Free chapter · Read without an account
CHAPTER 32 (Broken).
by Khadeejah Bint Ismail · NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)
Nan idanu suka mata caaa kamar ita d'aya ce mutum a hall d'in yayinda k'ananun maganganu suka fara tashi, Suleim dake gefenta ne ta rik'e mata hannu ganin yanda jikinta yake rawa sosai. Wani d'aci take ji a kan harshenta tare da wani mugun haushi da tsanar Islaam, Idan ma auren zai yi ai ba sai ya biyo ta wannan sigar ba don me ba zai je wurin Baba su yi magana a gida ba?.
Ita ko Umma mik'ewa tayi tana tafiya tana cewa " ai kya ce kin amince mana saboda ba ki san abinda ke miki ciwo ba, dubeni nan Nadeefah ko kin amince ni ban amince ba" ta rik'eta itama a lokacin da ta k'araso.
"Toh Sato ba gwara ta amince ba da wannan tijara da yake janyo mata? Wannan ma dan ba ki san kalar rashin mutuncin da yayi mata ba ne a gida" in ji Abba a harzuk'e.
Lumshe idanu tayi tana lallasar zuciyarta da kuma idanunta kar su ba da ita, don ta tabbatar ta sake tayi kuka yau toh akwai matsala. Cikin dauriyar tace " Umma kace-nace d'in nan ne bai da wani alfanu, musamman akan abinda halal ne hanawar kuma sab'o ne babba ina roƙon ku kawo k'arshen maganar nan a je a nema masa aure don Allah!".
"Ni ma ina rok'onku please kar ku hana Islaam yin aure don in aka masa haka an shiga hak'kinshi" Ummu ta furta cikin son shanye damuwarta sosai.
Maganar da ta fad'i ne ya k'ara sa d'akin ya d'auki zafi ƙananun maganganun da ake yi kuma suka koma hayaniya don ba ma ka jin abinda ake fad'i ko kad'an, kai kuma ya rabe gida biyu don daga Abbu, Baba Tijjani sai Daddy ne kawai suka goyi bayan yin aurenshi sauran kuma yara da manya kowa yana nuna ba sa tare da shi su kuma matan auren suna gudun kar ya zama silar fara musu kishiya a na zaman lafiya.
Hajjah ne ta dubi su YaMara da kamar 'yan d'akin sun manta da zamansu a wurin tace " a k'yale shi mana yayi aurenshi, wannan ai ba wani abun hayaniya ba ne".
"A k'yale waye Ya Hajjah? Ai bai isa yayi wani aure ba in ya ga dama kar ya hak'ura" fad'in YaMara tana huci kamar ita za a yi wa.
Ya Madari ce tace" Aa wannan rashin adalci ne bayyananna, kuma k'in yin auren matsala ne mai girma don tunda ya dage in aka hana shi ya na iya shiga wani yanayin da zai iya saka mu dana sani gabad'aya".
"Ni ma abinda nake hanga kenan, maimakon nuna k'iyayyarmu ga lamarin me zai hana mu yi adduar mafi alkhairi a auren da zai yi".
"Babu fa wani alkhairi a auren nan, kuma har abada ni dai ba zan amince da wata mace a gidan Islaam ba bayan Nadeefah me yarinyar nan ta mai da zafi ne har haka da ba zai iya zama da ita ba? Haba Hajjah kowa fa ya san hak'uri take na zama da shi ko cikin saointa da suka yi aure rana guda ban tunanin akwai mai rabin hak'urin da baiwar Allahn nan take yi sai a bar shi ya auro wata ya zo yana had'uwa da ita ya cusguna mata su kashe mana ita?".
"Ai shi aure d'an hak'uri ne in dai ta daure ta shanye sai ki ga Allah ya dubi sadaukarwarta ya mata zab'i mafi alkhairi sai ma ki ga auren ya sa shi ya fara kyautata matan da kuke ganin bai yi".
"Sosai kuwa, don Allah mu had'u mu k'arfafa musu guiwa dukansu namu ne ba wanda ya fi wani. Kar kuma mu sa son zuciyarmu sai Allah yayi fushi da mu" in ji Ya Madari, had'uwa suka yi da Hajjah suna ta tausarta har tace "Allah ya sanya alkhairi" ba dan tana so ba don kawai ba ta da yanda za ta yi da su.
Hajjah ce ta d'aga hannu nan Baba Tijjani ya tsawatar musu kowa yayi shiru yana komawa wajen zamanshi, tasowa yayi ya zo gabanta ya duk'a a hankali tace " a daina duk wani musu da jayayya gobe da yamma aje a nemawa Burhaan aure a wurin iyayen yarinya kamar yadda ake nemawa duk wani d'an Yerwa aure".
Abba ne ya dubeta cike da damuwa ta girgiza masa kai idanunta kan Lelenta, ita ko ba ma ta d'ago ba dukda tana jin idanu a jikinta. Gyaran murya Baba ya yi yana mai cewa " ya isa haka, za mu d'an gudanar da bincike kan ahalin yarinyar nan kafin goben da zamu je gidansu kai Burhaan ka ba mu number Babanta za mu yi magana da shi".
