Free chapter · Read without an account

Chapter 2

by Amanarcool · SAUTIN KARSHE

Katafaren gida ne na alfarma, irin gidajen nan na attajirai da idan mutum ya tsaya a gabansa yana kallo sai ya ji tamkar yana kallon wata babbar fada ce. Harabar gidan babba ce, an ƙawata ta da furanni da shuke-shuke , da suka haɗu suka ƙara ƙawata gidan.
Duk da kasancewar rana ce, hakan bai hana bayyanar hasken da fitillun da aka ƙawata harabar gidan da su fita ba, haske ne mai kyau da ɗaukar hankali, ga ruwa na fountain yana tsiyaya a tsakiyar harabar. Gidan ya kasance babban gida ne da yake da part daban-daban a ciki, ba ƙaramin haɗuwa ya yi ba, ya tsaru tsaf da shi kamar sabuwar villa. Cikin nutsuwa ya yi hon mai gadi ya buɗe masa get, danna kan motar ya yi ya shiga. A ƙayataccen parking space ɗin gidan ya yi parking. Yafi minti goma zaune a cikin motar kafin ya buɗe murfin ya fito. A hankali yake takunsa cikin nutsuwa ya nufi ɗaya daga cikin part ɗin da ke cikin gidan, yana isa babbar ƙofar shiga falon ya tsaya, hannunsa ya saka a jikin thumbprint ɗin da yake jikin ƙofar, sai gashi ta buɗe da kanta, ya sanya ƙafa ya shiga ciki. Zahra ce ita kaɗai kwance a falon a kan 3seater tana danna waya, jin motsin shigowar mutum ya sa ta ɗago ta kalli ƙofar falon. Da sauri ta ajiye wayar ta tashi zaune tana faɗin "Laaa Yaya Sudais ashe kai ne? Sannu da zuwa" . Hannu ya ɗaga mata kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Ina Mammy?". Zahra ta ce "Mammy tana ciki ba ta daɗe da shiga ba. Ya Faruk kum...." Ɗaga mata hannu ya yi ba tare daya bari ta ƙarasa maganar ba ya ce "Mammy kawai na tambaye ki" shiru ta yi tana rufe bakinta, sam ta manta da baya son a faɗa masa abin da bai tambaya ba, daga haka bai sake bi ta kanta ba ya fara hawa matatakalar benen cikin zafin nama. Bai fi taku biyu ba ya ji Zahra ta sake cewa "Yaya Sudais Aunty Ilham ta zo tun ɗazu take jiran ka, tana can ɗakin Mammy". Juyowa ya yi da sauri ya kalle ta, ai babu shiri Zahra ta ɗauki wayarta da sauri har tana haɗa hanya ta bar falon. Tsaki ya yi tare da girgiza kai ya bar gurin.

"Ke lafiya za ki shigo mini ɗaki haka kamar an jefo ki? Waya biyo ki ne?" Mammy ta tambayi Zahra da ta shigo ɗakin da gudu. Zahra sai zare ido take tana waiwayen bayanta, kafin ta ce "Mammy Yaya Sudais ne". 

"Sudais kuma? Ko wani abin ki ka yi masa ne? Ke dai bakinki ba zai taɓa yin shiru ba. Kin san halinsa baya son surutu da faɗi ba a tambaye ka ba". Cikin shagwaɓa Zahra ta ce "Mammy ba fa wani abin na ce masa ba, kawai dai kin san halinsa wasu lokutan".

"Idan ba laifi kika yi masa ba babu ta yadda za'a yi ki yi haka, ke kika sani ba ruwana idan ya kama ki" cewar Mammy tana yi mata dariya. 

Ilham dake zaune tana murmushi ta ce "Zahra yanzu ina Yaya Sudais ɗin yake?". 

"Oho masa, ko ya wuce ɗakinsa ni ban sani ba. A falo dai na bar shi". Tashi Ilham ta yi, ta ce musu "Bari na duba na gani" . Zahra ta ce "Aunty Ilham ki rufawa kanki asiri ki dawo, a yadda ya shigo kamar akwai abin da yake damunsa" .

"Sai na je" Ilham ta faɗa tare da barin ɗakin. 

Zahra ta yi dariya tana faɗin "Allah ya raka taki gona ko a jikin Zara'u, ni har tausayi kike bani wallahi, Allah ya haɗa ki da aiki". 

Mammy ta ce "Zara'u zan saɓa miki fa, ina ruwanki da ita ne?". 

"Haba Mammy ya za ki ce mini Zara'u kamar wata ƴar ƙauye?". Zahra ta yi maganar kamar za ta yi kuka. 

"Ina ce ai sunanki ne ko? Kuma kema yanzu kika gama faɗa" Mammy ta bata amsa. Ƙala ba ta sake cewa ba, ta haye gadon Mammy ta ci gaba da danna wayarta.

******

"Ke" 

Da ƙarfi Ma'u ta juya tana kallon Yaya Aliyu daya tsare ta da ido yana kallonta, fuskar nan tasa babu alamar wasa "Tsayuwar me ki ke yi a nan?" Ya jefo mata tambaya.

Cikin inda-inda Ma'u ta ce "In... In... Inna ce ta ce mini babu abinci, kuma yunwa nake ji". 

"Shine kika dawo soro kina yi wa mutane ihu? Kina sanar da jama'ar unguwa cewar gidanku babu abinci?". Cikin kuka ta ce "A'a Yaya, don Allah ka yi haƙuri, wallahi ba zan sake b..." "Rufe mini baki!" Ya katse ta, "Maza wuce ciki" wucewa ta yi ya bi bayanta, tafiya take tana waiwayen baya, "Idan kika sake juyowa sai na haɗa kanki da gini" ya faɗa a tsawace, tana jin hakan ba ta sake gigin juyowa ba, har ɗakin Inna ya bi ta, ko da suka shiga Inna na zaune, kusa da Inna, Ma'u ta je dan zauna, cikin tsawa ya ce "Waya baki izinin zama ne?" Da sauri ta miƙe tsaye jikinta na rawa.

 "Inna" ya kira sunanta

Ta ce "Na'am".

"Ina abincinta yake?". 

Inna ta ce "Ba'a yi girki ba, yau Halima ba ta jin daɗi ne, shine na ce ta bari tunda akwai garin kwaki sai mu kwaɗa shi muci, zuwa anjima da yamma idan ta ji sauƙi sai ta yi". 

Ya ce "Ok, ina nata garin yake?". 

"Gashi nan" Inna ta faɗa tana nuna masa inda garin yake, ta ce "Ai kasan halinta, wani irin bauɗaɗɗen hali ne da ita, tunda na sanar mata ba'a yi girki ba, ga gari nan ta kwaɗa ta ci muma shi muka ci, ta dira can ba za ta ci gari ba tunda ita ba akuya ba ce". 

Kallo ɗaya ya yi wa Ma'u babu shiri ta tashi jikinta na ɓari ta ɗakko garin nan, haɗa hannayenta ta yi, cikin kuka ta ce "Don Allah Yaya ka yi haƙuri na tuba zanci, wallahi ni ce akuyar ba su ba, Inna don Allah ki taya ni bashi haƙuri".

"Babu ruwana" Inna ta faɗa tare da kawar da kanta daga kallonta, don tsaf za ta iya yin dariya. Aliyu kuwa bai ce ƙala ba ya bar ɗakin. Yana fita Ma'u ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta zauna ta fara kwaɗon garin sai zumɓura baki take yi.


******

Tsaye take a bakin ƙofar shiga falonsa, knocking take yi tun ɗazu shiru ba'a amsa ta ba, gajiya ta yi da tsayuwar cikin dauriya ta tura ƙofar tare da yin sallama ta shiga. A kwance ta gan shi saman kujera, idanunsa a rufe, ƙarasawa ta yi ta zauna saman kujerar dake kallon tasa, bai motsa ba, haka kuma bai nuna wata alama ta ya ji an shigo ba, kallonsa Ilham ta yi tana mamakin wannan halin nasa, ta san sarai ya ji shigowarta ƙyale ta ne ya yi. Dakewa ta yi, cikin siririyar muryarta ta ce "Yaya Sudais sannu da hutawa". Shiru ya yi ba tare daya motsa ba, balle ta saka ran zai amsa mata. Ta sake cewa "Yaya Sudais ka yi mini magana mana, na san fa idonka biyu ba bacci kake yi ba". Nan ma shiru bai kula ta ba. Ilham ji ta yi kamar ta yi kuka, a Duniya tana masifar son Sudais, sai dai halin ko in kular da yake nuna mata, yana ɓata mata rai. Duk da kasancewarta ƴar uwarsa amma kwata-kwata baya nuna mata so, hasali ma tamkar ba 'yar uwassa ba. Ko ɗan jan nan a jiki na tsakanin cousins baya nuna mata.
"Yaya wulaƙanci bai dace da kai ba, ban san girman laifina zai iya zama haka a gurinka ba. Ita zuciya ba a yi mata shinge ne, amma shikenan bari na tafi... Ko ƙwaƙwƙwaran motsi bai yi ba, balle ta sanya ran zai ba ta amsar maganar da take yi.

******

ABS ORPHANAGE AND CARE FOUNDATION

Dogon gini ne da yake ɗauke da yalwatacciyar haraba. A bakin ƙofar gidan akwai security, inda yake zaune cikin nutsuwa yana lura da shige da ficen kowa. Gidan ba'a shigarsa kai tsaye sai an tabbatar da wanda ya zo ya samu cikakken izinin zuwa. Akwai bishiyoyi masu yawa a ciki, wanda hakan ke ba wa wurin yalwatacciyar inuwa mai daɗi da sanyin iska. Can gefe kana iya hango ƙaton filin wasa inda yara ke shaƙatawa. Daga can wajen ƙarshen ginin kuma, wani ginin ne da aka sake katange shi, inda ɗakunan kwana na yara da manya yake, sannan akwai ɗakin girki da banɗakuna da guraren buƙatunsu duk a ciki.
Gabaɗaya yanayin gidan yana cike da tsafta ko ina ƙal babu datti. Duk wanda ya shiga wurin zai fahimci cewa gidauniya ce ta gaskiya, wadda ke nuna taimako da tausayi ga marayu, tare da basu kulawa ta musamman. Ma'akaitan gidan ne ke shigo da buhunhnan kayan abinci, shinkafa da su taliya da macaroni, jarkokin mayuka da kwalayen magi, hadda kayan shayi. Ƙananun yaran dake gidan sai murna suke, suna tsalle tare da faɗin "Oyoyo ga Baba Sardauna ya zo!" 
Sai da aka gama shigo da kayan abincin duka. 
A hankali cikin dattako da kamala ya iso wurin, fuskarsa ɗauke da fara'a ya tsaya a gaban yaran yana murmushi. Mutanen dake kula da yaran suka gaishe shi cikin girmamawa, amsa musu ya yi fuska a sake yana tambayarsu ya fama da yara? Sannan ya mayar da dubansa ga yaran ya ce "Yaran Baba kuna lafiya?".

Suka amsa da "Lafiya ƙalau" Su na amsa masa su na riƙe rigarsa.

Yana dariya ya ce "Ma sha Allah, to ina fatan dai kowa ya ci abinci ya ƙoshi a cikin ku ba mai jin yunwa ko?". 

Suka amsa da "Eh suna tsalle-tsalle da murnar ganinsa.

Cike da farin ciki yake kallon yaran, ganin suna cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. A haka ya fara zagaya gurin yana duba sauran jama'a, sai da ya tabbatar da komai na tafiya yadda ya kamata sannan ya yi musu sallama ya bar gidan. 
Alhaji Bukar Sardauna kenan, mutum ne da Allah ya yi masa baiwa ta musamman. Mutum ne sananne sosai kasancewar sa mak yalwar arziki, wanda bai taɓa bari dukiyarsa ta sa ya raina talaka ba. A kullum zuciyarsa cike take da tausayi da son ganin mutane sun yi rayuwa cikin walwala, yana son taimakawa na ƙasa da shi. Ba irin mutanen nan bane da suke bayarwa domin a yaba musu ba. Duk wanda ya san Alhaji Sardauna ya san cewa mutum ne mai tsoron Allah, mai cika alƙawari, kuma mai son zaman lafiya. Baya son yaga mutane a cikin damuwa, duk inda ya ga maraya na kuka zuciyarsa zafi take yi masa, hakan ne ya sa ya buɗe gidauniyar taimakawa marayu da mabuƙata, domin ya rage raɗaɗin rayuwa ga zuciyar yara marasa gata. Alhaji Sardauna mutum ne mai kishin addininsa da al'umma, wanda ya fahimci cewa dukiyar da Allah ya ba shi ba amana ce da za a tambaye shi a gobe ƙiyama. Wannan ne ya sa yake yawan taimakon mutane cikin sirri, yana neman yardar Allah fiye da yardar mutane, mutum ne da kowa yake girmama shi saboda kyawawan ɗabi'unsa. Mutum ne mai albarkar hannu, da tsaftatacciyar zuciya, yana da halin dattako da kamala.

*****
"Zahra"

"Na'am Aunty Ilham"

"Dan Allah ina da wani aibu ne? Ko kuma akwai abin da bani da wanda sauran mata suke da shi?". Ilham ta yi tambayar cikin yanayi na damuwa.

Zahra ta ce "Baki da wani aibu Aunty, kuma babu abin da Allah ya rage da shi, hasali ma kin fi wasu matan abubuwa da yawa, gaki nan ma sha Allah kyakkyawa dake" ta ƙarasa maganar tana murmushi.

"Amma Zahra me ya sa Ya Sudais baya so na? Kwata-kwata baya ƙaunar gani". 

"A'a Aunty yana sonki mana, kawai dai kin san halinsa, yana da wani tsatsauran ra'ayi ne, but ki daina tunanin baya sonki, kefe ƴar uwarsa".

Ajiyar zuciya ta sauke, ba tare da ta sake yin magana ba ta kwanta, cikin tausayi Zahra take binta da kallo, tabbas ta san Ilham ba ƙara min haƙuri take yi ba, irin yadda Ya Sudais yake yarfata. A fili ta ce "Allah ya nuna mini ranar aurenki da Ya Sudais, ranar zan ba za capacity iya capacity". 

Duk da Ilham na cikin damuwa sai da ta yi murmushi ta ce "Amin ya hayyu ya ƙayyum".


Amanarcool 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol