Free chapter · Read without an account

Chapter 1

by Umaimah Ado Gaya · SARƘAƘIYA


SARƘAƘIYAH

Mallakar

Umaimah Ado Gaya (Ummu Ahmad)

Sadaukarwa
Ga
Auntyna mai daraja
Amina Haruna Hassan
New Edition 2026

***

Tsokaci
    Wannan shi ne littafina na farko da na fara fitarwa. Saboda haka ina roƙon masu karatu da su yi haƙuri da duk wani kuskure da za su iya gani a cikinsa.
   Bayan kun kammala karantawa, ku bar tsokacinku, ku yi like da share domin ƙarfafa mana gwiwa.
   Haka kuma ina roƙonku da ku sanya Auntyna Amina Haruna Hassan cikin addu'o'inku. Allah Ya ba ta zuri'a ta gari mai albarka.
Chapter 1 Page 1
Gabatarwa

    Fujeerat Muhammad Isma'il kyakkyawar yarinya ce mai kamala da nutsuwa. Allah Ya hore mata kyau gwargwadon iko. Sunanta na asali Hafsat, sai dai iyayenta da na kusa da ita suna kiranta da Fujeerat.
   Tana da fata mai launin chocolate, doguwa ce amma ba sosai ba, sannan tana da cikakkiyar sura irin ta "number 8". Allah Ya azurta ta da yalwar gashi, na kai da na gira, tare da dogayen gashin ido masu ƙara mata kwarjini.        
   Idanuwanta  farare ne masu sheƙi, yayin da ƙwayar idanunta ke da launin ruwan maroon mai haske.

    Mahaifinta, Malam Muhammad haifaffen Jihar Adamawa ne, yayin da mahaifiyarta 'yar asalin Kano ce. Sana'ar mahaifinta ta sayar da kayan miya ce, kuma Allah Ya hore masa ɗan abin hannu da yake ba shi damar kula da iyalinsa cikin rufin asiri.
   Fujeerat ita ce kaɗai ƴarsu, don haka tana samun kulawa da ƙauna ta musamman daga iyayenta. Suna rayuwa ne a cikin birnin Kano cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna.

******
    Wata rana bayan an tashi daga makarantar Islamiyya, Fujeerat da ƙawayenta suka kama hanyar gida cikin nutsuwa. Kowacce daga cikinsu tana tafiya cikin kamala da nutsuwa, suna ɗan tattaunawa cikin raha da annashuwa.
  Da suka isa layinsu, kowacce ta kama hanyar gidansu. Fujeerat kuwa kai tsaye ta shiga gidan da suke haya mai ɗauke da ɗakuna biyar da bayi guda biyu.
Lokacin sallar Magariba ne, don haka tsakar gidan babu kowa. Ta wuce ɗakinsu ta tarar da Umminta tana sallah. Cikin sauri ta cire kayan makaranta, ta sauya zuwa kayan gida sannan ta yi alwala ta shiga don yin sallah.Bayan ta idar, ta gaida Ummin cikin ladabi.
"Fujeerat, yau kuma ina kuka tsaya har aka kira sallah ba ku dawo ba?" Ummi ta tambaya.
Cikin girmamawa Fujeerat ta amsa, "Wallahi Ummi, mun je gaisuwa ne. Mahaifiyar wata ƴar ajinmu ce ta rasu."
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allah Ya jiƙanta da rahama," cewar Ummi.
"Amin Ummi," ta amsa cikin tausayi.
Ummi ta miƙe tana naɗe sallayarta.
"Ga abincinki can, ki ci kafin ya huce."
Ta nuna mata inda aka ajiye abincin, yayin da Fujeerat ta miƙe domin cin abincin cikin biyayya.

   Fujeerat ta miƙe ta nufi inda Ummi ta nuna mata. Ta buɗe kwanon abincin, shinkafa ce da miya, wadda ƙamshinta ya cika ɗakin a lokacin da ta buɗe kwanon,dominUmmi gwana ce gurin girki.

Murmushi ta yi tana cewa,"Allah ya saka da alkhairi Ummi."
Ummi ta amsa da,"Amin, ɗiyata. Ki ci sosai,ba na son ki na wasa da abinci."

   Ta zauna tana cin abincin cikin natsuwa yayin da Ummi ke gyara wasu kayan a gefe. Lokaci-lokaci suna musayar hira mai cike da ƙauna da raha.

   Bayan ta gama cin abincin, ta ɗauki kwanukan da suka ɓaci ta wanke sannan ta dawo ta zauna kusa da mahaifiyarta.

  Sai da suka ɗan yi hira kafin aka kira sallar Isha'i.Bayan sun idar da sallah ne Malam Muhammad ya dawo gida.

Tun daga ƙofar gida ya yi sallama cikin ƙaƙƙarfan muryarsa.

"Assalamu alaikum."

"Wa alaikumus salam."

Muryoyin matarsa da Fujeerat suka amsa a tare.

Fujeerat ta yi saurin miƙewa ta karɓi ledar hannunsa kamar yadda ta saba.

"Sannu da dawowa Abba."

"Yauwa ƴar Albarka. Ya makaranta?"

"Lafiya ƙalau Abba."

Ya shafa kanta cikin kulawa sannan ya wuce ya zauna.

   Bayan ya watsa ruwa ya ci abinci, suka haɗu a falo kamar yadda suka saba kowace rana.

Fujeerat tana matuƙar son waɗannan lokutan. Domin su ne lokutan da take samun damar zama kusa da iyayenta cikin annashuwa da kwanciyar hankali.

   Malam Muhammad kan tambaye ta yadda karatunta ke tafiya, sannan ya ɗan koya mata wasu darussa kafin ya saurari abin da ta haddace daga Alƙur'ani.

A daren ma haka suka yi.

Cikin farin ciki ta karanto abin da ta haddace, yayin da mahaifinta ke gyara mata inda ta yi kuskure.

Lokacin da agogo ya nuna ƙarfe goma na dare ne suka tashi domin kwanciya.

Malam Muhammad da matarsa suka shige ɗakinsu, yayin da Fujeerat ta shimfiɗa bargonta a falo kamar yadda ta saba.

Kafin ta rufe idanunta domin barci, sai da ta yi addu'ar Allah Ya tsare mata iyayenta.Domin a gare ta, babu wata ni'ima da ta kai kasancewar su a rayuwarta.Sannan tayi addu'ar kwanciya bacci.

***ABUJA***

    "Yaya, barka da hutawa."
Muryar wata matashiya kyakkyawa ta katse shirun da ya mamaye falon.
Ta yi kwalliya mai ɗaukar hankali cikin wata tsadaddiyar riga da wando. Gashin kanta kuwa ya sha gyara da ƙarin gashi, yayin da idanuwanta suka yi nauyi da kayan kwalliya.
Mutumin da take kira da Yaya ya ɗago ya kalleta.
"Yauwa, sannunki," ya amsa cikin taƙaitacciyar murya.
Ta yi murmushi tana matsowa kusa da shi.
"Yaya, don Allah ina son zuwa gidan Mummy. Kalifa ya kira ni yanzu ya ce ta dawo daga Dubai."
Ya sake dubanta daga sama har ƙasa, sannan ya ce,
"To, jeki ki shirya."
Nan take ta turo baki.
"Wani shiri kuma bayan wanda na yi?"
Ya ɗaga gira yana kallonta.
"Au haba?"
Sai ta dubi jikinta.
"Yaya, me ya samu shigar tawa?"
Ya girgiza kai da murmushi.
"Ba komai. Allah Ya kiyaye hanya."
Nan take farin ciki ya bayyana a fuskarta.
"Thanks, Yaya. I love you."
Ta juya cikin murna ta fice.
Muhammad ya bi bayanta da kallo kafin ya saki tsaki.
"Subhanallah! Wai wannan ce matar aure? Allah Ka shirye ta."
Ya girgiza kai sannan ya koma kan aikin da yake yi.
Ita kuwa Fukaihat, maimakon ta nufi gidan mahaifiyarta kamar yadda ta faɗa, kai tsaye ta shiga motarta ta ɗauki hanya.
Bayan mintuna kaɗan ta isa wani katafaren otal da ake gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar ƙawarta Kulsum.
Tun daga ƙofar shiga aka fara kaɗa mata ihu.
"Kalli wace ta zo!"
Kulsum ta taho a guje ta rungume ta.
"Babe! Wallahi har na cire rai za ki zo. Da na ga Mr. Muhammad yana gida sai na ce yau kam ba za ki samu damar fitowa ba."
Fukaihat ta ja tsaki.
"An gaya miki sakara ce ni? Da har irin wannan partyn ya wuce ni?"
Duk suka yi dariya.
"Ina kayan aikin?" ta tambaya tana murza hannuwanta.
Kulsum ta nuna wani teburi a gefe.
"Suna can."
Ba tare da ɓata lokaci ba Fukaihat ta ƙarasa wurin. Ta ɗauki wani babban kofi da aka cika da abin sha mai sa maye ta ɗaga kai tsaye ta fara sha.
Ta sha sosai kafin ta ajiye kofin.
Daga nan kuma ta fara ɗibar abubuwan da ke kan teburi tana ci ba tare da wata damuwa ba.
Da ta ƙoshi ta nemi wani kujerar alfarma ta zauna tana fesar da numfashi cikin gamsuwa.

***KANO***
Yau Lahadi,Kuma yau ne ranar da Fujeerat za ta koma makaranta.
Tun jiya ita da Ummi suka gama shirya komai da take buƙata domin komawarta makarantar kwana ta First Lady Secondary School da ke Mariri.
Daren jiya kusan ba su yi barci sosai ba. Hira suka yi tare da nasihohi masu ratsa zuciya daga iyayenta, musamman daga Abbanta.
Tun da  safiyar yau ta waye, zuciyar Fujeerat ke cike da wani irin yanayi da  ta kasa iya fassara wa.
Tana son komawa makaranta.Amma kuma tana jin wata irin kewar gida da ba ta taɓa jin makamancinta ba.
Sai take jin kamar wannan tafiyar tata za ta raba ta da wani abu mai muhimmanci a rayuwarta.
Da yamma Abba ya shirya domin raka ta.Fujeerat ta fito da kayanta yayin da Ummi ke share hawaye.
Ita ma hawayen suka cika mata ido.
A Kullum idan za ta koma makaranta haka suke yi ita da Ummi amma na yau ya banbanta da saura.
  
   Da suka isa makarantar sai kuma zuciyarta ta karye ta rungume Abba tana jin Kamar ta bi shi su koma gida.
   Abba ya yi murmushi tare da shafa bayanta.
"Ki yi haƙuri, Yar Albarka. Ki dage da karatu kin ji?"
Ta gyaɗa kai tana share hawaye.
"In sha Allah, Abba."
Ya ci gaba da cewa,
"Ai daga wannan ajin da kike yi idan kin gama, ba za ki sake nisa da mu ba."
Fujeerat ta yi murmushi duk da hawayen da ke sauko mata.
"To Abba. Ka gaida mini Ummina. Ina sonku sosai."
"Muma muna sonki, Ƴar Albarka."
Ya shafa kanta cikin ƙauna.
"Allah Ya tsare ki."Ya sake faɗa cikin murya mai sanyi.
"Amin." Itama ta amsa masa da muryar kuka.
Sai da ta tsaya tana kallon motar da suka zo a ciki har ta ɓace daga ganinta.
Daga nan ne ta juya a hankali ta nufi cikin hostel.
Sai dai da duk takun da take yi, zuciyarta na cigaba da raya mata cewa akwai wani abu da ke tafe...
Wani abu da zai sauya rayuwarta gaba ɗaya.

Chapter 1 Page 2
***ABUJA***

   Fukaihat ba ta dawo hayyacinta ba sai wajen ƙarfe goma na safe.

  Da sauri ta lalubi wayarta,Hankalinta ya tashi matuƙa da ta ga missed calls masu yawa daga mahaifiyarta.

A tunaninta, ko Muhammad ne ya kira ya yi mata sannu da zuwa, sannan ya gano ba ta dawo ba.

Ba tare da ta tsaya yin wanka ko gyara kanta ba, ta fito daga ɗakin otal ɗin da ko yadda ta kai kanta wurin ba ta tuna ba.Har ta bar harabar otal ɗin ba ta kula da ƙawayenta da ke ƙoƙarin yi mata magana ba.

  Kai tsaye ta shige motarta ta nufi gidan iyayenta.Da ta isa gidan, ta tarar da mahaifinta da mahaifiyarta zaune a falo suna hira cikin walwala.

Ko da suka ga yadda ta shigo cikin firgici, gaba ɗayansu suka miƙe a tare.

"Fukaihat, lafiya kuwa?" mahaifiyarta ta tambaya cikin tashin hankali.

"Lafiya lau, Mum. Na ga missed calls ɗinki ne da yawa, shi ya sa na yi tunanin ko wani abu ne ya faru."

Nan take suka sauke numfashi.

Mahaifiyarta ta ce,

"A'a, damuwata kawai ita ce ban ji daga gare ki ba. Kin ce za ki zo, sai kuma shiru."

Fukaihat ta gyara zamanta.

"Wallahi Mum, birthday party ɗin Kulsum na je. Daga baya dare ya yi sosai, shi ya sa na kwana a can."

"Halan a otal kika kwana?" Mahaifinta ya tambaya.

"Eh Dad."

"To ai babu laifi. Muddin kina lafiya."

Nan take Hajiya ta kalli mijinta da mamaki.

"Haba Alhaji! Maimakon ka tsawatar mata, sai ka ce babu laifi?"

Ta juya ta kalli Fukaihat.

"Kin san ke matar aure ce. Bai kamata ace kina kwana a waje ba, balle kuma a otal saboda wani party."

Alhaji ya katse ta.

"Ki ƙyale yarinyar nan mana, Hajiya. Ka da ki matsa mata da yawa."

Hajiya ta girgiza kai kawai.

"Allah Ya shirya."

Ta miƙe ta bar falon.

Fukaihat ta bi bayanta da harara kafin ta kalli mahaifinta.

"Wallahi Dad, da ace ba ta sona da tuni ta bar gidan nan ta fiye takura ni,komai na yi ni ban iya ba."

Alhaji ya janyo ta jikinsa cikin lallashi.
"Ki kyale ta. Kinsan yadda iyaye mata suke."

Fukaihat ta yi murmushi tana kwantar da kanta a kafaɗarsa.

Sai dai ko kaɗan ba ta fahimci cewa irin wannan sakaci da rayuwar da take yi ne zai iya jefa ta cikin matsalar da ba ta taɓa zato ba.

***KANO***

Ummi na zaune a tsakiyar ɗakinta ta zabga tagumi.

Tun da safe zuciyarta ke cike da wani irin yanayi da ba ta taɓa jin irinsa ba.

Da farko ta yi zaton kewar Fujeerat ce saboda komawarta makaranta, amma yanzu ta tabbatar ba haka ba ne.Wani abu ne daban.Wani abu mai nauyi da zuciyarta ta kasa fassara shi.

  A hankali ta fara jin hayaniya daga tsakar gida.Hayaniyar da ba ta yi kama da ta kowace rana ba.Yayin da hayaniyar ke ƙara kusantowa ɗakinta, bugun zuciyarta ya fara ƙaruwa.Hannayenta suka fara rawa.Jikinta kuma ya yi wani irin sanyi.Sai ta ji kamar ana cire mata wani muhimmin sashe na rayuwarta.

Cikin rawar murya ta furta:"Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla, wa anta taj'alul hazna iza shi'ta sahla."

Da ƙyar ta kammala addu'ar.

Kafin ta sauke numfashi, aka yi sallama tare da buɗe labulen ɗakin.

Mutane ne suka fara shiga ɗaya bayan ɗaya.Wasu na kuka.Wasu na share hawaye.Wasu kuma fuskokinsu cike suke da firgici.

A tsakiyarsu kuwa akwai wasu maza guda huɗu da ke ɗauke da wani mutum.Ummi ta zuba musu ido.

Da farko ba ta gane ko wa ba.Sai da suka ƙaraso cikin ɗakin.

A lokacin ne idanunta suka sauka kan Abban Nafisa maƙofcinsu.Fuskarsa ta kumbura saboda kuka.Idanuwansa kuwa sun yi jawur tamkar garwashin wuta.

Da suka haɗa ido da Ummi, sai ya durƙushe ƙasa yana wani irin kuka mai karya zuciya.

Cikin ruɗani Ummi ta ce,"Lafiya? Me ya faru? Ko Umman Nafisa ce ba ta da lafiya?"

Ya girgiza kai.Kuka kawai yake yi.Daga bisani cikin wahala ya furta:"Abban Fujeerat ne..."

Gabanta ya faɗi.Da sauri ta miƙe tsaye.
"Me ya same shi?"Abban Nafisa ya kasa magana.

Sai nuni kawai da yayi mata da Abban Fujeerat da aka kwantar.Da sauri ta matsa kusa da shi.A kallon farko da ta yi masa jikinta ya ɗauki rawa.
Malam Muhammad ne.Kayan jikinsa gaba ɗaya sun jiƙe da jini.Jini ya mamaye rigarsa, ya kuma bushe a wasu sassa na jikinsa.

Idanunsa a rufe.

Fuskarsa babu walwala kuma tayi fayau.Tamkar mai barci...

Sai dai shi ba barcin da za a farka daga gare shi yake yi ba.

Ummi ta zaro ido cikin firgici.Ta durƙusa a gefensa.Cikin wata irin murya mai cike da azaba ta kira sunansa."Malaaaam!"

Muryarta ta karade ɗakin.Sai kuma komai ya ɗauke mata.Idanunta suka birkice.Jikinta ya yi laushi.Ta faɗi ƙasa sumammiya.

Nan take aka ruɗe.

Abban Nafisa ya yi kanta yana kiran sunanta.

Amma shiru.Ko motsi ba ta yi ba.

Ɗaya daga cikin mutanen da suka kawo Malam Muhammad ya fita da gudu ya kira matan maƙwabta.

Cikin ƙanƙanin lokaci ɗakin ya cika da jama'a.

An zuba mata ruwa,an yi addu'o'i,an girgiza ta,an kira sunanta sau babu adadi,Amma ta ƙi dawowa hayyacinta.

Daga ƙarshe Abban Nafisa ya ce:"A'a, ba za mu ci gaba da zama haka ba. Ku ɗauke ta mu tafi da ita asibiti."

Da sauri aka ɗauke ta.A ranar gidan ya shiga cikin wani irin yanayi na baƙin ciki.Yanayin da babu wanda ya taɓa tunanin zai zo musu da wuri haka.

***FIRST LADY SECONDARY SCHOOL**

  Fujeerat da ƙawarta Nadeeya suna zaune a ɗakin kwanan su suna gyara kayayyaki.

Tun farkon dawowarsu makaranta, Nadeeya ta lura cewa Fujeerat ba ta cikin walwala kamar yadda suka saba.

  Ko da suna hira, tunaninta yana wani wuri daban.Ko a lokacin karatu,ta lura ba ta cika mayar da hankali ba.Sai dai duk lokacin da ta tambaye ta, sai ta ce babu komai.

   A ranar ma suna zaune ne cikin nutsuwa.Babu wanda yake magana.
Can sai Fujeerat ta ja wata doguwar ajiyar zuciya.Nadeeya ta ɗago da sauri.

Ta lura idanun ƙawarta sun cika da hawaye."Subhanallah! Fujee, me ke damunki ne?"

Kafin ta ƙarasa maganar, Fujeerat ta fashe da kuka.Nadeeya ta matsa kusa da ita.Ta rungume ta tana lallashinta.Sai dai duk ƙoƙarin da take yi, Fujeerat ta kasa yin shiru.

Bayan wani lokaci ne kukan ya lafa.Ta ɗora kanta a kafaɗar Nadeeya.Cikin murya mai cike da damuwa ta ce:
"Nadeeya, ki yi min addu'a."Nadeeya ta shafa bayanta."Me ya faru?"Fujeerat ta girgiza kai."Ban sani ba. Amma zuciyata ba ta min daɗi. Ji nake kamar wani abu mai muhimmanci yana ƙoƙarin rabuwa da ni."

Nadeeya ta yi shiru na ɗan lokaci.Sai kuma ta ce:

"Ki yawaita karanta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. In sha Allah za ki samu sauƙi."

Nan take Fujeerat ta fara maimaita kalmar.A hankali zuciyarta ta fara samun nutsuwa.

Daga bisani ta ɗago ta kalli ƙawarta.
"Nagode, Nadeeya."Nadeeya ta yi murmushi."Abokai ai saboda irin waɗannan lokutan ake buƙatarsu."

Fujeerat ta yi murmushi karo na farko cikin ranar,haƙiƙa, samun aboki na gari wata ni'ima ce da ba kowa ke dacewa da ita ba.
****
  A hankali rayuwa ta fara komawa yadda ta saba ga Fujeerat.Duk da cewa har yanzu tana fama da faɗuwar gaba da mafarkai masu tayar mata da hankali, addu'o'in da take yi da kuma ƙoƙarin da Nadeeya ke yi wajen kwantar mata da hankali sun taimaka matuƙa.

  Da shigewar kwanaki kaɗan, ta mayar da hankalinta kan karatu.

Musamman da yake wannan ita ce shekararsu ta ƙarshe a makaranta.Jarabawar WAEC ta rage saura kwanaki kaɗan.Saboda haka babu lokacin wasa.

   Wata rana suna zaune a wani kusurwar ɗakinsu suna karatun jarabawa.Nadeeya ta rufe littafinta tana kallon Fujeerat."Fujee." "Uhmm?" Fujeerat ta amsa ba tare da ta ɗago kai daga littafinta ba."Na tambaye ki wani abu?"

Fujeerat ta yi murmushi."Allah Ya sa na sani."Nadeeya ta ɗan yi shiru kafin ta ce,

"Idan kika yi nasara a WAEC ɗinki, za ki ci gaba da karatu?"A wannan karon Fujeerat ta ɗago kai."In sha Allah zan ci gaba."

Ta yi murmushi tana ci gaba da cewa:"Abbana bai da wani buri da ya fi ya ga na yi karatu mai zurfi. Shi ya sa nake ƙoƙarin yin iya bakin ƙoƙarina domin na cika masa wannan burin."

Nadeeya ta yi murmushi."Allah Ya taimaka." "Amin." Fujeerat taamsa.

Sai kuma Nadeeya ta yi shiru.Wani yanayi na damuwa ya mamaye fuskarta.
Fujeerat ta lura da hakan.

"Me ya faru kuma?"Nadeeya ta sauke numfashi."Ni ma ina son ci gaba da karatu."

"To me zai hana ki?" Fujeerat ta tambaya.

"Su Baba." Nadeeya ba ta amsa a raunane.

Fujeerat ta haɗe gira."Ban gane ba."
Nadeeya ta kalli ƙasa."A gidanmu ba a son yarinya ta wuce sakandare. Da zarar ta gama, aure kawai ake yi mata."

Fujeerat ta zaro ido."Da gaske?"Nadeeya ta gyada kai.

"Dukkan yayyena haka aka yi musu."

Sai idanunta suka cika da ƙwalla.
"A gaskiya ban taɓa gaya miki ba ne. Amma nima muna barin makarantar nan za'a yi mini aure,kuma bana son auren da aka shirya mini."

Fujeerat ta ajiye littafinta gaba ɗaya.
"An riga an zaɓa miki miji?"

Kai Nadeeya ta gyada."Kuma bana jin zan iya sonsa."

Hawaye suka gangaro mata.Fujeerat ta matsa kusa da ita.

Ta kama hannunta cikin tausayi."Ki yi haƙuri."

"Wallahi Fujee, mafarkina shi ne na shiga jami'a. Ina son na yi karatu kamar yadda sauran mutane suke yi."

Fujeerat ta shafa bayanta.
"Duk wani al'amari yana hannun Allah."

Nadeeya ta ɗago tana kallonta.

Fujeerat ta ci gaba:
"Idan auren nan alkhairi ne gare ki, Allah Ya tabbatar da shi."

Ta ɗan dakata."Idan kuma karatun ne mafi alkhairi a gare ki, Allah Ya buɗe miki ƙofofin da ba ki zata ba."

Nadeeya ta share hawayenta.

"Amin Ya Allah."

Fujeerat ta yi murmushi."Kuma ko da aure za ki yi, ai ba lallai ya hana ki karatu ba. Allah na iya haɗa ki da mutumin da zai taimaka miki wajen cika burinki."

Nadeeya ta yi murmushi karon farko tun da suka fara maganar."Nagode, Fujee."

"Ba komai."Fujeerat ta faɗa da murmushi a kan fuskarta.

A wannan lokacin babu ɗayansu da ya san irin ƙaddarar da ke jiransu a gaba.

Ko kuma cewa kwanaki masu zuwa za su zo da sauye-sauyen da ba su taɓa tsammani ba.

***FUKAIHAT**

Sai dare mahaifinta ya dawo da ita har gida.

Sai da ya raka ta har cikin falon gidan kafin ya tafi.A tunaninsa Muhammad yana gida, amma bai same shi ba.

Ya kuma jira kusan awa biyu, amma har lokacin M.D bai dawo ba.

Dole ya haƙura ya tafi ganin dare ya fara tsananta.

Bayan tafiyarsa, Fukaihat ta nufi ɗakinta.Ta yi shirin kwanciya cikin kasala kasancewar sai da ta  sha kayan mayenta kafin su baro gidansu.Ba ta sake sanin abin da ke faruwa ba.

Karfe uku na dare Fitsari  ya tashe ta daga barci.A hankali ta tashi tana tangal-tangal.Daidai lokacin ne ta ji ƙarar motar Muhammad na shiga harabar gidan.Sai dai ko kaɗan hakan bai dame ta ba.

***MUHAMMAD***

   Kai tsaye ɗakinsa ya nufa bayan dawowarsa.Sai da ya shiga banɗaki ya yi wanka mai tsawo na kusan mintuna talatin da biyar.Da ya fito, ya shirya cikin farar jallabiya mai kyan gaske.

Daga nan ya tada sallah kamar yadda ya saba yi a kowanne dare.

  Ya daɗe yana Sallah da karatun Alƙur'ani,Har sai da aka kira sallar Asuba.Bayan ya dawo daga masallaci ne ya nufi ɗakin Fukaihat.

Ko ƙwanƙwasa ƙofa bai yi ba.Domin ya san ba za ta ji ba.

Da ya shiga ɗakin, idanunsa suka sauka kan gadon.Wayam babu kowa.

Ya haɗe gira cike da mamaki.

kafin ya fara zagaya idanunsa a ɗakin yana duban  ko'ina.

Can kusa da ƙofar banɗaki ya hango ta kwance a ƙasa.

Kallo ɗaya kawai ya yi mata ya fahimci halin da take ciki.

Ajiyar zuciya ya sauke.Ba tare da ya ce komai ba ya ƙarasa inda take.

Ya ɗauke ta cak kamar ƙaramar yarinya,
Ya shiga da ita cikin banɗaki.

Kai tsaye ya zaunar da ita a cikin bathtub.Sannan ya buɗe shower.Ruwan sanyi ya sauka kanta gabaɗaya.

Cikin firgici Fukaihat ta zabura da sauri.Idanunta suka sauka kan Muhammad.

Tsoro ya cika mata zuciya.Mamaki kuma ya ƙara biyowa baya.

A take duk mayen da ke jikinta ya fara raguwa.Ta sunkuyar da kanta ƙasa.

Domin duk da yawan rashin jin tsoronta, akwai mutumin da take matuƙar tsoro a duniya.

Muhammad.

Sai dai abin mamaki...

Maimakon ya yi mata ihu kamar yadda ta zata, sai ta ji muryarsa cikin natsuwa.

"Ki yi wanka."

Ta ɗago ido a hankali.

"Ki ɗauro alwala."

Ya ci gaba.

"Sannan ki yi sallah."

Ya ɗan dakata.

"Idan kin gama, ki same ni a falona. Ina son magana da ke."

Fukaihat ta kasa cewa komai,Kai kawai ta gyada.

Muhammad ya juya ya fita.Ya bar ta cikin mamaki da ruɗani.

Yana tafiya zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa.A karo na farko ya fara tuhumar kansa ko ya yi adalci ga Fukaihat.

Ko da yake bai taɓa son auren ba...Amma yanzu ita  amanar da Allah Ya ɗora masa ce.Tarbiyyarta,Kiyaye mutuncinta,Da kuma gyara rayuwarta Duk suna kansa.

Ya girgiza kai a hankali.

A zuciyarsa yana tunanin
"Da ace Khairat ce ko Lamrat a irin wannan halin, shin zan yi shiru ne?"

Amsar da zuciyarsa ta ba shi ita ce:

"A'a."

Daga wannan rana...

Ba tare da Fukaihat ta sani ba...

Rayuwarta ta fara shiga wani sabon babi.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.