"Toh Allah ya ba da sa'a amma Yaya da Hajjah ku yi hak'uri ba wai na raina ku ba ne amma ni dai kowa yai shaida babu ruwana da wannan auren haka iyalaina ma shi dai da ya zab'i yayi ga hanya nan" Abba ya furta a d'an fusace yana mai jin kamar yayi fiffike ya bar musu d'akin taron, Hajjah ce ta dube shi tace " kayya Abdoulaye, wannan bai kamata daga gareka ba ko ba komai ka sa musu albarka tunda ba ka san me Allah ya sa a auren ba".
"Haka ne Hajjah, amma dai a mini afuwa ba saboda wani abu na zare hannuna ba sai don ya nuna min ban isa da shi ba. So sa hannuna ko bakina a lamarin bai da wani amfani".
"Yaya ka yi hak'uri tohm, a madadinshi muna baka hak'uri in shaa Allah kuma ba za a kuma ba wannan ma kuskure ne zamu gyara" Abbu ya fad'i cikeda tausasawa, harararshi Abban yayi kawai yana tsaki a k'asan ranshi yana tanadar kalar wulak'ancin da zai wa Abbun don ya lura akwai sa hannunshi a lamarin.
K'wafa yayi bai sake sa musu baki a maganar ba, in da ma yana da dama da fita yayi ya ba su wuri amma ya san me hakan yake nufi. A wurin suka tsaida magana inda bisa zab'in rai aka sa Abbu, Baba Tijjani da Daddy ne za su neman auren, duk su kad'ai ne suka goyawa Burhaan baya sauran 'yan d'akin ma haushinsu suke ji sosai. Adduoi aka yi aka shafa a kan za a je ayi Azuhur sai a dawo a ci abinci, a wurin sallahr ne 'yan family suka tasa maganar a gaba kamar yi Ya Budu tayi masifa kamar za ta ari baki. Duban Lele tayi tana cewa " a kan me zaki wani amince ma shi ya k'ara aure ehnn?".
Shiru tayi tana had'iye yawu don ita har ga Allah da za su k'yaleta da maganar da sun taimaketa ainun, Ainah tace " kamar mara wayau ba? Wai ke Nadeefah miye matsalarki ne ko an gaya miki a kanki aka fara aure ne da zai dinga juya ki iya son ran shi?".
"Wai ita mai biyayya ba, yoh ai ni babu namijin da zai ce min zai k'ara aure in goya masa baya har kuma ana maganar hana shi in saka baki ai maganata a wurin will only be wlh ban amince ba in saka musu kuka" cewar Insiyyah tana haki kamar ita za ai wa kishiyar.
Fadwah ce tace " ba laifi a biyayya ai kawai dai akwai lokacin da mace zata murza kambunta kuma ko namiji ya so ko ya k'i dole ya bi ta".
"Shi ne ai abinda mu ke maganar don ai maganar aure ai dole a lallashi mace,,,, ban san ma mai maza suke nema ba 'yan iskan kaya" in ji Ainah tana tsaki.
"Nima dai abinda nake fad'i kenan, mai mace kamar Nadeefah me zai yi da wata macen ". Fad'in Najwah tana k'yacci.
"Had'ama fa" in ji Bahaja.
Ya Budu ta d'aura da " da kuma iskanci ba".
"Marasa godiyar Allah " fad'in Khaleesah matar Yaa Hafeez, maganar ne ya sa su dariya mai k'arfi suka ko dinga yi da k'yak'yatawa.
Ita dai idanu ta zuba musu ba tare da ta ce musu uffan ba, dukansu ne suka fita alwala suka bar ta da su Suleim sai lokacin ne Zulfaa da abin duniya ya isa ta dubeta tana cewa " Ni ban ma san ta ina zan fara ba, an bar Ni da jimamin rayuwa, jama'a me ya samu Yaa Islaam?".
"Ai yanzu ba ta wannan ake ba Babe, zancen kuma ɓata mata rai zai yi hak'uri kawai za mu bata".
"Haka ne, kiyi hak'uri dear in shaa Allah zai saka miki da mafificin alkhairi a tsakankanin zamanki da su gabad'aya".
"In shaa Allah ".
Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa " Ai na riga na yi hak'uri aure kuma ko mata d'ari ne yaje yayi ga hanya nan".
"Still dai ki yi hak'uri please" fad'in Suliem tana dafa kafad'arta, ok ta furta a hankali tana fita wurin alwala.
Ko da aka yi sallah aka dawo Lele ba ta yarda ta zauna ba, itama sahunsu Abba ta bi amma ita zuwa gidan Ummu ba tareda ta bi ta kan Sairah da ke hannun Ya Budu ba. Ba ma da mota ta fita ba drivern Ummu da ya kawo lunch shi ta bi zuwa gidan, tana shiga direct d'akinta ta wuce tayi kwanciyarta Allah da ikon shi sai bacci ya d'auketa ba ita ta iya tashi ba sai after 5 har lokacin babu kowa a gidan.
Alwala ta d'auro tayi sallah ta fita parlor abinci ta zubo ta zauna ci sai ta jiyo k'arar honk alamun sun dawo, ba ta ko motsa ba Ummu ta turo k'ofa tsayawa ta yi tana kallonta tana cewa " au ke nan kika gudo kenan?".
Hamma tayi tace " hayaniya ce ta min yawa na samu na zo na kwanta, ya akayi kuka dad'e yau?".
"Gidansu Ummanku muka je don sun d'au maganar auren nan da zafi kin san tafiya suka yi tun Azuhur".
Murmushi tayi kawai ba ta ce uffan ba, zama tayi gefenta ta dubeta a tsanake tace "na san da ciwo, musamman ke da ba auren soyayya kuka yi ba yanzu ne lokacin da kuka fara fahimtar juna sai ga lamarin nan kwatsam ya taso. Toh ban son ki sa damuwa ko d'aya a ranki da zai sa miki wata matsala ko ta d'agawa mijinki hankali support him and stay with him hakan shi ne zai sa ya samu natsuwa da kwanciyar hankali, kuma ban son ki zargi mijinki da tozarci ko kad'an auren nan wani dama ne da zaki gane matsayinki a wurinshi wanda na tabbatar ba a k'ask'antacciya zaki fito ba".
"Uhmm Ummu na ji kuma in shaa Allah ba zan d'aga masa hankali ba, amma Ummu Abulkhairi fa yana supporting ɗin shi........"
"My baby.....dole ne ta sa Abbunku goya masa baya ba komai ba, don a lokacin aurenku da shi yayi masa alk'awari a kan hakan..................
Labari ta fara bata daga kan lokacin da Burhaan ya kira Baba Prof. A kan maganar ya sa baki a fasa auren zuwa sanda Abbu ya ji har ya d'aura niyyar shige masa gaba a fasa auren sai kuma Abba ya kira ya tsawatar da hakan kawo zuwa sanda ta ba shi shawarar ya lallashi Burhaan sannan ya mishi alk'awarin idan ya samu wacce yake so zai tsaya masa har sai hakan ya tabbata but ba su tab'a tunanin zai iya bijiro da maganar auren ba.
Shiru Lelen tayi tana sauraran Ummun wato Burhaan ya jima yana tijarata a duniya, wato har a gaban iyayenta ya nuna mata bai son ta lallai ma. Ajiyar zuciya ta sauke cikeda son kawo k'arshen maganar ba wai don ta gama deciding abinda zata yi ba ta ce " ba komai Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi, wai ina Sairah ne?".
"Ameen ya rabbi, wani ya san inda kika baro ta ne? Ki ke tambayata".
"A hannunku mana na bar ta, in ko kun b'atar da ita sai ku fita nema".
"Mu fita neman wa ye? Wani ya sa ki bar ta".
"Hehehe Ummu biya ne ya kamaki don ki ji ".
Dariya Ummun ta yi itama ganin yadda Lelen ta saki jiki har da dariya tace " ashe za ki bushe kuwa".
"Wai Ummu ina kika ji Hausa har haka?".
"Tambayeni ko ki tambayi yarinyarki da ta b'ace".
"Ta na gidan Umma ai na sani".
"Ta na can kuwa yarinya sai iyayin tsiya wai ba za ta zo wurin kowa ba sai Safwaan Abbunku da Abba sun yi sun yi ta k'i".
"Lallai sai fa iyayi, ko aina ta san Safwaan da har zata k'i zuwa wurinku sai shi oho".
"Ke ko yana kama da Babanta".
"Eh lallai, shi ma Baban nata da wani lokaci k'yuiya ta ke masa in ba ta ga dama ba".
"Dama ai haka yara suke, ke ma haka kika dinga zab'en mutane time d'in muna Hungary".
Dariya tayi tana cewa " amma yanzu ai na daina".
"Gaskiya, wa ye zai ce Nadeefah zata saki jiki da mutane har da yin k'awa? Da na zaci irin masu tsoron mutanen nan za'a yi sai bayan kin girma na ganki kin zama opposite".
"Waiii, Allah ya taimake ni"
Dariya suka din ga yi ita da Ummun tana tuna musu yarintar Lelen tun daga kan abun dariya da na takaici, hakan ko ya d'auke mata hankali har ba ta san time ya tafi ba sai da aka kira Magrib.
Ta shiga sallah ne ta tarda misscallls birjik na Hajjah wanda tana da tabbacin maganar da zata mata bai fi akan zancen da aka gama ba which by Allah she's not ready for it. Ba ta bi ta kan shi ba sai kawai ta kira Ya Budu da ita ma tayi missing call d'in ta, tana shiga tace " da alamu kin manta zafin haihuwa yarinyar nan".
"Wane ni in manta da wannan azabar Ya Budu".
"Ga shi nan kin manta da shi tunda kin bar yarinya gidan Umma ko kin samu wasu ne".
"Ba wainda aka samu ni Nadeefah".
"Za ma kiyi bayani ne, kina ina ne haka?".
"Gidan Ummu yanzu take ban labarin wai ta musu k'yuiya".
"Ai ba su kad'ai ba har da mu ma, nace fuskar Burhaan ta gani a jikin Safwaan d'in ai yanzun nan ya dawo da ita da zai wuce masallaci wai in ya dawo zai kaita yawo".
"Dad'ina da Yaa Safwaan iyayi, wa ye zai kai yawon?".
"Kya tayani gani dai, amma tana da hak'uri tunda fa Umma ta had'a mata go grains ba ta yi kuka ba sai in ta ga gifcin Safwaan ".
"Ai ko a gida haka take yi, sai fa ta tashi daga barci ta sauka k'asa tayi ta wasa sai in ta gaji ne ta ga kuma ban tashi ba ne take dawowa gadon tana tashi na".
"Ai akwai wayo kam, bari in yi sallah dai in samu in shirya tafiya kafin ya zo mu tafi, Safwaan ya ce wai zai kawo miki ita".
Ok tace suka yi sallama.
Shi ko Burhaan tun da ya samu aka tabbatar masa da zaa je nemo masa auren Fareesah yake d'an jin wani iri shi dai ba zai ce be yi farinciki ba amma yana jin kamar bai kyauta ba, tare suka shiga masallaci da su Sadeeq da bai ko tanka masa ba sai da suna komawa ne Farhaan yace " amma wai kai Islaam me kake son yi wa aure ne?".
"Ka ji wani tambaya, toh ra'ayi da kuma raya soyayya Sadeeq ya ba shi amsa a d'an cunkushe, murmushi Islaam d'in yayi yana cewa " saboda musulunci ya ba ni dama".
"Ai cewa aka yi zaka iya adalci ko?".
"Ni ko san da haka and......"
"You are very sure ba zaka iya ba right? Toh ga ka ga hanya nan kaje kayi ta yi Allah ya ba saa".
Daga haka ya wuce har ran shi yana sababi,Sadeeq ne yace "ka fi kowa sanin darun Farhaan sai a hankali, so kar ka bari ya dameka Allah ya sanya alkhairi".
"Ameen" ya amsa yana gyad'a kai da mamakin dalilinsu na k'in mata biyu bayan ba haramci yake k'ok'arin aikatawa ba, haka suka koma wurin cin abincin inda daga nan yayi wa gidansu Fareesah tsinke don kai mata goron albishir tayi murna sosai amma ta kanne ba ta nuna ba sai murmushi kawai tayi daga k'arshe ya d'auketa zuwa Kilimanjaro don su yi celebrating in ji shi da fad'i.
Hajjah da ta gaji da kiran Lele ne ta sako mayafi bayan Magrib ta yo wa gidan Ummu tsinke don ta tabbatar da 'yar gidan ta ta tayi fushi ainun, da k'afa ta taka har ta k'arasa tana tafe tana lissafi. San da ta shiga gidan Ummu kad'ai ta iske a parlorn nan ta saki jera abincin da take yi tana wa Hajjahr barka da zuwa, da murmushi ta amsa tana duban parlorn tace " Lele ta wuce ne halan?".
"Aa tana ciki, kamar sallah take yi" ta furta tana ajiye mata ruwan da ta kawo mata.
"Masha Allah, ya gidan ya jama'a?".
"Alhamdulillah ya k'arfin jiki?".
Ruwan ta sha kana tace "Mun gode Allah Sameeha, tana wani d'akin ne?".
"Bari a kira miki ita Hajjah, na san ma bata ji shigowarki ba ne".
"Aa ba sai an kirata ba, ki rakani kawai inda take".
"Toh Hajjah" ta furta tana rik'e mata hannu, a hankali suke tafiya har suka hau stairs d'in a k'ofar d'akin Lelen na da suka tsaya knocking Ummu zata yi Hajjahr tace " bar shi kawai Sameeha Allah, bari in shiga wurin ta".
"Toh Hajjah a fito lafiya ".
"Ameen".
Zaune take a kan sofa tana danna wayarta, kayanta da tayi order take clearing don sun iso Lagos saura a yi waybill d'in su zuwa Kaduna. Ji tayi an turo k'ofar d'akin a tunaninta ko Ummu ne sai ba ta d'ago ba gudun kar a samu mishkila sai kuma ta jiyo k'amshin turaren Hajjah da ko a cikin mata duhu ta ji k'amshin ta san ita ce. Sai ga kammalalliyar muryarta ta yi sallama, da sauri ta d'ago tana kallonta ba ta iya amsa mata ba.
Murmushi tayi ya k'araso kan sofar da take zaune a kai ta zauna, d'ukar da idanunta tayi k'asa don ganin Hajjahr ya karya mata zuciya abinda kuma take ta gudu kenan shiyasa ta k'i amsa kiranta. Dafata tayi a hankali tace " Shalelena fushi kike da Hajjahr ta ki?''.
"Yaushe na isa in yi fushi da tauraruwar mata? A kan kuma wani dalili?".
"Shi ne ai na biyo sahu Habibtie".
"Hajjah da ba ki zo ba, kin san dole in name ki".
"Na sani, sai dai hankalina ne ya gaza kwanciya da halin da kike ciki".
" I'm okay Hajjah ".
"Ko d'aya Lele, ba kuma laifi ba ne ki gaya min duk abinda kike ji Habibtie in ma kuka ne kiyi kar ki hana kan ki hakan zai rage miki rad'ad'in dake zuciyarki".
Lumshe idanu tayi tana mai bawa hawayenta damar fitowa, don tun d'azu take dauresu kuma Allah ya taimaketa ba su zubon ba sai yanzu shi ma har da ganin Hajjahr ne ya sanya ta yi.
Rungumeta tayi a k'afad'arta tana mai tapping bayanta a hankali har ranta tana jin tausayin Lelen nata, yana d'aya daga cikin abinda take jiye mata tun farko wanda a ciki ma ko rabi ba a yi ba ko ma tace yanzu aka fara. Sai da tayi iya yinta kafin da kanta ta share hawayenta tana cewa " na kasa dannewa Hajjah, zuciyata tana ciwo".
"Kiyi ta istigfari Habibtie zaki samu sauk'in abinda kike ji ba dad'i ko d'aya amma yanzu ba lokacin yin sanya ko sarewa ba ne. Wannan d'aya ne daga cikin k'alubalen da nake jiye miki a muamularki da Burhaan ba kuma zan sare miki guiwa ko in razana ki ba ne amma tabbas sai kin zage dantse kin sake jajircewa".
"Hajjah anya zan iya?".
"Za ki iya Habibtie, ba wani abu ba ne mai wuya ba in zaki tuna na miki bushara da hakan so bai kamata wai yazo miki a bazata ba. Hakan kuma wani dama ne Allah ya kawo domin gane matsayinki a idanun Islaam".
"Hajjah wani matsayi ne bayan na k'iyayyar da yake min mara misali?".
"Ke a tunaninki Islaam ya tsane ki ne? In da bai sonki zai kusanceki ne har ku haihu tare ?".
"Hajjah kenan? A iya gani da hangena Ya Islaam bai tab'a so na ba sha'awata kawai yake yi".
"A tunaninki da shi kenan, amma a zahiri yana sonki amma ko shi bai san hakan ba bai kuma san hanyar da zai iya gaya miki ba".
"Hajjah kenan kina dai son saka ni in ji sauk'i ne because in dai har yana sona ba zai tab'a son b'acin raina ba balle har ya had'a ni da wata mace ba".
"Hmmmm Habibtie kenan, hala ba ki san maza ba ne? Namiji da kike gani yana k'ara aure ne ba wai don ya gaji da matar gidanshi ko bai sonta ba. Suna yi ne saboda ra'ayi da kuma k'asaita, ke ko sarauniya mutum yake aure sai ki ga ya sake aure saboda a jininsu son mace yake shi yasa ma bature kan ce ' man is polygamous in nature ' so k'arin aure ba wani abu ba ne a wurin su halitta ce ".
"Shi ne ku na ku mazajen ba su muku kishiya ba?".
"Ba su da ra'ayi ne Lele, amma in gaya miki babu sarauta da ta kai ta uwargida a tsakanin matan mijinta ko da sun kai d'ari ne amma fa sai in ta san kanta ta kuma iya sarautar gidanta. Ai kalmar uwar gida sarautar mata ba a banza take ba Habibtie''.
"Hmmm".
"Eh fa, don haka ki cire duk wasu tunani marasa kyau don ba abinda zasu yi sai d'amauta ki su saka ki layin neman magani da k'uruciyarki ki kashe kanki ki bar mijin da ita wacce ba ki son ba kuma yadda za ki iya tashi ki raka ni zan wuce".
Mik'ewa tayi ta gyara zaman hijabin da ta saka ta rik'e mata hannu suka fito waje still tana lallashinta a kan maganar, a parlor suka had'u da Ummu tana kallo. Mik'ewa tayi tana cewa " har kin sauko Hajjah?".
"Eh Sameeha na ji gidan tsit ina hajiyar b'anna?".
"Tana can gidan Ummansu".
"Kina son k'ure baiwar Allahr nan fa Nadeefah".
"Ai ba ta yi kuka ba ne ko, akwai kuma abincinta a can gidan ".
"A dai din ga kiyayewa Lele, Sameeha mu zamu tafi ".
''Hajjah tun yanzu? Ga shi nan za a kawo abinci".
"A bar abincin nan Sameeha, Lele na zo gani kuma na ganta yanzu zan koma kafin a kira ishai".
"Kaf d'in lallaima Hajjah saboda yaranki su ji suce ina sa ki wahala ko? Ai ko k'afaraki k'afar abincin nan Ummu yana ina?".
Dariya suka saka ita ko bata dubesu ba ta wuce kitchen basket ta d'auko ta fito, abincin Hajjahr da aka kammala a gefe ta jera a ciki sannan tace " mu je tohm in raka ki".
"Tunda ga saar ki ko?".
"Ni dai Hajjah please mu je mana ko sai an kira sallahr ne wai?".
"Ba a sani ba, Sameeha sannu da d'awainiya Allah ya muku albarka ya shirya zuria".
"Ameen ya rabb" ta amsa tana mik'ewa ita ma har k'ofa ta raka su kafin ta koma cikin gida, ita ko Lele rik'e hannun Hajjah da ke ta k'orafin wai ta maida ta tsohuwa tayi tana ba ta amsa da " dama wacece in ba tsohuwar ba". Suna tafe suna daru kamar yadda su ka saba har zuwa gidan Hajjah, da suka shiga ma wuri ta samu ta zauna a nan tayi ishai taci tuwo kafin ta baro gidan.
