Free chapter · Read without an account

.....

by MARYAM STAR · RAYUWAR SAMHAD

BOOK TWO PAGE 2⃣5⃣


Yanda na ɗaga hankalina ne ya ƙara tadawa Abbu hankali har jinya sai da yai ta kwana biyu, dama ga jimamin rashin Ummana, sannan kuma ga rashin lafiyar da nike fama da ita, dan yanda nike data hankina, sai ƙunar ta nemi komawa baya, sosai aka linka gata da kulawar da ake min saboda halinda nike ciki.



Bayan anyi sadar ukun Ummana kowa ya watse, inda riƙona ya koma hannun Umma Suwaiba, gidanta aka maida ni, dan direct Hajiya Adama ta nuna ba zata iya wahala da ni ba, acewarta ƙarni ni ke, duk da ƙarya ta ke, dan magungunan da akemin amfani da su masu kyaune da ƙanshi, sam ba wani ƙarni da nike sharrine da son zuciya kawai irin nata, idan ba son zuciyaba mi zaisa ta ce hakan, bayan ɗiyarta ce ta jawo min koma miye ya sameni.


BAYAN SHEKARU UKU.


Bayan shekaru uku da rasuwar Ummanah rayuwa taimin tsanani sosai, kasancewar tunda na warke daga ƙuna Abbu ya dawo da ni gida, wanda sam Umma Suwaiba ba ta so hakanba, kawaide babu yanda zata yi ne, wahala gami da azaba babu irin wacce bana sha a gidanmu, Yanzu ina shekara tara da watanni na mallaki hankali, kuma nasan abubuwa da dama akan yanda rayuwar gidanmu ke gudana.

Sharar gida da wanke-wanke duk aikina ne, wankima dan a washing machine ake shiyasa wahalar tawa ta ragu, a ɓangaren girki kuwa, nice ke haɗa komai girkawa ne kawai banayi, shima dan Abbu ya tsawatar akai ne, dan ya taɓa iske ni wa ta rana Hajiya Adama tai baƙuwa shine ta saka ni girka fatar shinkafa tunda akwai miya a friedge.

Sosai ran Abbu ya ɓaci lokacinda ya iskeni na cike kitchen ɗin da hayaƙi, dan shinkafar ban saka ma ta ruwa ba, sai ƴan kaɗan gudun karta caɓe, gashi na balbala wutar gas.

Ɓangaren zuwa makaranta kuwa, kullum nice makararriya dan su Zainab tun bakwai suke tafiya, ni kuma sai na gama shara da wanke-wanke sannan nike tafiya hakan ya saka kusan kullum sai anyimin dukan makara, ga shi malaman naji da ni saboda kwanya da Allah ya bani, duk abinda aka koyar dani na riƙeshi kenan har abada.
Hakama ɓangaren isilamiyya, ina maida hankali sodai dan na wuce Anty Zee da Fauzy tunda su ba karatu ne ke kawosu ba, shiririta da ciye-ciye kawai suke idan sunzo.

A islamiyyarmu akwai malaminda kowa ke tsoronshi saboda rashin sakin fuska da tsare gida da yake, uwa uba wajen hukunta me laifi baida sauƙi ko kaɗan, shiyasa kowa ke shakkarshi, amma kuma sai Allah ya haɗa jinina da nashi, ko makara nai bai cika dukanaba saboda kusan kowa yasan halinda nike ciki a gidanmu.

Tafiya tai tafiya kullum da irin ƙalubalen da ke fuskantar rayuwata, abu na farko da na kuma na ƙarshe da ya zama babban tabo a rayuwata shine, rashin Yayana, Yaya Abubakar da tun rasuwar Ummana aka nemeshi aka rasa, duk wani abu daya danganceshi babushi babu dalilinshi, koda photonshi ba,a gani ba, wannan lamarin shine abinda ke girgiza zuciyata, nakanyi kuka duk lokacinda na tuno da shi, ko Anty Zee sukaimin gori, ni kaɗai nike rayuwata, banida abokin shawara, banda ƙawa ko aminiya, banda wanda zan kaiwa kukana, dan babu wanda ya damu da rayuwata, kowa ya manta da ni, hatta da dangin Ummana ba nemana suke ba, Abbu ma ya fita a rayuwata sam yanzu ya daina kulawa da ni, kuma baya shiga lamurrana, har takai a gabanshi za'a dakeni amma ko uffan bazaiceba.


Tun ina damuwa da halin shariyar da Abbu ya ke min har na sakawa kaina dangana na daina damuwa.

🌹RAYUWAR SAMHAD🌹(Abar tausayi ce😭)

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol