Free chapter · Read without an account

56

by Halima Zakariyya Haruna · LULLUƁIN BIRI

Turaki ya lumshe idanunsa a hankali, yana jin wani irin zafi na cin zuciyarsa. Zafi mai tsanani da ya kasa samo kalmar da zata iya siffanta shi. Sai dai idan zai yi kwatance, to zai ce tamkar ana rura wutar dafa naman kai ne a cikin ƙirjinsa. Wutar da ba wai tana ƙonawa kaɗai ba, tana kuma narkar da duk wata nutsuwa da ya yi tunanin ya samu.

Duk da ya rufe idanunsa, hakan bai rage nauyin da yake ji ba. A maimakon haka ma sai idanun suka ƙara yi masa nauyi. Nauyin da yake ji kamar an ɗora masa manyan duwatsu a saman murfinsu.

Haka ake ji dama? Bai sani ba, bai ma san ta yadda zai kwatanta irin halin da zuciyarsa take ciki ba.
Sai yanzu ya fahimci cewa wani lokacin farin ciki da tashin hankali idan suka zo lokaci guda, suna iya gagarar zuciyar mutum fiye da kowannensu idan ya zo shi kaɗai.

Da fari yana cikin tashin hankalin Fullo da ke hannun masu garkuwa. Yana cikin azabar ganin ta kwance tsakanin rai da mutuwa. Kwatsam Allah ya dawo masa da Mahaifiyarsa. Ya tsinci kansa a cikin farin cikin da bai taɓa sanin akwai irinsa ba. Sai kuma Fullo ta farka. Wani sabon farin cikin ya sake mamaye shi.

Yanzu kuma...
Mum ce kwance a gabansa. Idanunta a rufe, drip na ratsawa a hannunta. Ruwa na biyu da aka saka mata. Kuma har yanzu ba ta farka ba. Ba su san lokacin da zata farka ba. Ba su san me likitoci za su ce idan ta farka ba. Abin da kawai suke da shi shi ne fata. Fatan ta buɗe idanunta lafiya. Fatan kada Allah ya nuna musu wata sabuwar jarabawa bayan wannan farin cikin.

A hankali ya sake buɗe idanunsa. Sai dai ba a yadda ya rufe su ya buɗe su ba. Domin a tsakanin daƙiƙun nan kaɗan da suka shuɗe, wani mummunan tunani ya gifta masa. Tunani mai firgitarwa, tunanin da ya sa zuciyarsa yin wani irin duka.
Me zai hana idan ya ɗauke idanunsa daga kanta, ya sake rasa ta wannan karan kuma har abada, ba kamar yadda ya rasa ta shekaru da suka wuce ba.

Nan take idanunsa suka dawo kanta. Suna bibiyarta cikin tsoro da tsananin fargaba. Ɗakin ya yi shiru tsit, shiru mai nauyi. Shirun da kowacce zuciya a cikinsa take nata yaƙin fargaba da taraddadi.

Hajiya Madina na zaune kusa da gadon. Hannu ɗaya riƙe da na Hajiya Ramla. Ɗayan kuma ta zabga uban tagumi. Idanunta sun yi ja, fuskarta cike da damuwa.

A gefe kuma Zaytuna ce tsaye, ta haɗe hannayenta a ƙirji. Idanunta ƙyam akan fuskar Mum. Hawaye suna sauka a kan kumatunta ɗaya bayan ɗaya. Bata damu da goge su ba. Zuciyarta kuwa tana bugawa da ƙarfi. Bugun da har Hajiya Madina da ke kusa da ita tana jin sautin sa a cikin shirun ɗakin.

Sauran yaran ma duk haka suke. Daga wanda tun ɗazu yake jan hanci saboda kukan da ya tsaya masa a maƙoshi. Sai wanda idanunsa suka yi jawur saboda yawan zubar hawaye.
Sai Khalil da ke kai hannu lokaci zuwa lokaci yana goge fuskarsa, kamar yana son ɓoye damuwar da ke bayyane a fili.

Sai dai dukansu suna da abu guda ɗaya iri ɗaya a zuciyoyinsu. Tsoro! Tsoron sake rasa abin da suka dawo suka samu bayan shekaru masu yawa.
Turaki ya sauke idanunsa kan fuskar Mum, na ɗan wani lokaci, sannan a hankali ya lumshe su.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."
Ya furta ƙasa-ƙasa. Muryarsa ba ta da ƙarfi. Amma duk wanda yake cikin ɗakin ya ji nauyin da ke cikinta.

Bello da ke tsaye kusa da shi ya ɗan waigo ya kalle shi. Sannan ya sauke idonsa kan hannayensu da ke haɗe. Yana jin yadda Turaki ya sake matse hannunsa fiye da da. Kamar wanda yake neman wani abu da zai riƙe yake gudun kar ya tarwatse.

A hankali Bello ya matsa kusa da shi. Ya ɗaga hannu ya shafa kafaɗarsa.
"Ka samu natsuwa."
Ya faɗa cikin sanyin murya.
"Ka kwantar da hankalinka."
Sai ya ɗan yi shiru kafin ya ƙarasa da cewa,"Babu abin da zai faru da izinin Allah. Khairan in sha Allahu."

Turaki bai amsa ba. Amma furucin Bello ya gifta cikin kunnensa kamar iska mai ɗauke da wani tsohon sauti. Nan take zuciyarsa ta buga. Domin kalmomin nan, kalmomi ne iri ɗaya da ya ji awa biyu da suka wuce.
A lokacin da likita ya fito daga ɗakin da aka shigar da Mum. A lokacin da suke tsaye a waje suna jiran hukuncin da zai fito daga bakinsa. A lokacin da kowannensu yake jin kamar numfashinsa zai tsaya tsakaninsa da Bello.

Sai likitan ya kallesu ya ce,"Ku samu natsuwa. Ku kwantar da hankalinku. Na faɗa muku babu wata damuwa, barinta zaku yi ta huta kawai."

Idanunsa suna kan Turaki.
"Babu abin da zai faru da izinin Allah."
Sai ya ɗan murmusa.
"Khairan in sha Allahu. Hajiya zata farka cikin amincewar Ubangiji."

A lokacin ne Turaki ya sauke wani numfashi mai nauyi, numfashin da bai san yana riƙe da shi ba. Sai dai duk da kalaman likitan. Duk da ƙoƙarin da yake yi na kwantar da hankalinsu. Har yanzu zuciyarsa ta ƙi yarda ta natsu. Saboda awa biyu kafin wannan lokacin. Ba a wannan ɗakin yake ba, ba a gaban Mum yake tsaye ba.

Yana wani ɗakin ne, rungume da ita a jikinsa, yana shafa gashinta a hankali, tana faɗa masa cewar zafi, yana maimaita mata kalmar sorry cikin kunnuwanta.
Kuma a lokacin da ƙofar ɗakin ta buɗe. Ya ji motsin shigowar mutum. Ya ji sautin ƙafar da ta taka tiles ɗin ɗakin. Sai dai hakan ba shi yasa shi sakinta daga jikinsa ba, bai ma yi yunƙurin hakan ba.
Kamar a lokacin babu wani abu da ya fi muhimmanci a gare shi fiye da kasancewar ta a cikin hannayensa.

Don haka kawai ya miƙa wuya. Ko waye ya shigo. Ko me zai gani. Ko me zai faru. Babu abin da ya dame shi. Ko da kuwa ace Mum ko Maama ne.

Mintuna kaɗan suka wuce, shiru babu wanda ya yi magana. Wannan shirun ya isa ya gaya masa ko waye.
Domin babu wani mutum da zai tsaya yana kallonsa haka ba tare da magana ba sai Bello. Shi kaɗai!
A hankali Turaki ya buɗe baki zai yi magana. Amma furucin Bello ya katse shi.
"MT..."

Muryarsa ta fito a sanyaye. Cike da wani irin takaici da rashin jin daɗi. Duk wanda ya san Bello zai fahimci cewa a wannan yanayin ba ya buƙatar magana mai yawa. Domin idan muryarsa ta kai wannan matakin nutsuwar, to yana nufin masifar da yake son yi ta fi wadda zai yi da ihu nauyi.

Ya bawa Bello baya. Amma duk da bai waigo ba, ya san irin yanayin fuskar da ke kansa. Domin sautin murmushin takaicin da Bello ya yi ya fito ƙuru-ƙuru a cikin muryarsa, har ya fi bayyana a sautin da ya yi magana da shi fiye da yadda zai bayyana a idanunsa.

"MT tsakani da Allah ka kyauta mun? Wallahi ban taɓa tunanin haka daga gare ka ba."
Shiru ya biyo bayan maganar!
"So kake ka nuna min bani da haƙƙin sani ne?"
Ya girgiza kansa yana haɗiye yawu.

"Idan ban zama mutum na uku da zaka ɗaga waya ka kira ka sanarwa ba, zan zama mutum na biyu da ya cancanci ya sani bayan Maama da Baffa."

Muryarsa ta ɗan karye.
"Mahaifiyarmu ta dawo bayan duk shekarun nan, amma ace sai da na zo asibitin nan tukunna zan sani... Ashe banza a watse ka ɗauke ni cikin rayuwarka, haka ne matsayin amintar ta mu MT? Ka ware ni kenan kana so ka nuna min cewa ba zamu iya raba mahaifiya tare ba... A lokacin da na rasa tawa mahaifiyar, da na ɗaga waya kafin na kira kowa, kai na fara kira na sanar maka cewa Muhammad Turaki Mamanka ta rasu."

Turaki ya yi saurin rufe idanunsa. Ya san gaskiya Bello yake faɗa. Ya san bai kyauta masa ba. Ya san da ace akasin haka ne, shi ma zai ji ciwo.
Sai dai bai san ta yadda zai bayyana wa Bello irin yanayin da ya tsinci kansa a ciki ba.
Tun daga lokacin da ya ga Mum, komai ya rikice masa. Tunaninsa. Numfashinsa. Zuciyarsa. Har ma da ikon yanke shawara. Yana jin kamar wani ne ya zo ya janye shi daga rayuwar da ya saba, ya jefa shi cikin wata sabuwa da bai shirya mata ba.

A yau komai ya zo masa lokaci guda ne, ya yi farin cikin da bai taɓa yi ba. Kuma a yau ɗin ne ya ɗanɗani tsoron da bai taɓa ji ba. Tsoron rasa ɗaya! Farin cikin samun ɗaya!.
Ta yaya zai tuna da waya? Ta yaya zai tuna da sanar da kowa?

A hankali ya buɗe idanunsa, Fullo na kwance a jikinsa. Numfashinta mai ɗumi yana bugun gefen wuyansa. Shi kuma yana jin kalaman Bello suna sauka masa ɗaya bayan ɗaya.
Da ƙyar ya haɗiye abin da ya tsaya masa a maƙoshi. Akan hakan bai da wasu kalamai ga Bello wanda ya wuce,"Ka yi haƙuri Bello."

Shirin da ya yi kamar yana neman wasu kalmomin ne, amma ya rasa.

Daga ƙarshe ya sake cewa,"Ka yi haƙuri Bello, ban da wata hujjar kare kai. Ban da wani uzuri da zai sa ka daina jin haushi na."

Ya sauke numfashi.
"Amma na san idan ka natsu... zaka fahimce ni."

Bello ya daɗe yana kallonsa. Sai daga ƙarshe ya girgiza kansa kawai. Ba wai ya huce gaba ɗaya ba ne. Amma ya fahimta. Saboda shi ne Bello. Kuma shi ɗin ne ya san Muhammad Turaki ciki da bai, duk wanda ya yiwa Turaki irin sanin da ya yi masa, zai fahimci cewa yau ba ranar da za a nemi cikakken hankali a wajensa ba ne.

Turaki ya sake maida hankalinsa kan Fulani. Har yanzu tana manne a jikinsa, tana ta sauke numfashi cikin natsuwa alamar lafiya ta samu.
Ba don halin ciwo ba, ya san rikicinta ba zai taɓa sawa ta zauna a jikinsa cikin nutsuwa ba.

Sai ya ji ta ɗan motsa. Da sauri ya matsar da bakinsa kusa da kunnenta.
"Ki koma bacci..."

Ya raɗa mata a hankali.
"Please."

Murfin idanunta ya motsa, Da ƙyar ta buɗe baki ta ce,"Ruwa..."

"Kike so ki sha?"

A hankali ta gyaɗa masa kai. Sunan Bello ya ambata kawai, tare da ce masa ruwa kamar yadda itama ta faɗa masa.
Kuma Bello ya gane duk da bai ji ƙarin bayani ba. Ya juya zuwa dispenser ɗin ɗakin. Cikin daƙiƙu kaɗan ya dawo da cup ɗin ruwa ya miƙa masa.

Turaki ya karɓa ba tare da ya ce masa komai ba, ya sauke idanunsa kan Fulani. Ya naɗe ƙafa yana bawa kansa damar zama sosai akan gadon.
Ya tallabo kanta sosai kamar yadda ake yiwa jariri idan za a shayar da shi.

A hankali ya kai cup ɗin zuwa bakinta.

"Ki sha." Ya faɗa a tausashe, ganin ba zata iya buɗe bakin ba, yasa hannunsa ɗaya ya buɗe laɓɓan nata tukunna ya kafa mata cup din, amma duk da haka bata iya sha ba. Saboda haka kawai zuciyarsa ta yanke masa yin abu ɗaya, ya zuba ruwan a bakinsa, tukunna ya kai bakinta ya kama leɓen ya buɗa, sannan ya shiga zuba mata ruwan a hankali, sai ga shi ita ɗin ma tana haɗiyewa a hankali, tamkar wadda ke shan ruwa da ga kofi.

A wannan lokacin ne Bello ya kauda kansa gefe, ya juya yana ba su baya. Ba don yana son fita daga ɗakin ba. A'a! Sai don ba zai iya tsayawa yana kallon yadda Turaki ke shayar da Fullo ruwa daga bakinsa ba.

A rayuwarsa ya ga abubuwa da yawa. Ya ga ma'aurata. Ya ga masoya. Ya ga mazajen da suke ikirarin suna tsananin son matansu.
Amma wannan? Wannan daban ne.
Wannan ba irin soyayyar da ake furtawa da baki ba ce. Ba irin wadda ake nunawa mutane ba ce. Wannan irin soyayya ce da take fitowa kai tsaye daga cikin zuciya ba tare da mai yinta ya shirya ba, irin soyayyar da ke sa mutum ya manta da kansa ya manta da kowa da komai ta yi ta sarrafa shi yadda take so.

Ya haɗiye wani abu a maƙoshinsa. A lokacin ne tunaninsa ya janye daga ɗakin. Ya koma baya lokacin da ya iso asibitin.
A lokacin bai shigo asibitin da niyyar komai ba sai yiwa Turaki masifa. Tun daga parking lot yake ta haɗa kalaman da zai farfaɗa masa.

_"Wato kai baka da hankali ko? Yaya za ayi preparation na tafiya United States cikin ƙasa da awa ashirin da huɗu? Alhalin ita wadda za a je saboda ita bata taɓa yin passport ba. Yanzu kuma tana kwance a gadon asibiti... Kai fa ɗan iska ne MT, wai yaronka ma ka mayar da ni ne dan ubanka. Kai me yasa ba zaka je ka yi da kanka ba, kuma tsabagen ma ka gama raina ni, kai da kanka ba zaka kira ka mun bayani ba, sai Zaytuna zaka sa. Shege uban ƴan jin kai, idan ka yi wasa sai na fallasa wanna auren sirrin naka ta fashe da kai ɗaya."

Yana ta murmushi shi kaɗai saboda yadda ya san zai takurawa Turaki.
Sai dai yana isowa cikin reception komai ya canja. Domin tun daga nesa ya hangi Samha ita da wata nurse suna tura gadon marasa lafiya da gudu, fuskokinsu a rikice.

"Samha!"
Ya kira sunanta da ɗan ƙarfi. Sai dai bata tsaya ba.
"Samha!"
Ya sake kira yana ƙara saurin tafiyarsa, har yana ƙoƙarin yin tuntuɓe wajen tare hanyar tasu.

Amma Samha bata ji shi ba, bata san ma yana yi ba don sam bata lura da shi ba. Ita da Nurse ɗin suka wuce shi.
Sai ya ji wani irin faɗuwar gaba ya saukar masa. Faɗuwar gaba irin wadda mutum kan ji idan zuciyarsa ta rigaya sanin wani abu kafin ƙwaƙwalwarsa.
Nan take zuciyarsa ta fara kawo masa munanan tunani. Fullo? Fullo ce? Ko wani abu ya faru ne bayan gama wayarsu da Zaytun?

Numfashinsa ya fara nauyi. Nan ya ƙara saurin tafiyarsa. Yana shan kwanar corridor ya hango inda suka nufa da gadon. Sai dai abin da ya gani ya sa shi tsayawa cak.
Zaytuna ce! Durƙushe a ƙasa. Hannayenta a saman kanta. Kukanta na amsa kuwwa cikin wajen. Kukan da Bello bai saba jin ana yin irinsa ba sai idan mutuwa ce ta ɗauke wani jigo na rayuwar mace. 

Da sauri ya ƙarasa gareta.
"Zaytun!"
Ya kirata da muryar tashin hankalin da shima ya shiga a yanzu. Jin muryar tasa ta ɗago ta dubesa. Idanunta duk sun kumbura da hawaye.

"Me ya faru?"
Ba ta amsa ba. Kuka kawai take ruzga.
"Zaytun me ya faru?!"
A wannan karon ya ɗaga murya. Da ƙyar ta iya haɗiye kukan.
"Hamma Bello..."
Muryarta na rawa ta furta hakan.

Dole ya durƙusa gabanta. Ya kai hannu zai kama kafaɗunta sai ya dunƙule hannu ya fasa.
"Ki yi magana mana."

Muryarta a karye ta fito da cewa,"Bana so ta mutu."

Gabansa yay tsananin sake faɗuwa. Kuma nan take sunan mutum guda ya wanzu cikin kansa. Maama!

Kai tsaye sunan Hajiya Madina ya faɗo masa. Domin shi har lokacin bai san komai game da dawowar Hajiya Ramla ba.

Don haka cikin firgici kuma da sauri ya tambaya,"Maama! Me ya samu Maaman? Ina suka kai ta?"

Zaytuna ta ɗago tana kallonsa. Sai ta girgiza kai. 
"Ba Maama ba..."
Bello ya ƙara ruɗewa.
"To wa?"
"Mum."
Bello ya yi shiru.
"Mum kuma? Wace Mum?"
Ta fashe da sabon kuka.
"Mum ɗinmu..."

Bello ya tsaya cak yana kallonta. Tamkar ba Hausa ta yi masa ba, juye masa ta yi tamkar wani yare ce da bai taɓa ji ba. Ya maimaita.
"Wacce Mum kike magana Zaytun?"
Sai ta ƙara fashewa da kuka tana cewa,"Mum ɗinmu da ta tafi ta barmu."

Lokaci guda Bello ya ji tamkar duniya ta tsaya. Kamar wanda ya manta yadda ake motsi. Kunnuwansa suka fara kaɗawa. Zuciyarsa ta yi wata irin bugawa da shiga mamaki da al'ajabi. Wanda ya ɓata sama da shekara ashirin da biyar shine za a ce ya dawo? Anya ƙwaƙwalwar yarinya bata sami damuwa ba.

Farko ya rasa me zai sake cewa da ita. Don bai san kalaman da zai harhaɗo don sake faɗar wani abun ba. 
Kuma cikin rikicewa ta shiga gaya masa komai, a ƙarshe ta kama inda indar.
"Shine, shine, shine..."
"Shine what Zaytun?"

Ta haɗiye wani abu.
"Shine ina tureta ina ce mata bana sonta. Ina ce mata ba zan yafe mata ba. Shine ta yanke jiki ta faɗi. Ina girgizata ta ƙi buɗe ido, an zuba mata ruwa bata farka ba, Hamma Bello bana so na sake rasata, do something please..."

A wannan karon Bello bai jira jin ƙarshen maganar ba, ya miƙe tsaye kamar wanda aka harba. Ya damƙi hannunta bisa umarnin zuciyarsa.
"Mu je."

Haka suka shiga bin corridor ɗin asibitin. Daga ɗaki zuwa ɗaki. Daga sashe zuwa sashe. Har suka iso ƙofar wani ɗaki. Nan suka tarar da su hajiya Madina curko curko, kaf ɗinsu suna kaiwa da komowa kowa da tashin hankalinsa, addu'arsu duk bata ɓoyuwa daga bakinsu.

Mintuna suna tafiya kamar awanni, ƙofar ɗakin ta buɗe.
Likita ya fito yana zare safar hannunsa. Sannan ya kallesu dukka, tukunna ya ce,"Da wa zan yi magana a cikinku?"

Hajiya Madina ta juyo tana duban wurin da Turaki ya kamata ya kasance amma babu shi. Ta sake dubawa har lokacin babu shi.
Sai ta ce,"Ina Mai Babban Suna?"

Sameer ya ce,"Tun ɗazu fa da ya tafi har yanzu bai dawo ba... Bai san ma abin da ya faru ba."

Ta sauke numfashi. Sai ta juya ta kalli inda Bello yake tsaye.

"Bello."
"Na'am Maama."
"Bi bayan likitan."

Ya juya ya bi bayan likitan da sauri, har zuwa office ɗinsa. Likitan ya zauna, ya buɗe file ɗin da ke gabansa, sannan ya ɗago yana kallon Bello.

"First of all, ku kwantar da hankalinku. Alhamdulillah, for now babu wani abu da yake nuna mana cewa condition ɗinta zai zama dangerous in sha Allah."
Ya sauke numfashi kafin ya ci gaba.
"Abin da ya faru da ita ba ordinary sickness ba ne. Jikinta da mental state ɗinta sun shiga severe trauma ne."

Ya sake kallon takardun da ke gabansa.
"Daga tests and observations da muka yi, mun gano cewa ta daɗe tana rayuwa cikin extreme stress, fear and emotional pressure. Jikinta ya yi weak sosai saboda poor nutrition da kuma lack of proper care na tsawon lokaci. Haka kuma akwai signs na sleep deprivation and chronic fatigue."

Ya ɗan dakata.
"Lokacin da ta shiga wannan emotional shock ɗin, musamman biyo bayan abin da aka faɗa mata, jikinta bai iya handle na pressure ɗin ba. Shi ya sa Heart rate ɗinta ya yi spike, blood pressure nata ya tashi lokaci guda, sannan jikinta ya shiga severe shock response."

Bello da ya tattara hankalinsa gaba ɗaya ya ce,"Doctor matsalar da ta shiga daga kalaman da aka faɗa mata ne kenan, I mean idan an yi solving emotional issue ɗin nan, zata yi recover completely?"

Likitan ya girgiza kai a hankali.
"Not exactly."
Ya ɗan gyara zamansa.
"Abin da aka faɗa mata wasn't the real problem. It was just the final trigger. Kalaman sun zama kamar ɗigon ruwa na ƙarshe da ya sa kofin da ya daɗe yana cikowa ya cika ya zube."

Ya ɗora file ɗin a gefe.
"Muna kuma zargin tana fama da Post-Traumatic Stress Disorder... PTSD. Wato irin ciwon da mutum yake samu bayan ya fuskanci abubuwa masu tsananin firgita rai ko azaba na dogon lokaci. Irin waɗannan experiences ɗin suna barin scars a mind da emotions, ko da jiki ya warke."

Ya haɗa hannayensa wuri guda.
"That's why ba lafiyar jikinta kaɗai za mu kula da ita ba. Her psychological and emotional wellbeing is equally important."

Daga ƙarshe ya ce,"Yanzu muna sa ran idan Allah ya so zata farka lafiya. Amma tana buƙatar kulawa sosai, da kuma natsuwa. Saboda jikin nata ya yi yaƙi da abubuwa da yawa kafin ya kai wannan matakin."

Bello ya sauke numfashi a hankali bayan ya dawo daga duniyar tunanin da ya yi. Ya ɗan waigo, har yanzu Turaki yana manne da Fullo. Ya kwantar da gefen fuskarsa cikin gashinta, Idanuwansa a lumshe, kamar wanda ya gaji da yaƙi da duniya gaba ɗaya, ya samu wurin hutawa na ɗan lokaci.
Bello ya lumshe ido, ya ji wani irin tausayinsa ya cika masa zuciya.

Yana tunanin ta yadda zai sanar ma Turaki abin da ke faruwa. Kamar dai yana tsoron sanar masa condition ɗin da Mum ke ciki. Sai da ya sha fama da kalaman bakinsa kafin ya iya cewa cikin murya mai natsuwa.
"MT..."
Bai amsa ba.
Don haka ya sake kira.
"Am Am... MT."

Wannan karon Turaki ya ɗan motsa kansa kaɗan kawai alamar yana sauraro. Bello ya haɗiye yawu.
"Ina ga ka kwantar da ita ka zo mu je..."
Bai ƙarasa ba.
Turaki ya katse shi ba tare da ya buɗe idonsa ba.
"Ka je kawai Bello."
Ya ɗan ja numfashi.
"Abu ɗaya nake buƙata a wurinka. Ina so a fara processing komai yau. Gobe zamu fita da Fulani zuwa America. Tana buƙatar manyan likitoci da cikakkiyar kulawa."

Bello ya tsaya yana kallonsa na wasu sakanni. Sai ya ɗan girgiza kansa. Murmushin takaici ne ya kuɓuce masa.

"Sai ka yi haƙuri, amma wannan tafiyar ba zata yiwu a gobe ba."

A karo na farko Turaki ya buɗe idanunsa babu shiri. Ya ɗago kansa daga gashin Fullo ya waiga ga kalli Bello.
"Why?"
Bello ya yi guntun murmushi.
"Why?"
Ya maimaita.
"Saboda Fulani ba parcel ba ce da zaka ɗauka a saka a jirgi kawai."
Ya matsa kusa da gadon.
"Ta taɓa yin passport?"
Turaki ya yi shiru.
"Ta taɓa fita ƙasar nan?"
Har yanzu bai amsa ba.
Bello ya ɗaga hannayensa sama.
"To ga amsar ka nan. Passport babu. Visa babu. Medical clearance babu. Travel documents babu. Medical transfer approval babu."

Ya ɗan tsayar da numfashi.
"Ko da kuɗinka zai iya motsa duwatsu ne MT, akwai wasu abubuwa da lokaci ne kawai ke yin su. Ni ma da farko haka na yi tunanin komai zai yiwu, but da na kira waya abin da suka gaya min shi ne fastest possibility ma ba gobe ba ne."

Turaki ya zuba masa ido kawai.
Bello ya ƙarasa da cewa,"So ka kwantar da hankalinka. Za mu yi komai ɗin, amma ba cikin awa ashirin da huɗu ba."

Ya faɗa masa gaskiyar lamarin kai tsaye. Domin tun kafin ya iso asibitin, ya riga ya kira immigration officer ɗin da ke kula masa da duk wasu harkokin passport da visa. Sai dai amsar da ya samu ba ita ce yake son ji ba.

"Sir, ko da emergency case ne, akwai wasu procedures da ba za a iya tsallakewa ba."
Muryar officer ɗin ta fito cikin nutsuwa.
"Biometrics dole ne a yi. Verification ma dole ne. Ko da za a yi express processing, ba za a iya kammala komai cikin awa ashirin da huɗu ba."

A lokacin Bello ya jingina kansa da kujerar motarsa, yana kallon sama na wasu sakanni. Ba mamakin abin ya ba shi ba. Ya san akwai wuraren da kuɗi ke aiki, amma kuma ya san akwai wuraren da tsarin tsaro ke da nasa ƙa'idodin.

Duk da haka ya sake tambayar,"What's the fastest possible timeline?"

Officer ɗin ya ɗan yi shiru kafin ya ce,"Idan za a hanzarta komai, maybe within few days. Amma akwai wani abu da za mu iya yi. Idan patient ɗin ba za ta iya zuwa office ba, za mu turo mobile biometric team zuwa asibitin. Za a ɗauki fingerprints, passport photograph da sauran bayanai a can."

Bello ya gyara zamansa yana sauraro.
"Approval process fa?"
"That one must follow due process Sir."

A nan ne Bello ya fahimci cewa babu yadda za a yi a tashi daga Najeriya cikin ƙasa da awa ashirin da huɗu kamar yadda Turaki yake fata. Kuɗi na iya hanzarta hanya... Amma ba ya share hanya gaba ɗaya.
A irin waɗannan harkoki na passport da tsaron ƙasa, akwai matakan da dole sai an bi su, ko da kuwa emergency ne.

Shi ya sa daga ƙarshe ya haƙura da gardama. Ya dai ce musu su hanzarta duk abin da za a iya hanzartawa. Domin ko kwanaki uku ma, a wajen Muhammad Turaki, sun zamar masa kamar shekaru uku ne.
Haƙurin da ya ba Turaki ya san ya wadatar, tsakaninsu akwai wata irin amana da fahimtar juna da ba sa buƙatar dogon bayani da hujjah. Sau da yawa idan ɗaya ya ce abu guda, ɗayan kan fahimci sauran maganganun da ba a furta ba.

Don haka sai ya sauke numfashi ya sake cewa,"MT ka kwantar da ita ka taso mu je."

Turaki ya girgiza kai a hankali.
"Ka je kawai Bello. Tana jin zafi, ina ƙoƙarin rage mata zafin ciwon da take ji."

Ya ɗan matseta kaɗan a jikinsa.
"Ka barni a tare da ita don Allah."

Bello ya yi shiru na ɗan lokaci, Sannan ya ce cikin sanyin murya,"Ba zan barka ba MT, dole ka tashi. Saboda yanzu Mum ma na buƙatar ta buɗe ido ta fara yin kwalli da kai akan gadon da take kwance, bayan yanke jiki da tayi ta faɗi."

Kamar walƙiya haka maganar Bello ta haska masa. Ya ɗago kansa da sauri. Lokaci guda dukkan launin fuskarsa ya sauya. Hannayensa suka ƙara matse Fullo ba tare da ya sani ba. Numfashinsa ya tsaya cak a ƙirjinsa. Ganin yadda idanunsa suka sauya ne ya sa Bello saurin kama kafaɗarsa.

"MT..."
Ya kira da ƙarfi kaɗan.
"Samu nutsuwa don Allah."
Ya ɗan matsa kusa da shi.
"Just recite Ya Hayyu Ya Qayyum."
Turaki ya runtse idanunsa da ƙarfi.
"Ya Hayyu Ya Qayyum..."
Ya maimaita a hankali.
"Ya Hayyu Ya Qayyum..."
A karo na biyu.
Sai ya ji numfashinsa ya fara dawowa daidai-daidai. A karo na uku kuma zuciyarsa ta ɗan samu natsuwar da zata ba shi damar tsayawa a kan ƙafafunsa. Ba don ya so ba. Ba don ya shirya ba. Amma dole ya mayar da Fullo ya kwantar akan gadon.

A hankali ya kwantar da ita saman gadon. Har lokacin idanunsa na kanta.
Ba yadda zai yi ne kawai, amma da sai ya goyata ya tafi da ita. Ya kwantar da ita a gefen Mum, sannan ya zauna a tsakiyarsu yana jinyar su duka biyun.

Bello ne ya kama hannunsa. Kuma Turaki bai ƙi ba, ya bishi kawai. Domin yana jin kamar ƙafafunsa sun manta yadda ake tafiya. Suka fito daga ɗakin, Suka nufi room ɗin da aka kwantar da Mum. 
Sai dai suna isa bakin ƙofar. Suka yi karo da Dr Habib da ya sake duba lafiyarta, yana fitowa daga ɗakin. Bayansa kuma Baffa ne ke biye da shi cikin sassarfa.

****
Kuka take yi sosai a saman dardumar da take. Ta ɗaga hannayenta sama tana roƙon Ubangijin talikai cikin tsananin ƙanƙan da kai.
A wannan lokacin babu wani ƙarfi da take ji a tare da ita. Babu wata dabara. Babu wata hanya da za ta iya bi domin ta taimaki ƴarta. Abin da take da shi kawai shi ne addu'a.

Addu'ar da take fitowa daga cikin zuciyar mahaifiya. Tsawon kusan awa biyu da ƴan kai babu abin da take yi sai roƙon ubangiji cikin kuka. Wani lokaci sai ta yi shiru tana jin kamar kalmomin sun ƙare mata, amma da zarar ta tuna Fullo kwance a asibiti, sai wata sabuwar addu'ar ta sake fitowa daga cikin zuciyarta.

Duk da sanyin AC ɗin da ke ratsawa a cikin parlon, fuskarta sharkaf take da hawaye da gumi. Cikin muryar da kuka ya sauya, ta sake ɗaga hannuwanta.
"Ya Zul-Jalali wal Ikram... Rai da lafiya dukka suna hannunka. Allah dan girman mulkinka da buwayarka ka ba wa Halimatu lafiya. Ka sa ta farka cikin ƙoshin lafiya. Ya Allah yadda muka rabu tsawon shekaru, sannan ka sake haɗa fuskokinmu bayan wannan dogon lokacin, Allah kada ka sake raba ni da ita. Ya Rahmanu, ya Rahimu... ba don ni ba. Ba don cancantata ba. Amma saboda rahamarka da soyayyar da ke tsakaninka da fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, ka ji kukana. Ka dubi raunin zuciyata. Ka sa ƴata ta buɗe idanunta lafiya."

Ta dafe ƙirjinta.
"Allah ina son na sake rayuwa da ita. Ina son na ji daɗin ƴata. Ina son na ga aurenta. Ina son na ga jikokina daga gareta. Ya Hayyu Ya Qayyum... kada ka katse min wannan burin."

Kalaman nata suka ƙare cikin wani irin kuka mai karya zuciya. Yusuf ya cika bakinsa da iska ya fesar a hankali. Tun ɗazu yana kallonta. A yau ya sake fahimtar cewa idan zuciyar mutum ta kai ƙarshen ƙarfin da take da shi, wajen Allah take komawa. Ya waiga ya kalli Kaka. Ita ma kanta jingine yake a bango, tasbaha a hannunta, laɓɓanta suna motsi da ambaton Allah. Sai tausayinsu ya ƙara kama shi.

A hankali muryarsa ta ratsa cikin shirun ɗakin ya ce,"Na samu kira daga asibiti."
Nan take duk idanu suka dawo kansa.
Ya ɗan yi murmushi."Doctor Anas ya ce ta farka."

Kamar iska ta gifta a wurin. Numfashin da kowa yake riƙe da shi ya kuɓuce lokaci guda.
"Alhamdu Lillah..."
Kalmar ce ta fara fitowa daga bakin Kaka kafin kowa. Sai kuma ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta. Hawaye suka sake kwaranya. Amma wannan karon, hawayen godiya ne ga Allah.

Yusuf ya ci gaba.
"Ta farka lafiya. Alhamdu Lillah ba kamar yadda muka zata ba. Sai dai yanzu tana bacci. Amma baccin hutu ne, ba wani abu mai hatsari ba."

Da jin hakan sai wurin ya kaure da hamdala.
"Alhamdu Lillah."
"Alhamdu Lillah."
"Alhamdu Lillahi Rabbil Alamin."

Kaka ta miƙe da sauri kamar wadda aka saka wa lantarki. Ta fara naɗe dardumarta cikin gaggawa.
"Ni kam ba zan iya zama a nan ba. Mu tafi tare yanzu."

Ta faɗa tana share hawayenta. A daidai wannan lokacin ne Mommi ta shafa addu'ar. Ba ta ce komai ba. Ba ta kalli kowa ba. Ba ta jira kowa ba.
Ta miƙe tsaye.
Ta nufi ƙofar parlo da wani irin sauri. Saboda ita kaɗai ta san abin da ke cikin zuciyarta. Tsoro ne! Farin ciki ne! Fargaba ce! Fata ne!

Da kuma wani irin raɗaɗin da bai da suna. Domin ko da an ce mata Halimatu ta farka. Har yanzu zuciyarta ba ta gama gasgatawa ba. Sai ta ga ƴar tata da idanunta. Sai ta ji muryarta. Sai ta taɓa ta. Sai lokacin ne kawai zuciyarta zata amince cewa Allah ya amsa addu'arta.

Kuma yayin da take isa bakin ƙofar, Wata kalma guda ɗaya ce ta maimaita a cikin zuciyarta.
"Alhamdu Lillah..."

Waigowa ta yi tana kallon Yusuf da har yanzu ke tsaye bai motsa ba, kamar ba yanzu zai je ya ƙara bincikar lafiyaf ƴartata ba.
Ta sauke numfashi a hankali sannan ta ce,"Ko zaka bani kuɗin mota na tafi?"

Murmushi mai faɗi ya kubce wa Yusuf.
Shi bai san cewa a wannan lokacin Mommi ji take kamar idan ba ta tashi ta tafi ba zuciyarta zata fito daga ƙirjinta ba. Duk da tana jin kamar mafarki take, kuma duk da cewa har yanzu akwai abubuwan da ba su da amsa, amma lamarin Allah ya wuce gaban mamaki da duk wani tunanin ɗan Adam.

Ta yi shekaru tana addu'a. Ta yi shekaru tana kuka. Ta yi shekaru tana kwanciya da fatan wata rana zata sake ganin fuskar ƴaƴanta da mahaifiyarta.
Yanzu kuma ga shi...
Allah ya nuna mata abin da ita kanta ta kusa daina tsammani. Shi ya sa lokacin da take tsaye tana kallon Fullo ta cikin glass ɗin ɗakin da aka kwantar da ita, ta ji kamar ƙafafunta sun daina ɗaukarta.

Kamar zuciyarta zata tarwatse saboda tsananin farin ciki da kiɗima. Yusuf yana ta magana.
"Mommi tukunna dai. Yanzu DNA nake so ayi muku. Shi ne zai tabbatar mana komai. Domin Allah yana halitta masu kama da juna da yawa. Zai yiwu wata yarinya ce mai tsananin kama da ke..."

Muryarsa na shiga kunnenta. Amma zuciyarta tana wani wuri daban. Tun kafin Yusuf ya gama maganar, tun kafin a ambaci DNA. Tun kafin wani ya ce mata komai. Allah ya riga ya saka wani abu a cikin zuciyarta.
Wani tabbaci. Wata irin natsuwa. Wani irin abu da ba a iya bayyana shi da kalmomi. Ai uwa ba wasa ba ce. Lokacin da tafin hannunta ya taɓa glass ɗin nan. Lokacin da idanunta suka sauka kan fuskar Fullo.
A wannan daƙiƙar Allah ya raya wata igiya da ta daɗe a yanke. Igiyar da ke tsakanin uwa da ɗiyarta. Igiyar da ba nisa ke iya tsinkar da ita ba. Ba shekaru ke iya goge zanenta ba. Ba duniya baki ɗaya ke iya datse ta ba.

Hawaye suka cika mata ido. Har ta ɗaga ƙafa da niyyar nufar ƙofar ɗakin. Da alama ma ba zata iya jira ba. Sai dai cikin sauri Umma ta riƙo hannunta.

"A'a..."
Ta faɗa cikin tausasasshiyar murya.
"Ba haka ake gode wa Allah da ni'imarsa ba."
Mommi ta waigo tana kallonta. Umma ta dafa kafaɗarta.
"Ki fara gode wa wanda ya dawo miki da abin da kika rasa. Idan har kin amince a ranki cewa Allah ne ya nuna miki ƴarki, to ki fara yi masa godiya. Ki fara yi masa sujudush-shukr. Domin ni'ima idan ta zo, godiya ce take ƙara mata albarka. Kuma bala'i idan ya tafi, godiya ce take tabbatar da cewa bawa ya gane daga wajen wa taimakon ya fito."

Kalaman Umma suka sauka a zuciyar Mommi kamar ruwa mai sanyaya wuta.
Nan take ta ji kunya. Kunya irin ta bawa da ya kusa mantawa da Ubangijin da ya amsa masa addu'ar da ya yi shekaru yana yi. Kafin ta sake cewa komai. Sai ta juya a hankali. Ta nufi gefe guda sannan ta durƙusa.

Hawaye na gangaro mata, ta kifa goshinta a ƙasa. Sujudush-shukr. Ba addu'ar neman wani abu ba. Ba addu'ar kuka ba. Sai godiya kawai.
"Alhamdu Lillahi Rabbil Alamin..."

Ta furta cikin kukan da ya zo mata.
"Alhamdu Lillahi kama yanbaghi lijalali wajhika wa'azimi sultanik..."

Hawayenta suka jiƙa tiles ɗin wurin. A karon farko bayan shekaru masu yawa, ba addu'ar neman Allah ya maidata cikin yaranta ba tare da ta raɓi duniyar Hayyo take yi ba. Addu'ar godiya take yi. Saboda Allah ya nuna mata cewa idan ya ce abu zai faru. Ko duniya baki ɗaya ta ce ba zai yiwu ba. Shi kaɗai ne mai ikon cewa,"Kun..." Sai abin ya kasance.

A wannan lokacin da Turaki ya saki hannun Mommi ya nufi mahaifiyarsa. Yusuf ne ya matso wajen Mommi. Matar da ta zauna tare da su tsawon lokaci. Matar da ya san tana ɓoye wani babban sirri. Matar da tun farkon ganin hoton Fullo jikinsa ya kasa amincewa cewa kamanceceniyar da yake gani ta zama bazata.

Ya buɗe baki zai yi mata maganar da yake ta so ya yi mata tun da jimawa, sai kuma kalmomin suka ƙi fitowa.
Saboda bai san ta inda zai fara ba. A wannan lokacin Nuratu ce ta matso, a hankali ta kama hannun Mommi.

"Mommi please mu ɗan isa can."
Ta faɗa cikin sanyin murya. Mommi ba ta yi musu ba, kawai ta bi ta. Har suka isa dab da glass ɗin ɗakin da aka kwantar da Fullo.
A hankali Nuratu ta sauke numfashi, ta juya tana kallon Mommi.

"Har yau bamu san cikakken labarinki ba Mommi."
Ta fara magana cikin nutsuwa.
"Tsawon zaman da kika yi tare da mu... kin kasa bayyana mana komai akanki. Ke kaɗai kika san dalilin da yasa kika zaɓi yin hakan."

Ta sauke numfashi. "Sai dai yau ina son ki taimaka min."
Mommi ta ji gabanta ya faɗi, Wani irin faɗuwar gaba. Irin wanda ba ya zuwa sai idan wani abu mai girma yana dab da faruwa. Tun daga lokacin da ta ga Turaki. Tun daga lokacin da ya riƙe hannunta. Tun daga lokacin ta ji zuciyarta tana bugawa ba bisa ƙa'ida ba. Ta fara jin kamar ƙaddara tana shirin buɗe wani babi da ta daɗe tana gudun karantawa. Ta ɗan haɗiye yawu.

"Ina jinki Nuratu. Idan har tambayoyinki na da amsa daga bakina... zan amsa miki."

Nuratu ta ɗan gyara tsayuwarta.
Sannan ta ce,"Mommi ke uwa ce?"
Tambayar ta sauka tsakanin su kamar jifan dutse. Mommi ta ɗan ɗaga gira alamar rashin fahimta. Nuratu ta ci gaba.
"Akwai mata masu shekarunki da yawa da Allah ya jarabce su da rashin aure."

Ta sauke numfashi. "Ban sani ba ko kina ɗaya daga cikinsu."
Mommi ta girgiza kai a hankali lamar a'a. Sai kuma ta ce,"Ni uwa ce."
Muryarta ta fito da wani irin nauyi da kuma rauni.
"Uwa ta gaskiya. Macen da ta haifi yara uku ta hanyar auren sunnah."

Idanuwan Nuratu suka ɗan buɗe. Mommi ta maida kallonta cikin glass ɗin ɗakin.
"Na rayu a gidan aure. Gidan auren da ya cika da tarin ƙalubale. Gidan auren da rashin miji na gari ya mayar da shi wata irin jarabawa mai wahalar cinyewa."

Ta girgiza kai kaɗan.
"Kada ki zurfafa tambayoyinki Nuratu."
Shiru ya biyo baya na wasu sakanni.
Sai Nuratu ta sake cewa,"Yaran naki suna raye?"

Mommi ta lumshe ido.
"Suna raye a lokacin da na tafi..."
Ta buɗe idanunta a hankali.
"Aƙalla hakan shi ne abin da nake addu'ar ya cigaba da kasancewa tsawon shekaru."

"Kuma a ina suke?" Nuratu ta tambaya.
Mommi ta girgiza kai. "Ba sai kin san inda suke ba."

Ta ɗan yi murmushi mai ciwo.
"Yarana uku. Ɗa namiji ɗaya. Ƴaƴa mata biyu."
Numfashinta ya ɗan sarƙe.
"Babbar yarinyata ta rasu."
Ta faɗa da wata murya da ta nuna har yanzu ciwon yana sabo.
"Abdulhamid wataƙila yanzu ya zama babban mutum."

Sannan muryarta ta ƙara yin ƙasa.
"Sai autata. Halimatu."

Sunan ya fito daga bakinta kamar addu'a take, kamar kuka.
"Ban san a wacce irin rayuwa take ba. Ban san ko tana cikin farin ciki ko akasin haka ba. Duba da irin uban da ubangiji ya jarabceta da samu."

"Halimatu?" Nuratu ta maimaita.
Sannan ta ɗaga hannunta ta yi nuni zuwa cikin ɗakin.
"Mommi wannan ce Halimatu?"

Lokaci ɗaya numfashin Mommi ya tsaya. Ƙwayar idanunta ta koma kan fuskar Fullo. Ba labari ba. Ba zato ba.
Da idon uwa. Da idon da ya yi shekaru yana nema. Da idon da bai taɓa daina jira ba. Kuma a wannan karon. Ƙafafunta suka kasa motsi. Numfashinta ya tsaya. Zuciyarta kuma ta furta suna guda ɗaya.
"Autah..."


Akwai comment section a ƙarshen charpter da zaku iya faɗin ra'ayoyin ku. wurin da aka rubuta discussion shine wajen comment.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol