Free chapter · Read without an account
Zazzafan labarin
_______________________________BOO TWO 2️⃣ PAGE ONE 1️⃣__________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
Kafin daga bisani ya tsaya akan shawarar Mubeen.
Komawa barcin shima yayi dan kansa har yanzu bai bar juyamasa ba ga ciwo da yake masa mai tsananin, barci sosai Daddy yayi dan yakai kusan awa biyu kafin ya tashi ya taras da Sadeek ya kawo masa kayan kari daga sashen Mubeen wanda Samhad ta haɗa masa.
Yaji daɗin shayin sosai kasancewar tun farkon aurensu Aisha ta saba masa da shan shayi kullum dare tu bayan rasuwarta bai sake samun kalar wanda ya keso ba sai wannan da Samha ta kawo masa.
Barci suka Samha da Mubeen suka sha sosai kafin Samha ta farka dan ta gaji da kwanciya duk ta takura a jikin Mubeen ko lumfashi bata shaƙa da kyau saboda yanda ya kanainaye ta cikin jikinsa ya na shaƙar sassanyan ƙamshin da ke fitowa daga jikinta.
Lallaɓawa tayi za ta zare jikinta amma sai taji ya sake ƙanƙame ta kuma barci ya ke ahakan. murmushi ta yi tare da kai hannu ta shafi gashin da ke kewaye da doguwar cikakkiyar fuskarsa, a hankali ta ke shafa gashin nasa ta na wasa da shi dan Allah yayi Samhad mace mai sha,awar gashin gemu da saje.
Ƙarewa fuskarshi kallo tayi tsaf dan ko wane lungu sai da ta kalla sannan ta sake yunƙurin janye jikinta daga nashi amma mi? sai taji ya sake janyota ya matse acikin kunne ya raɗa mata "ina zakije baki gama kallon mijin naki ba"?.
Kunyace ta kamata babu shiru ta ɓoye kanta a ƙirjinsa ta na dariya ƙasa -ƙasa. buɗe idonsa yayi tar akanta ya na kallon yanda take dariyar kyawunta na sake bayyana, bai san ya shagala da kallonta ba sai da yaji tace "kai Ya Mubeen wannan kallo haka ai saikasa in ƙware" tallabo fuskarta yayi yace "idan ma kin ƙware ai ga mijinki a kusa zai baki taimakon gaugawa" waro fararen idanuwanta tayi tace "kai Ya Mubeen wane temakon gaugawar zaka bani".
"Hummm ki gwada ƙwarewar sai ki gani ai" far Samhad tayi da ido sannan tace "to ai ba nice zan kware ba kaine zaka kwareni da kallonka"
Saka idonsa yayi cikin nata yana aika mata da kallo mai kashe garkuwar jiki sun kai kusan minti biyar ahaka Samhad nason janye idonta amma Mubeen bai bata damaba har saida ya tabbatar saƙonsa ya isa inda yake buƙata sannan ya janye nasa idon da har sumfara canza launi.
Cikin kasalalliyar murya yace "yadai Samhadidina ko kin kwareɗin inkawo agajin gaugawa? yayi maganar cikin sigar tsoka.
Shiru Samha tayi batace komai ba dan sosai Mubeen ya kashe ilahin jikinta da wannan kallon nasa mai sakar mata kasala.
Tashi yayi ya sauka akan gadon yana miƙa ya janyo Samhad yayi hanyar toilet.
DAGA ALKALAMIN ✍️
MARYAM STAR ⭐⭐⭐(ƳAR BAIWAR JAJURTATTU💪🌹).
🌹RAYUWAR SAMHAD 🌹(Abar tausayi ce😭)
DAGA ALKALAMIN✍️
MARYAM STAR⭐⭐⭐