Free chapter · Read without an account

.....

by MARYAM STAR · RAYUWAR SAMHAD

BOOK2️⃣PAGE9️⃣

___________________________________________________________________________

بسم الله الرحمن الرحيم.


Gyara tsayuwarsa ya yi tare da ƙawata fuskarshi da murmushi.

   "A,aha Mubeen har ka ƙaraso da wuri haka." Baban Saniga ya yi maganar ya na miƙawa Mubeen hannu alamar musabaha, miƙo mashi hannu Mubeen ya yi su ka  yi musaba yana faɗin.

    "Eh wallahi Baba har na ƙaraso dama babu abinda ni ke shiyasa na taho."

     "To ma sha Allahu, mu shiga daga ciki ka tsaya waje kamar wani baƙo."

Bin shi Mubeen ya yi su ka shiga cikin gidan a tare, Mama ce ta fito da ga ɗaki jin muryar Mubeen cikin nuna kewarsa ta matso kusa da shi ta na shafa sumarshi kamar yanda ta saba ta ce.

  "Yarona na yi tsananin kewarka, mi ya sa za ka manta da Mamarka tsawon lokaci ko waya ka daina kira fatan dai komai lafiya."

Shafa ƙeya ya yi tare da faɗi.
   "lafiya lau Mamata wallahi ayyuka ne suka shamin kai a ƴan kwanakinnan shiyasa ban samu lokaci na zo ba amma kiyi haƙuri dan Allah hakan ba zai sa ke faruwa in sha Allah."
    "Allah ya yarda yaronah".

   "Idan kin gama ƙorafin sai ki shigo da shi bawan Allah daga zuwanshi kin tisa shi gaba sai mita ki ke masa ko zama baiyi ba bare ki bashi ruwa." Cewar Baba  da ya ɗaga labulen ɗaki ya shiga.

Bayan sun zazzauna aka gaisa sannan Baba ya yi gyara murya ya fara korawa Mubeen jawabi.

   "Bayan mun yi lissafin ribar wannan watan aka fidda kudin kamar yanda ka ce na saka a wannan account din to bayan na saka kuɗin da awanni kaɗan sai ga alart ya shigomin an ciri kudi ta banki, cikin tashin hankali na garzaya banki  bayan zuwana su ka sake tabbatar min da lallai andatsi bankina kuma kuɗi sun riga da sun fita,  banyi kasa a gwuiwa ba na gazaya wajen jami'ai na yi report su ne suka jajirce da bincike har aka samo wasu alamomi na sanda ya datsi bankin yanzu dai Alhamdulillah anata bincike akan lamarin kuma in sha Allah nasara na fuskantomu da yardar Allah."


 Cikin jimami itama Mama ta cigaba daga faɗin "Wallahi lamarin ƙasarnan sai addu'a kawai yanzu kowa ya baci da son abin duniya ba manyanba ba yaranba kowa ya dage a lallai sai ya zama wani abu a rayuwa dan yaga wani daga cikin abokai ko yan uwansa Allah ya budamai shikenan sai hassada da ganin kyashi, mutum ya dage yaki haram yaki halak a lallai shima sai yayi arziki, Allah ya sa mudace ya kuma tsaremu da sharrin zukatanmu,  kai kuma Allah ya yi wa rayuwarka albarka ya baka sa'a akan ayyukanka."


   Amsawa suka yi da ameen. 

Mubeen ne ya fara magana "Ma sha Allah Baba da Mamana sannunku da ƙoƙari nagode sosai Allah ya biyaku da gidan Aljannah ya gafarta muku zunnubanku."

Amsawa suka yi da ameen su na saka mashi albarka,  ci gaba da magana Mubeen ya yi. 
"Amma Baba da tun farko ka sanar da ni ba sai ka wahalar da kanka cikin sauƙi zansa a binciki lamarin tunda ga Sadeek nan aikinsa ne."



       "Allahu akbar, Allah sarki Sadiku wallahi na shafa'a kasan zance indai na kuɗi ne ba ni sanya musamman ma idan wata matsala ta gifta." Cewar Baba,  "kwarai kuwa malam wannan zance haka ya ke." Mama ta sanya baki. 



Sun daɗe suna tattaunawa kamin daga bisani Mubeen ya kwantar musu da hankali akan babu wata matsala zaisa a binciko ma sa koma waye keda hannu a lamarin za'a gano, fatan alkairi sukayi masa tare da sake bashi hakuri akan ba laifinsu ba ne,  murmushi kawai ya yi tare da tabbatar musu da babu komai,  dazai tafi ɗaurin kuɗi ya ajiye musu tare da godiya a garesu ya tashi zai wuce. 


Babane ya hanashi akan lallai ba zasu amshi ko sisi da ga kuɗinsa ba, sosai ya rarashi Baban harya haƙura yabar maganar, Mamace ta tsaidashi akan zata bashi sako yakaiwa amarya tunda dai yanzu bayayinsu ya canza iyaye ko auren sai de su ka ji labari a bakin Saniga kuma baikawo musu amaryar sun gaisa ba. 

Haƙuri ya bayar tare da tabbatar musu da zai kawota In sha Allah, sallama ya yi musu tare da godiya sannan ya wuce. 

Bayan ya shiga mota ya kira wayar Saniga danjin inda ya ke sai ya je su gaisa amma ba,a ɗaga ba haƙura ya yi ya tafi gida kai tsaye. 

Akan hanya ne ya ga wani sabon store da aka bude harya wuce sai kuma ya dawo da baya ya shiga wajen don yin siyayya. 



ALHMDLLH RAYUWAR SAMHAD BOOK 2️⃣ YA KAMMALA 'YAR UWA KIZO KI MALLAKI NAKI DAN KARANTAWA CIKIN SALAMA AKAN  KUDI KALILAN NAIRA 400 KACAL. 


***
MARYAM UMAR 
OPAY

Shaidar biya ta wannan layin ***.



DAGA ALKALAMIN✍️MARYAM STAR⭐⭐⭐(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU💪🌹).🌹RAYUWAR SAMHAD🌹(Abar tausayi ce😭)

DAGA ALKALAMIN✍️MARYAM ⭐⭐⭐(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU💪🌹).

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol