tada sallah. Karon farko a rayuwarta da ta rasa mai zata rok'a don duk adduointa a baya samun Burhaan ne amma a yau in da za ta iya da ta rok'i Allah ya hukunta shi da irin abunda take ji a kan shi a yau d'in nan but zuciyarta ba za ta iya aikata hakan ba ko ta so, sai kawai ta samu kanta da adduar neman sassauci da dangana tana mai fashewa da kuka a sujjadar da take.




Sosai kukan nata ya ke tab'a shi ya kuma san a lokacin ya zafe ta don haka ko k'arar shi ta kai ma Allah ba ta yi laifi ba, shi dai fatan shi tayi hak'uri ta samu salama ko zai samu k'warin guiwar tunkarar manya.



Ta dad'e a sujadar kafin ta d'ago sallama tayi ta sake tada wata, tayi raka'oin da zata iya don sai da ta ji tsayuwar na gagararta kafin ta koma ta zauna Qurani ta bud'e da niyyar ta karanta ko zata samu sauk'in zuciyarta sai dai ya gaza yiwuwa don jik'a fallen ta yi da hawaye rufewa tayi ta d'auki carbi duk azkar d'in ya zo bakinta ja take ja a hankali kuma ta ji zuciyarta tana saki saboda Innalillahi da istigfarin da take ta ja da hasbunallah sai da ta ji sanyi sosai kafin ta yi addua ta shafa hijabin ta cire ba ta koma gadon ba ganin ya koma bakin gadon ya zauna sai kawai ta yi zamanta kan carpet.


A ranar bacci ko da gigi bai tunkari gefen da wainnan ma'aurata suke ba balle kuma duk iya k'warewarshi a sata ya gwada sace su , dukkan su kwana suka yi da zullumi da fargaba tana jin kukan zai dawo take cigaba da maimaita Innalillahi. A haka har aka yi kiran sallahr asuba tashi tayi ta sake d'auro alwala ta fito ba ta same shi a d'akin ba sai kawai ta tada sallah, a natse tayi azkaranta da ta saba na safiya ta sake rok'on Allah a kan ta bata juriya da dangana sannan ta tashi daga kan daddumar ta zare duk manyan kayan jikinta ta koma kan gado.




Juyi take yi tana mai neman mafita a take wani shawara ya bijiro mata wanda take fatan ya fiddata idan ta bi shi ( toh Ameen Lele) a hankali wanda ba a cin bashin shi a zauna lafiya ya sid'ad'o ya d'auketa zuwa k'asar bacci mai nisa. Ba ita ta iya farkawa ba sai kusan 10 a zaune a carpet ta ga Yusairah tana wasanninta wato ta farka har ta sauka k'asa kenan.



Saukowa tayi tana murmushi a bayyane tace " Sairah Mammee" da sauri ta fara d'aga hannu tana dariya " Masoyiya ta". Rarrafowa tayi ta zo inda take duk'awa tayi ta d'auke ta, nan ta fara gwalangwalan irin na yara. 



Murmushi tayi tana cewa " ai na sani, kin cika diaper tas ".


Kamar yarinyar ta san me tace ko ta sake washe baki tana cigaba da zancenta alamun masuruciya za a yi, wucewa ta yi zuwa toilet ta wanke ta kafin ta fito  shiryata tayi cikin baby gown na velvet red color. Gashin yarinyar da ya ji mai tayi wa wani style na manyan ƙitso ta gaba kamar za tayi all back but ta bar shi a tsakiyar kai guda biyu sai ta kama bayan da k'aramin ribbon black. Baby wax ta shafa a gaban ya kwanta sannan ta saka mata band mara flower shi ma black, black shoes ta sanya mata bayan ta sanya mata socks white da yayi matching da kayan.




Turare ta sa mata sannan ta zaunar da ita, abinci ta had'a mata ta sa mata bib ta zauna ta na bata. Sai da ta tabbatar da ta k'oshi kafin ta saka ta a keken yara ta fara aikin gyaran d'akin tana yi tana mata wasa, ko da ta gama sai ta turata parlor a haka har ta gama gyaran tsaf ta sanya turare. A kan dining ta had'u da abincin da ta dafa da ba su ci ba, kwashe su tayi ta kai kitchen ta cire wainda ba su lalace ba ta saka a fridge su kuma wainda suka lalace ta yi zubar sannan ta fara had'a sabo.



Mini chocolate pancakes tayi da yawa ba laifi sannan ta ciro nutella ta ajiye a gefen shi, sai ta dafa tea da ya ji kayan k'amshi. Ta shirya komai a tray ta fita da su, zaune ta iske Islaam a kan kujera yana kallon TV cikin rashin natsuwa. Kawar da fuskar ta tayi daga kalllonshi ta koma kitchen d'in, turo keken Yusairah tayi zuwa nan parlorn tana ganin babanta ko ta fara wage murya tana gwaranci har da mik'ewa wanda shi ne ya dawo da shi hayyacinshi.



"My baby" ya furta yana mik'ewa zuwa inda suke, sakin keken tayi ya duk'a ya d'auke ta. Ta ko d'afe tana murmushi d'an sassauta fuskarta tayi tace " good morning".



Dubanta yayi a cikin ido don son ganin yanayinta don har ga Allah bai expecting gaisuwa daga wurinta, ita ko tayi abinda ta saba wato shanye fushi. Hakan ya tilasta mi shi risina na shi yace " morning dear, how's your night?".



Kallon ka raina min hankali tayi masa wato mutumin nan d'an rainin wayau ne, in ba raini ba miye zai tambayeta ya darenta bayan ya san a cikin k'unci da bak'in ciki ta kwana?. Ba ta ko tanka shi ba ta juya da nufin shigewa d'akinta ya rik'o hannunta yana cewa " dear ".




Cije lips d'in ta tayi kamar ya yarfa mata wuta jin sabon munafurci irin na d'a namiji wai 'dear' waigowa tayi ta sauke idanu akan hannunsu da ya sark'e ba tareda ta amsa ba. Ajiyar zuciya ya sauke don haka nan tayi masa mugun kwarjini yace " I'm so sorry dear, na rantse zan kuma rantse miki cewa zan yi auren nan ne ba wai don cin zarafinki ko kin kasa da komai ba I'm just.......".




"Ni ko na kasa Yaa Islaam, na kasa wajen ba ka soyayya wanda shi ne ka ke nema ko? Ai ba laifi ka yi ba so stop saying sorry".


"Ko d'aya ba ki kasa ba wajen ba ni soyayya, kin bani abinda ya fi soyayya dear".



Kallonshi tayi in da tana iya masa rashin kunya da ta ce ' ashe ko baka da godiyar Allah' amma ta gaza cewa komai sai kallonshi take yi kamar zata cinye shi, had'iye yawu yayi yace " in ma nace ba ki ba ni so ba na yi wa kaina k'arya na kuma yi wa ubangijina k'arya, yin auren nan is something from Allah a k'addarata take and ba zan iya kuɓcewa hakan ba......"





"Ga kuma kasantuwarshi a sunnah mai k'arfi ba? Well congratulations".



"Ki yi hak'uri".


In da ya san yanda take jin zafin kalmar hak'urin da yake furtawa da bai dinga fad'i ba don ji take kamar yana zuba mata wuta a k'irji, juya idanu ta yi tace " ni fa ba ka min laifin komai ba, so ka je kayi aurenka Allah ya sanya alkhairi".




Baki ya bud'e zai yi magana tace " ni kam Yaa Islaam ka k'yale ni haka please, na ce na hak'ura kana son uzzura min haba mana ni wanka ma nake son yi if zaka bar ni".



Sakin baki yayi yana kallonta ta janye hannunta hankali kwance ta wuce ta bar shi a wurin ta na jan k'aramin tsaki a ranta, shi ko zama yayi cikin sanyin jiki yana mamakin sauyin halinta sai kuma wata zuciyar ta tunatar da shi cewa kishiya fa zai mata ba komai ba. Lumshe idanu yayi ya bud'e yace " so help me god".






Sai da ta ci kukanta ta k'oshi kafin ta iya jan jiki ta shiga cikin toilet, wanka tayi cikin natsuwa yanda ta saba sannan ta fito sanye da towel. A bakin gado ta tarda shi kwance shi da 'yar shi su na kallon ta, wucewa tayi gaban mirror ta zauna shafa ta fara shi ma kamar kullum cikin natsuwa da kwanciyar hankali kamar ba abinda ke damunta. Sai dai yau ta gaza shafa hair color ko tayi waxing hair spray kawai ta shafa sai turaruka ta wuce closet, doguwar rigar plain material ta ciro maroon color.



Ta sa milk d'in hula ta zare slippons d'in k'afarta ta zura flat shoe bak'i ba ta ko dubi inda suke ba ta nufi waje, zama tayi a dining ta yi serving kan ta pancakes ta cika nutella da condensed milk don har yanzu tana son kwad'ayi ta had'a tea. Sai dai duk yanda ta so ci kasawa tayi sai kawai ta din ga kurb'ar ruwan tea, bud'e k'ofa yayi ya fito yana kallonta cewa yayi " shi ne abun babu jira?".



"Ina jin yunwa ne shiyasa" ta amsa masa a tak'aice ta na danna pancake d'in, cikin ko sa a ta samu ta fara ci a hankali kamar ba ita ta gama struggling ba. Zama yayi a kujerarshi bai ko jira ta ba yayi serving kan shi shi ma ya fara ci, ta na samu ta ci iya yanda za ta iya d'auka ta zame hannunta tissue ta ja ta goge bakinta ta koma d'aki. Samu tayi ashe Yusairahn bacci take yi sai ita ma ta kwanta gefenta tana lumshe idanu, after like 15mins ya turo k'ofar ya dawo cikin lumshe idanu tayi kamar mai bacci don ko d'aya ba ta son ganinshi shi ko ganin kamar ta na bacci duk da jikin shi ya ba shi ba bacci take yi ba sai kawai ya juya ya koma inda ya fito don dama office yake son fita duk da ko lattin da ya zabga suit d'in shi ya d'auka da backpack ya fita daga gidan.




San da ya isa asibitin cike yake da mutane sai dai ba wanda zai iya gani don haka ya shaidawa nurse cewa ba zai ga kowa ba, Adnan da aiki yayi wa yawa ne ya sauke ajiyar zuciya don ya hango zuwan Burhaan d'in ta window. Cikin nishad'i ya shiga system d'in shi ya rage patients zuwa office d'in Burhaan sai dai yayi bouncing back wai he's unavailable, tsaki yayi ya san halin kayan shi ya sa ya mik'e zuwa office d'in ba tareda yayi ko knocking ba ya fad'a ciki da sallama.




Yana zaune kan sofar da ke parlorn kan shi a k'asa da sauri ya k'arasa cikin office d'in a d'an rud'e, dafa shi yayi ya d'ago da sauri yana kallon shi absent mindedly. Sai kuma ya maida idanun ya rufe su, cewa yayi "dude, what's wrong with you?".



"Me ka gani?".


"Au kai ba ka san me na gani ba? Duk ka wani yamutse ne, me ya ke faruwa?".



Girgiza kai yayi yana cewa " ni ba abinda yake faruwa da ni".


"K'arya kake yi Malam, rabon da in gan ka haka tun farkon aurenka ko dai ban kai ka gaya min ba ne?".



"Ai kuma sai ka yi " ya furta yana wucewa kan kujerarshi ya zauna, k'wata Adnan yayi kawai yana juyawa cikeda jin zafin shi. Ba tun yau ba ya fuskanci yana da damuwa ba amma kuma ya k'i fad'in masa, ga kuma na yau da ya fi kowanne d'aga masa hankali don a iya sanin da yayi wa Burhaan bai b'oye masa abubuwa shiyasa ma ya san da soyayyar da yake wa Suleim da kuma k'iyayyar da yake wa Nadeefah.



Shi ko Islaam ranar haka ya yini tunani ko kiran Fareesahr ta shi bai iya d'agawa ba, sai da yayi la'asar ne ya biya ya d'auke ta daga makaranta inda ta din ga masa k'orafin wai ya daina son ta. Sai dai daga response d'in shi ta gane kamar yana damuwa ko yana shirin komawa Burhaan d'in da ta san shi a watannin baya, Dr. Burhaan d'in da ta fara had'uwa da shi a deluna da yammaci misalin k'arfe 5 da wasu mintuna.



Sanye ta ke cikin doguwar riga bak'a mai matsakaicin farashi d'inkin dubai wacce aka yi mata ado da stones golden color, kan ta yane yake da madaidaicin jersey scarf shi ma bak'i k'afarta flat shoe ne black sai jaka tote bag da ta rataya a kafad'a ash color. A zahirin gaskiya ba wai wani kyau ta yi masa ba kawai yanayin jikinta ne ya burge shi a matsayinshi na mutum mai son mace chubby, hakan ya sa har yayi gaba ya juyo ta d'ayan u-turn d'in a gabanta yayi parking.


Matsawa yayi gaba ganin ya tsare mata hanya, sake matsowa ya kuma shi ma ta matsa gaba ba tareda ta dube shi ba. Abinda ta yi kuwa ya sark'afe masa zuciya don haka sai kawai ya fito daga cikin motar ta shi ya tsaya a gabanta, a ganin farko sai da k'irjinta ya buga da ganin cikar zati da jamalarshi. Har Allah ba ta tab'a ganin namiji mai cika irin shi ba, sallama ya mata kan ta a k'asa ba ta iya amsawa ba saboda rud'u shi kuwa hakan sa wa yayi ya k'ara ganin mutunci da martabarta a zahirance.




Maimaita sallamar yayi ta d'an d'ago ta dube shi, kwantar da murya tayi ta amsa masa cikeda aji. Murmushi ya saki cikeda jin dad'i yace " 'yan mata ya kike, sai kuma ina haka da yamman nan?".



"Ina lafiya, abu na zo na siya".


Dubanta ya sake yi da kyau yace "zan iya rage muku hanya?".



"No thanks, zan nemi abun hawa kar ka damu".




"Gaskiya ni kam zan damu".



"Allah na gode, kar ma ka matsa don ba zan shiga ba" ta furta don ita ba wani son shiga motar maza take yi ba, musamman shi da ta lura da maik'o a wurinshi haka nan ta shiga ya aikata mata halin 'yan banza duk da dai shi bai mata kama da hakan ba amma ta san dai mazan ba wani amana suke da shi ba ba kuma kama suke da shi na musamman ba balle.




"Toh tunda kin rantse, za a iya ba ni digits d'in da zan kira? Kar kuma ki rantse don ba yarda zan yi ba".



Ajiyar rai ta sauke tana mai mik'a hannunta alamun ya ba ta wayar ta shi, mik'a mata yayi ta sanya masa number ba tare da yayi dialing ba yace " kar in yi saving d'in gaibu, ya sunan?".



"Fareesah" ta furta tana mai jin irin ta b'aro wasan nan.



"Nice name, I'm Burhaan by the way" ya k'arashe yana adana number na ta, murmushi tayi tana maimaita sunan a ranta don ya sake tafiya da ita ainun. Da kan shi ya tsare mata keke napep drop zuwa ung dosa don dama ba wai babu ba ne kawai dai ba ta iya biyan kud'in da suke ta yanko mata ne, shi ya biya kud'in sannan ya shiga motar shi ya ja zuwa gidan.




A ranar ya so kiranta ya ji ya ta koma sai dai Nadeefah ta mantar da shi wata Fareesah gabad'aya, ita ko ta zuba idanun ganin kiran na shi sai dai shiru kake ji wait maye ya ci shirwa. Ta zuba idanu har ta gaji ga kuma kasancewar bai ba ta tashi numb ba da babu abinda zai hanata kiranshi, duk ta bi friends d'in ta da labarin sabon guy d'in da tayi suna ta mata dariya a tunaninsu irin mazan zamanin nan ne da ke tare mace for pleasure in ma ta bibiya wani abu ya so mora a tattare da ita da ya ga ba alamun zai samu sai ya kama gabanshi.



Ita dai tana jin su ne kawai amma haka nan bai mata kalan da suke siffantawa ba duk da ko ba sanin shi tayi ba, sai dai kuma wani gefe na zuciyarta ta fara yarda da abinda su ke fad'i tunda har an kusa share wata babu shi babu dalilinshi. Kwatsam ranar wata talata sai ga kiranshi in da daga fari nunawa tayi ba ta gane mai magana ba, bai yi k'asa a gwuiwa ba ya sake maimaita sunanshi d'an ware idanu ta yi kamar tana gabanshi tace " ohhh Mr. Burhaan ya aiki?".


"Akwai aiki kam, kin ji ni shiru ko?".


"Nope, na san aiki ne yayi maka yawa".


"Actually, kuma ina son ganin ki fa".


Ji tayi kamar ya mata bushara da aljanna tace " toh fa Allah ya sa lafiya?".



"Yeah lafiya lau, yaushe zan zo?".


"Duk san da ka shirya" ta furta tunanin ta ko zai zo yau ko gobe amma ga mamakin ta sai cewa yayi " ok zan duba schedule d'ina, zan ga time ɗin da yayi dai-dai zan zo".



Ok ta furta sai kawai ta ji yace bye yana datse kiran, tsayawa tayi sororo da waya a hannu tana mai jin kamar ya tsinka mata mari. Shi kam wannan wani irin mutum ne haka ba vibes babu wasu kalaman soyayya suna tsaka da magana zai wani ce bye haka ake yi shi a garinsu? (Goga na Lele a ke gaya miki).



Cije baki tayi ba ta kuma yi k'asa a guiwa ba tayi saving da  'lifeline❤🔐' don ita tun had'uwar farko jikinta ya bata ba zata iya rayuwa babu shi ba don tabbas yayi mata illa a zuciya, sai dai shi ma bayan gama wayar ta su da shi sun kai kusan sati guda ko fi ba tareda ya nuna ya tuna da ita ko da a WhatsApp ne ba.




Sai ranar wata talata kusan 3 sai ga kiran shi lokacin tana school, fita tayi daga LT 5 d'in da suke lectures a ciki tana amsa kiran. Gaishe shi tayi ya amsa cikin muryanshi ta kullum cewa yayi " kina ina haka?" Bayan gama gaisawar ta su.




"School".



"KASU hala?".



"Yup KASU".



"Yayi, kin gama lectures ne in zo in yi dropping d'in ki ko ba yanzu za ku gama ba sai kawai mu gaisa in wuce ina school ɗin ku".




"Na gama sai kuma gobe dama yau class d'aya na yi kawai" tayi masa ƙarya.



"Ok, in na gama I'll call you".

Kafin ta kai ga amsawa ya datse kiran tura baki ta yi jin ya datse kiran maimakon ta koma class sai ta shiga IT park ta zauna bayan kamar 30 mins sai ga kiran shi yana tambayarta ina take shaida mai ta yi yace ga shi nan tafe.



Ba a yi ko 5 mins ba sai ga zazzafar aventador d'in shi fara tas tayi parking a wajen shiga, ai sai kallo ya koma sama don d'aukacin mutanen wurin ne suka zubawa motar idanu don ganin wani k'usan ne zai fito daga ciki. Inda galibi suka bada ko dai wani k'usar a gwamnati ko yahoo boys. Cikin masu kallon har da ita da jikinta ya ba ta Burhaan ne amma kuma ta tsaya tana jiran kiran na shi, sai ko ga kiran na shi tana d'agawa yace " ina waje cikin farar mota".




Ok ta furta sai da ta kasa kimtsawa sannan cikin takun k'asaita ta nufi motar kamar ba zata taka k'asa ba, nan itama aka zuba mata idanu kamar za a cinyeta da idanu ita ko cikin son sake kankaro girma ta nufi motar. Bud'e mata yayi kafin ta k'araso yana mai zura mata idanu bai san me yake jan shi gare ta ba, tana sanye da bubu gown na adire maroon da ash ta yafa jersey scarf ash color.



Passenger's side ta bud'e da kyau ta shiga tana mai lumshe ido don k'amshin car freshenern da ya cakud'e da turarenshi da kuma AC, sallama tayi tana gaishe shi ya amsa yana k'ureta da idanu. Ajiyar zuciya ta sauke tana duk'ar da kan ta k'asa, shiru ne ya biyo baya don shi d'in ba gwanin hira ba ne musamman ma da 'yan mata.




Sai kuma ya muskuta yana tambayarta ya school, Alhamdulillah ta amsa tana wasa da hannun jakarta da ta d'aura a kan cinya.



"Wani course ne hala? Na ga kin gaji sosai".



"Journalism".




"Ohhh really? Matata ma course ɗin tayi".



Murmushi tayi tana jinjina kai a tunaninta da ita yake yi juya k'ananun idanunta tayi tana cewa " your wife or wife to be?".




Dubanta yayi da kyau ya fahimci kamar ba ta gane mai yake nufi ba ne ya kuma fuskanci har da kishi a lamarin amma da yake Burhaan bai da mutunci sai ya ce " my wife, ko ba ki san ina da mata Nadeefah da 'ya Yusairah ba ko?".



Wani yawu ta had'iye da k'yar tana kallonshi tana mai jin wani zafi a rai da jikinta, kai ba ta ma yarda yana da wata aba mata ba in ko yana da ita ya zata yi ne? Don Allah ya sani tana son shi sosai kuma ba ta shirya sharing d'in shi da wata ba don haka ta yi shiru ba ta iya magana ba shi ma bai sake magana ba sai da ta taushi kan ta kad'an kafin ta ce " but baka yi kama da mai aure ba".




Dariyar rainin hankali ya saki jin abunda ta fad'i don ta kasa jurewa har kishinta ya nuna a tone d'in ta yace " ba dai baki yarda ba, kawai dai baki son yarda ne amma ni Burhaan Yerwa is married to my cousin Nadeefah Yerwa muna kuma da d'iya Yusairah ga ma proof ki gani".



Ya k'arashe yana mai mik'a mata wayarshi da kyakkyawan hoton Nadeefah tana sanye da doguwar riga kan ta babu d'ankwali hannunta kuma Yusairah ne suna dariya su duka aka d'auki hoton, runtse idanu tayi ta bud'e hannunta yayi scrolling sai ga mirror selfie da Lelen ta d'auke su su uku yana rik'e da Sairah ita kuma waya sun saka matching rigar sanyi ne na puma na shi blue na ta pink ita ma Yusairahn pink ne an rubuta angel a gaban rigar ita ta siya masa su bai san na couple ba ne sai da ya saka da zai fita sai ga shi nan ta fito itama sanye da su shi ne ta matsa sai da suka yi hoto.




Tsura musu idanu tayi a rayuwarta ba ta tab'a ganin couples da suka yi matching da juna ba sai yau, gefe guda kuma tausayin kan ta yana kamata don yanzu kam ta fara yarda da maganar k'awayenta cewa yana ɓata mata lokaci scrolling tayi sai ga pic d'in Yusairahn tana tsaye ta dafa kujera tana dariya.




Mik'a masa wayar tayi cikin k'arfin hali tace " she's beautiful, Allah ya raya muku ita".




"Ameen ya rabbi, tana da kyau kam da mamanta take kama".




Had'iye yawuta yi in dai har ta fahimci Burhaan toh yana masifar son matar shi to in haka ne miye amfanin sa wa ta fad'a a soyayyarshi mai zafi har haka?. Wannan ai d'aukar alhaki ne da cin zali cewa tayi " kai ma ai tana kama da kai sosai".



"Ke ce mutum na farko da ta fara faɗin haka".



"Amma ai na fad'i gaskiya ko, ko kuma idanuna ne ya gane min haka?".




"Maybe " ya furta yana tada motar.



Tafiya suke yi a hanya sai tambayarta wasu abubuwa yake yi a kanta da abinda ya shafeta, maimakon ya bi ta baya ya b'ulla ta kashim ibrahim way ta inda zai fi masa sauk'in zuwa ung dosa sai ya yanka ta alk'ali road da ta tambaya yace " matar shi zai siyawa kifi " ita dai na ta idanu, tsayawa yayi ya fita ya yi order da yake da zafinsu sai bai b'ata lokaci ba aka yi masa packaging d'in su aka sa mai a baya sannan ya tada motar suka tafi.



Har k'ofar gidansu dake rock road ya ajiyeta gida ne madaidaici na 'yan uwan 'yan gayu, a tare suka fito da shi suna cigaba da hira bayan motar ya bud'e ya ciro mata leda d'aya ya dubeta yana cewa "yanzu sai yaushe kenan?".



"Sanda baka busy ko?".




"Uhmm tohm zan samu time ɗin gaskiya don ina son mu zauna da ke mu yi magana sosai".



"Toh fah".



"Yeah".


"Toh Allah ya kawo ka".


"Ameen" ya furta yana murmushi, ledar ya mik'a mata ta amsa tana d'an murmushin kunya shi ko har da cewa wai ta gaida Mommy. Godiya tayi masa ta juya ta shige sai da ya ga shigewarta kafin ya ja ta shi motar ya tafi .



Kamar yadda ta fad'in kuwa sai da suka shanye kusan 3 weeks ba ta sake saka shi a idanu ba, ran da ta gwada kiranshi ko nuna mata yayi bai son kira yana sane da ita ba wai ya manta ba ne. Ranar sai da ta kusa kuka don har a zuciya tana k'aunar shi but ji tayi like she made a mistake of loving him, ko da ta yi wa k'awayenta zancenshi sai suka sake sagar mata da guiwa musamman da ta gaya musu wacece matarshi Khauthar cewa tayi ma ta rufawa kan ta asiri da shi don mai irin wannan matar ba abinda zai yi da ita don ta bakin Khauthar d'in cewa tayi ko ita mace take da kamar Nadeefah ba zata tab'a d'aukar Fareesah ba.




Jiddah ce ta kwantar mata da hankali akan cewa in Burhaan rabonta ne zata same shi but kar ta sawa ranta do or die, kawai dai ta sa probability a rai in ta samu ta gode in bata samu ba ta hak'ura kar tai forcing kan ta a inda zata sha wuya. Ta b'angaren mamanta cewa tayi kar ta wani sare in dai har tana son shi toh ta sameshi sai dai in basu da rabon kasancewa tare sai dai kamar yadda Jiddah ta bata shawara itama cewa tayi kar tayi rushing ta bi komai a sannu.




Ai ko ta bi shawarin su don ba ta sake kiran shi ko neman ganinshi ba, duk da ko ranar tana tsaye a Sarah cafe ta hango motar shi. Shi ma fa ya gan tan amma kasancewar shi da Adnan ne ya sa bai kirata ba gudun abun magana, sai bayan kwana biyu ya ɗauko ta daga school d'in ne zuwa gida suna hira sai ga kiran matarshi da yayi saving number da wife.



Picking yayi yana cewa " how far?".



''Yaa ya aiki? Kana ina ne?".



"Me ya faru?".


"Please whipping cream zaka taho mana da shi namu ya k'are".



"Eh lallai ki dai ce aikena zaki yi".



"No Yaa, sai yanzu na lura babu kuma ina son yin amfani da shi da safe ne"




"Uhmmm toh na ji sai me kuma? Kar sai na dawo a sake cewa 'Yaa ba mu da paper towel".



"Yawwa Yaa tissuen ma ya k'are sai fruits da bread".


"Ok tohm, ki shiga storen ki duba abinda babu sai kiyi forwarding min list d'in".


"Ok Yaa, barin je ".



"Ina baby fa?".



"She's sleeping ".


"Ohhh baby da bacci".



"Wallahi kam ko gajiya ba ta yi".



"Ke ta biyo ai".



"Laaa Yaaa!".



"Na yi k'arya ba?".



"Aa, ai Yaya is always right ".



"Iya magana, ki tura min list d'in yanzu fa".


"Ok sai ka dawo".



Daga haka ya datse wayar ita dai Fareesah tana zauna ta kuma fara nadamar sa shi a rai, ji yanda yake magana da matarshi kamar wani sarki don duk yanda yayi k'ok'arin ya zama romantic a cewarta wannan isar da ke jinin na shi bai je koina ba.




Ajiyar zuciya dai ta sauke har yayi parking a k'ofar kanti plus supermarket da ke kan isa kaita road, kallonshi tayi da yayi parking shi ma dubanta yayi yana cewa " ba zaki raka ni ba?".



"Ohhh na zaci ai ba ka so ne".



"Toh mu je"

Ok ta furta tana bud'ewa ta fito, tare suka shiga yace mata ta d'auki cart itama ta zab'i abinda take so shi kuma ya shiga siyayyar kayan gidan da Nadeefah ta tura masa. Sun d'an jima suna siyayyar ko da ya gama sai da ya jirata ta zo da tarin kayan k'walamar da ta jibga, biya yayi aka sa musu a leda aka kai musu har mota ya ja suka nufi ung dosa. Yana ajiyeta bai wani dad'e ba ya wuce gida, ita kuma ta shiga da jimami kasa jurewa tayi sai da ta sanar da Ammah.





 Shiru tayi tana saurararta cikeda nazari in ta fahimci 'yar tata soyayya ce mai zafi take d'awainiya da ita ba komai ba a kuma wurin wanda bai kuma son ta irin wanda ita take masa in ma yana son na ta kenan, kamar yadda ta saba hak'uri ta ba ta da kuma tabbaci mai k'arfi na Burhaan zai iya zama na ta in dai da rabon ta da shi in kuma babu duk yanda suka so ba zai zama na ta ba so ta kwantar da hankali.




Maganar ko ya sa ta samun natsuwa in da ta sake ajiye Burhaan da tarkacenshi gefe, in ya kirata ta d'aga in ya zo ta fita a hankali kuma sai ta fara ganin canji daga gefenshi ya fara kiranta sosai ga uban kud'in da yake kashe mata kamar bai san zafinsu ba, ga kuma yawon da suke yawan fita musamman da dare ta yawon eatery da joint sai kuma kwatsam ya fara mata maganar aure kamar an ingizo shi kuma bai daina magana ba. A da ba ta da plan d'in yin aure amma saboda son da take masa ya sa ta amince ya zo ya ga Babanta a yanzu haka zancen zuwan iyayenshi ake yi yau kuma ya zo fuskar shi a cunkushe bayan ita ya kamata tayi fushi tunda shi ne bai kira ta ba jiya ta kuma kira bai d'aga ba.........




Sake kallonshi tayi tana cewa " ka tabbatar kana lafiya kuwa babe?".



"Yes I am, hungry nomad d'in zamu je d'in ko shawarma corner ?".




"Da red bricks na ce but mu je shawarma corner ".



"Alright" ya furta yana karya motar shi yana hawa kan titin da zai sada su da inda ta fad'in.




Bacci ta sha sosai sai kusan 2 ta iya tashi kallon agogo tayi tana mamakin baccin da ta yi da kuma yanda Sairahn ba ta farka ba, lallab'awa ta yi ta sauka daga gadon toilet ta nufa fitsari ta samu ta yi tai alwala ta fito sallah ta gabatar sannan ta nufi kitchen noodles ta dafa saboda masifaffiyar yunwar da take ji. Bedroom d'in ta ta nufa da ta gama nan ta samu har ta farka sai tayi zaman shayar da ita sai da ta k'oshi sannan ta zauna nan k'asa ta kunna TVn dake dak'in ta ci abincinta, ta ci sosai don tana jin yunwa ba laifi nan k'asa ta kwanta tana wasa da Sairah sai da tayi la'asar ta fito ta d'aura dinner tana mai k'ok'arin kawar da damuwar da ta b'ullo mata.





Ko da ya shigo tunda ga barka da dawowa ba ta sake kallon ko gefen da yake ba ta cigaba da hidimarta ko da yace mata ga shawarma thanks kawai ta furta tana mai barin masa parlorn. Da idanu ya rakata kawai yana jin babu dad'i don treatment d'in da take ba shi gasa shi yake yi sosai gabad'aya bai son haka kuma har ga Allah ya na damunshi yau ma dai kamar jiya bai iya bacci ba ita ma tayi ne ba don tana da niyya ba sai don shi d'in ya isa gurin sata kuma k'yale mutane da yake yi ba wai yana tsoron su ba ne Aa bai ga daman d'aukar su d'in ba ne. Sake tunkarar ta yayi da maganar da safiya sai dai ta sake maimaita masa da cewa aurenshi bai dameta ba ya je yayi tayi Allah ya sanya alkhairi, duk da ya ji babu dad'i da yanda ta amsa shi amma sai ya daure don son a zauna lafiya maganar kuma da ta sanya shi samun k'warin guiwar tunkarar su Abba da zancen.





Da sauri take saukowa daga matakalan bene jin kiran gaggawar da mijin na ta yayi mata, har ga Allah in akwai abinda ta tsana toh bayan kiran kwatsam d'in da yake mata ne wanda har yaransu sun gado. Ya na kiranta kawai umurni yake yi kafin ta amsa ya katse wayar, ya kwana biyu kuma bai mata irin kiran ba koma tace rabon da ta ji muryarshi a haka tun kafin auren Burhaan.




Samu tayi ta sauka lafiya ta nufi parlorn na shi, zaune yake kan kujerar da take fuskantar k'ofar fita while gabanshi Burhaan ne yana zaune yana mai duban shi kan shi k'asa kamar yayi laifi. Maimaita sallama tayi suka amsa ba tareda shi Abban ya dubeta ba Islaam d'in da take zaton laifi yayi ne kawai ya dubeta. Ita ma kallon me ya faru tayi masa kafin ya kai ga ba ta amsa Abban yace.



"Zo ki zauna ya sake maimaita abinda ya zo yake fad'a min don na fahimci ni d'aya ya raina".



Duban natsuwa tayi mishi again sai kuma ta maida hankalinta kan Abban tana cewa "Zauj me ya faru ne? Me ya gaya ma ka ne har haka da ya fusata ka?".




"Ga shi nan ya fad'i don ubanshi, ka fad'i shirmen da ka zo kana gaya min nace don ubanka".




D'an kallon Umman yayi ya ga yanda ita ma take bin shi da duban tuhuma, sai ya maida kai k'asa ya san ba laifi a maganar shi amma ya tabbatar ba za a kwashe ta dad'i ba.



"Wai Islaam za kai magana ne ko zaka tsare ni da idanu kamar shege a rabon gado?".




"Kallon rashin kunya da munafurci ba, ka maimaita abinda ka fad'a min na ce".


"Uhmmm.....dama yarinyar da nake zuwa gidansu ne Babansu yace in fito".




"Miye kuma yarinya miye kuma had'inmu da Babanta?".


"Ni ne fa nake zuwa wurinta".


"Na me fa?".



Shiru yayi ya kasa k'allonta don daga yanayin maganar ya gane ba ta son zancen kuma tana so ne shi ya fad'i maganar ba tareda ita ta taya shi ba. Ganin yayi shirun ko ta zaburo masa tana cewa " wai Islaam akwai tsaranka ne a wurin nan da za a dinga maka magana kana sharewa, zaka yi magana ne ko mu bar maka wurin " yawu ya had'iye yace.


"Umm.....Umma ki yi hak'uri don Allah  dama........dama.......aure na ke son yi!".




"Dama ba ka da aure ne ?" ta tambaya cike da izgili.


"Kya taya ni tambaya". Abba ya faɗi.




Inda-inda ya fara kamar sakarai don ya lura iyayen na shi akwai gasa mutum cikin ruwan sanyi "uhmmm wai k'arawa zan yi".




"Innalillahi!! Aure fa ka ce? Na menene auren ?".



"Na cin mutunci da k'ask'anci mana ba mun masa wanda bai so ba ai dole ya nuna mana k'arshen mu ko kuwa?".




"Eh tabbas Zauj yanzu kam ya nuna mana iyakarmu, ni Sato ina ganin banu".



"Walh Umma ba haka ba ne....."




"Toh in ba bamu isa da kai ba Burhaan toh menene? Ehnnn tell me!".




"Ina son ta ne wallahi".



"Ita kuma wacce muka aura maka ba ka son ta ko?" Fad'in Abba a zafafe.



Girgiza kai yayi yace " ko kusa".



"So kake kawai ka nunawa duniya cewa ba mu kai mu saka ko mu hana ka ba ko".



"Aa Abba".



"Toh mu dai in dai ta bakinmu kake son ji then ka ji ka kuma rik'e ba mu amince da yin aurenka ba, amma in kuma kace kana son yi toh ga hanya nan Allah ya bada saa".




"Ki dai gaya masa bai isa yayi aure ba matuk'ar Nadeefah ce a cikin gidanshi, in kuma mu ne ba mu isan ba toh".




"Abba Umma ku yi min adalci a rayuwa please kar ku haramta min abinda mahaliccina ya halalta mini, besides Nadeefahr da kan ta ta amince inyi auren nan kar ku hana ni don Allah " ya k'arashe cikin sanyin murya kamar zai musu kuka.



"Eh tabbas Lelen ce tace maka ta yarda ka yi aure?".



"Ba dole ta amince ba Ameenah, tana da abun cewa ne bayan ya mata jan ido da nuna mata duk abinda ya so shi zai yi ko an gaya miki shawararta ya nema ba umarni ya bata ba".




"Allah Abba ban tilasta ta ba".



"Dallah rufe min baki a wajen, toh ni dai bai shafe ni ba ko kuma waye ya yarda ni dai ban yarda ba in kuma za ka yi ga hanya nan".



Umma ko cewa tayi " da kuma kake wani cewa halalinka ba ka san akwai inda bahaushe yake cewa ana barin halal ko dan kunya ba ko an gaya maka a banza ya fad'i hakan, kai ni ba ma wannan ba a kaf familyn nan wa ka ga an wa kishiya har ya burge ka?".



Girgiza kai yayi alamun babu shi ma kuma a da policyn shi ne mace d'aya amma had'uwarshi da Fareesah komai ya sauya, so yake ya aureta ko ta halin k'ak'a ne ji yake in bai sameta ba toh wani abu zai iya samun shi.



"Ko bata gamsar da kai ne?".


"Aa".



"Tana da wani mugun hali ne mai muni da ba zaka iya da shi ba?".



"Ko d'aya".



"Ibadanta fa?".



"Tana da tsare ibada ba ta da wasa da shi".



"Then an gama magana ba zaka k'ara aure ba tunda ba ta inda ta gaza".




Abban yana fad'in haka ya mik'e ya shiga ciki matarshi ma ta mara masa baya suka bar shi a wajen kamar tsinkakken silifas, bin su yayi da ido yana jin kamar ya fashe da kuka jin maganar da suke yi kamar ba shi suka haifa ba. A da yana tunanin Abba zai fahimta ashe yayi kuskure don bai ga alama ba ko kad'an kuwa.



Haka ya ja sanyayyun guiwar shi ya koma gida wurin matarshi da take jin duniyar ya fice mata a kai ainun, ganin ba ta kula shi ba ya sa shi tafiya wajen Fareesah cikeda son kawar da damuwa a ran shi sai dai bai samu ba don itama b'ata mai rai tayi da request d'in kud'ad'e masu kauri ba kuma don sun fi k'arfin shi ba sai don kawai ya tsani rok'o a rayuwar shi ainun.




Da ya dawo wanka ya baza cikeda mugun son kasancewa da Nadeefah don yayi mugun kewarta, yau kuma 4 days kenan  rabonshi da ko farcenta ya tab'a. A zaune a kan gado ya tarda ta tana waya da Ummu da ke tambayarta me yake damunta don kwana biyun nan she's very low, da ko sakin jiki ba ta iya yi da su ko a waya kamar yadda ta saba dama ita Hajjah tayi na ta tambayar ta gaji don ba ta kwana d'aya ba ta zo inda take ba yanzu kuma kwana uku a jere ko k'afarta ba ta gani ba. Amsa mata tayi da lafiya lau take kawai tayi busy ne so take in ma ta samu dama ta d'an zo Abujan ta huta, a sonta ma wake take son fita but ta san ba barinta zai yi ba so zata yi managing Abujan.




Ummun ne tace "ki dai bari mu zo meeting next week kafin nan kin samu kin rage abubuwa in ya so sai mu taho tare" ok Ummu ta furta tana ture kan Burhaan da ya d'aura a kafad'arta, sake maidawa yayi yana mai shinshinarta sai kawai tayi sallama da Ummun tana mik'ewa tsaye janyota yayi ta fad'o kan shi ya fara k'ok'arin had'e bakinsu sai ta dage ta sakin masa kuka mai d'aci da zafi.



Tsayawa yayi sororo yana kallon ta tana kuka sai kuma yace " Nadeefah tab'a kin da nayi ne kike wa kuka?".



"Dole in yi kuka mana tun da ni a wurinka ba ni da wani daraja sai na biyan buƙatar ka, a shimfid'ar ka ne kawai nake da daraja da mutunci in ban yi kuka ba Yaa Islaam me kake so in yi? Dariya ko murna".


Kallon ta yake yi cikeda tausayi don yanda take kukan ya tab'a shi ainun bai kuma tab'a jin tausayin ta ba kamar yau, wani miyau ya had'iye da k'yar yace " ko d'aya Nadeefah, waye yace miki baki da daraja a idanuna sai a shimfid'a kawai?".




"Abubuwan da kake aikatawa su suka faɗi haka, Yaa baka da wani respect kai na don ban iya tsinana maka komai a zamantakewar mu sai ta gefen biyawa rai buk'ata and shi yake min ciwo ba kuma zan maka k'arya ba".




"I'm sorry wife ".



"Ai ban ce kayi min laifi ba ko kukan nan da nake ba dan kai nake yi ba sai don kai na" sai ta sake fashewa da kukan, rungumota yayi jikinshi yana mai lallashinta duk wata kalmar lallashi da ya sani. Amma ba ta iya tsagaitawa ba don kukan nan abu ne da take son yi dama ne kawai ta nema ta rasa, yanzu ne ta same shi ba tayi ƙasa a guiwa ba wurin amayar da abinda ke ranta ba, a haka barci ya d'auketa shi kuma duk wata k'walama da ya d'ebo nemanta yayi ya rasa karon farko da damuwarta ya tab'a shi kenan.





Haka suka cigaba da lallab'a rayuwa babu wata jituwa tsakaninsu da juna don ta k'i sakin jikinta da shi shi kuma sosai yake yin d'ari-d'ari da ita kamar yana tsoranta kuma tun ranar bai sake attempting tab'a ta ba kamar yadda bai fasa shirin auren da yake ji babu mai hana shi ba.




Tare suka shirya suka nufi meeting da shi tayi kyau sosai cikin bak'ar atamfa mai adon ja an yi mata d'inkin kaftan ba tayi kwalliya ba ta shafa lip gloss da kwalli, Chantilly veil ta yafa red ta rik'e birkin bag black color da mahad'in takalminshi shi ma black. Idanu ya tsura mata da ta fito daga ciki tayi kyau ainun sai dai fuskar nan babu walwala ko na sisin kwabo, Sairah dake zillon zuwa wurin shi ya karb'a idanunshi a kanta yana amsa gaisuwar da take masa.




Tare suka zauna a table tayi serving d'in shi ta ajiye masa plate d'in a gabanshi yayi murmushi yana godiya ɗaya daga cikin abinda yake so a tattare da ita shi ne duk yanda take nuna masa tana jin haushinshi bai sa ta tab'a hana shi abinci ba, jikinta ne dai ta hana sau d'aya wanda bai kuma sake tambaya ba duk da yanda yake a matse da ita.




Silently suka ci abincin babu magana yana yi yana sa wa Sairah da ke jikinshi a baki, da suka gama kuma sai da tayi wanke-wanke kafin ta rik'e jakar suka tafi. Sun tarar an gama hallara don suna shiga hall d'in motar su Hajjah tana shigowa, ganin mutane sai ta d'an gwada sakin fuska kamar ba abinda yake damunta musamman da ta tarar da su Suleim sun zo garin. Tare suka gaida iyayen ba ma su kai ga zama ba su Hajjah suka shigo yanda ta sake tarbarsu haka ta musu sai da suka zazzauna kafin ta koma cikin su Zulfaa suna tsokanarta wai ta d'ashe ko ciki ne da ita.





Gabatar da dalilin zaman watan suka yi in da mak'asudin zaman bai wuce na tallafin da zasu tura Maiduguri akan annobar wutar da da ta afka, nan a take kowa ya tura iya abinda yake da shi a account d'in da aka bud'e sabo don tallafin. Sai aka sake tattaunawa akan business da ribar da aka samu, sai kuma hannun jarin da za a siyar nan su Burhaan, Farhaan da ElSadeeq suka siyawa su Yusairah, Azad da Afdhal a nan akai sealing d'in aka yi signing da shaidu da komai kafin Baba Tijjani ya dube su duka yana cewa " akwai mai wata matsala a cikinku?".




Kowa shiru yayi don babu wani mai babbar matsala a ciki a take wani tunani ya zo masa yana mai jin kamar in yayi shiru babu hanyar warwarewar ta shi don haka ya mik'e zumbur kamar an ingiza shi yana cewa " sai ni Baba".



Umma da Abba ne suka kalle shi cikeda mamaki don su sun sha sun gama magana ashe ba su isan ba kamar yadda suka ce d'in.



Baban ne yace " kai kuma Islaam miye matsalarka?".



Duban gefen Nadeefah yayi kan ta yana k'asa bai ko gigin kallon gefen Umma ko Abba da suke ta jefa masa muggan kallo ba ya dubi Baban yace " eh baba akwai matsala, amma kafin fad'arta ina son in ba wainda suke zagaye da ita hak'uri I'm really sorry".



"Ka san dai nan ba fada ba ne balle ka ce za kai mana fadanci a nan ko? Besides fadancin ma ba kyau yake maka ba so just be Islaam and talk" Baba ya fad'a cikeda k'osawa don shi bai son kwana-kwana sam.



Sake duk'ar da kai k'asa yayi yana cewa " Baba aure nake son ku nemo min please ?".



Ai sai d'aukacin hall d'in ya kacame da hayaniya ba ka jin komai na tashi sai kalmar Aure yayinda idanu suka yi yawa a kan shi da Nadeefah, Baban ma sandarewa yayi sai dai bai ce uffan ba sai da ya samu ya fita daga shock kafin ya tsawatar nan kowa ya natsu amma ba a fasa zura musu idanu ba yacce kasan sun ci zab'e.




"Masha Allah Islaam da alamu kai zaka fara zama Barden Yerwa don ka gan mu nan duka matsorata ne su Mommynku sun hana mu kuma mun hanu" Baban ya sake fad'i cike da barkwanci.



Sai dai ba wanda yayi dariya sai Abba ne daya mik'e yace " ba Barden da zai zama Yaya don shi ma mun gama magana ba auren da ya isa yayi".




"Tabbas kuwa, ba zai yi aure ba" Umma ta fad'i cikin son nuna goyon baya ga mijinta.




"Saboda ku ne kuka haife shi ko? ".



Inji Daddy Senator yana duban su Abban.




"Shi ne dai nake gani Senator hala bayan haihuwa ma halittar shi suka yi da zasu hana shi raya sunnah" Baba ya ƙara da faɗi.




"Ko d'aya Yaya saboda dai bai da hujjar yin auren a yanzu may be a nan gaba".




"Saboda yana auren 'yar ku ko?".




"Ko d'aya Yaya, saboda a hujjojin da ya kawo babu wainda suka cancanta yayi aure".




"Baba ku duba min please ko babu komai ni ma na muku biyayya a tsakar hall d'in nan kuka ba ni Nadeefah na kuma saka hannu na karb'a ba tareda bin diddigi ko muku bore ba, ni ma ku bani dama yanzu in auri wacce na ke son aure"


Duban Nadeefah yayi yana mai jin tausayinta don maganar Burhaan d'in ta tab'a shi ta kuma tuna masa da wani alk'awari mai k'arfi da ya d'aukar masa, wanda ya san cika shi dai dai yake da tab'a farincikin d'iyarshi amma gwara farincikinta ya tab'u da ya karya alk'awari.




"Ka yi hak'uri Islaam ka yi wa iyayenka biyayya a yanzu, ni kuma na maka alk'awarin duk randa ka samu wacce kake so zan tsaya maka ko babu kowa a bayanka har sai ka sameta". 



Wannan su ne kalaman da ya gayawa Islaam a lokacin boren shi na bai son Nadeefah a she ranar yana nan zuwa, idan kuma ya sake ya nok'e ba zai taɓa yafewa kan shi ba kallon Ummu yayi da ita ma shi take kallo da idanu yayi mata alamar ya zai yi? Kai ta gyad'a masa alamun ya aikata kawai ai ko ya mik'e tsaye yana cewa " ina son nima in ba ku hak'uri a kan katsalandan da nayi muku a yanzu but a adalci bai kamata a hana Islaam yin aure ba, don tabbas yayi mana biyayya gaya why yanzu za mu hana shi abinda Allah ya yarje masa?".




"Kar ka sake magana Yusuf, in kai ma ban isa da kai ba ne toh kai ma kayi" in ji Abba wanda yake ji kamar ya make Abbu, Baba ne yace " ka rantse ba zaa gaya maka ka ji ba ko?".




"Ko kad'an Yaya kun isa har kun yi yawa ba kuma son zuciya ba ne ya sanya nake k'in auren Islaam but sigar cin fuskar da auren ya zo da shi duka yaushe yayi aure da yake shirin k'ara aure?".



"A kai auri mace biyu a rana d'aya ma Abdoulaye ? Ai in dai yana da halin rik'e iyali toh yin auren na shi bai tab'a zama laifi ba ko kuwa?".




"In ma dai ta nine na amince masa tuntuni ina rok'on su Abba su yi hak'uri su bar shi yayi auren nan please................"


Deejasmah ✍🏼

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol