Free chapter · Read without an account
Mi Dahlia 🌸
by ZAHRAA · Zumar Hamada 🍯 🏜️
Ajiyar zuciya mai cike da bacin rai Alhaji Kamal ya sauke ,Ya tashi gaba ɗaya daga kan gadon, ya nufi wata kujera (armchair) dake tsakiyar ɗakin ya zauna ,gabadaya ransa a bace yake da abinda falmata tayi masa
Kwanaki biyu da ya yi a fannin Dr. Mariya sam babu wani abu na shauƙi da ya shiga tsakanun su,don Dr. Mariya mace ce mai wuyar sha'ani da girman kai, sai sanda ta ga damar kanta take ba shi haɗin kai shi Kuma Allah ya yi shi namiji ne mai tsananin buƙata ,Yau kuma ya zo wajen Falmata tana ce masa she's not in the mood.
Cikin fushi da neman abin da zai dauke masa hankali, ya ɗauko wayarsa ya shiga WhatsApp. Shi ba abokin harkar yanar gizo ba ne, domin yana iya fita fiye da mako guda bai shiga WhatsApp ɗinsa ba. Yana shiga, ya tarar da dubun-dubatar saƙonni (messages rurutu) yawanci daga 'yan mata ne na gari masu nuna suna son sa, shi kansa yakan rasa a ina suke samun lambarsa ta sirri
Yana cikin dubawa, idanuwansa suka sauka a kan sunan Tadala Ya ga tana nan online a daidai wannan lokacin ,Nan take ya ji wani farin ciki ya mamaye zuciyarsa.
Ba ɓata lokaci ,ya danna sunanta ya tura mata saƙo
Baki yi bacci ba har yanzu, fine girl ?
Tadala dake kwance a ɗakinta tana juye juye , tana ganin saƙon Daddy, gabanta ya fadi bata tare da sanin Dalili ba ,reply ta masa Na kusa yi Daddy, karatun gobe nake ɗan dubawa Fatan kana lafiya?
Lafiya lau nake, amma baccin ne ya ƙi zuwa . Kina sane da cewa tun daren jiya nake tunanin alƙawarinmu na wata shida, ko?
Tadala ta ɗan ciji laɓɓanta na ƙasa cikin kunyar kalaman nasa Daddy don Allah... kar wani ya ga chatting dinmu ,Ina fatan dai ba ka cikin damuwa? Ina cikin damuwa sosai, Tadala... musamman idan na tuna yadda kike nisa da ni a daren nan Ki daure ki turo mini da hoton fuskarki yanzu, ko zan sami sassaucin baccin da ya gudu daga idanuna.
Tadala ta zuba wa saƙon ido,Kalaman biloniyaren nan suna neman girgiza duka dabarun da ta tsara a ranta...ta dade tana kallon saƙon Daddy, tana tattaunawa da zuciyarta ,Ta san ba ta da wani hoto na musamman a tata wayar, sai kawai ta tuna da hotunan da Farida ta ɗauke ta kwanaki da kyamarar wayarta lokacin da suke tare. Ta shiga galary , ta zaɓo guda ɗaya mai matuƙar kyau wanda fuskarta ta fito fes, dauke da murmushi mai sanyaya rai.
Ba tare da ta ƙara ce uffan ba, ta danna send ta tura masa hoton.
Alhaji Kamal dake zaune , yana ganin hoton ya sauka, ya gyara zamansa cikin sauri. Ya kura wa hoton ido na tsawon daƙiƙu, wani dumi yana ratsa shi. Yarinyar ta cika kyakkyawa ta kowane fanni, babu maraba da sunanta.
Wannan shi ne mafi kyawun abin da idanuna suka gani a daren nan, Tadala Kinyi kyau sosai, kyawunki yana kwashe mini ragowar natsuwa ta."
Tadala ta ɗan murmusa ta tura masa saƙo.
Nagode Daddy. Amma don Allah ka kwanta ka huta haka, daren ya yayi ,Ta yaya zan iya bacci alhalin zuciyata tana can tana bugawa da sunanki? tun ranar farko da idanuna suka sauka a kanki na san na shiga tarkon da ba zan iya fita ba. Ko da matan gidan nan duka suna nan, ke kaɗai ce kike da sirrin da zai iya kwantar mini da hankali yanzu. Son ki nake with all my heart and soul ,lalle ma daddy Dama haka ya iya soyayyah ji kalamai Kamar ba daga bakin sa suke fitowa ba?
Sun daɗe sosai suna tura wa juna saƙonni, inda Alhaji Kamal ke ta kwararo mata kalaman soyayya da lallashi, ita kuma tana ba shi amsa cikin ladabi da kiyayewa har sai da ta ji jikinta ya yi sanyi lau, bacci ta soma fizgarta.
Daddy, idanuna duk sun kumbura saboda bacci. Zan kwanta yanzu, sai da safe.
Ba a ɗauki daƙiƙa guda ba, saƙon Alhaji Kamal shigo "Sleep well, Little Desert Flower Nothing will happen to your dreams while I’m here beautiful. I love you.
Tadala ta kura wa waɗannan kalmomi guda uku ido. "I love you." Sosai kalmar ta daki tsakiyar zuciyarta, ta ratsa duka jijiyoyin jikinta. Duk da cewa saƙon a rubuce yake a kan allo, amma ta ji shi har cikin ranta tamkar muryarsa ce ta raɗa mata a kunne.
Ba ta san dalilin da ya sa zuciyarta ta ƙara bugawa ba Ta kashe wayar ba tare da masa reply ba Bayan daƙiƙu kaɗan…Wayar ta sake haske Wani saƙon And yes… I mean every word I want to marry you
Tadala ta zaro ido Da sauri ta ajiye wayar kamar ta ƙone ta Wani irin tsoro da fargaba suka sake mamaye ta lalle Mutumin nan da gaske yake Ba tare da ta ba shi amsa ba, cikin sauri ta kashe data , ta jefa wayar a gefen katifa, ta ja bargo ta takure ta rufe fuskarta tana sauke numfashi da sauri-sauri har bacci ya yi awon gaba da ita...
A wajen ɗakin kuma Alhaji Kamal yana tsaye a balcony ɗinsa, yana kallon ruwan sama.
Wayarsa na hannunsa Wani murmushi ya bayyana a fuskarsa You’re in trouble, Kamal,ya fada yana shafa gemun sa
Amma duk da haka…Bai taɓa jin zuciyarsa ta yi nauyi da wani suna kamar yadda sunan Tadala ya yi masa ba Ashe wannan ne soyayya?To me yasa ta zo a Wajan cousin din matarsa ?
Washegari da safe, saƙon Alhaji Kamal ne ya tashe ta daga baccin da ta sha Bayan ya idar da asubah Tana buɗe idanunta, ta jawo wayar
"Good morning, Mi Dahlia. My night was full of your thoughts. Yau da daddare ki shirya, zanzo zance . Have a nice day.
Tadala ta kura wa saƙon ido, musamman kalmomin nan guda biyu dake ta mata yawo a kai. Ta rinka maimaita sunan a fili Mi Dahlia... Mi Dahlia." Wani irin baƙon sun-a ne wannan da Daddy ya raɗa mata? Ta yanke shawarar , "Idan naje school yau, zan tambayi Farida menene ma'anar wannan sunan.
Ta fito sashen gidan don shirin tafiya makaranta, ta tarar garin baki ɗaya a cike yake fam kamar ana taron siyasa saboda zirga-zirgar jama'a , wanda hakan ya sa aka ɗan samu tsako a hanya
Saboda wannan zirga-zirgar, Tadala ta isa jami'ar a makare sosai (very late). Ta nufi ajinsu da sauri-sauri ganin lecturer nasu yasa ta ja birki ,Wannan fa shi ne karo na uku a jere tana makara, kuma abin mamaki, duk sanda wannan sabon malamin (lecturer) zai shigo musu aji, to kuwa sai ta yi latti
A sanyaye ta tura ƙofar ajin ta shiga, duka ɗaliban ajin suka zuba mata ido. Ta ƙaraso cikin ladabi ta ce, Good morning, sir.
Malamin ya tsayar da bayanin da yake yi a jikin projector , ya juyo a hankali ya zuba mata kaifafan idanunsa. Sama da ƙasa ya kalle ta , fuskarsa babu alamun wasa.
"You again?" Why are you always late?"
Shiru Tadala ta yi ta kasa ba shi amsa, ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da gefen mayafinta ,Malamin ya gyara tsaiwarsa, This is your last warning, Tadala Attahier. Get in!ta ɗaga kai da sauri ta kalle shi, Sosai ta yi mamakin yadda akayi wannan sabon malamin ya riƙe sunanta har da na mahaifinta, bayan ita ba mai cika surutu ko shiga harkar mutane a aji.
Suna fita break , kai tsaye rukunin cin abinci na jami'ar (cafeteria) suka nufa domin samun gurin zama. Suna zama, duka biyun suka haɗa baki lokaci guda Ina da labari!"
Ganin yadda suka yi magana a tare ya sanya kowannensu tsayawa kallon ɗan uwansa, kafin duka biyun su kwashe da wata dariya
Farida ta gyara zamanta tana murmushi, "Go first, Tadala! Ina jinki, fuskarki kadai ta nuna labarin naki yana da zafi.
Nan take Tadala ta zaro wayarta ta buɗe WhatsApp, ta nunawa Farida duka hirar daren jiya da suka yi da Daddy, da kuma saƙon safe da ya tashe ta da shi.
"Duba ki gani, Farida, Kinga fa, har wani sabon suna ya sa mini... Wai 'Mi Dahlia'. Shin ko menene ma'anarsa oho? Tunda na tashi nake ta juya sunan a kaina na rasa gane kansa.
Farida ta kwashe da dariya ta ce, "Haba Tadala, yanzu fa muna zamanin na'ura mai ƙwaƙwalwar ƙwarƙwata (AI) ne. Kar ki damu , bari mu duba menene ma'anar sunan google
Take Farida ta ɗauko tata wayar , ta shiga gurin sanya tambayoyi, ta rubuta what is the meaning of Mi Dahlia?
Ba a ɗauki daƙiƙa biyu ba, sai ga amsar ta bayyana fes a kan allon wayar Farida. Farida ta zuba wa bayanin ido, fuskarta ta washe da wani murmushi na kissa. Ta matso kusa da Tadala ta nuna mata bayanin tana fassara mata
"Tadala, ashe Alhaji Kamal ya iya zuba soyayya haka? Mi' a yaren mutanen Spain yana nufin 'Tawa' (Mine). Ita kuma 'Dahlia' wata kyakkyawar fulawa ce ta dake nufin 'Alheri, Kyawu, da kuma Jarumta'. Ma'ana baki ɗaya Alhaji Kamal yana kiranki ne da 'Kyakyawar Fulawa ta ta Alfarma'
kunya ya rufe ta lokacin da taji ma'anar sunan. Dabarun Alhaji Kamal da gaske suke neman ruguza katangar zuciyarta.
Farida ta turo baki tana ta tsokanar Tadala, fuskarta shake da dariya. "Masha Allah! Shikenan fa Tadala, tsuntsu ya kama kansa. Daga gani Daddy ya riga ya shiga tarkon son ki . Shawarata a gare ki, take it easy! Ki zama safe place ɗinsa a kowane lokaci. Duk sanda ɗaya daga cikin matansa ta ɓata masa rai, ke kuma ki zama mai faranta masa Daga ganin bayanin sa na daren jiya, ko bai faɗa miki a fili ba, tabbas ransa a ɓace yake da wani abu a gidan.
Tadala ta sunkuyar da kanta tana murmushi , ta kasa cewa uffan.
Farida ta ɗan leƙa gefe da gefe, ta ga yadda ɗalibai ke ta ƙara tururuwar shigowa gurin cin abincin. Ta miƙe da sauri ta ce, "The walls have ears! Muje motata na ba ki nawa labarin, naga cafeteria ɗin nan ya fara cika da mutane."
Suka nufi gurin ajiye motoci, Ta zuge duka gilashin motar tsaf, sannan ta ware musu (AC) wanda ya gauraye cikin motar da sanyi.
Farida ta juyo ta kalli Tadala cikin annashuwa, "Tadala, kin tuna wancan mutumin da na labarta miki yana yawan zuwa strip club ɗinmu? Wanda na gaya miki ya ba ni the best s…xof my life makonni biyu da suka wuce?
Tadala ta ɗan gyara zama, "Eh, na tuna shi sarai."Yauwa! Kin san dai na gaya miki tun bayan ranar na daina ganinsa har nake ta fargaba? To sai gashi jiya kwatsam ya bayyana
Nan take Farida ta baje wa Tadala labarin darensu, da mafi girman sirrin dake neman haukatata yadda ya ambaci asalin sunanta
Tadala ta zaro idanu cikin mamaki, "Farida! Amma baki tambaye shi an ina ya san asalin sunanki ba?
Farida ta buga tsaki ta ce, Zan tambaya kenan Amma yana jina soma magana ya katse ni da wuri wai 'No more questions'. Haka muka kwana, yau da safe ma shi da kansa ya kawo ni har gidana a motarsa, daga nan na shirya na taho school.
Tadala ta dube ta, To bai ba ki kudi ba daren jiyan?dan kwanaki banji kince ya baki kudi ba
Farida ta saki w murmushi "Haka nima na zata bai ba ni komai ba . Sai dazu da nake ƙoƙarin buɗe handbag ɗina don na ɗauki wani abu, kawai sai na ga damin daloli (dollars) a ciki, tare da wani ƙaramin takarda (note) an rubuta
"Take care.
From Nawaf. Tadala ta ja numfashi, tana kallon dalolin dake hannun Farida. Sirrin rayuwar birni yana neman canza musu taku baki ɗaya, duka biyun suna fuskantar mazaje masu iko da kuɗi...