Free chapter · Read without an account
Episode 45
Misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe jirginsu Humaira ya yi landing a Abuja.
Tun daga cikin jirgin Humaira ke kallon birnin ta window, zuciyarta cike da tunane-tunane. Wannan shi ne karo na farko da ta taɓa hawa jirgi, kuma karo na farko da ta bar Kano zuwa wani gari da ba Potiskum ba, duk abin na mata kamar mafarki.
Yusuf ne ya zo ɗaukar su a airport ɗin.
Inaya ta zauna a front seat, yayin da Mami, Humaira da Inara suka zauna a baya.
A hanyar gidan Inara da Inaya ke ta surutu suna ba Mami labarin abubuwan da suka faru a school bayan tafiyarsu, sun gani a group chat na class ɗinsu, yayin da Humaira ke zaune cikin nutsuwa tana kallon sabuwar rayuwar da take gani ta glass ɗin motar.
Suna isa gidan kuwa suka tarar da Anty za ta fita wajen aiki.
Da murmushi ta ƙaraso wajen motar tana gyara handbag ɗinta a kafaɗa. Buɗe ƙofar baya ta yi, Mami ce ta fara sauka.
“Barka da hanya Yaya.” Anty ta faɗa tana rungumeta.
Mami ta yi murmushi itama tana rungume ta back.
“Yauwwa Antyn yara. Har kin fito?”
“Eh mana.” Anty ta amsa tana dariya kaɗan.
Sannan ta sake Mami ta rungume su Inaya da Inara da suke gaisheta.
A lokacin ne idanunta suka sauka akan Humaira da ke tsaye daga gefe riƙe da ƙaramin handbag ɗinta da Meenat ta ba ta da za su zo, da kuɗin da Ahmad yake tura mata, da kuma dubu goma da Umma ta bayar a ba ta. Kallonta da ta yi ya sa Humaira sunkuyar da kanta cikin ladabi.
“Baƙuwa muka yi ne?” Anty ta tambaya tana kallon Mami.
“Eh wallahi.” Mami ta amsa.
“Masha Allah.” Anty ta faɗa tana kallon Humaira da murmushi. “Sannu da zuwa baƙuwa.”
“Yawwa…” Humaira ta amsa a hankali tana gaisheta cikin kunya.
Daga wajen suka ɗan gaggaisa, sannan Anty ta shiga motarta ta fita daga gidan saboda ta makara.
Mami kuwa ta juya tana kallon Humaira.
“Mu shiga ciki ko?”
Kai Humaira ta gyaɗa a hankali, ta bi bayansu zuwa cikin gidan da zai zama sabon mafakarta.
Ɗakin su Inaya Mami ta saukar da Humaira, ba wai don babu empty room ɗin da za ta sauka ba, a’a. Mami ta yi hakan ne saboda tana son Humaira ta sake jikinta, ta ji kamar tana cikin gidansu ne tare da ƴan uwanta, ba gidan baƙi ba.
Humaira na shiga ɗakin ta ji wani irin sanyi a zuciyarta. Ɗakin yana wani irin ƙamshi mai daɗi, komai a gyare cikin tsari da tsafta.
Wanka ta fara shiga domin ta cire gajiyar tafiya, da ta fito kuwa, sai ta tarar su Inara ba sa ɗakin, hakan ya sa ta tsaya daga bakin gadon tana ƙarewa faffaɗar ɗakin kallo.
Da ta gan ɗakin Fa’iza tana tunanin shi ne mafi girma da kyau da ta taɓa gani, amma da ta ga wannan ɗin sai ta raina na Fa’izar.
Manyan Italian twin beds guda biyu ne a jere, kowanne da side drawer ɗinsa. Sai wani babban wardrobe mai ƙofofi har guda takwas, a gefe kuma akwai giant dressing mirror da aka shaƙe gabansa da kayan shafe-shafe, turaruka da body mists iri daban-daban. Babban plasma TV ne manne a bango yana facing gadajen, yayin da centre carpet mai laushi ya mamaye tsakiyar ɗakin.
A wani gefen kuma shoe rack ne cike da takalma sama da talatin, yawancin takalmar ma bibbiyu ne iri ɗaya, kasancewar masu ɗakin ƴan biyu ne.
Humaira na tsaye tana kallon komai cikin mamaki daman akwai na su kudi haka a ƙasar nan, aka tura ƙofar ɗakin aka shigo.
Inara ce ɗauke da tray mai ruwa da juice, a hankali ta ajiye tray ɗin a kan side drawer, tace;
“Ga ruwa ki sha.”
Daga nan ta nufi wardrobe, ta buɗe shi ta ciro wani sabon cotton three-quarter gown pink color, rigar na da buttons tun daga sama har ƙasa.
Ta miƙawa Humaira tana cewa;
“Mami tace ki yi manage wannan kafin zuwa anjima mu je a siyo miki naki.”
Da hannu biyu Humaira ta karɓi rigar.
“Nagode.” ta faɗa a hankali.
Murmushi Inara ta yi mata.
“Idan kina buƙatar wani abu muna falon downstairs. Sannan if you're bored, za ki iya kunna TV, ko ma ki sauko ƙasa mu sha hirarmu.”
“To, nagode.” Humaira ta sake furtawa.
Inara ta fita, ta bar Humaira ita kaɗai cikin ɗakin.
Sai dai bayan ƴan seconds ta sake leƙowa tana faɗin;
“Ki shafa duk man da ya miki a gaban mirror.” Daga haka ta sake fita.
Murmushi Humaira ta yi, ta ƙarasa gaban mirror ɗin ta zauna a dressing stool.
Ɗaya daga cikin man masu ƙamshi ta ɗauka ta shafa a jikinta, sannan ta ɗan fesa body spray kafin ta saka rigar da Inara ta bata.
Rigar ta yi mata kyau sosai. Pink ɗin ya fito da hasken fatarta, duk da ta rame kuma idanunta sun ɗan kumbura saboda yawan kuka.
Ta daɗe fiye da mintuna goma tsaye gaban mirror tana kallon kanta.
A hankali ta taɓa gefen idanunta da suka kumbura, sannan wani ƙaramin murmushi ya suɓuce mata.
“Humaira…In Sha Allah kukanki ya zo ƙarshe.” ta faɗa wa kanta a hankali kamar tana lallashin zuciyarta.
Ta zauna a bakin gado ta buɗe juice ɗin da Inara ta kawo mata, ta sha sosai kafin ta rufe ta mayar gefe.
Ɗakin ya yi shiru sosai, irin shirun da ke sa mutum ya fara jin kaɗaici idan ya daɗe shi kaɗai. Humaira ta zauna na ɗan lokaci tana kallon ɗakin, amma daga ƙarshe ta gaji da zaman, ta miƙe ta nufi gaban TV domin ta kunna, amma ta rasa ta inda za ta fara, ba ta taɓa ganin irin TV ɗin ba balle ta san yadda ake kunna shi. Haka ta haƙura ta koma bakin gadon ta zauna.
A lokacin ne idanunta suka sauka akan wani shelf da ke a wani corner na ɗakin, kusa da wardrobe.
Shelf ɗin cike yake da litattafai iri-iri.
A hankali ta ƙarasa gabansa tana dubawa. Yawanci takardun makarantar su Inara ne da Inaya na boko da kuma islamiyya, sai idanunta suka sauka akan Alƙur’ani.
A hankali ta ɗauko shi ta koma bakin gadon ta zauna, ta buɗe, karatu ta fara yi cikin nutsuwa. Daɗin karatun da sanyin da yake sauka a ranta ya sa ta manta da komai na ɗan lokaci.
Kiran sallar Azahar ne ya katse ta.
Ta rufe Alƙur’anin cikin girmamawa, ta ajiye shi sannan ta shiga bathroom yin alwala.
Da ta fito kuwa sai ta tarar da su Inara suna ta jan towel kamar yara ƙanana.
“Menene haka?” Humaira ta tambayesu cikin mamaki.
“Ba ki san rainin hankalin Inaya bane!” Inara ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwace towel ɗin. “Wannan towel ɗina ne fa, ta sani amma wai lallai shi za ta yi amfani da shi!”
Inaya ta turo baki.
“Ai kema kina amfani da nawa!”
Da ƙyar Humaira ta iya shiga tsakaninsu ta karɓe towel ɗin kafin ya yage.
Ta kalli Inara tace;
“Ki yi haƙuri ta yi amfani da shi tunda ƴar uwarki ce. Wataƙila nata ne na jiƙa.”
“Amma ai tana da wasu!” Inara ta faɗa tana harar Inayar.
Humaira ta yi murmushi kaɗan.
“Tana sonki ne shiyasa take son amfani da abin ki, kema sai ki yi amfani da na…”
Ba ta gama magana ba kuwa, Inaya ta fisge towel ɗin ta ruga zuwa bathroom da gudu.
“Inaya!” Inara ta kwalla mata kira tana bin bayanta.
Girgiza kai kawai Humaira ta yi tana murmushi.
Ta ɗauki darduma da hijabi da ta gani a prayer corner, ta shimfiɗa sannan ta tada Sallah.
Bayan su Inara sun gama kokowarsu, daga ƙarshe dai dole Inara ta barta da towel ɗin.
Ta yi alwala ta fito tana share fuskarta da ƙaramin towel.
Da ta ga Humaira na Sallah akan dardumarta sai ta yi murmushi.
Ita ma ta ɗauki ta Inaya ta shimfiɗa ta shiga Sallah.
Inaya na fitowa daga bathroom idanunta suka sauka akan Inara.
“Kanbu!” ta faɗa tana ware ido. “Amma lallai Inara kin raina ni, yanzu kika gama kokowa da ni akan towel ɗinki, amma kika zo kina amfani da dardumata?”
Humaira na cikin addu'a amma sai da murmushi ya suɓuce mata.
“Wallahi kin ci albarkacin Sallah kike yi da na yi miki tijara!” Inaya ta cigaba da surutu.
Ko da Inara ta idar, ko kallonta ba ta yi ba. Ta miƙe kawai ta shige bathroom ɗin tana dariya ita kaɗai.
Humaira kuwa dariya sosai faɗar tasu ke bata.
Wato ƴan biyun kam ba a raba su da drama.
Bayan Inaya ta idar da Sallah, Inara ma ta fito daga wanka ta shirya cikin irin kayan Inaya, doguwar rigar kanti baƙa mai sauƙin nauy8.
Dukansu suka zauna suka kunna TV suna kallon sabon Nigerian film ɗin da aka sake, MONICA.
Humaira na zaune tsakaninsu tana kallon yadda suke commenting akan duk wani scene kamar su ne directors ɗin film ɗin.
Raliya mai aikinsu ce ta leƙo ɗakin tana cewa;
“Mami tace ku sauko ku yi lunch.”
Nan take Inara ta miƙe ta ja hannun Humaira.
“Mu je.” Sai ta raɗa mata a kunne; “Kar ki yi magana da Inaya, she’s very troublesome.”
Inaya da ta ji maganar ta ɗaga kafaɗa kawai alamar ko a jikinta, sannan ta sha gabansu ta fice daga ɗakin tana tafiya irin ta rainin wayo.
Humaira sai dariya take yi musu a zuciyarta.
Fried rice da peppered chicken Raliya ta yi serving ɗinsu a dining.
Humaira ce ta fara ture plate ɗinta bayan ta ci kaɗan tana faɗin;
“Alhamdulillah.”
A lokacin ne idanunta suka sauka akan wani babban family photo frame da ke manne a bangon dining ɗin kusa da fridge.
Hoton ya yi mata kyau sosai, ta daɗe tana kallonsa ba tare da ta sani ba.
“Family frame ɗinmu kenan.” Mami ta faɗa tana lura da kallon da Humaira ke wa hoton.
Ta miƙe ta cire frame ɗin daga bangon, sannan ta dawo ta zauna kusa da Humaira tana ajiye hoton a kan table.
Da yatsarta ta fara nuna mata su ɗaya bayan ɗaya.
“Wannan shine Abbanku.”
Humaira ta kalli mutumin dake tsakiyar hoton, fuskarshi cike da nutsuwa da dattako.
“Wannan kuma Antynku.” Mami ta cigaba tana nuna matar dake gefen Abba. “Ita ce wacce kuka gaisa ɗazu…kishiyata ce.”
Humaira ta ɗan zaro ido kaɗan, amma sai ta yi saurin maida hankalinta kan hoton.
“Wannan kuma shine babban ɗana Hamza. Yana da mata da yara, ƙila ma ya shigo anjima.”
Sai ta nuna wani kyakkyawan saurayi.
“Wannan kuma shine ɗana na biyu, Muhammad Hunaif. Shi ma yana da mata, suna nan few houses daga nan… amma jiya ya bar ƙasa.”
Daga nan ta cigaba da nuna mata Hameed, Yusuf, sai kuma Inara da Inaya.
Humaira na kallon hoton cikin ban sha'awa, family ɗin ya yi mata kama da irin families ɗin da take gani a films.
Mami ta mayar da frame ɗin wajen zamansa sannan tace;
“Anjima bayan sallar La’asar, su Inaya za su raka ki ku je siyayyan abubuwan amfani.”
Humaira ta yi saurin kallonta.
“Toh… nagode sosai. Allah ya saka da alkhairi, ya ƙara buɗi.”
Mami ta yi murmushi kawai.
Da yamma misalin ƙarfe biyar, Mamuda direba ya kai su Humaira babban shopping mall.
Tun daga entrance ɗin wajen Humaira ta fara jin kanta na juyawa saboda girman wajen da yawan mutane. Su Inara kuwa sun riga da sun saba da zuwa, suka shiga jido mata kaya iri-iri,; dresses, shoes, handbags, skincare, hijabai, perfumes har da pyjamas.
Humaira kam sai binsu take da ido.
Duk lokacin da ta ce;
“Wannan ya isa” sai Inaya ta ce; ke dai ki yi shiru.”
Ko Inara ta ce;
“Mami ce tace mu siyo duk abinda za ki buƙata.”
Da suka isa paying counter aka haɗa lissafin kayan.
“Naira miliyan uku da rabi.”
Lokaci ɗaya Humaira ta buɗe baki cikin mamaki.
Miliyan uku da rabi, akan kaya?
Ta kalli su Inaya cikin rashin yarda, amma ko a jikinsu.
Inaya ta ciro ATM card ɗin da Mami ta ba su, ta yi payment ɗin kamar ba komai.
Ma’aikatan shopping mall ɗin suka taimaka musu suka kai kayan mota saboda yawansu.
Bayan sun dawo gida, su Inara suka empty wani gefen wardrobe, suka fara jera wa Humaira kayanta.
Humaira tsaye take tana kallonsu, zuciyarta cike da wani irin jin daɗi da godiya.
Tun da aka haifeta babu wanda ya taɓa yi mata irin wannan hidimar.
Da daddare kuwa, Mami har ɗakin Abba ta kai Humaira, ta yi masa bayanin case ɗin Humaira dalla-dalla, da kuma manufarta akanta.
Abba ya yi shiru na ɗan lokaci bayan ya gama sauraro, sannan ya kalli Humaira da tausayi sosai.
“Allah sarki…” shine kawai abinda ya fara furtawa, yana mai jin tausayin yarinyar na shigar sa.
Daga nan yace shi zai ɗauki nauyin karatun Humaira gaba ɗaya.
“Zan biya miki school fees har sai kin ce kin gaji da karatu dan kanki, kuma zan taimakawa Maminku wajen ganin an hukunta wannan Lukman ɗin ta hanyar da ta dace.”
Sai ya ɗan yi murmushi.
“Daga yau Humaira kin zama ƴata. Feel free ki faɗa min duk abinda kike buƙata.”
Humaira ta sunkuyar da kanta hawaye na zubo mata. Ta rasa irin addu’ar da za ta musu, godiya da addu'o'i ta fara kwararo mishi.
Haka kuma daga nan Mami ta kai ta ɗakin Anty suka gaisa cikin mutunci.
Sannan ta sanar da ita cewa daga yau Humaira za ta fara zama tare da su a gidan. Anty ba ta tambayeta ko wacece Humairan ba, balle kuma dalilin da ya sa za ta zauna da su, murmushi kawai ta yi, tace; “Barkan ki da zuwa baƙuwa. Me sunanki?“
“Aisha Humaira." Humaira ta amsa a hankali.
“Masha Allah, be of your good behavior Aisha Humaira.“
“In Sha Allah.“
Daga nan Mami ta rakata ta koma ɗakinsu, ita kuma ta shige nata.