Free chapter · Read without an account

Chapter 1

by Hauwau Umar · MATAR ARO..






🌺MATAR ARO..🌺🥀


      BY


HAUWA'U OMAR 

  (Cutiemeerat)




Page one…1



      بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ.             









Ba abin da kake ji sai kukan tsuntsayen dare da busar iskar dake karkarwa. A tsakiyar wannan dokar dajin, inda ko kura ba za ta sha'awar yawo ba, wata yarinya ce take takawa cikin sanɗa. Kanta ɗauke da wani katon tulu wanda ya riga ya addabi wuyanta, nauyinsa yana neman murkushe kasusuwan bayanta.


Kowane taku daya da take yi, hawaye masu dumi suna rige-rige a kan fuskarta, suna ɗiga a kan kirajinta dake bugawa da sauri saboda tsoro. Ba takalmi a kafarta, haka take takawa a kan busassun ganye da ɓoyayyun kayoyi.


Kwas!


Ta taka wani busasshen icce, wanda ya soke karkashin kafarta har cikin jijiya. Yarinyar ta gimtse baki, idanuwanta suka firfito waje saboda azaba, amma ba ta da ikon sakin kukan da yake cin makogwaronta. Ta san idan ta tsaya, duhun dajin zai haɗiye ta, idan kuma ta koma gida ba ta cika tulun nan ba, abin da yake jiran ta ya fi duhun dajin nan ban tsoro.


Ta saki wani nishi mai nauyi, tana jin dumin jinin dake fita daga kafarta yana gauraya da kura. Ta kalli sararin samaniya wanda hadari ya lullube, muryarta a rafe ta ce, "Ya Ubangiji, shin ni kadai ce ba ni da gurin fakewa a duniyar nan?


Iskar dajin ta kara karfi, tana tura ta baya, yayin da take ci gaba da jan kafarta mai jini, tana fatan hantsi ya yi mata a cikin wannan dajin koda za ta ga hasken rayuwa...





"Wai ashe kin dawo?" Muryar Maman-Yara ta fito, ba tare da ko digon tausayi ba. Ta fito tana gyara ɗaurin zanenta, idanunta suka sauka akan tulun ruwan. "Daga zuwa diban ruwa sai kace wacce aka kora yaƙi? Maza wuce ki hura wuta, ki ɗora ruwan zafi na wanka, sannan ki tabbatar kin share dukkan gidan nan kafin kowa ya farka."


Yarinyar ta buɗe baki za ta yi magana, muryarta ta dashe. "Hajja... ƙafata..."


"Dalla rufewa mutane baki!" Hajja ta katse ta da wani hargitsi  mai cike da tsana. "Koda ƙafa ɗaya kike da ita, yau sai kin yi aikin gidan nan. Idan kuma kika kuskura kika zauna, to wallahi ba ke ba abinci har sai randa kika ga dama."


Yarinyar ta runtse idanunta, ta juya tana dingishi ta nufi wurin icce. Tana ji a ranta cewa wannan rayuwar ta yi mata nauyi. Ta ji kamar ita ɗin wani tsumma ne da aka ara, wanda mai shi bai damu da ya yage ko ya ɓaci ba.



 "Ya Allah, idan har a gidanmu ni din 'Matar Aro' ce wadda ba ta da daraja, to a ina zan sami tawa madafar? Shin mutuwa ce kawai mafitata?"


Ba ta gama wannan tunanin ba, Hajja ta fito da wani lallausan zanen gado (bedsheet) ta wurga  mata a kai. "Maza wanke wannan yanzu, kuma ki shanya shi ya bushe kafin azahar. Idan na dawo ban ga ya bushe ba, yau a waje zaki kwana wallhi shegiya dangin mayu!".....





Cikin wani hamshakin ɗaki da yake ɗauke da sanyiv(AC) wanda yake ratsa kowane lungu, wani matashi ne yake tsaye a gaban katon madubin dakinsa.


Aryan.


Sunan da kowa yake kira da tsoro ko girmamawa. Sanye yake da wata farar riga ta kamfanin Gucci, wadda ta nuna faffadan kirajinsa da cikakkiyar surarsa ta namiji. Fuskarsa a murtuke take, babu alamun murmushi, idanuwansa masu kaifi tamkar na shaho suna kallon agogon dake tsintsiyar hannunsa.


Aryan ba mutum ne mai yawan magana ba; a wurinsa, magana daya ta isa, kuma idan ya murtuke fuska, ko mahaifinsa, Alhaji Yusif Mai Dala, yakan san cewa ran zaki ya baci.


A bangaren mahaifiyarsa, Hajiya Safiya (Amaryar gidan), yanayin ba ba daɗi. Duk da ita ce tauraruwar gidan, tana fama da wata irin rashin lafiya ta paralysis (shanyewar jikin bangare daya) wanda ya sanya take rayuwa a kan keken guragu. Wannan shi ne babban ciwon da Aryan yake ji a ransa, wanda ya kara sanya masa miskilanci da kyamar mutane.


Kofar dakin aka turo a hankali, Nusaiba, kanwarsa tilo kuma guda daya da yake raga wa a gidan, ta leko da tsoro.


"Yaya Aryan... Dad yana kira a falon kasa. Yana magana ne akan canjin masu kula da Mommy."


Aryan bai juyo ba, sai dai kawai ya gyara agogonsa. Muryarsa ta fita a dake, mai sanyi amma cike da izala. "Ina zuwa."


Kalmomi biyu kacal, amma Nusaiba ta san tana bukatar janyewa kafin numfashinsa ya takura mata.


A gidan Alhaji Yusif, mata uku ne. Matan farko guda biyu suna ganin cewa Aryan da mahaifiyarsa ne suka mamaye dukiyar gidan, don haka kishi da ƙiyayya suke yawo a kowane lungu na falon. Amma babu wacce ta isa ta daga murya a gaban Aryan.





Aryan ya fara takawa a kan lallausan kafet din da aka shinfida tun daga saman bene har zuwa babban falon gidan. Kowane takunsa yana bada sauti mai nuna iko, yayin da ƙanshin turarensa na Oud mai tsada yake bazuwa a cikin iskar sanyin AC dake ratsa ko'ina.


Falon gidan Alhaji Yusif Mai Dala ya kasance tamkar gidan sarauta na kasar Ingila. Kayan daki (furniture) ne na alfarma wadanda aka shigo da su musamman daga kasar Italiya, komai na falon a tsare yake 


A can karshen falon, Alhaji Yusif yana zaune a kan wata kujera mai fadi, sanye da riga ta gaske ta mulki. Matansa biyu na farko, Hajiya Babba da Hajiya Ta-tsakiya, suna zaune kowacce a gefe, fuskokinsu cike da kissa da son jin me za a tattauna.


Aryan ya karaso, fuskarsa kamar ba ta taba sanin dariya ba. Bai kalli kowa ba, bai kuma ce komai ba, sai kawai ya samu wuri ya zauna, ya dora kafa daya kan daya. Wannan miskilancin nasa shi ne yake kara tsorata mutanen gidan.


"Aryan," Mahaifinsa ya kira sunansa cikin murya mai nauyi.


Aryan ya dan daga kai kadan, amma idanuwansa suna kan wayarsa ta iPhone ta karshen yayi. "Dad, ina jinka."


"Maganar mahaifiyarka ce. Ka sani sarai cewa ita ce farin cikinmu, kuma rashin lafiyarta yana damuna. Wadannan masu aikin da muke kawowa daga kamfani duk sun gaza gamsar da ni. Ina son mace ta musamman, wadda za ta zauna da ita dare da rana, wadda za ta zama tamkar inuwarta."


Aryan ya ajiye wayar, idanuwansa suka yi sanyi lokacin da aka ambaci mahaifiyarsa, amma har yanzu fuskarsa a murtuke take. "Na riga na ce maka Dad, zan iya biyan kowane irin kudi a nemo kwararru daga waje."


Hajiya Babba ta yi gyaran murya, tana gyara zamanta cikin kissa. "Ai Aryan, ba kudi ne matsalar ba. Kulawa ce ta zuciya ake bukata. Yarinyar da za ta zauna da Hajiya Safiya dole ta kasance mara gata, wadda za ta san darajar kudin da ake ba ta, kuma ba za ta rika mana girman kai ba."


Aryan ya kalli Hajiya Babba da wani irin kallo mai sanyi wanda ya sanya ta haɗiye sauran maganar. Shi ya tsani yawan magana, kuma ya tsani shishshigin kishiyoyin mahaifiyarsa a cikin lamarinsa.


"Dad," Aryan ya kira mahaifinsa, "Muddin wannan matar da za a kawo za ta mayar wa Mommy farin cikinta, to babu damuwa. Amma ka sani, ba na son ganin wata mace tana yawo a cikin idanuna idan ba aikinta take yi ba. Ba na son surutu, kuma ba na son takura."


Ya mike tsaye, tsayinsa da kwarjininsa suka cika falon. Bai jira amsar kowa ba, ya nufi sashen mahaifiyarsa. A can, ya tarar da Hajiya Safiya a kan keken guragu, tana kallon window. Duk da shanyewar jikin da take fama da shi, kyawunta na asali yana nan, sai dai idanuwanta sun nuna tsananin gajiya da kaɗaici.


Aryan ya tsuguna a gabanta, ya kama hannunta mai sanyi, ya ɗora a kuncinsa. A nan ne kawai kwarjinin fuskarsa yake raguwa, ya zama kamar wani karamin yaro. "Mommy, zan samo miki farin cikinki. Ko da hakan yana nufin zan nemo mace ce in aro rayuwarta in mallaka miki."


Cutiemeerat..✍️***


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol