Free chapter · Read without an account
Forbidden deal
by ZAHRAA · Zumar Hamada 🍯 🏜️
Tadala ta kura wa yatsunsu da ke sarƙafe ido, zuciyarta kamar za ta fito fili. Cikin sanyin jiki tace Daddy… wallahi tsoro nake ji Idan Anty Sadiya ta ganu mu fa? Idan ta gane abin da ke faruwa a tsakaninmu, wace fuska zan nuna mata? Ita ce fa ta ɗauko ni daga Agadez…Dan inganta rayuwata ,Alhaji Kamal ya sauke ajiyar zuciya ,A hankali ya ƙara matse hannunta cikin nasa ,Babu wanda zai sani, Ki daina tsorata kanki haka Alkawari ne na wata shida, Idan bayan wannan lokacin baki ji komai a rainki ba, zan mutunta shawarar ki I promise you
Tadala ta yi shiru Kalaman nasa suna rikita mata tunani,Wani ɓangare na zuciyarta na gaya mata ta fita daga wannan al’amari tun bai yi nisa ba ,Wani ɓangaren kuma yana tuna mata irin alherin da zata samu idan ta gama karantun ta
Ki kalle ni, Tadala muryar sa ya dawo da ita daga tunanin data fada ,Tana dagowa suka hada ido ,Ba zan cutar da ke ba Nima Ina da yara mata kuma bazan so Abinda zai cutar dasu ba so ki saki jikin ki kinji ?gyada masa kai tayi alamun ta gamsu da maganar sa
“To yanzu dai kin amince da pinky promise ɗinmu?
Tadala ta yi shiru na wasu daƙiƙu Daga ƙarshe, ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ɗaga kai a hankali alamar eh.
Wani murmushi ya bayyana a fuskar Alhaji Kamal Good girl, good nyt kinji ya fita tare da rufo mata kofar ,ta dade Tana sake sake Kafin bacci ya dauke ta
Washegari da safe, part din sadiya sai hada hada ake na breakfast dik Sun hallara a dining Alhaji Kamal yana zaune am yana danna wayarsa cikin natsuwa , fuskarsa a tamke Kamar ba shi ya gama fadawa Tadala zafafan kalamai a daren jiya ba.
Tadala ta fito daga ɗakinta sanye da doguwar riga material tayi shirin Tana tafiya makaranta, sadiya da daddy ta gaisar suka amsa mata sama sama as usual yan biyu da Ahmad ma suka gaishe ta ,zama tayi Tana cin abincin ta nutse ,har ta kamallah
sallamar wata baƙuwar murya mai cike da kamala ta ratsa babban falon gidan.
Alhaji Kamal ne ya fara miƙewa yana murmushi lokacin da ya ga wacce ta shigo. Zaheera? Ke ce haka da sassafe? Sadiya ma tabi Bayan sa ,sallama Tadala tayi ta Ahmad ita ta sauka kasa dan tayi latti Yau har kasa Tadala tsuguna ta gaishe da bakuwar jin sunan zaheera yasa ta gane yayar dady ce daya Kira ranar a mota
Sosai Zaheera ta tsayar da idanunta a kan Tadala, ta kura mata ido na wasu daƙiƙu, sannan ta ɗan juya ta kalli ɗan uwanta Cikin ƙanƙanin lokaci, tsohuwar dabarar Zaheera ta sanya ta gano asalin karatun Alhaji Kamal ,ta hango tsantsar son Tadala dake boye a cikin idanunsa
Motsa bakinta tayi a hankali ta kalli kamal She’s beautiful ,kawar da kai yayi Kamar be gane me zaheeran tace ba
Tashi tashi kinji yan mata ,ta rike hannun tadala ,A daidai lokacin ne ragowar matan gidan suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya kowa na shirin tafiya wajen aiki tunda gari ya waye ,Ganin Twin Sisterɗin mijinsu da sassafe haka ya sanya duka kishiyoyin jan birki suka tsaya cirko-cirko, kowa fuskarsa cike da mamaki.
Daya bayan ɗaya suka soma gaishe da Zaheera cikin girmamawa, ta amsa ba yabo ba fallasa ,inda ita kuma ta kauda kai ta kalli sadiya yanzu Sadiya, kina nufin cousin ɗinki na nan garin tun lokacin taron suna aminatu ... amma shine ban ganta ba ko sau ɗaya?
Sadiya ta ɗan sosa ƙeya Cike da borin kunya tace Eh wallahi tana nan... Itace ta ƙi zuwa wajen taron,dayake ba ta da sabo da mutane sosai
Tadala ta ɗaga kai ta kalli sadiya cikin mamaki, sadiyar ce da kanta ta hanata zuwa Wajan sunan , tace ta zauna a ɗaki kar taje ko'ina . Amma sai gashi yau Mami ta juya maganar a gaban kowa
Zaheera ta taɓa kafaɗar Tadala cikin nuna iko ta ce To daga yanzu a dinga sata a cikin kowace harka ta gidan nan, itama memba ce na wannan gidan Makaranta zaki tafi ko?
"Eh, Anty ,Tadala ta amsa a hankali cikin sanyin murya.
To shikenan. Idan baki da lectures kiyi magana da Sadiya, sai Awaisu ki ya kawo ki gidana, kin ji ko?
To Anty, nagode," Tadala ta faɗa tana wasar da yatsun hannunta,, gaba kan Sadiya ya gama fashewa saboda daɗi! Ganin yadda Zaheera—wacce kowa ya sani ba mace bace mai son mutane ko saurin sabo—ta nuna tsantsar ƙauna da fifiko ga Tadala a gaban sauran kishiyoyinta, ya sanyaya mata rai sosai Ta ji wani irin alfahari ya cika
A can harabar jami'ar Base University, Tadala da Farida suna zaune a ƙarkashin wata bishiya mai inuwa, nesa kaɗan da sauran ɗalibai. Gaba ɗaya hankalin Tadala a tashe yake, Ta kalli Farida ta soma ba ta labarin daren jiya
Farida, wallahi yanzu haka tsoro ya sani kuka wani irin Masifa ne haka ?Nadamar duniya ta dame ni na yarda da wannan shauraɗin na Alhaji Kamal... Kawai fa na amince masa ne saboda tsoro da kuma son ya bar ɗakin na huta, amma gaskiya ba zan iya ba Ya zan yi da rayuwata?
Farida ta ɗan gyara zamanta, fuskarta cike da son jin labarin ,Wane ne ma wannan Daddy' ɗin naki ne, Tadala? Menene ainihin sunansa da kowa ke shakka haka?
Tadala ta matso kusa da ita ta raɗa mata a kunne Sunansa dai Alhaji Kamal Usman Kibiya... amma naji Ana kiransa da Gidadon Katsina
Wani uban tsalle Farida ta yi, What the hell?! Tadala, a gidan biloniyare kike ashe?Shin kin san ko wanene mutumin nan da kike magana a kansa kuwa? Kin san darajar da yake da ita a ƙasar nan? Chapdi
Tadala ta girgiza kai cikin sanyin jiki, hawaye ya ciko mata ido ,Ni ba ruwana da ko shi wanene ne, Farida! Kuɗinsa ko mulkinsa ba su gabana. Kawai ki ba ni mafita... ya zan yi in fita daga wannan tarkon?
Farida tayi fari da idanu, ta taɓa kafaɗar Tadala cikin kwantar da hankali tace, Maza irin su Alhaji Kamal, idan suka ba da baki, suna da riƙe alƙawari sosai, Shawarata a nan ita ce ki ba shi dama kawai tunda har kin riga kin yi masa pinky promise. Idan har kin san zuciyarki tana da ƙarfi kuma ba za ki faɗa cikin son sa ba (falling for him), to ki biyo masa ta yadda yake so.
Ta ɗan matso kusa da ita ta ci gaba da cewa, Idan wata shidan nan suka cika kuma baki nuna alamun soyayya ba, za ki gani da kansa zai rabu da ke cikin sauƙi ba tare da wata matsala ba. Kinga idan kika yi haka, kin huta da damuwa, kuma duka dabarunsa za su tafi a banza
Tadala ta sauke ajiyar zuciya, tana tunanin kalaman Farida, ko da yake har yanzu akwai wani tsoro dake rurruƙa a ranta na abin da zai faru idan dabarar biloniyaren ta fi tata ƙarfi...
Bayan sun gama lectures , Farida ta ja Tadala suka nufi wani kanti dake tsakiyar birnin Abuja. Suna shiga, idanun Tadala suka kaɗa lokacin da ta gane shagon ne na siyar da kayan baccin mata masu bayyana sura (sexy lingeries & undies) kala-kala, gwanin ban sha'awa.
Tadala ta tsaya tana kallon yadda Farida ke ta zaɓar matsattsu da marasa nauyi a ciki, sosai ta yi mamakin yadda Farida ba matar aure ba amma take siyan waɗannan kayan. Sai dai kuma ta sake tunani a ranta, ta ga ba abin mamaki ba ne duba da yanayin rayuwar Farida da irin wayewarta ta birni.
Suna kan hanyarsu ta dawowa cikin mota, Farida ta yi fakin a gefen hanya, ta ɗauko wayarta ta kunna kyamara tana murmushi.
"Hey guys! It’s your girl Farida Gayu ,Yau ina tare da ƙawatata ta musamman, ta juyo da kyamarar da sauri ta fuskantar da ita daidai fuskar Tadala. "Tadala, say hi to the camera!
Tadala ta juyo cikin kunya, ta ɗan sunkuyar da kanta tana murmushi. Hiii... sannunku.
"Guys, ga Tadala buzuwa tana gaishe ku!Farida ta faɗa tana dariya kafin ta kashe kyamarar.
Daidai lokacin, wayar Tadala ta soma ruri. Ta duba taga kiran Moussa ne Bayan sun gaisa cikin sanyin murya, Moussa yace Tadala, naga kin turo mini da maƙudan ƙudi ina kika sami wannan kuɗin?
Tadala ta yi saurin katse shi cikin farin ciki ta ce, "Moussa, don Allah ka je ka siyo kayan abinci mai yawa ka kai gida Ka siya muku buhun shinkafa da sauran kayan amfani ,A dibarwa fiza Sannan ka siyo Kaji guda biyu a yi miya mai daɗi yau.
Moussa ya ƙara daure fuska, Ina kika sami kuɗi , Tadala? Laaa "Mijin Anty Sadiya ne ya ba mu kyauta, ni da duka yaran gidan baki ɗaya ,To naga kuɗin ya yi yawa a gurina, shi yasa na tura maka ,Wata nannauyar ajiyar zuciya Moussa ya sauke, sannan ya ce, "
Allah ya miki albarka Tadala, ya tsare mini ke ki kula da karatun ,yanzu Zan tafi kasuwar Yau Aghali sai yafi kowa Murna zai ci kaza
Bayan sun gama wayar, Farida ta juyo tana kallon Tadala dake ta fara'a. "Yanzu yaya kike da kika tura waɗannan kuɗi gida, Tadala?
"Daɗi sosai Farida... har ban san yadda zan bayyana miki ba, Tadala ta amsa tana murmushi Farida tayi murmushi tace, "To ko don wannan daɗin da kika ji ma, ya kamata ki kula Alhaji Kamal Ina yawan jin labarinsa a gari akan irin kyautar gwal da kudi da yake yiwa matansa Allah kaɗai ya san nawa zaki tara a cikin watan shidan nan na pinky promise ɗinku