Free chapter · Read without an account

.....

by MARYAM STAR · RAYUWAR SAMHAD




BOOK TWO PAGE 3⃣3⃣


Alhaji Bashirne ya ce su ƙaraso ciki, nan suka shigo jikinsu a sanyaye amma ganin Mubeen sai suka ji hankalinsu ya kwanta, duk da suma sun shiga ruɗani da ganinshi.

Jawabi Alhaji Baahir ya hau yi.

(Da farko dai duk wand ya san Abdullahi yasan cewa yana da yaro me suna Abubakar wanda ya ɓata tun ya na ƙarami, to wannan matashin da kuke gani shine Abubakar wannan kuma mutumin shine wanda ya tsinceshi kuma ya reneshi."
Kallon Baba Alhaji Bashir yai tare da bashi damar gabatar da kanshi da kuma ta yanda akai ya tsinci Abubakar.

Sallama yai da farko tare da gabatar da kanshi da matarshi ga dukkan mutanen wajen sannan ya fara da faɗin.

"Wa ta rana na je Katsina ziyara wajen ƴan uwana, kasancewar ni a nan garin Abuja nike aiki, a hanyata ta dawowa na gamu da wannan yaro shi kaɗai gefenshi ga jikkar kayanshi zaune a gefen hanya, kasancewar magariba ta gabato ni kuma na saba yin tafiyar dare ya saka na tsaida me babur ɗin da nike akai na sauka naje wajen wannan yaro, bayan na tada shi daga barcin gajiya da yunwa da ya zauna ya na ta layi, tambayarshi nike waye shi amma cemin yake be sa ni ba, kuma ya roƙeni da intafi da shi, mamanshi ta faɗa ma shi shi shegene baida uba, rain ya ɓaci da jin wannan labarin nashi hakan ya saka na ɗaukeshi ba tare da wani jinkiri ba, bayan na je masaukina na bashi abinci tare da yimai wanka na canza ma shi kaya na ɗauke shi muka kama hanyar zuwa Abuja cikin daren.

Kafin wayewar gari muka isa unguwar da nike zaune ni da matata, da  farko ta yi musu lokacinda na gabatar ma ta da wannan yaron, amma da aka kwana biyu ta fahimci yaron ya samu tarbiya sai da rungume shi ta riƙe kamar ita ta haifeshi, bamu taɓa samun saɓani da Abubakar wanda muke se ma Saniga ba, kullum cikin yi mashi addu'a muke akan Allah ya bayyanar da mahaifanshi, ƙalubale ɗaya Saniga ya fuskanta a wajenmu shine daga dangina har na matata basu ƙaunarshi, kullum cikin kƴararshi suke wanda hakan ya saka ma shi damuwa har ya fara biyewa abokan banza suna bashi ƙwayayo yana sha. Shigowar wannan bawan Allahn Mubeen a rayuwarmu ne ya ɗan mutsar da shi, shine ya sama bashi aikin yi tare da bashi wani ɓangare daga cikin dukiyarshi akan ya juya ma shi, munji daɗi sosai da shigowar wannan bawan Allah a rayuwarmu dan sosai ya ke temaka mana kuma shine ke ɗaukar nauyin ɗawainiyarmu gaba ɗaya."


Kuka ne ya kwacewa Abbu yayinda ya taso ya nufi Saniga ya rungume shi yana shafa bayanshi, shima kukan ya saki ganin yanda babban mutum kamar wannan ke kuka akanshi, ga kuma tashi sa tsikar jikinshi ke yi jin kalaman da Abbu ke faɗi cikin kuka.
"Nayi kewarka yarona Allah ya isa tsakanina da duk wani me hannu a wajen nesanta ni da kai."


A hankali ta tarrafo dan gaba ɗaya ƙarfin jikinta ya ƙare gashi saboda kukan da ta sha yanzu muryarta ta dashe ko fitowa bata yi, kama ƙafafuwan Abbu da na Saniga tai tare da ƙanƙamewa tana zubda sabbin hawaye, ƙoƙarin tashi tsaye ta ke amma ina sam ƙagafuwanta sun gaza bata haɗin kai, lokacinda ta samu ta miƙe tsaye cike da dauriya wani irin wawan sarawa kanta yai, ƙafafuwanta suka lankwashe tai baya luuuuuu a sume, babu wanda ya lura da zuwan Mubeen wajen sai kawai gani akai ya saɓeta a jikinshi tare da girgiza fuskarta cikin matsanancin tashin hankali, Doctor ne ya zo wajen da sauri tare da umutar Muneen akan ya zo ya shimfiɗar da ita kan kujera zai dubata.

Babu musu ya kaita ya kwantar amma har lokacin bai bar hawaye yana ƙiran sunanta ba, da ƙyar su Abbu suka rarrasheshi yabar Dr. yai aikinshi.

Can gefe na hango Hajiya Adama na zare idanuwa kamar mujiya ta na sanɗa da niyyar guduwa tabar ɗakin, wani irin kukan kura Abbu daya hangota ta wutsiyar ido yai tare da fizgota ya hau sauke ma ta tagwayen maruka ji kake "Tasss tasss taras."
Da kyar Alhaji Bashir y zaunar da shi tare da tausarshi dan zuciya ta gama kawowa yuwa so yai abarshi da ita kawai ya haɗa mata jini da majina.


DAGA ALƘALAMIN MARYAM STAR ⭐⭐⭐

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.