Free chapter · Read without an account
02
***KANO***
Ummi ta ɗan fara samun sauƙin damuwa, amma har yanzu ba ta fita daga takaba ba. Sai dai a duk lokacin da ta tuna irin alherin da marigayin mijinta ya yi mata, musamman yadda ya tsaya mata a lokacin da kowa ya juya mata baya, zuciyarta sai ta ƙara raunana.
Shi kaɗai ne ya yarda da ita, ya karɓe ta da duk wani kallon ƙasƙanci da mutane ke yi mata. Har ya kai ga cewa zai aure ta duk da suka da cin mutuncin da mutane suke mata. Idan ta tuna waɗannan abubuwan hawaye ne suke zubo mata.
Yayanta ya yi iya ƙoƙarinsa wajen lallashinta da yi mata nasiha, amma abin ya fi ƙarfinsa. Da ya gaji, sai ya zuba mata ido kawai.
Ranar da ta kammala takabarta, don dole sai da aka sa ta yi kwalliyar da ta dace da macen da ta gama takaba.Amma maimakon farin ciki, zuciyarta ta cika da baƙin ciki.
Musamman da tun a ranar ne wani bazawari ya zo neman aurenta.A lokacin da ta ji maganar, sai ta fashe da kuka. Kuma yayanta ya matsa mata cewa dole ta fito ta ganshi.
Mutumin da ta gani kuwa ya ba ta mamaki don ko ba baƙo ba ne. Abokin marigayin mijinta ne.Hakan ko ya taɓa ranta sosai,sai da ta ci masa mutunci tass, sannan ta dawo gidan,haka ta wuni ta kwana tana kuka da Yi wa malam Muhammad addu'a.
Washegari ma sai da aka garzaya da ita asibiti saboda tashin hankalin da ta shiga.A asibitin kuwa ta sha faɗa a wurin Malan Musa (Yayanta). Har suka koma gida bai daina sababi ba har sai da suka yi baƙi. A lokacin ne ya yi musu sallama ya fice bayan sun gaisa da baƙuwar.
Yana fita matarsa Fauziyya ta miƙe cikin farin ciki tana ambaton sunan baƙuwar"Salimah?"
"Na'am Fauziyya." Baƙuwar ta amsa da murmushi.Nan take suka rungume juna cikin farin ciki da kewar juna.Sun ɗauki lokaci kafin su saki juna.
"Ku zauna mana," Fauziyya ta faɗa tana kallon ƙannenta biyu da suka rako Salimah.
Bayan sun zauna, ta tashi ta ɗebo musu ruwan sanyi da lemo daga firinji da yake sana'arta ne. Ta kawo ta ajiye musu sannan ta wuce kitchen ta ɗora abin da za ta dafa kafin ta dawo ta zauna tare da su.
"Yaushe a gari in ji maƙi baƙo?" ta tambaya tana murmushi.
Salimah ta dubi Ummi wadda tun bayan fitar Malan Musa take ta share hawaye,a maimakon ta amsa tambayar da Fauziyya tayi mata sai ita ma ta jefa mata tambaya, "Fauziyya, wannan ai kanwar Abban Kamal ko?"
"Eh wallahi, ita ce. Mijinta ne ya rasu. Jiya ta fita daga takaba amma har yanzu ta kasa kwantar da hankalinta."
Ta ɗan yi shiru sannan ta ci gaba da cewa, "Wallahi lokacin da ya rasu sai da ta yi kusan sati biyu a asibiti. Mu kanmu ba mu san da mutuwarsa ba sai ranar bakwai. Tana can kwance ba a hayyacinta ba."
Ta nuna Ummi da hannu.
" Kin gan ta nan,Jiya ma haka ta wuni ta kwana tana kuka kamar ranta zai fita. wani mutum ya zo neman aurenta, amma kin ganta kamar yarinya, ta ci mutuncinsa ta dawo. Wai mai yasa zai ce yana sonta alhali abokin marigayin mijinta ne."Fauziyya ta girgiza kai.
"Ki ji fa, Salimah. Shekarun Samira talatin da biyar ne. Idan ba ta sake aure ba, me za ta yi?"
Salimah ta yi murmushi.
"Fauziyya kenan. Har yanzu baki canza halinki ba."
Duk suka yi dariya kaɗan.
Salimah ta ci gaba da cewa,
"Yaushe mace za ta rasa mijinta sannan kafin ta gama jimami ku fara mata maganar aure? Musamman ma idan irin mutuwar da ta zo farat ɗaya ne ko?"
Fauziyya ta sauke ajiyar zuciya."Eh wallahi. Ya dawo daga kai yarinyarsu makaranta ne. Yana tsallaka titi a bakin unguwarsu wata mota ta bugeshi. Direban ko tsayawa bai yi ba ma ya gudu.
Salimah ta girgiza kai cikin tausayi.
"Allah Sarki. Allah ya jiƙan sa."
Sai ta matsa kusa da Ummi, ta dafa kafaɗarta.
"Ki kwantar da hankalinki. Mamaci addu'a yake buƙata, ba kuka ba. Ke da za ki zama abin lallashi ga yar ki, ke ce za ki zauna kina kuka haka?"
Ummi ta share hawayenta ba tare da ta ce komai ba.
Salimah ta sake tambaya,
"To ina yarinyar taku?"
Fauziyya ta amsa,
"Tana makarantar kwana. Ba a je ɗaukarta ba. Mahaifiyarta ta hana saboda tana da jarabawa. Ta ce kada a tayar mata da hankali."
Salimah ta gyaɗa kai.
"Hakan ne ya dace. Ai kwanaki kaɗan suka rage su gama. Allah ya jiƙan marigayin da rahama."
"Ameen," suka amsa gaba ɗaya.
***ABUJA***
M.D yana zaune a kan cushion cikin falon Yana jiran shigowar Fukhaihat,Ai kam ba jima wa sosai ta shigo ba tare da tayi sallama ba.
Ya ɗago kai ya kalleta.
"Baki iya sallama ba ne?"
Da sauri ta ce,
"Sorry, Yaya."
Ta juya ta fita sannan ta yi sallama yadda ya kamata.
Sai da ya amsa kafin ta shigo ta zauna.
"Yaya, gani."
Ya gyada kai.
"Eh, na gan ki ai."
Ya gyara zamansa sannan ya dubeta sosai.
"Fukhaihat, wacce makaranta kika yi?" Sai da ta Yi jimm na wani lokaci kafin tace "British School, sannan University of America."
Ya girgiza kai "Ba wannan nake nufi ba. Ina nufin Islamiyya."
Ta ɗan yi tunani sannan ta ce,
"Yaya... mene ne Islamiyya kuma?"
M.D ya zaro ido cikin mamaki.Na ɗan lokaci ya kasa magana.Daga ƙarshe ya girgiza kai kawai.
"Shikenan. Ki je ki shirya kayanki. Cikin wannan satin za mu tafi Mexico tare."
Ta miƙe tsaye da sauri.
"Really?"Ta faɗa cikin murna.
M.D ya gyaɗa kai kawai.
Tuni ta juya da gudu tana murna.
Ya bi ta da kallo har ta fice daga ɗakin.
Sai ya sauke ajiyar zuciya. "Alhamdulillah. Allah Ya saka wa iyayenmu da mafificin alkhairi da suka tsaya tsayin daka akan mu gurin koya mana tarbiyya da nema mana ilimin da zai amfane mu a duniya da lahira. Ya Allah Ka saka musu da Aljannatul Firdausi.""Ameen. "
***FIRST LADY***
Alhamdulillah, a yau Fujeerat da sauran ɗalibai suka kammala jarabawar WAEC.Saboda akwai tazara tsakanin WAEC da NECO, makarantar ta ba su hutun mako ɗaya zuwa biyu kafin a ci gaba da jarabawar NECO.An aika wa iyayen ɗalibai saƙo ta wayoyinsu domin su zo su ɗauki 'ya'yansu.
Fujeerat da Nadeeya suna tsaye ƙarƙashin wata bishiya suna jiran a zo a ɗauke su. Amma har Lokaci ya ja sosai ba wanda ya zo.Sai wajen yamma ne yayan Nadeeya, Lukman,ya iso da ƙaramar motarsa.
Fujeerat ta raka ƙawarta har bakin motar.Ta gaidashi, ya amsa cikin fara'a.
"Yau Fujeerat Abbanki bai zo ba ne?"
Ta girgiza kai.
"Eh wallahi Yaya Lukman. Wataƙila bai samu dama ba."
"To ki shigo mu tafi, sai mu sauke ki a gida."
"A'a Yaya, kar na tafi ya zo mu yi saɓani."
Lukman ya ɗan yi tunani.
"To baki haddace lambarsa ba?"
"Na haddace."
"Madalla. Ga wayata nan, saka mu kira shi."Fujeerat ta karɓi wayar, ta saka lambar mahaifinta.
Sai da Lukman ya kira sau uku kafin a ɗaga.Sai dai ba muryar namiji ba ce.
Muryar mace ce.
Da sauri ya miƙa wa Fujeerat wayar.
"Yi magana. Na ji muryar mace."
Da sauri ta karɓi wayar ta kara a kunne, nan take ta gane muryar Ummi.
"Assalamu alaikum, Ummi."
"Wa alaikumus salam."
"Ummi, Abba bai taho ba ne? Tun ɗazu muke jiransa."
Ummi ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce,"Eh, bai samu damar zuwa ba."
"To Ummi, Yaya Lukman yana so mu tafi tare da su."
"Shikenan, ku zo tare da su. Amma ku zo gidan Yaya Musa kai tsaye."
Fujeerat ta yi mamaki.
"Gidan kawu kuma? Ummi, me ake yi a gidan?"
Ummi ta ɗan yi murmushin da Fujeerat ba ta Saba jin sa daga gare ta ba.
"Ke dai ku zo. Idan kin zo za ki gani."
"To shikenan Ummi. Sai mun iso."
Ta kashe wayar sannan ta juya ta kalli Lukman.
Ta yi masa bayanin abin da Ummi ta ce.
Lukman ya yi murmushi.
"Kin ga amfanin kiran ko? Da mun tafi mun bar ki kin ta hira da bishiyu"
Fujeerat ta yi murmushi kawai.
Daga nan ta shiga motar.
***KANO***
Kamar yadda Ummi ta faɗa, gidan Kawu Musa suka nufa da Fujeerat.
Da suka isa, Fujeerat ta kalli Lukman tana cewa,"Don Allah Yaya Lukman, ku shigo ku gaisa da su Ummi mana."
Da farko kamar zai ƙi, sai kuma ya fasa. Ya juya ya dubi Nadeeya.
"Malama, fito mu shiga. Kuma Wallahi saura ki fara zubar zancen nan kamar kanya."
Nadeeya ta turo baki tana gunguni a zuciyarta ba tare da ta bari ya lura ba.
Ummi ta nuna farin cikinta ƙwarai da zuwansu, tare da yi musu godiya.
Da suka tashi tafiya ma, sai da suka raka su har bakin mota. Sai da suka ga tafiyarsu sannan suka dawo ciki.
Tun kafin ta zauna, Fujeerat ta dubi Ummi cikin damuwa."Ummi... ina Abbana? Kuma me ya kawo ki nan gidan?"
Ummi ta kalleta na ɗan lokaci kafin ta ce,"Ki fara shiga ki cire kayan jikinki, ki yi wanka, ki ci abinci sannan ki huta. Daga baya za mu yi magana."
Fujeerat ta ji amsar ba ta gamsar da ita ba, amma ba ta sake cewa komai ba.
Ta juya ta shiga ɗakin Ummi.Zuciyarta cike take da tambayoyi da kuma mamakin dalilin da ya sa Ummi take gidan don da alamun ta daɗe a cikinsa.
*** MASARAUTAR AGADAS***
Zaune yake a gaban wani dattijo mai cikar kima da mutunci. Wato Tsohon sarki mai murabus.
Yarima Iqbal, magajin kujerar masarautar Agadas kuma ɗa tilo ga Sarki Muhammad Saifuddeen, yana danna ƙafafun tsohon cikin girmamawa yayin da suke tattaunawa kan harkokin masarauta.
Ya ɗago kyakkyawar fuskarsa cike da mamaki.
"Amma ranka ya daɗe, ka tabbatar an gudanar da binciken yadda ya kamata kuwa?"
Murmushi tsohon ya yi.
"Har yanzu bana jin ka fahimci yadda masarautar nan take, Iqbal."
Ya ɗan yi shiru kafin ya ci gaba."Wannan masarautar da kake gani cike take da maƙiya na gida da waje, da kuma makirce-makirce na ban mamaki. Ba kowa ake yarda da shi ba,don wani murmushin iyakarsa fuska ne ba har zuci yake ba."
Iqbal ya sauke numfashi."To Allah Ya kawo mafita mai kyau."
"Ameen, yarona. Wannan ita ce addu'ar da ta rage mana."
***ABUJA***
Alhaji Mus'ab Mai Dala da iyalansa suna zaune a babban falon gidan suna jiran isowar M.D domin yau zai tafi Mexico tare da Fukhaihat.
M.D ya yi sallama ya shigo falon, kasancewar ƙofar a buɗe take.
Gaba ɗaya suka amsa masa.Ya ƙarasa ya gaida iyayensa sannan ƙannensa suka gaishe shi.
Hajiya Salimah, wadda kowa ke kira da Mammy, ta ce,
"A'a Son, ina Fukhaihat ɗin?"
M.D ya sunkuyar da kai cikin kunya.
"Mammy, tana gidansu. Tun jiya ta je sallama. Mun yi waya da ita, ta ce mahaifinta zai rakota nan."
Bai gama maganar ba suka yi sallama daga bakin ƙofar falon.
Kowa ya juya ya kalli ƙofar.
Fukhaihat ce tare da mahaifinta suka shigo.Tana sanye da wata kyakkyawar rigar kanti da ta yi matuƙar mata kyau.
Alhaji Mus'ab ya miƙe ya tarbi Daddyn Fukhaihat.Suka gaisa cikin mutuntawa kafin suka zauna.
Fukhaihat ma ta gaida kowa cikin ladabi.Duk da sangartarta, idan Mammy tana wurin ba ta wasa da ladabi.
Alhaji Mus'ab ya dubi mahaifinta.
"Alhaji, yau ga ka a gidanmu. Dama ba ka san iyalina ba."
Mahaifin Fukhaihat ya yi murmushi.
"Hmm... ai ba su kaɗai ba. Ko sirikina ban waye shi sosai ba bare sauran iyalan gidan."
Kowa ya dubi juna cikin mamaki.
Alhaji Mus'ab ya dubi M.D.
"Muhammad, me ya sa haka?"
M.D ya ci gaba da sunkuyar da kansa.
Kafin ya yi magana, mahaifin Fukhaihat ya ce,
"A'a Alhaji, ba laifinsa ba ne. Ka san ba mazauna gari ba ne gabad'ayanmu. Duk lokacin da nake gari shi baya nan, idan kuma ya zo ni bana nan."
Alhaji Mus'ab ya girgiza kai.
"Wannan ba hujja ba ce. Shekaru kusan uku kenan da auren ƴarka da shi,amma ace ba ku san juna sosai ba."
"To shikenan Alhaji. Yanzu dai mun haɗu, komai ya wuce."
Hajiya Ni'ima ta dubi M.D.
"To kai ka ɗago mana ku gaisa. Ka wani sunkuyar da kai kamar tsohon munafuki."
Nan take Mammy ta ce,
"Hajiya! Kar ki faɗi haka mana."
Mahaifin Fukhaihat ya ɗan kalli Mammy.
A take wani irin bugun zuciya ya taso masa.Abin ya girgiza shi.
Sai dai ya ɓoye komai a ransa.
Alhaji Mus'ab ya ce,
"To Alhaji, ka kalli sirikinka da kyau."
Ya juya ya dubi M.D sosai.
Nan take mamaki ya bayyana a fuskarsa.
Wani irin tashin hankali ya ratsa shi.
Sai dai ya danne komai.
"Lafiya kuwa?" Alhaji Mus'ab ya tambaya.
Ya sauke numfashi.
"A'a... kawai mamaki na yi."
Sai ya yi murmushin dole.
"Ban yi tsammanin zan ga Balarabe a cikin Hausawa ba."
Dariya ta sake tashi a falon.
"Amma dai wannan ce mahaifiyarsa?" ya tambaya yana nuna Mammy.
Alhaji Mus'ab ya girgiza kai.
"A'a. Ita ce ta raine shi dai. Amma wannan ce mahaifiyarsa."Ya nuna Hajiya Ni'ima.
Ya ɗan yi shiru.
"Allah Mai iko. Amma suna kama sosai"
Sai ya dubi Fukhaihat.
"Allah Ya sanya albarka. Bari na wuce yanzu."
Fukhaihat ta turo baki.
"Daddy, ai ka ce har airport za ka raka ni."
Ya shafa kanta "I'm sorry dear. Wani muhimmin abu ne ya taso min. Amma kin ga akwai mutanen gidan nan da za su raka ku."
Ya yi murmushi.
"Da zarar na samu lokaci zan zo in ganki har cancel."
"Okay Daddy."
Ta amsa cikin sanyin murya.
Ya yi sallama da kowa ya fice.
Amma zuciyarsa ta kasa samun natsuwa.Ganin Mammy da M.D ya tabbatar masa da cewa akwai wata alama da ya kamata ya bincika.Kai tsaye ya yanke shawarar zuwa wajen Surkulu domin ya nemi cikakken bayani.
***KANO***
Da Ummi ta gama sanar da ita gaskiyar abin da ya faru, Fujeerat ta zaro ido tana kallonta tamkar ba ta fahimci abin da ta ji ba.
"Ummi... me kika ce?"
Muryarta na rawa.
Ummi ta kasa maimaita maganar. Hawaye suka cika mata idanu.
A lokacin ne zuciyar Fujeerat ta tabbatar mata da mummunan gaskiyar da take ƙoƙarin musantawa.
"Abbana... ya rasu?"
Ta faɗa cikin wata irin murya mai karya zuciya.
Nan take ta fashe da kuka mai ƙarfi.
"Ya Allah! Abbana! Baya doron duniya yanzu! Mutumin da ya fi kowa sona!"
Ta riƙe ƙirjinta da hannu biyu tana kuka.
"Yau Abba ya tafi ya bar ni? Ba zai ga ranar da zan cika masa burinsa ba? Ba zai sake kirana 'yar albarka ba?"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..."
Ta faɗi hakan tana rushewa da matsanancin kuka.
Ita kanta Ummi sai da mutuwar ta dawo mata sabuwa. Dukkan haƙurin da ta yi ta tara wa watannin baya ya watse a wannan lokacin.
Ta rungume Fujeerat suka ci gaba da kukan tare.Duk ɗakin ya cika da sautin kukansu.
A lokacin ne Fauziyya ta shigo.Tun daga falon gidan take jin kukansu.
Ta tsaya tana kallonsu kafin ta tafa hannu.
"La'ilaha ilallahu! Wato sata kika yi a gaba tana kuka, ke kuma kina tayata?"
Ta girgiza kai cikin takaici.
"Samira, wannan shi ne abin da kika ga ya dace? Ke da ya kamata ki lallashe ta?"
Ta dubi Fujeerat.
" Fujeerat, ki yi haƙuri. Allah baya barin wani saboda wani ya ji dadi. Mamaci addu'a yake buƙata, ba kukan da zai ƙara masa azaba ba."
Ta juya tana mita.
"Wallahi ni kam na gaji da wannan halin naki Samira,ace mutum Sam bai San tawakkali ba."
Tana fita daga ɗakin, Ummi ta share hawayenta.Ta kamo hannun Fujeerat.
"Ki yi haƙuri yar al'barka. Addu'a ce kawai kyautar da za mu iya yi masa yanzu."
Fujeerat ta gyada kai.Amma hawayen da ke zuba daga idanunta sun ƙi tsayawa.Wani irin zafi da raɗadi ne ke cin zuciyarta.Raɗadin da sai wanda ya taɓa rasa masoyi yake iya fahimta.
***MEXICO***
A wani tsararren hotel su M.D suka sauka. Ɗakin ya kasance mai ɗauke da parlour da kuma bedroom guda ɗaya.
Suna shiga Fukhee ta faɗa kan kujera tana cewa,
"Oh my goodness, I'm tired wallahi."
M.D kuwa girgiza kai kawai ya yi ya shige cikin bedroom ɗin da ƙaramar jakar kayansa wadda bai ta kaya kala uku ba ne a ciki.
Bayan ya ajiye ta akan gado, kai tsaye ya shiga bathroom.Kusan awa guda ya ɗauka a ciki kafin ya fito sanye da bathrobe da towel a kafaɗarsa.
Da sauri ya shafa mai, ya sanya jallabiya, sannan ya shimfiɗa darduma ya tada sallah.
Sai da ya gama ibadarsa sannan ya fito parlour.
Ya tarar da Fukhee tana nan yadda ya barta, sai dai bacci ya ɗauke ta.Girgiza kai kawai ya sake yi, ya nufi landline ya kira a kawo musu abinci.
Daga nan ya dawo ya tashe ta domin ta yi sallah.Tana turo baki ta shige ciki.
Shi kuwa ya zauna yana jiranta.Kafin a kawo masa abincin ma ya tashi ya karɓo.
Bayan kusan mintuna ashirin, ta fito.
Ta canza kaya zuwa doguwar riga tare da ƙaramin mayafi.
Ya ɗago daga cin abincin da yake yi ya kalleta."Har kin yi me?"
Ta turo baki.
"Wanka da sallah mana."
Ya gyaɗa kai.
"Da kyau. Ga abincinki nan, ki ci."
Ta zauna tana ci tana satar kallonsa.
Bayan sun gama ne ya dawo ya zauna yana kallonta.
"Fukhaihat."
"Na'am."Ta amsa tana kallonsa saboda yadda ya kira sunanta cikin wata murya mai nuna muhimmancin maganar da zai yi.
"Yaya kike yin alwala?"
"Na'am?"
Ta faɗa kamar ba ta ji ba, alhali kuma ta ji shi sarai.
"Kin ji ai. Kuma kin san bana maimaita magana."
Ta ɗan turo baki kafin ta ce,
"To... ina wanke hannu, baki, fuska, hannu, kai da ƙafa."
Ya ɗan ɗaga gira.
"Kawai wankewa ake babu wata ƙa'ida kenan?"
Ta ƙara zumɓuro baki.
"Kai Yaya! Ai na yi ƙoƙari fa. Da kaina na koya, babu wanda ya taɓa koya mini."
Kallonta kawai ya yi.
Tausayinta ya kama shi ƙwarai.
Yarinya musulma amma babu wanda ya koya mata ko mafi ƙarancin ilimin addini.A zuciyarsa kuwa takaici da haushin mahaifinta suka cika shi.
"Yaya, na ji ka yi shiru."
Fukhee ta katse shi.
Ya gyaɗa kai.
"Eh, kin yi ƙoƙari sosai. Amma a ina kika ga ana yi har kika koya?"
"Wata yarinya ce a makaranta. Duk lokacin break tana yin sallah. Sai nake ɓoye wa ina kallonta."
Nan take zuciyar M.D ta karye da tausayinta."Shikenan, kina ƙoƙari sosai. Amma idan lokacin sallah ya yi zan koya miki yadda ake alwala yadda ya kamata."
Da sauri ta ce,
"Ina so Yaya. Nagode sosai."
"Har karatu ma idan kina so zan koya miki."
Fuskarta ta cika da farin ciki.
"Da gaske?"
"Da gaske. Amma sai kin mayar da hankalinki sosai, sannan ki daina waɗannan shaye-shayen."
Ta sunkuyar da kai.
"Yaya, ka bar ni ko kaɗan ne. Idan ban sha ba bana iya komai."
Ya jinjina kai.
"To shikenan. Yanzu ki je ki kwanta. Zan ɗan fita amma kafin lokacin sallah zan dawo."
"To Yaya."
Ta amsa tana miƙewa.
Sai da ta sha abin da ke sa ta bacci sannan ta kwanta.Shi kuwa M.D kusan mintuna goma bayan nan ya fita daga ɗakin.
Kamar yadda ya faɗa, tun kafin lokacin sallah ya dawo. Sai dai har lokacin Fukhee ba ta farka ba.
Komawa falon ya yi ya kunna T.V, yana jiran lokacin sallah ya cika, yayin da zuciyarsa ke ta nazarin yadda zai ceto Fukhee daga halakar da take ciki.
Yana cikin wannan tunanin ne ta fito daga ɗaki bayan ta yi wanka. Ta sake sauya kaya zuwa t-shirt mai dogon hannu da dogon wando. Ƙafafunta sanye da safa, yayin da kanta ke sanye da hular sanyi.
"Welcome back, Yaya."Ta faɗa. Hakan ne kuma ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya lula.
"Yauwa, kin tashi?" Ya Amsa da kulawa
"Eh Yaya. Kuma ka ce za ka koya min alwala, shi ya sa na fito na ga ko ka dawo."
"Okay. To bari na fara shiga toilet ɗin, zan nuna miki. Sai ki zo ki gani."
"To Yaya."Ta amsa cikin zumudi.
Da ya wuce ɗakin, ita kuma ta zauna a kan cushion tana jiransa.
A zuciyarta kuwa farin ciki ne fal.Yau ita ce za a koya wa wani abu da ya shafi addininta.Ta daɗe tana sha'awar sanin irin waɗannan abubuwa, amma tana jin kunyar tambayar ƙawayenta.
"Gaskiya na yi sa'ar miji."Ta faɗa a ranta.
Sai kuma ta tsaya.
"Kai! Wai Yaya mijina?"
Dariya ta kubce mata.
Tana son M.d tun daga ganin farko,Amma bayan aurensu da ta fahimci M.d ba ya kallon ta a matsayin mata,ta tattara ta watsar da komai itama, ko ba komai dai akwai igiyoyin aurensa a kanta,hakan kaɗai ya wadatar da ita.
Jin muryar M.D daga cikin ɗaki yana kiranta ya sa ta yi saurin miƙewa.
"Na'am Yaya."Ta amsa tana nufar ɗakin.
A bakin bathroom ta tarar da shi yana jiranta.
Yana ganinta ya shiga ciki, ita ma ta bi bayansa.
"Ba kya jin fitsari?"Ya tambayeta.
"Eh Yaya, ai yanzu na yi kafin na fito."
"Okay. Kin yi tsarki dai ko?" Ya Kara tambayarta
"Eh Yaya."
Ta amsa tana sunkuyar da kanta saboda wata irin kunya da ta tsinci kanta da ji a gabansa.
"To matso kusa. Ki yi amfani da wannan fanfon, ni kuma zan yi da wannan."Ya nuna mata.
Ba tare da musu ba ta matsa kusa.
Sai ya fara bayani.
"Da farko, abu mafi muhimmanci idan za ki yi wani ibada shi ne niyya. Wato ki kudurta a ranki abin da za ki yi. Misali yanzu kin yi niyyar yin alwala. Domin duk abin da za ki yi idan babu niyya ba ya inganta. Kamar yadda ya zo a hadisi ingantacce,Manzon Allah salallahu alaihi wa sallama yace "Dukkannin ayyuka ba sa ingantuwa sai da niyya." Kuma niyyar taki ta kasance saboda Allah ba don wani abun ba.
" Ina fatan Kin fahimta?"
"Eh Yaya."Ta amsa cike da zumuɗi.
"Yauwa Shalele. Sannan ya kamata mutum ya kasance cikin nutsuwa. Kada ya yi abu cikin gaggawa. Ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya kan abin da yake yi."
Nan ma ta gyaɗa kai.
"Sannan abu na biyu shi ne ki tabbatar kina da tsarki sannan sai ki yi Basmala. Wato ki ce Bismillah."
Ya dubeta."Faɗi mu ji."
"Busmullah."
Ta faɗa kamar yadda ta ji.
M.D ya girgiza kai.
"No. It's not Busmullah. It's Bismillah."
Ya yi murmushi kaɗan.
"It means 'In the Name of Allah' in English, ko kuma 'Da Sunan Allah' a Hausa."
"Kin fahimta?"
Ta gyada kai.
"To faɗi mu ji."
"Bismillah."
"In the Name of Allah."
"Da Sunan Allah."
Murmushi ya suɓuce masa.
"Good girl."
Ya ɗan yi dariya.
"Amma ɗaya kawai za ki faɗa. Na yi miki haka ne domin ki fi fahimta."
"To... Bismillah."
Ta amsa da sauri.
"Yauwa Shalele."
Ya kunna fanfon.
"Yanzu ki bi duk abin da kika ga na yi."
"To Yaya."
Ita ma ta kunna nata fanfon.
Sun ɗauki lokaci mai tsawo suna yin alwalar tare.
Yana yi yana bayyana mata kowane mataki cikin nutsuwa har ta fahimta sosai.
Da suka fito daga bathroom, M.D ya ce,
"Ki je ki ɗauko hijabinki."
Sai ta tsaya tana kallonsa.
"Ni ban taɓa saka hijabi ba."
Maganar ta tsaya wa Muhammad a zuciya.Wani irin tausayinta ya sake kamashi.Musamman idan ya tuna yawan kayan da ta cika trolley da su, amma babu ko mayafi guda ɗaya da ya wuce wuya.
Bai san lokacin da ya tambayeta ba.
"Fukhaihat... Daddy da Mommy ɗinki iyayenki ne kuwa? Ina nufin su suka haife ki?"
Dariya ta yi.
"Me ka gani Yaya?"
"Just answer me, Madam."
Ya faɗa fuska a haɗe.
Ta ɗaga hannayenta sama.
"Sorry Yaya. Daddy ne ya haife ni. Amma Mommyna ta rasu tun ina ƙarama. Wannan Mommy ɗin dai ita ce ta raine ni."
Ya jinjina kai a hankali.
"Okay."
Sai ya nuna mata kujera.
"Ki zauna. Bari na yi sallah. Idan na idar sai mu fita na yi miki siyayyar kayan da suka dace."
Ya dubi shigar jikinta."Saboda ba kyau a riƙa yin sallah da irin wannan shigar."
"To."
Ta amsa cikin sanyin murya.
Shi kuwa ya shimfiɗa sallaya ya tada sallah.Fukhee ta zauna tana kallonsa.
A karon farko a rayuwarta, tana jin wata irin sha'awar sanin addininta fiye da da.
✍️ UMAIMAH ADO GAYA