Tana shigowa gidan a haraba ta had'u da Safwaan yana shirin shiga motar shi, ganinta ya sa shi tsayawa yana cewa "gaskiya K'amshin Yerwa za mu yi fad'a da ke, haka ake yi sai ki bar yarinya tun safe saboda ba ki san zafinta ba".
"Ina zan sani tunda ban tab'a haihuwa ba" ta amsa har da murgud'a bakinta.
"Ehh lallai K'amshi kya min gori mana kin haihu ni ban haihu ba".
"Wannan kuma sharri kake shirin yi min ba komai ba".
"Hehehe ashe ma?! Sai yanzu kika dawo?".
"Éh, ai na kira Ya Budu take ce min ka fita da Sairah nace iyayi yayi maka yawa".
"Iyayi a ina fa? Wani ice cream date na fita da wata babe zan ma kawo miki ita ki ganta".
"Date d'in ne zaka fita da Sairah saboda kashewa kai kasuwa?".
"Kiran kasuwa dai".
"Kiran kasuwa aina? Ai sai ka sa gabanta ya fad'i ta yi tunanin ko ka saki matar ka ne".
"Hehehe, tayi tunani mana ba ruwanta ba ne? Besides ta ma san Sairah ai a wajena shiyasa ma na fita da ita".
"Ko ta san ta dai bai kamata ba, dates dai na masoya ne suyi enjoying moments d'insu su biyu ba katsalandan ba komai amma ka wani kinkimeta. Just imagine ita ce tazo da sisternta ya zaka ji?".
"Me zan ji kuwa zan hanata zumunci ne?".
"Ba wani zumunci Malam iyayi dai, kuma ba kyau".
"An ji d'in ina ruwanki?".
"Ohonma, yanzu ina nawa ice cream d'in".
"Mijinki ya sai miki ban siyo da ke ba".
"Ba zai siya ba d'in, kai zaka siya".
"Za ki shekara ashe baki sha ba".
"Auntyn ta ka? Don't forget nice fa uwargida".
"Mtswww, ji wani abu wai uwar gida ko ina kika nemo shi oho" ya furta da tsaki yana mai jin mugun haushi kamar zai kai duka.
''Kai kuma miye ya faru da masifa haka?".
"Allah ban san abun haushi ne K'amshi, shi wai Yaa Islaam ya rasa me zai yi duk duniya sai aure haba jamaa!".
Kallonshi tayi da kyau tace " ha a Malam in bai yi aure ba me zai yi".
"Hey, ke fa na lura ko a jikinki kamar ma murna kike yi ko, saboda baki son shi auren dole aka miki da shi ko?".
"Ji ka da wani magana dai".
"Me nace ni kam?".
"Toh me kake so in yi? ".
"Duka abinda mata suke yi in za a musu amarya mana".
"Hakan zai canja wani abu ne?".
"Definitely, wallahi wani irin haushin Ya Islaam nake ji akan maganar auren nan ta ya mutumin da Allah ya bawa ke zai yi tunanin miki kishiya?".
"Saboda ga hurul ein on a ban ƙasa ba?".
"Ni fa maganar gaskiya na ke yi, wallahi in da na isa a familyn nan yau Yaa Islaam bai isa ya auri wata 'yar iska ba".
Bud'e baki tayi da niyyar ba shi amsa aka saki honk a gate, dukan su kallon wurin gate suka yi aka bud'e. Cadillac d'in Islaam da suka fita da ita ne ta shigo cikin gidan kallo d'aya tayi wa motar ta maida kai ga Safwaan tana cewa " me zai sa ka hana shi bayan yana da halin yin auren".
"Mtswww, ba za ki gane ba ne".
Dariya ta sanya jin yanda ya ja tsaki, dai dai lokacin Islaam d'in na fitowa daga motarshi. Kallonta yayi ya ga ba ta dube shi ba sai dariyarta take yi da k'yak'yatawa. Safwaan ne ya kalleshi yana cewa " barka da dare Yaa".
"Uhmm" ya furta yana wucewa ciki, ran shi a b'ace cikeda takaicin ganinda yayi musu.
Safwaan ne yace " ga mijinki nan da alamu ya zo ne ku tafi, yarinyar ma kuka take yi".
"Shi ne baka gaya min ba?, oya good night ka gaida in-law" ta furta ba tareda ta jira ta cewarshi ba ta wuce ciki.
Burhaan ne zaune rungume da Sairah dake k'ananun kuka na gajiya yana rarrashinta, yana mai jin zafin kukan da take yi wanda yana shiga da shi ya fara cin karo. K'arin haushin kuma da Ummu take ce masa wai tana gidan Hajjah kuma wayarta tana d'aki ba ta tafi da shi ba bayan kuma ya ganta a waje, wato daga can ba ma ta shiga cikin gidan ba ta tsaya wurin Safwaan har tana washe masa baki kamar sakarya.
Mik'ewa yayi da niyyar fita da ita sai ga ta ta turo k'ofar da sallama, nan fa yarinyar ta k'ara sautin kukanta hakan ya sa ta shigowa da sauri tana amsar ta. Zama tayi a kujera ta fara k'okarin shayar da ita nan Ummu ta fara mata fad'a kan rashin sawa a kawota tun Magrib ta lura tana son k'ure hak'urin yarinyar. Ita dai hak'uri ta ba ta tana jijjiga yarinyar da ta lafe a jikinta tana sauke ajiyar zuciya, k'wafa yayi kawai yana daga zaunen bai tanka musu ba.
Sai da yarinyar ta k'oshi kafin ta zareta daga nonon tana cewa " Allah sarki Umma har da wanka aka saka ta yi".
"Toh waye zai ajiye yaro babu wanka tunda dai ita uwar ba ta damu da ita ba".
"Kayya Ummu, sanda fa na kira da magrib d'in cewa fa aka yi ta fita da Safwaan".
"Ba kuma zaki iya kiran Safwaan ɗin ba ko?".
"I'm sorry Ummu".
Kafin ta amsa Burhaan yayi tsulum ya mik'e yana cewa " Bari mu zo mu tafi Ummu".
Kallonshi tayi a kaikaice wato ita yake gayawa ta tashi su tafi, tab'e baki tayi ta tashi ta shiga ciki tana jiyo Ummu na amsa masa har da sai ya yi hak'uri. Ita dai kimtsawa tayi ta had'a kayansu ta fito daga d'akin. Ummun kad'ai ta tarar alamun ya fita waje, a hankali tace " Ummu za mu tafi".
"Nadeefah please kar ki bari shaid'an ya ziga ki kiyi punishing yarinyarki saboda babanta ya miki laifi".
"Ummu bana punishing kowa wallahi ban san an dawo da ita ba, amma tun asr take zuciyata kawai dai ban son in nuna musu rashin kawaicina ne".
"Da ko shi Burhaan d'in kin kira ya kawota or Safwaan".
"Zan gyara in shaa Allahu".
"Allah ya yarda sweetheart, ga shi nan Safwaan ya kawo miki ice cream a wancan ledar".
"Ayyah Yayana, na ko gode".
Ummun ce ta rakota har gaban motar ganin kaya yayi mata yawa ga Sairah ta k'i yarda ta sauka daga jikinta, yana ganin Ummun da kaya ya fito ya amsa shirya su ya yi a baya kafin ya koma ya kwanta. Sai da suka gama magana kafin ta bud'e motar ta shiga ciki, ja yayi cikin natsuwa yana sakewa Ummu sallama.
Tafiyar tasu irinta zuwa ne in da shi hankalinshi ya rabu gida uku ; murnar an yarda da batun Fareesah, na biyu kuma tausayin Lele da ya mamaye ran shi na uku kuma kishin ganin tana wa Safwaan dariya wanda shi rabon da tayi masa irinta ya manta. Don haka ya kud'iri niyyar a yau ba sai gobe ba zai kawo k'arshen hakan, shiyasa ma ya k'ara gudun motar zuwa gida.
Ko da suka isa da yayi parking Sairah kawai ya tayata d'auka zuwa cikin gidan ita kuma ta kwashe kayanta ta bishi a baya, ta k'ofarshi suka shiga direct d'akinta ta wuce don shi ma can ya nufa da ita. Kwantar mata da ita yayi ya juya bai tanka ba, kayan ta ajiye kafin ta nufi wurin closet d'in Yusairahn. Pjs ta ciro ta sanya mata tayi mata shirin bacci tsaf, kafin ta wuce toilet ruwa ta tara tayi wanka mai kyau ta fito.
Turus ta tsaya ganin Islaam a bakin gado yana danna waya, ganin bai kalleta ba sai ta d'an had'iye miyau gaban mirror ta tafi ta shirya cikin kayan bacci masu tsantsi kalar burnt orange. Tana taje kai ta ji hannunshi lumtsum cikin gashin, matsawa taso yi ya hanata damar hakan don d'agata yayi sama bai direta a koina ba sai kan gado. Bakinta ya fara laluba ta gumk'e shi sai kawai ya zarce da yin wasu abubuwan a jikinta, a da ta fara k'ok'arin kokawa da shi sai kuma zuciyarta ta haneta kawai ta sakin masa jiki ba tareda tayi hob'basan tallafawa k'ok'arin shi ba.
Still bai kula ba don yayi mugun missing d'in ta jikinshi sai rawa yake yi kamar wanda ya shekara bai yi ba, sosai ya bata wuya musamman da ya zama ba ta taya shi komai ba shi yayi kid'anshi ya kuma taka rawan shi har zuwa sanda ya samu natsuwar da yake muradi. Kamar kuma yadda ya saba bai saketa ba rungumeta yayi a jikinshi yana maida numfashi sai da suka natsa tukunna ya d'auketa suka tafi toilet wanka ya tayata suka yi ya d'aukota suka fito kan gado ya kwantar da ita ya maida ta jikinshi, haka da asuba ma bai k'yale ba sai da ya k'ara hakan ko ya sa shi makara sallahr asuba.
Ranar da yamma su Abba suka tafi neman auren Islaam gidan Alh. Musa mai katifa, wato mahaifin Fareesah wanda asalinshi bakano ne cikakke kasuwanci ne ya kawo shi cikin garin Kaduna a kasuwar bacci inda yake sana'ar siyarda katifa. Shago yake da shi madaidaici ba kuma wani kud'i yake da shi shahararre ba akwai dai rufin asiri yafi k'arfin duk wasu buƙatu na rayuwa.
Kasantuwar shi dattijo ya sanya ya karb'e su hannu bibbiyu, da shi da wani abokin shi a nan Unguwar tasu Alhaji Yunus. Bayan gabatar da kansu da abinda ya kawo su sai da gabanshi ya fad'i don ba wanda bai san su waye 'yan Yerwa ba, kama daga kan iko da kuma auren zumuncin da suke yi sai dai bai nuna ba. Sai murmushi da yayi yana cewa " masha Allah".
"Toh da fatan ba muyi latti ba, ma'ana wani bai riga mu ba" fad'in Abbu yana murmushi.
"Ko d'aya don a iya sanina Fareesah ba ta tsayawa da kowa, kuma Dr shi ne namijin farko da ya fara shigowa gida ya gabatar da kan shi a matsayin maneminta".
"Masha Allah, cikar tarbiyyar 'ya kenan" in ji Daddy shi ma yana murmushi.
"Tabbas, da fatan dai ya sanar muku yana da mata da 'ya d'aya". Baba Tijjani ya tambaya kai tsaye.
"Eh ya gaya mata ita ma ta shaida min".
"Toh haka yayi, yanzu mu da a zuwan nan da muka yi muna so ne a sa rana a yanka sadaki da sauran abubuwa mu bayar mu tafi".
"Eh ai hakan ya fi gwara a gama once and for all ba ai dinga je-ka-ka-dawo ba".
"Toh ku muke saurare".
"Ban son a bada duk wani abun al'ada, abinda addini ya yanke sadaki ne kawai kuma mun zartar da shi akan naira dubu d'ari biyu".
Baba Tijjani yace " hakan yayi kyau, amma kuma wani hanzari ba gudu ba. Ba wai mun raina da azancinka ba ba ne ko d'aya kawai dai muma muna da namu hangen ne, don mu nan da kake gani muna da al'adu sosai wanda musulunci bai hana ba. Tun da kowani mahaluki da al'ada yake ado bayan addini toh ba zamu tab'a hanawa ka yi listing na abinda yake a al'adarku in shaa Allah zamu kawo".
" hakane zamu yi list, amma matakin farko na auren bahaushe yana farawa ne da kud'in gaisuwa, kayan sa rana sai sadaki.........".
A take a wurin suka tsayar da kud'in gaisuwa da na gani ina so da sadaki, Abbu ya biya a aljihunshi kayan sa rana kuma sun ce zasu kawo sati mai zuwa sai dai kuma sun rok'i alfarmar bikin nan da wata hud'u don zai yi sabon ginin in da zai ajiye amaryar in da Alhaji Musan yace zai yi shawara da iyalinshi and he'll get back to them. A haka suka rabu cikin raha da mutunta juna, suka kama hanyar gida kowa yana yaba dattijantakar Baban yarinyar.
Da suka koma ne Baba Tijjani ya tara meeting da dare na isu-isu mazan, cikeda murna suka bada labarin abinda ya faru a gidan da suka je neman aure sai dai ba wanda ya nuna he's way excited da abinda aka gaya masa don gum suka yi. Abba ne ma yace " ya gaya muku inda zai ajiye yarinyar?".
"Filinshi zai gina ya sata ofcourse".
"Gida zai raba musu kenan?".
"Eh, amma ai a cikin layin ne".
"Ban amince ba na kuma yi magana da shi akan zai gina wa ita amaryar part d'in ta a nan cikin gidan shi so maganar raba gida bai taso ba".
"Wani had'a gida a na zaune lafiya".
"Ai gidan akwai filin da zai ishe shi ya ajiye mace, in kuma ba zai isa ba sai dai ya nemi filin da zai ishe su su biyu ya musu gini".
Baba ne ya so magana sai dai ganin yanda ya d'aure fuska ne ya sa kawai yayi shiru, tsare-tsare suka cigaba da sanarwa in da su saurara suka yi tunda dai ba wai da ruwan su ba ne a ciki.
Haka aka watse ba tareda sun saka baki ba, Abbu ne ya kira shi ya sanar masa da yanda aka yi. Ya kuma kira Lele yayi mata nasiha sosai akan maganar auren, tayi kuka sosai da maganar yayinda damuwarta ta dawo sabuwa fil a zuciya.
Dad'in damuwarta kuwa sai ga Burhaan ya fito daga d'akinshi ya d'agata cak akan wai an ba shi Fareesah, tsayawa tayi cak kamar ruwa ya cinyeta don ita a yanzu lamarin Burhaan tsoro yake bata saboda k'iri-k'iri yake nuna mata ba ta da daraja a idanunshi. In ba haka ba yaushe mijin macen da zai k'ara aure zai dinga murna an ba shi mata, shin da gangan yake yi ko dai bai ma san yana yi ba?................
Deejasmah ✍🏼