Free chapter · Read without an account

RAYUWAR SAMHAD

by MARYAM STAR · RAYUWAR SAMHAD

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐



PAGE 2️⃣0️⃣🌹2️⃣1️⃣




___________________________________________________________________________

بسم الله الرحمن الرحيم.
Sa Beela tayi ta shirya suka tafi gidan ƙawarta dake cikin gari, Suna isa itama ta shirya dan Maman Nabila ta gaya mata zasuzo , mai napep suka tara su ka bar unguwar zuwa ƙarsgen gari can cikin dadi.


Wani baƙin mutumne zaune shi kaɗai ya na zane-zane kamar ma ƴaƴan Aljannu yake zanawa tunda suka isa wajen Beela ke yamutse fuska kamar zatayi amai.



Kora mashi bayani Hajiya Larai tayi akan abinda ya kawosu, wani ƙullin magani yabasu wanda zasuyi amfani dashi, ƙudi suka aje mashi tareda godiya suka bar wajen.


Sosai Hajiya Larai ta gargaɗi Beela wajen yin amfani da maganin.



A ɓangare Aisha tunda aka sallamota Asibiti ƴan barka ke zarya saida suka ƙara sati guda sanan tayi taron sunan da ya jijjiga zuciyar Sarhabila da ta Maman Nabila.




Yaro yaci Sunan Muhammad Mubeen ake  kiranshi da Mubeen zallah.


Bayan sunyi arba,in Muhammad ya matsa akan sukoma aiki ya taso masa.


Sosai Aisha tayi kewar Mamanta da ƙannenta su Khaleel da aminiyarya Nabila da kullum sai ta zo ta ɗauki Mubeen.



Tunda su Aisha suka tafi basu sake dawowa ba sai bayan shekara uku sannan mubeen ya girma sosai harta sake samun wani ciki dande Ƙarami ne.



Wannan dawowar a gidansu suka sauk wanda Muhmmad ya sake gyarashi tunda ba.a taɓa zama cikinshi ba sosai gidan ya ƙawatu da kayan more rayuwa.


Sanda Nabila zataje gidan Beela tace itama zata je daga ɗanta Mubeen tadade bata ganshinba, 

Badan Nabila ta so ba taje da Beela gidan Aisha aiko  a haukace Beela ta dawo dan can ta baro Nabila, tararta mama tayi tana tambayarta ko lafiya?.


Beela ta kwashe labarin komai ta bawa Maman Nabila aiko suka ɗauki mayafai sai wajen malam dan sanar dashi Muhammad ya dawo.




Wani magani ya basu ya ce suyi amfani da shi inda Muhammad ke zama zasu binne wasu layoyi tare da harin maganin da zasu sanya mishi a abici.





Bayan kwana biyu Beela ta je gidan sukasha fira da Aisha harda taya ta girki da yake cikin Aishar ya fara tsufa, bayan sungama ta kuma tarkato ƴan share-share tanayi Aisha ce ta tayata tace dama tanason ta gyara ɗakinda Muhammad ke aiki idan ya dawo gida amma jikinta babu ƙarfi. hartintuɓe Beela  keyi wajen zuwa taya Aisha aikin gyara dakin zuwa tayi tana kakkaɓe files dake kan wani ɗan table da kujera ke wajen anan tayi dabarar saka layoyin da boka ya bata ba tare da Aisha ta luraba.



Bayan sungama da Beela zata tafi gida ta haɗa mata sha tara ta arziki tace ta kaiwa Maman Nabila babu kunya ta amshe babu ko godiya tana raya idan ta shigo gidan zata koyawa Aisha hankali.





Bayan kwana biyu Aisha ta kasa gane kan Muhammad, sai daga baya taji labari wai aure zai ƙara tasha kuka sosai ga tsohon ciki ganin babu inda damuwa zata kaita yasa ta fawwala ma Allah komai taci gaba da rainon cikinta.



Ranar da Aisha ta haihu a ranar aka ɗaurawa Muhammad aure da Sarhabila.


Aisha bata san wacece Muhammad ya auraba sai bayan taga wankan.


Sosai Aisha tayi kukan har saida ta fara rashin lafiya aka kaita asibiti tayi kwana biyu aka sallamota.


Sosai Aisha ta shiga damuwa data zauna sai tunani da hawaye wani lokaci sai idan yaronta Sadeek yayi kuka take dawowa daida.


WAI SHIN MIYENE YAYISILAR RASUWAR AISHA?.
BAYAN BEELA TA TARE MIYASA MUHAMMAD BAI KAITA WAJEN AISHA SUNGA JUNABA?

KU BIYONI DAN JIN YANDA ZATA KAYA


KU KASANCE DA ALKALAMIN MARYAM STAR DANSAMUN DADADAN LABARAI MASUZAFI

      NAGODE 

DAGA ALKALAMIN
 MARYAM STAR✍🏻⭐⭐⭐.

🌹RAYUWAR SAMHAD 🌹( abar tausayi ce 😭) 




DAGA ALKALAMIN MARYAM STAR✍🏻�⭐⭐⭐

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.