Free chapter · Read without an account

Chapter Twenty Six

by The Healer's Pen · ƘWAI BIYU

Ɓangarensa ya nufa kai tsaye. Amma da mamakinsa ya iske Radiya ta gyara ko'ina da kanta tana fesa air freshener a kowanne lungu da saƙo na bedroom ɗin nasa.


Sannan sanye take da wasu ƙayatattun kayan bacci riga da dogon wando farare, ga cikinta ya tasa kaɗan gwanin sha'awa. 


Daga can gefe kuma ga abincin darensa ta jera akan wani ƙaramin carpet.


Take yaji duk nauyin da yake kansa da ƙirjinsa ya sauka. Yanayinsa ya fara daidaita, musamman yadda ɗakin yake tashin wani ni'imtaccen ƙamshi mai sanyaya zuciya.


Da sanɗa ya ƙarasa in da take, ya rungumeta ta baya, tare da tura kansa a tsakiyar bayanta yana shaƙar ni'imtaccen ƙamshin jikinta, sannan ya zagayo da hannunsa daidai saman cikinta yana shafawa.


Da sauri ta juyo ta fara ƙoƙarin janye shi, amma ya riƙe ta gam.


"Ka daina acting kamar soyayya muke yi fa...tam, ba ruwana idan na tafi kayi kewa ta."


Murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba, tare da sake ƙanƙame ta a jikinsa.


Ajiyar zuciya tayi, saboda yadda taji ya takureta da yawa, sannan ta sake cewa:


"Don Allah ka bari..ko so kake yi mu faɗi?"


Sai sannan ya sake ta, sannan ya juyo da ita ta fuskance shi yace:


"It's just cuddling."


Ture shi tayi gefe tare da hararsa. Sannan tace:


"Kayi wanka kaci abinci, ina son zamu yi wata magana."


Jinjina kansa yayi fuskarsa da alamar tambaya, sannan ya taɓe bakinsa tare da faɗin "OK" sannan ya nufi banɗaki.


Bayan ya fito ya zauna yana cin abinci, a nutse ta kalle shi tace:


"Don Allah me ya saka ka hana ni zuwa aiki?"


Kawar da kansa yayi gefe ba tare da yace komai ba, ya ci gaba da cin abincinsa.


"Don Allah ka barni na koma, kaji?"


"Ke baki san abinda yake cikin ki bane?"


Ya faɗa yana nuna cikinta da cokali.


Ɓata fuskarta tayi a sigar shagwaɓa, sannan tace:


"Haba Sultan, kamar a kaina aka fara yin ciki?"


"A kanki aka fara mana. Ko kin mata?"


Ya faɗa yana kallon cikin idonta.


"Ni dai don Allah ka barni na koma. Kaga ni kaɗai na ke zama ka hana ni fita, idan ka fita sai dai nayi ta tunani ni kaɗai. Nayi maka alƙawarin idan naje bazan yi aiki da yawa ba."


Ƙura mata ido yayi na ɗan lokaci, sannan ya ci gaba da cin abincinsa. Ba tare da yace komai ba.


Duk da wannan miskilanacin nasa yana matuƙar ɓata mata rai. Amma haka ta daure ta ci gaba da rarrashinsa. 


Amma da ta lura bashi da niyyar barinta, dole ta haƙura ta kyale shi.




BAYAN KWANA UKU 

(Ƙarfe takwas da mintuna goma na dare).


Ba ƙaramin farinciki ne ya bayyana a fuskarta ba a daidai lokacin da taga sun ƙaraso daidai inda me balangunta na kwanaki yake, har sunyi parking.


Wani ƙayataccen murmushi ta saki, sannan ta kalli Sultan da ya ƙura mata ido tace:


"Amma dai Allah ya saka maka da gidan aljanna. Daman nan zamu zo?"


Murmushi kawai yayi a daidai lokacin da ya sauke glass ɗin motar. Da sauri mai balangun ya ƙaraso tare da risinawa.


"Baba ka gane ni?"


Radiya ta faɗa tana murmushi. 


Shima murmushi yayi, sannan yace:


"Sosai ma kuwa ranki ya daɗe. Ta yaya zan manta ki?"


Cike da zaƙuwa tace:


"To ka bani kamar na rannan, guda biyu."


"An gama ranki ya daɗe."


Ya furta tare da komawa cikin sauri.


Kallo kawai Sultan yabi ta dashi tare da yin murmushi ya girgiza kansa.


Ita kuwa kafin ya ƙaraso duk ta ƙagu, yawunta ya gama tsinkewa. Allah ya taimake ta tun ranar ta manta da balangun, da ta sake ta tuna dashi, da ko za'a yi yaƙi sai ta ci.


Cikin hanzari ya miƙe mata. Sultan ya damƙi daloli da bai san adadin su ba ya miƙa masa. Cike da mamaki dattijon nan yayi ta godiya tare da jero addu'o'i. 


Sannan daga bisani suka bar wajen.


Wani shahararren gidan abinci suka nufa, ya nemi waje yayi parking. 


Sannan ya juyo ya kalli Radiya da tayi nisa wajen cin namanta yace:


"Ranki ya daɗe...kinga na baki abinda kike so ke da ɗa na ko? To ki zauna a motar nan kar kice zaki fito. Zan shiga na karɓi saƙo."


Jinjina masa kai kawai tayi alamar gamsuwa. Don ita tayi nisa a harkar gabanta, bata da lokacin yin magana.


Girgiza kansa ya sake yi, sannan ya sake ja mata kunne tare da miƙa mata ledar ruwa da lemo yace:


"Bazan wuce 20 minutes ba In shaa Allahu. Karki sauke glass ko ki buɗe ƙofar. Kin ji ni ko?"


"OK sir."


Ta furta tana girgiza kai.


Murmushi ya sake yi, sannan ya zaro face mask ya saka a fuskarsa, sannan ya fice.


Kai tsaye wani keɓaɓɓen lambu ya nufa wanda aka ƙawata shi da dadduma carpets masu tsadar gaske. A zaune a wajen, team ɗinsa ya hango su uku.


Suna ganinsa suka ɗago da kansu alamar girmamawa amma a sirrince.


Waje ya nema ya zauna, bayan sun amsa sallama. Sannan ya kalle su yace:


"Offline analysis operation only."


"OK sir."


Suka amsa tare da kashe wayoyinsu, da router wajen gabaɗaya.


Sannan cikin gaggawa Aliyu ya kalle shi yace:


"Sir, mun kammala binciken bin diddiginsu, mun samo mutum uku, biyu a Lagos, ɗaya daga Port Harcourt. Dukkanninsu muna bin diddiginsu tare da hukumar DSS da taimakon NCC."


Ya ƙarasa bayanin tare da karkata fuskar laptop ɗinsa zuwa ga Sultan.


A nutse yayi nazarin komai, sannan ya kalle shi yace:


"Zuwa nan da yaushe za'a kama su?"


"DSS sun bada 48-72 hours saboda suna so su kama su ne a lokaci guda saboda gudun kar ɗaya ya sanar da ɗayan."


Sake jinjina kansa yayi. Sannan ya kalli Sandra yace:


"Mene bayanin asusun bankunan?"


"Sir, mun samo bayanan ne ta hanyar kuɗin da aka tura daga wani account na mazaunin garin Kaduna wanda ya kasance tsohon driver A.S Malami ne.


Sannan an rarraba kuɗaɗen a asusu daban-daban ciki har da wani account na daban na wata mace mazauniyar Kano da aka tura da wasu kuɗi ƙalilan. 


Sai dai binciken ya nuna cewar babban wanda yake ɗaukar nauyin aikin yana ɓoye kansa, kamar su ma umarni kawai aka basu ba tare da sun san ko waye ba.


Mun gane hakan ne ta binciken kiraye-kirayen wayar da suka yi da text messages wanda hukumar NCC ta bamu damar dubawa. "


Sake nutsuwa yayi sosai ya karanta abinda binciken ya nuna daga laptop ɗin Sandra, ba tare da ya ɗago ba yace:


"Me binciken lambobin ya nuna?"


Musa ne ya gyara zamansa sannan yace:


"Sir, mun tabbatar da waɗannan mutanen guda uku sun aikata wannan harin ta binciken kiraye -kirayen wayoyinsu. Amma sai dai akwai wasu account guda biyu da suka karɓi kuɗaɗen kamar yadda Aliyu yayi bayani.


Ɗaya account ɗin namiji ne, ɗaya kuma na mace. Sai dai kuɗin da aka tura a na macen basu da yawa, sannan anyi musu laƙabi da 'kuɗin sayen waya.'


Amma babban abun dubawar anan shine sunyi waya har sau biyu da wanda ya tura kuɗin kuma ga dukkan alamu a Lagos yake da zama.


Hakan ya saka muka bi diddigin kiraye-kirayen wayar wadda aka turawa kuɗin sai dai bamu samu komai ba sai hirarrakin yau da kullum wanda basu da alaƙa da bincikenmu.


Sai kuma wata babbar barazana da muka iske acikin hirar tasu wadda zata iya sakawa a rasa rai."


Ba tare da fuskar Sultan ta sauya ba yace:


"Wacce irin barazana ce?"


"Yunƙurin kisan kai ne. Sir."


Shuru ne ya biyo baya. Sannan Aliyu yace:


"Idan ka bada izini Musa zai kunna maka kaji."


Gyaɗa kansa Sultan kawai yayi. Sannan Musa ya kunna sautin kamar haka:


"Kin san Allah...sai da malamaina suka faɗa min arziƙi na yana jikin yarinyar nan shiyasa na aure ta. Amma sunce sai nayi da gaske saboda zata waye sosai idonta zai ƙara buɗewa zata iya bijire mun. Shiyasa wallahi tana dawowa da kuɗin nan zan turmushe su...da wuri."


Dariya aka yi ta ɗaya ɓangaren, sannan akace:


"Haba baby ita bata da wayo da zata baka kuɗin ta?"


"Naki wasa ne baki san yadda Radiya take so na bane. Ke bari na faɗa miki gaskiyar abinda na shirya. Wallahi in dai tayi gardama akwai gubar da na shirya zan haɗa da kaina na zuba mata a abinci. 


In dai ta ci a hankali zata lalata mata zuciya, ƙoda, da hanta. A kasa gane me yake damunta, ina mai tabbatar miki a ƙasa da wata uku zata mutu. 


Kinga babu wanda yasan wannan shirin namu, babu wanda yasan tazo da kuɗin, sai na ɗauke ki mu gudu mu bar ƙasar."


Aka fashe da wata irin dariyar mugunta.


"Gaskiya yau baby ka cake da yawa. Irin wannan hira haka..."


A daidai nan Musa ya katse hirar.


Jim...Sultan yayi yana ƙoƙarin ɓoye yanayinsa. Zuciyarsa tana daɗa tariyo masa hirar, musamman da yaji an ambaci sunan macen da yafi ƙauna a duniya. 


Saboda sarai ya sani 'Radiya' ba suna bane da yake gama gari. Jikinsa yana bashi cewar tabbas Radiyarsa ake nufi.


Daidaita yanayinsa yayi, Sannan ya kalle shi yace:


"Voice authentication. Full biometric analysis."


Da sauri yayi danne-danne a computer sannan yace:


"Mun samu daidai da muryar, ga bayanansa."

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.