Free chapter · Read without an account

Zazzafan labari

by MARYAM STAR · RAYUWAR SAMHAD


𝑷𝒂𝒈𝒆 1️⃣1️⃣ 𝒕𝒐 1️⃣2️⃣

___________________________________

بسم الله الرحمن الرحيم 


Bai tsaya ko ina ba se part dimshi da ke can ɗayan gefe,

se huci yake kamar kumurcin maciji, saboda ɓacin rai idannuwansa sunyi jah sosai kamar gauta, ga jijiyoyin kanshi duk sunyi raɗo-raɗo sun tashi sunyi tsanwa sharr, abinka ga farar fata.


Samhad binshi kawai take duk inda yasa ƙafa saboda ita kwata-kwata kanta ya kule da abubuwan dake wakana a cikin wannan gida.

sai da yashiga da ita bed room ɗinsa sannan ya saki hannunta da yayiwa ƙyakkyawan riƙo, kafin tayi wani yunƙuri ya fizgota jikimshi ya rungume ta ƙam kamar me gudun kar wani ya ƙwace mashi ita.

ajiyar zuciya ya ke sauke wa ajere kafin wasu zafaffan hawaye su shiga zubo mashi.

tsuma jikin samhad yahau yi jin ɗumin hawayensa a kafaɗarta, 


kukan babba abune da bata taɓa gani ba tsawon rayuwarta shiyasa yanzu kanyarta ta yamutsa har tana ƙoƙarin hadewa da jinin da ke gudana acikin kanta.

zuciyarta ke faɗa mata akwai gaggarumar matsala a cikin gidanan tabas akwai abinda ake yi ba dai-dai ba amma ba kowa ya fahimta ba.

ɗayan sashen zuciyar tane yake tambayar ta wai mi Mamy take nufi ɗazu? taga sanda tayi wani makirin murmushi da kuma sanda ta ɗagawa Mubeen hannu tai mashi wata alama wanda ba kowa ya fahimta ba....



tunanita ne ya katse jin tana neman faɗuwa daga tsayen da take rungume da Mubeen da zuwa yanzu sautin kukanshi yafara fitowa.


cikin rawar jiki tafara ja baya hankali har ta dangane da jikin gadon dake dakin.
Cikin dabara ta lallaɓa da nufin ta zauna amma takasa saboda ya sakar mata dukkan nauyinsa.

A ƙoƙarinta na zama ƙafarta ta zame baya ba shiri suka faɗa kan kagon atare.

runtse ido tayi jin yanda ya sake matse ta ajikinshi kamar ƙaramin yaron da beson uwarsa ba tashi ta barshi.

jin hawayen nasa munƙi tsayawa ya sanyata zame hannunsa da ya riƙeta tashi ahankali. 

Bayan tayi nasarar ɓamɓareshi daga riƙon da yayi mata ahankali ta janye jikinta daga nasa amma ba dukaba.

Tallabo fukarshi tayi ta siraran hannayenta tashiga share mashi hawayen da ke gudana daga idanuwansa kamar ambude famfo. 

Dafa kanshi tayi ta na kallon jijiyoyin da sukayi raɗo-raɗo a gaban goshin, addu,oi ta shiga karanto wa ta na shafa mashi.
kwanciya ya sake gyarawa a jikinta yana jin wata nutsuwa na safko masa a cikin barcin.

kallonshi take tana yaba kyawun da tsarin hallitar fuskar ta, a  zuciya ta ke faɗin wai dama rayuwar duniya haka take? ko wa da irin ƙalubalenda, ga misali nan tana kallo babba dashi yana kuka akan rayuwa, kenan ba kuɗi bane jindaɗin rayuwa? kenan ahali ba sune farin ciki ba?.
"Ya Allah ka dubi rayuwar mu ni da wannan bawan naka, Allah ka bamu ikon fuskantar ƙaddararmu, Allah ka bashi juriya akan rayuwa, Allah ka sassauta mashi raɗaɗin da yake cikin zuciyarshi ALLAHUMMA AMEEN."




Tana kammala addu,ar taɗan janye jikinta da ga nashi ta kwantar da kanshi akan cinyar ta tajingina da filo yana lumshe ido alamar barci.

ahankali nannauyan barci yayi awon gaba da ita.




Daddy ne ya tashi daga kan dinning ɗin cikin sanyi jiki, kwata-kwata baya son abin da Mubeen keyi, shi yanzu abin da yasa ya kasa nutsuwa be wuce yanda ya ɗauki yarinyar mutane ya fita da ita ba.


Alhaji ka daina damuwa akan lamarin wannan yaron tun da kasan halinshi, ka kyaleshi kawai bade matarshi bace kuma ya ɗauka, to suje can su ƙarata.

Ficewa Daddy yayi daga sashen ba tare da yabi ta kan maganar da Mammy ke yiba.

Sashen Mubeen ya nufa dan zuciyarshi tunzura shi take akan yaje ya dawo da Samhad kar Mubeen ya cutar da yarinyar mutane tunda yasan halinshi da baƙar zuciya kamar kuturu.

Yana isa ya tarar da ƙofar parlon abude, aiko zuciyarshi ta doka da mugun ƙarfi,dan har ya fara hasaso ya riga da ya cutar da Samhad.

ƙofar bed room ɗin da suke ya buɗe, 
turus yayi yana kallon ikon Allah, dan abune da bai taɓa faruwa ba.

murza idomshi ya sakeyi dan ya tabbatar da gaske Mubeen ne ke barci haka cikin nutsuwa ba tare da ya sha abinda ya shaba.

Muneeb ne yau kwance a gado kamar kowa yana barci cikin nutsuwa babu surutai kuma babu warin aman giya ko kwalbar magani.

Hawaye ne suka gangaro idon Daddy, saurin fita yayi yana jinjina girman ikon Allah, dama ance aure na nutsar da mutum tabbas wannan gaskiya ne tunda ga sheda ya fara gani wajen Muneeb aure duka kwana biyu matar da ko tare wa batayi ba amma harta fara nitsar dashi.

Godiya yayiwa Allah tare da yima Mubeen dan Samhad addu,ar zaman lafiya da haɗin kai harda zuri,a ɗayyiba.

Yana tafiya ya na sakin murmushi kamar ba shiba har ya iso part ɗinsa....



𝑫𝑨𝑮𝑨 𝑨𝑳𝑲𝑨𝑳𝑨𝑴𝑰𝑵 𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑺𝑻𝑨𝑹✍️⭐⭐⭐




𝑳𝑰𝑻𝑻𝑨𝑭𝑰𝑵 𝑹𝑨𝒀𝑼𝑾𝑨𝑹 𝑺𝑨𝑴𝑯𝑨𝑫 𝑵𝑨 𝑲𝑼𝑫𝑰 𝑵𝑬 𝒁𝑨𝑲𝑰 𝑩𝑰𝒀𝑨 200 𝑲𝑨𝑪𝑨𝑳 𝑲𝑰 𝑴𝑨𝑳𝑳𝑨𝑲𝑰 𝑳𝑰𝑻𝑻𝑨𝑭𝑰𝑵.

𝑨𝑪𝑪𝑶𝑼𝑵𝑻 𝑵𝑼𝑴𝑩𝑬𝑹
  ***
𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑼𝑴𝑨𝑹
𝑶𝑷𝑨𝒀.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol