Free chapter · Read without an account
Chapter 3
by Amanarcool · SAUTIN KARSHE
Ringing ɗin da ya ji wayarsa na faman yi ne ya sa shi buɗe idonunsa ya mayar ya sake lumshe su. Jin wayar ta ci gaba da ruri, ya sanya a hankali ya miƙa hannu ya ɗauki wayar yana duba waye yake damunsa da kira, sunan Hanif ya gani a kan screen ɗin, tsaki ya yi ya ajiye wayar yana sake lumshe idonsa. Wani kiran ne ya sake shigowa, a hasale ya tashi zaune yana ɗaga kiran, kafin ya yi magana Hanif ya ce "Sannu sarkin ƴan wulaƙancin duk duniya da rashin son takura, Sudais wane irin wulaƙanci ne ina kiranka tun ɗazu baka daga mini waya ba? Kuma na san ka ga kirana".
"Kar ka sake damuna da wannan banzan kiran naka" cewar Sudais, daga haka ya kashe wayar.
Cikin takaici Hanif ya sake kiransa, sai dai bai ɗauka ba. Daga ƙarshe ma ya kashe wayar gabaɗaya ya yi kwanciyarsa.
*****
"Inna don Allah ina so ki nema mini alfarma a gurin Ma'u".
Inna dake zaune a tsakar gida saman tabarma ta ce "Alfarma kuma? Wace irin alfarma Halima?".
"Dama ina son ta karɓo mini suga kantin Isah ne, to kin san halin ƴar taki ko na yi mata magana ba zuwa za ta yi ba, shine nake so ki ɗan saka baki". Inna ta yi murmushi ta ce "Kai Halima ban da sharri fa".
"Allah Inna babu zancen sharri kin san Ma'u hukuma ce sai da rarrashi". Dariya Inna ta yi, sannan ta fara kiran Ma'u dake cikin ɗaki.
Daga can cikin ɗakin Ma'u take faɗin "Na'am Uwata! In fito ne? Allah ya sa wani abin kwaɗayi ne za ki bani?". Inna ta ce "To acici, ba abinci ba ne, fito ki karɓowa Halima suga kantin Isah".
"Haba dai, Inna dama aike ne? Kuma aiken bama naki ba na wannan matar, ina ƴarta take da ba za ta aike ta ba sai ni? Gaskiya ba zan je ba, ni bacci ma nake yi yanzu haka duk wannan zancen da muke yi a cikin bacci ne. Don Allah kar a sake tashi na idan ina bacci kin san aljanuna ba sa son haka".
Dariya ce ta kusa suɓucewa Inna, amma sai ta dake ta ce "Ma'u bana son shashanci, gidan uban wa kike da aljanu? Za ki fito ne ko sai na isko ki da abin duka ɗakin nan?". Shiru Ma'u ta yi ba ta tanka mata ba. Inna ta yi magana har ta gaji Ma'u ko tari ba ta yi ba. Tashi ta yi ta ɗauki mafecin dake kusa da ita ta nufi ɗakin. Da sauri Halima ta ce "A'a Inna, don Allah kar ki dake ta ko ki yi mata dole, ki rabu da ita ni na haƙura ma. Yanzu idan kika ce za ki yi mata dole daga ƙarshe abin a kaina zai ƙare ko ta ce za ta dake Abida gashi yau ba ta jin daɗi, zazzaɓi ne ya rufe ta sai da na ba ta magani".
"Yawwa Alhamdulillah, gara da Allah ya kawo ka, kaga Ma'u ce ake ta fama da ita tun ɗazu ta je ta karɓo wa Halima suga ta ƙi, kai je ka yi mata magana da kanka ko za ta j...." Ai Inna ba ta gama rufe bakinta ba sai ga Ma'u ta fito a guje tana zare ido. Jikinta na rawa ta ce "Aunty Halima kawo kuɗin na karɓo miki" ta yi maganar tana leƙen inda Yaya Aliyun yake. Miƙa mata kuɗin Halima ta yi, da sauri ta karɓa, Inna ta ce "Ai ya shiga banɗaki ne, yau ko kin karɓo sugan nan sai ya zane ki". Ma'u dai ba ta ce komai ba ta bar gidan kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki. Tana fita Halima ta tuntsure da dariya tana faɗin "Kai Inna, kinga yadda kika ɗaga mata hankali? Wato a gidan nan baban Abida kaɗai Ma'u take tsoro". Inna ta ce "Na san haka kaɗai zan yi mata ta je aiken nan, to ya jikin Abidar da sauƙi?".
"Eh jikin da sauƙi, tana shan gama shan maganin ta yi bacci".
Koda Ma'u ta fita sauri ta dinga yi saboda kar ta daɗe ta ƙarawa kanta wani laifin a wurin Yaya, bayan ta karɓo sugan ne a daidai kwanar da za ta karya ta shiga layin gidansu ta ci karo da Sa'a ƙanwar Sani da ya yi mata dariya lokacin da ta dawo daga makaranta. Shan gabanta Ma'u ta yi, cikin fargaba Sa'a take kallonta, kafin ta ce "Ma'u lafiya kika tare mini hanya?".
"Kutumelesi, ke dan uwarki Ladi me daddawa ni kike kira da Ma'u haka gatsal? Ban hana a kira sunana kai tsaye ba? Ba cewa na yi a riƙa kirana da Aunty Ma'u ba? Lallai kin ƙarawa kanki laifi kan laifi, da wanda Yayanki ya ja miki da wanda kika jawowa kanki yanzu". Ma'u ta kai ƙarshen maganar tare da kai wa Sa'a wani bahagon mari.
Dafe kunce ta yi ta fashewa da wani marayan kuka, ta ce "Haba Ma'u, me na yi miki da za ki mare ni? Wallahi Allah ya isa ban yafe b...." Ai ba ta rufe baki ba Ma'u ta sake kai mata wani marin tana faɗin "Dan ubanki ban hana ki kiran sunana kai tsaye ba shi ne kika sake faɗa? Yau sai kin gane Allah ɗaya ne" ɗaga hannu ta yi za ta kuma kawai mata duka ta ji an riƙe hannunta ta baya, koda ta waiwaya Sani ne yana huci, cikin rashin tsoro ta ce "Dan Allah malam sake mini hannu ka wani riƙe ni sai ka ce matarka" ta ƙarasa maganar cikin tsiwa.
"Uban me ta yi miki kika mare ta?" Ya tambaya yana kallon Ma'u.
"Dakata! Kar ka kuskura ka zage ni, dan wallahi ka zagar mini uba gabaɗaya danginku na uwa da uba sai na ɗebe musu albarka".
"Tambayarki nake yi me ta yi miki kika zage ta?".
"Ban sani ba!". Ma'u ta ce tana huci.
Sani ya dubi Sa'a ya ce "Ke zo ki rama marin da ta yi miki" ƙin zuwa ta yi, ta ja ta tsaya gefe ɗaya tana matsar ƙwalla. "Ba magana nake yi miki ba ne? Zo ki rama na ce".
Cikin kuka Sa'a ta ce "A'a na haƙura kawai, na yafe mata". Takaici ne ya kusa kashe Sani. Ma'u ko wata uwar dariya ta yi, ta ce "Yarinya ashe kina da hankali da wayo, kin taimaki kanki, kuma kin rufawa kanki asiri, inda kin yi gigin marina, hmmm da idan na riƙe ki sai na mayar da hancinki kamar na mai tafiya da sanda". Ta kai ƙarshen maganar tana sake fashe wa da dariya.
Da sauri Sani ya ce "Ke uban namu ma baki bari? Wallahi ba don ina ganin mutumcin Yayanki ba da yau sai na naɗa miki shegen dukan da sai kin kasa moruwa na wasu ƴan kwanaki".
Kallon sama da ƙasa Ma'u ta yi masa, sannan ta ce "Sake mini hannu".
"Ba zan saki ba".
Sake mini hannu!".
"An ƙi ɗin".
"Sani ka sake mini hannu tunda bana uwarka Ladi me daddawa ba ne!". Ɗaga hannu ya yi zai kai mata mari jin yadda ta ambaci sunan mahaifiyarsa. Da sauri Ma'u ta duƙe tare da ɗakko ƙaton dutsen da ta gani a ƙasa ta kwaɗa masa shi a goshi, nan take wurin ya yi tsini ya kumbura. Duk da haka Sani yaƙi sakin ta. Babu za to ya ji Ma'u ta kurma wani uban ihun da sai da Sa'a ta tsorata ta bar wurin aguje. "Wayyo Allah! Jama'a a kawo mini ɗauki Sani zai keta mini haddi, jama'a ku zo ku yi ceton ra...." Ba ta gama rufe bakinta ba Sani ya sake ta, da wani irin gudun bala'i ya bar wajan. Dariya Ma'u ta yi ta ce "Shege ka ce ba ka ji, da ka tsaya wallahi in yi maka sharrin da ba mai fitar da kai sai Allah". Juyawa ta yi za ta tafi, sai dai me, sugan da ta siyo ni ta ganshi zube ya watse ga ƙasa, tun lokacin da ta je marin Sa'a sugan ya faɗi ba tare da ta sani ba. Hannu ta ɗora a kai tana faɗin "Wayyo Allahna ni Asma'u, shikenan yau ƙaryata ta ƙare, na san Yaya Aliyu kashe ni zai yi". Ta yi maganar tare da nufar hanyar gida.
*****
Cikin nutsuwa yake sakkowa daga saman benen har ya ƙaraso cikin falon, gabaɗaya jama'ar gidan na zaune, Mammy, Zahra, Faruk, sai kuma Ilham da ke zaune a gefen Mammy. Kallonsa suke yi yadda ɗaure fuska kamar bai taɓa yin fara'a ba, ba tare da ya kula kowa ba ya nemi guri ya zauna. "Sannu da fitowa Yaya". Faruk ya ce yana kallonsa, a maimakon ya amsa masa gaisuwar sai ya mayar da dubansa ga Mammy ya ce "Barka da hutawa Mammy". Murmushi ta yi tare da girgiza kai ta ce "Kafin ka gaishi ni ai ya kamata ka fara amsa gaisuwar ɗan uwanka mana". Sudais kallon Faruk ya yi ya ce "Yawwa Faruku" daga haka ya sake kallon Mammy ya ce "To na amsa masa, nima amsa mini". "Yawwa Adamu". Sake haɗe fuska ya yi, ya kalli Zahra da Ilham da suka sunkuyar da kai suna dariya. "Mammy a gaban yara za ki kira sunana haka?".
"Kai da ka kira sunan yarona da Faruku fa, kuma ka san baya son haka" Mammy ta yi maganar tana dariya. "To ai sunansa ne".
"Eh ai kai ma sunanka ne Adamu". Cewar Mammy.
"Mammy sunan sirikinki ne fa kike faɗa?". "Eh na ji ɗin ba komai, ai ba shi na kira ba kai Adamu Sudais". Shiru Sudais ya yi bai sake magana ba, saboda ya lura idan ya biye wa Mammy za ta saka yaran nan su raina shi. Daga Faruk har su Zahra kowa ƙume dariyarsa ya yi, ba su da ikon saka baki a cikin wannan dramar matuƙar ba shi ne ya sako su ba. Sudais ya kalli Zahra da Ilham ya ce "Kai ku sauko ƙasa ku kama kunnuwanku".
Da sauri Mammy ta kalle shi ta ce "Me suka yi maka kuma? Bayan tun ɗazu ina tare da su ban ga wani laifin da suka yi maka ba?".
"Mammy wai me ya sa wani lokacin kike son cakar dani a gaban yaran nan ne?" Ya mayar da dubansa gare su, cikin tsawa ya ce "Kai ba magana nake yi muku ba ne?". Babu shiri suka diro daga saman kujera suka kama kunnensu.
Kallon agogon hannunsa ya yi, ya ce "Yanzu ƙarfe shida, kada wadda ta tashi a gurin nan sai 7 ta yi".
"A yi haƙuri babban Yaya ina nema musu afuwa" Faruk ya yi maganar yana kallonsa, kallon da Sudais ya yi masa ne ya sa babu shiri ya ce "Tuba nake" .
Mammy ta ce "To ina nema musu afuwa, a yi haƙuri, kaga lokacin sallah ya kusa ai". Tashi Sudais ya yi yana kallon saƙon da Hanif ya turo masa a waya ya ce "Idan lokacin sallar ya yi su tashi". Daga haka ya bar falon gabaɗaya.
Dariya Faruk ya fara yi yana kallon su Zahra da suka fara mutsu-mutsu, ya ce "Ai Allah ya ƙara waya aike ku yi masa dariya?". Mammy ta ce "Ba wata dariyar da suka yi masa, sai dai ko in laifin da Zahra ta yi masa ɗazu ne, shi ne yanzu ya haɗa hadda Ilham ɗin da babu ruwanta ya hukunta su tare".
"Mammy ina kallonsu fa da kika ce masa Adamu suka riƙa dariya".
"Au haka aka yi?" Mammy ta faɗa tana dariya. "Ai lamarin Yaya sai shi, kuma wai hadda Ilham amaryar tasa" Faruk ya faɗa yana dariyar su.
Mammy ma dariyar take yi. Zahra kuwa tuni ta fara shashekar kuka saboda ta fara gajiya.
****
Koda Ma'u ta isa gida duhun magariba ya fara yi. A zauren gida taja burki ta tsaya tana leƙen cikin gidan ko za ta hango Yaya Aliyu, tana nan tsaye ta bayanta ta ji an ce "Me kuma kike yi wa tsayuwa a nan?". Zabura ta yi da sauri ta waiwaya baya tana zaro ido, "Ba magana nake yi miki ba?". Cikin inda-inda ta ce "Ba... Ba... Ba komai". Kallonta ya yi da kyau, ya san ba banza ba, kuma yanayinta ya nuna ba ta da gaskiya. Da hannu ya nuna mata alamar ta shiga ciki, kamar wata munafuka haka ta shiga cikin gidan. Da sauri taga Ya Aliyu ya shiga ɗakin Halima, tana ganin haka a guje ta faɗa ɗakin Inna, sai dai ba ta tarar da ita a ɗakin ba. Kamar maganar Inna ta ji a ɗakin Halima, don haka ta dawo baƙin ƙofa tana leƙe. Ya Aliyu taga ya fito yana dafe kansa, ya jingina da gini, taga Inna ta fito ta tsaya kusa da shi tana faɗin "Gadanga ba tsayi ya kamata mu yi ba, kamata ya yi mu san abin yi, wannan karon naga alamar ciwon nan bai zowa yarinyar nan da sauƙi ba". Ya Aliyu ya kalli Inna da rinannun idonsa ya ce "Inna, ina tunanin yadda zan yi ne, wallahi bani da isasun kuɗi a gurina, yanzu ko cewa muka yi mu kai ta asibiti bamu da kuɗin da zamu biya a duba ta, kwata-kwata abin da yake hannuna bai wuce dubu biyu ba". Inna ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihim raji'un, nima bani da kuɗi a hannuna, amma Gadanga ina wannan asibitin da ake taimakawa marasa ƙarfi, me zai hana mu ɗauke ta mu kai ta can?". Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya ce "Inna bana son wulaƙanci ne, kada mu je a yi mana wulaƙanci tunda bamu taɓa zuwa ba, kinga bamu san yadda tsarin abin yake ba?".
Inna ta ce "A'a, ni dai a yadda na ji labarin asibitin ba'a wulaƙanta kowa, an ce file ma kyauta ake buɗe wa mutum shi. Duk wani abu da ake yi kyauta ne, ita fa wannan asibitin an buɗa ta ne kawai domin taimakon al'umma".
Kallon Inna ya yi, kafin ya ce "To shikenan bari na samo abin hawa" daga haka ya fita ya bar gidan. Yana fita Ma'u tayi but ta fito tana faɗin "Inna kar dai Abida ce ba ta da lafiya?".
Tsabar ruɗewa ya sa Inna ta manta da aiken da aka yi wa Ma'u ta ce "Eh ita ce". Da sauri Ma'u ta shiga ɗakin Halima, nan ta tarar da Abida a kwance, idanunta na kakkafewa, numfashi ma da ƙyar yake fita. Halima na zaune a gefe ta zuba mata ido tana kallo. Shigowa Inna ta yi, ta ce "Halima canza mata kayan jikinta yanzu zamu tafi asibiti da ita. Gadanga ya je ya nemo abin hawa, ke kuma sai ki tsaya a gida ke da Ma'u ku kula da gidan".
"To Inna" Halima ta faɗa tana miƙewa cikin sanyin jiki ta canza mata kayan jikinta. Inna ta tafi nata ɗakin domin ta shirya, Ma'u fitowa ta yi gabaɗaya jikinta ya yi sanyi, ta nemi guri a tsakar gidan ta zauna tare da yin tagumi.
Amanarcool
***