Free chapter · Read without an account
25
by Rufaida Umar · ALWASHI 2
ALWASHI
50
Bai ga saƙon Haseenah ba sai yamma bayan an kammala daurin aure da hotuna da Amarya da iyaye. Kansa dake ciwo ga kuma bacci ya sanya shi komawa masaukinsa na ɗakin hotel da suka kama, koda ya yi wanka bayan ya yi sallar la'asar ya ɗan runtsa ba don yana son bacci a lokacin ba, sai domin fin ƙarfinsa da ya yi. Sai wuraren ƙarfe shida ya farka. Wayarsa ya soma jawowa yana daga kwance a saman gado. Saƙonni suka fara shigowa har da na missedcalls. Ganin cikin whatsapp notifications har da saƙon Haseenah ya sa shi tafiya kai tsaye ya buɗe. Hotuna ya gani da suka ɗauki hankalinsa. Laila Adam, ta yi kyau sosai. Kayan sun yi cif a jikinta. Fuskarta ya yi zooming yana karantarta, babu ɗigon annuri a saman fuskar. Idanunta kuwa ko ba a fadi ba ya san kuka ta yi. Kallonta yake, wani abu mai kama da tausayi da ƙaunarta domin Allah na fisgar zuciyarsa. Ya sani ranar ba zai taɓa zamewa Sameera na farin ciki ba, aure ne ta yi shi da ya tabbatar ba don tana kaunarsa ba. Aure ne kamar na dole za'a ce don karewa kanta mutunci a idanun duniya. Muddin ko ta auri wanin shi da ya lalata rayuwarta, ya sani ba za ta taɓa daraja ba. Ya ji har abada ba zai bari ta yi kuka a zaman aurensu ba, ya yi wa kansa alƙawarin riƙe ta amana. A hankali ya kai hannu ya shafi screen din wayar.
"Allah ya ba ni ikon kula da ke, ya sanya mana ƙauna da soyayyar juna a zuƙatanmu Sameera. Allah ya ba ki ikon yafe laifin da na aikata maki."
Ya furta a fili sannan ya sauke ajiyar zuciya. Yana ajiye wayar da zummar ya miƙe ya yi wanka kuma sai ga kira ya shigo. Detective dinsa ne mai bibiye da Daddy Affan.
"Ranka ya daɗe barka da yammaci. Allah ya sanya alheri, ina taya murna kwarai."
Ɗan murmushi Areef ya yi.
"Ameen, nagode Ma'aruf, fatan komai lafiya?"
"Alhamdulillah. Akwai muhimmin bayani da nake tattarawa dangane da shi wannan dattijon nan Adamu da ya zauna hannun yaran Alh Affan. Dama jira nake idan ka ƙara samun nutsuwa sai na yi maka bayani a rubuce ko na tako har wajenka, kan nan komai ya kammala. Sannan shi kansa Alh Affan dawowar da ya yi ƙasar nan, ba na tunanin haka siddan ya dawo Boss, you have to be very very careful. Ban kai ga gano komai ba, sai dai ina ta bibiyarsa don na sani yana tare da ku a nan Adamawa. Shi ma zan yi ƙoƙarin samo bayanin komai."
Jinjina kai Areef ya yi.
"Ba matsala Ma'aruf, just carry on. Duk abin da ake ciki, a kowane lokaci kana iya contacting dina. Ba ni da matsala, ko yau ka samu wani bayanan sirri, kawai ka taɓo ni."
"Ok Boss."
Daga haka suka yi sallama shi ma ya tashi ya yi wanka ya ƙara wata kwalliyar da tsadadden yadinsa sky blue an mishi dinkin Senator's style sai ko hula da ta zauna ɗabas. Bayan ya feshe jikinsa da turarukansa tsadaddu, ya kai duba ga wayar da ke ta faman ruri tun yana bandaki, suna Fareed ne a kai. Koda ya ɗaga kawai ya rufe shi da faɗan ya shanye mutane har suna shirin wucewa airport bai fito an yi sallama ba. Sam Areef ya manta akwai wasu abokansu da zasu koma a yau, ya shiga ba da hakuri ya ce yana tafe.
Ya je aka yi sallama da duk masu tafiya, wasu ko masu bin mota tuni suka juya ana kammala ɗaurin aure.
Bayan sallar Magriba ya shiga gidan su Mami. Ya sha dai tsokana wurin dangi, a karshe da aka yi isha'i ya yi gidan su Kausar.
Falon da yake sauka na Abbanta, nan aka mishi masauki. Ba jimawa ta fito sanye da abayarta coffee mai adon golden yellow. Ya kasa kauda idanu a kanta har ta ƙaraso, bai san sadda ya miƙa mata hannunsa ba alamun ta rike ta zauna gefensa ba yana fidda murmushi, ta yi sauran sunkuyar da kai ta nemi gefe guda a ƙarshen kujerar da yake ta zauna tana gaida shi. Ya shafi ƙeyarsa kaɗan har lokacin murmushi yake.
"Ba zan amsa ba tunda an ƙi bin umarnina bayan kin san shigar da kika yi mai buƙatar tukwuici ce ko?"
Kausar dai wasa take da faratanta da suka sha jan ƙunshi da baƙi sai ɗaukar idanu suke, mamaki take wai Areef ke sakin layi haka? Kawai sai ta dinga murmushi tunawa da zancen mahaifiyarta da ta yi, ta ce muddin ta dage da nuna masa kulawa da kuma addu'a, to a sannu za ta dafa dutse ta sha romonsa, tana ta kuma ganin alamomin nasara ba tun yau ba, sai dai na yanzun ya fi kowanne shayar da ita mamakin. Ba ta yi aine ba sai shaƙar ƙamshin turarensa ta yi a gefenta, da sauri ta ɗago idanunsa kuwa ya faɗa cikin nata, nan ma mayar da kan ƙasa ta yi. Ya yi murmushi ya matsa ya ba da tazara tsakaninsu.
"Ina magana kamar hankalinki bai jikinki. Ni kike so kuma yanzun kin zama mallakina, akwai wata damuwar bayan shi?"
Ta girgiza kai, daɗin kalamansa na shawagi da ita.
"Gobe zamu juya by 7am in sha Allah, akwai abin da kike da buƙata? Ko sai an rufo ki an kawo min ke gidana?"
Ta kuwa juya masa ƙeya tana runtse idanu, murmushi har haƙoranta na fitowa.
Ya bi ta da kallo kawai ya murmusa karo na ba adadi. Kunyarta na daga cikin abin da ke burgeshi. Uwa uba kuma nutsuwarta da haƙurinta, ya sani ba ya mata son da ya kai so, ji yake kamar har yanzu zuciyarsa ba ta isa ta karɓi soyayya daga kowace mace ba matuƙar ba ya sulhunta da Sameerah ba. Ya ga murmushinta na gaskiya ba wai jabu ba. Ya tabbatar ita ma ta yi farin ciki a nata duniyar, ya yi nasarar fidda ta daga dukkanin ƙunci, a sannan ne yake da cikakkiyar nutsuwa. Hakan dai ba zai taɓa sanyawa ya shiga haƙƙin Kausar ba, ya kuma saka mata da irin nasa salon kulawar da kyautatawar fiye da yadda ta tsammata, wannan alƙawari ne ya ɗaukar kansa, albarkacin ƙaunar da ta nuna masa da kuma zumunci.
"Allah ya tsare, ya kaiku lafiya." Ta furta da siririyar muryarta. Ya amsa da amin.
Haka ya sa suka jera zasu bar ɗakin, ya dawo baya ya kama hannunta ba ta yi aune ba ta ji ya kai bakinsa ya sumbata. Ta kuwa yi saurin janye hannun wanda hakan ya so ba shi dariya. A ganinsa to me ma aka yi? Ita ko a nan ta cake, rakiyar da ba ta ƙarasa ba kenan, ya fice ya na mata bye bye. Bayan fitarsa har da tsallenta, ta dinga kallon inda tausasan leɓɓansa ya taɓa a hannunta, haka ta koma ciki ranta fari ƙal kamar takarda.
***
Washegari jirginsu ya tashi zuwa Kano. Abba da su Daddy Affan gaba suka yi bayan sun sauka zuwa Katsina, yayin da Areef da wasu cikin tawagarsa sun kai goma suka soma yada zango gidan daya daga cikin abokansa, Yakubu Gezawa. Lafiyayyen abin kari aka shirya musu. Sun bari sai wurin sha biyu za'a shiga gidan su Laila daga can su wuce Katsina. Sai dai wayar Areef ta yi ƙarar shigowar kira. Koda ya duba, mamaki ya cika shi, kiran Laila ba yana nufin don jin lafiyarsa ba ko abin daɗi ba, ya tabbatar akwai dalili don haka ya miƙe ya fito barandar gidan.
"Assalamu alaikum." Ya yi mata sallama bayan ya ɗaga. Ta amsa mishi sallamar murya na rawa.
"Fatan lafiya? Na ji muryarki wani iri?".
"Ka yimin alfarma ɗaya mana."
Ya maimaita kalmar alfarma a fili har da ɗan fidda wayar a kunne ya kalla kafin ya maida ta kunnensa, yau Sameerah ke neman ya yi mata alfarma.
"Ta me kenan?"
Har ajiyar zuciya ya ji ta sauke kafin ta ba shi amsa.
"Please kar ku zo, ku wuce Katsina kawai. Zuwanka na nufin abubuwa da dama. Kar ka manta Mama ba ta jima da dawowa ƙasarnan ba, haƙiƙanin gaskiya ban sanar da ita ko kai waye ba yanda za ta fahimci komai. Koda ace na sanar da kai da yawunta, kawai na faɗi ne. Ganinka zai iya haifar da tashin hankula da tonuwar sirrina da ba na son dangi su kalle ni da shi. So please...kar ku zo."
Ta ƙarashe muryarta da wani irin karyewa, ya kuma fahimci bil haƙƙi neman agajin take yi, alfamar take so ya yi a karon farko tun haɗuwarsu. Ya ji wani abu a ransa na suka, ya yi shiru ya kasa magana. Meyasa ya aikata abin da ya aikata ne wai? Meyasa ya tarwatsa rayuwar Sameerah? Yarinyar da sau ɗaya ma ya taɓa tozali da ita, bai ma ko iya tuna ya taɓa ganinta ba sai bayan da tsautsayin can ya afku ya ji Mami na ihun Sameera mai kitsonta ce. Ƙila tunda aurenta na cikin ƙaddararsa, can a wata duniyar zasu haɗu su yi aurensu, ya kuma kusanceta matsayin halaliyarsa.
"Hello?"
Ta maimaita kafin ya dawo hayyacinsa. Lumshe idanu ya yi ya shafi saman idanun, a hankali ya buɗe sannan lokaci guda ya amsa.
"Anything for you, Sameerah, anything."
Ta ɗan yi shiru itama, wayar babu komai sai sautin hawa da saukar numfashinsu na ƴan daƙiƙu. A ɓangarenta kiranta da Sameerah da ya yi ya motsa mata ciwonta. Shi ɗin ma Sameerah da ya ambata ya jefa yanayinsa a tariyo baya.
Da ƙaramar murya mai ɗauke da wani kwantaccen amon motsa zuciya ta amsa.
"Thank you."
Karon farko shima da ya yi abu Sameerah ta gode masa. Dif ta kashe wayar, ya ji daɗi kaɗan, ko babu komai yana hango alamun nasara a tsakaninsu a watarana.
Fareed ya kira gefe ya sanar da shi cewa akwai matsala kawai su wuce Katsina. Koda Fareed ya matsa, sai yace bakomai bayan family issue na gidan su Lailar. Dalilin kenan da Fareed ya fasa kiran Haseenah da ya yi niyya. Haka suka ba abokansu haƙuri gami da ce musu an fasa kawai a wuce Katsina.
Ba su yi bincike mai zurfi ba suka yarda da ƙaramar hujja da Fareed ya yi rufa-rufa ya haɗa sannan suka wuce. A motar ma Areef sai da ya yi dabarar ɗauke wayar Fareed da ya sjiye a gefe yana tuƙi. Duk don kar Haseenah ta kira shi.
Ya shirya ya yi komai don farin cikin Sameerah. Ya gwammace duk a ji babu daɗi.
***
A gidan su Laila kuwa cewa Haseenah ta yi su Areef sun fasa zuwa saboda wata ƴar matsala. Haseenah ranta bai yi daɗi ba sam, sai dai dayake kanta masifar ciwo yake ma, sai ba ta tsawaita mitar ba. Dangi da suka zuba idanun ganin mijin Laila su ma haka suka shanye nacinsu idan an je can a cewarsu dole ai zai zo a gaisa.
***
WASHEGARI
Tun ƙarfe takwas na safe masu jere suka wuce da motar kayayyaki zuwa Katsina.
Ƙarfe biyu an kammala shirya Amarya Laila.
Kwalliyar appilqué atamfa-lace ta yi wanda kuɗinsa ya haura dubu ɗari biyu, Daddy Mu'az da kansa ya siya mata na fitar biki. Fari ne da aka yiwa adon ruwan golden yellow da dark green. Ta ɗora laffaya dark green a sama. Fuskarta babu ko hoda don ta yi wani irin ja tsabar kukan da ta ci. Mama ko ƴar nasihar nan ba ta yi mata ba ban da sanya mata albarka da ta yi, ita ta san halin mahaifiyarta, ta san cewa har yanzun ba ta saki rai da auren nan ba, ba ta gama yarda da ita ɗari bisa ɗari ba.
Tun a daren jiya Gwaggonninta suka saka ta a ɗaki kowanne ya yi mata na sa faɗan.
Daddy ko da safe ya yi nasa sannan aka yi shirin tafiya, Mama ta nemi alfarmar a biya da Laila gidan Baba Tsoho. Shima dai nasihar ce da sanya albarka, haka Laila na kuka ta shige mota. Wasu motocin ma sun yi gaba, su ma nasu ya tashi zuwa Katsina, zuciyarta a cunkushe da wani nadama da baƙin ciki, tana mai jin tsanar kanta. Tun farkon lamarin kusan wannan ne karon farko da ta ji har a rai da ace Areef zai sauwaƙa mata idan ya so ta ɗauki fansa ta wata hanyar daban, shakka babu da ta ji daɗin hakan. Sai dai kuma bakin alƙalami ya riga da ya bushe, saura ta shiga gidansa ta ga kalar wainar da za su toya ita da Hajja Zayha.
***
Detective Ma'aruf ya buɗe idanu saman system dinsa, cike da mamaki yana karanta tarihin Adam Kibiya da ya samu wani abokin aikinsa ya haɗo masa. Sunan Laila Adam Kibiya da Sameerah Adam Kibiya ke mishi yawo a kwakwalwa. Ya sa hannu ya ɗauki wayarsa da sauri ya buɗe saƙon taya murnar da ya ga wani abokinsu ya ɗora na sunan Areef da cikakken sunayen matansa biyu.
"Laila Adam Kibiya."
Sunan ya ɗauki hankalinsa matuƙa kawai ya miƙe tsaye.
"Allah is the Greatest!"
Ya furta cikin maɗaukakin mamaki da kuma jinjina wannan lamari na Ubangiji.
©Rufaida Umar