Free chapter · Read without an account

Secret ,Promises and Cracks

by ZAHRAA · Zumar Hamada 🍯 🏜️


Farida… wannan mutumin yana bani tsoro fa kiga kudin daya baki,Tadala ta fada Tana kara juya kudin a hannunta 

Ni ma tsoro yake bani Tadala ta yaya mutum zai san asalin sunana, ban taɓa ganinsa ba sai a club Kafin Tadala ta ba ta amsa, wayar Farida ta yi ƙara  Ta na dubawa ta kwashe  da dariya  yan Comment section ɗina kenan

Matso kiga mai suke cewa ,

Ina Tadala Buzuwa?

Dan Allah  farida ki kara mana video da Tadala buzuwa 

Farida yi mana tagging din account din Tadala 

Tadala ta zaro ido Ni? mutane ke  tambayata haka ?kwarai da gaske kin birge su ne shiyasa ,miko min wayarki ki gani ,Tadala ta mikawa farida wayar  direct ta shiga TikTok Ta buɗe sabon account

@TadalaBuzuwa Yauwa gashi na bude miki account zanyi tagging dinki a page Dina 

Farida! Ni kam ban san komai a kan wannan app ɗin ba. Me zanyi a TikTok din ?

Shi ya sa kike dani Ni zan koya miki,Daga yau kin shiga duniyar TikTok ,shikenan farida Nagode ,daga nan sukayi sallama ko wacce ta nufi hanyar gidansu 


Friday Night – Dining Table

dining ya cika da ƙamshin abincin already chefs sun gama girki ,dan  matan gidan kaf dinsu basa girki  Tadala ta fito  cikin doguwar rigarta mai launin ruwan madara.

tana karasowa ,idanunta suka sauka a kansa Alhaji Kamal sanye cikin farar jallabiya Riƙe da fork yana kokarin kai fried spaghetti bakinsa  ,yana ɗaga kai…suka haɗa ido A hankali idanunsa suka bi ta daga sama har ƙasa Kamar dai shi kaɗai ne ya lura da zuwanta 

Wani lallausan murmushi ya bayyana a gefen bakinsa,Tadala ta yi saurin kauda kai Ta nufi dining table ta zauna daya Bayan daya ta gaishe da matan sa suka amsa mata as usual dr mariya na tambayar ta ya karatu ,Ina yini daddy ?Cike da basarwa ya amsa Kamar irin baa son ransa din nan ba ,Munafincin alhaji kamal a gaban matansa yana ba Tadala mamaki ,ji yadda take amsa mata gaisuwa ,haka ta fara cin abinci … tun dazu take Jin idanunsa a kanta Ta kasa ɗaga kai ta kalle shi

A ɗaya gefen dining ɗin,  dr mariya  tayi gayran murya Khalifa zai dawo daga Boston  da next week Nan take hankalin kowa ya koma Kanta

Da gaske umma?Ahmad ya fada cikin zumudi kasancewar shi da khalifa ne kadai maza a gidan duk shekarun dake tskaninsu Akwai shakuwa Shida yayan nasa 

Be fada maka bane ?ina ga suprise yake son maka Ai an kusa shiga wata mai tsarki. Shi ya sa ya ce zai dawo gida ya yi Ramadan tare damu as usual .Mami ta yi murmushi.

ay gara yazo An daɗe ba a ga Khalifa ba.

Tadala Ta lura yadda kusan kowa a dining ɗin ya yi farin ciki da jin sunansa harda su falmata 


Tadala ta kulle ƙofar ɗakinta  ta yi alwala  tayi addu’o’inta ta kwanta chan wayarta ta yi kara, Daddy Calling….dan Jim Tayi Chan kuma ta daga 

Assalamu alaikum, Daddy…

Shiru yay na daƙiƙa biyu.

muryarsa mai zurfi ta cika kunnenta.

Wa alaikumus salam… Mi Dahlia Kawai yadda ya kira sunan yasata cikin yanayi mara misaltuwa 

Kana lafiya, Daddy?ya office ?

Daga ɗayan ɓangaren, Alhaji Kamal ya jingina bayansa a kan kujerar balcony ɗinsa, yana kallon hasken wata da ya rufe sararin Abuja. Lafiya lau… amma dazu na lura da wani abu

Me ka Lura dashi ?Ya yi ɗan shiru kafin ya ce Yau a dining, baki kalle ni ko sau ɗaya ba.

Tadala ta lumshe idanunta Ashe ya lura?

A’a… ba haka bane.

To yaya ne?Ta yi shiru dan ta rasa abin cewa 

Muryarsa ta sake sauka a hankali Kina gudu  nane? A’a Daddy To me yasa kika kasa ɗaga kai?Tadala ta ciji laɓɓanta Ta tuna yadda idanunsa suka riƙa bibiyarta a dining.

Wani irin kunya ne ya sake rufe ta ,Ban sani ba…” ta faɗa a hankali  Daga can ya saki murmushi mai sauti Ita kanta sai da murmushi ya kusan subuce mata tayi saurin danne shi Mi Dahlia….Na’am.

Kin san wani abu?Aa sai ka fada ?

Tun da kika shigo gidan nan… abubuwa sun canza Ta yi shiru tana sauraron sa 

Na fara komawa gida da wuri. Na fara murmushi ba tare da wani dalili ba. Kuma duk ranar da ban ganki ba… ina jin kamar Banda lafiya ,Zuciyar Tadala ta sake bugawa ,Ba ta san dalilin da yasa kalamansa ke shiga ranta haka ba 

Daddy… ni kam ban san me zan ce ba.

Ya yi murmushi Ba sai kin ce komai ba ki rika sauraro na kawai ya wadatar 

Shiru ya ɗan ratsa tsakaninsu 

kin koshi dai ko dan naga kamar ba wani abincin kirki kika ciba ?Eh na koshi 

Dukansu suna jin numfashin juna ,Yana son yadda take amsa masa cikin ladabi da natsuwa Bayan sun ɗan yi wasu hirarraki na makaranta da rayuwar Agadez, ya sauke wata ajiyar zuciya.

Mi Dahlia… Na’am?”Muryarsa ta ɗan yi ƙasa Buɗe ƙofar ɗakin ki 

“Daddy?Ina son ganinki na minti biyu kacal. Ba zan daɗe ba kallon ki kawai zanyi na tafi 

Tadala ta miƙe zaune Ta kalli ƙofar ɗakinta.

ta sake komawa kan wayar  ,Daddy… kar ka ce min kana wajen ƙofata.

Ina nan yanzu na sauko 

Daddy… don Allah a’a ka tafi ni dai 

Me yasa? Ta lumshe idanunta Tsoro nake ji Ban saba da irin wannan ba Kuma bana so wani ya gan ka a nan 

muryarsa ta sake fitowa, a hankali minti daya  fa ?Tadala ta girgiza kai kamar yana ganinta ,Don Allah ka yi haƙuri, ba zan iya b

Shiru ya sake ratsa layin Na wasu daƙiƙu har ta fara tunanin ko ta ɓata masa rai ne 

Alright, Mi Dahlia good night ,Ba ka yi fushi ba?banyi ba mi dahlia 

Da gaske? Da gaske nake  Idan har kina jin tsoro ba zan taɓa tilasta ki yin abin da baki shirya ba Wani irin sanyi ya ratsa zuciyar ta  bata san dalilin da ya sa ba  jin yadda ya mutunta  tata ya sa ta sake kara ganin girman sa  

Nagode, Daddy 

You’re welcome, Mi Dahlia.

Ki kwanta ki huta. Sai mun yi magana gobe, In Sha Allah.

“To Daddy… Allah ya tashe mu lfy 

Murmushi ya sake bayyana a fuskarsa.

Ameen… ke ma, haka  kyakkyawar fulawata Kafin ta sami damar ba shi amsa…Ya kashe wayar  ta sauke wayar a hankali  sanna ta kalli ƙofar ɗakinta A karo na farko…

Ta yi murmushi ita kaɗai a cikin ɗakin


LIFE CAMP ABUJA 

Cikin wani katafaren falon alfarma dake unguwar life camp Abuja, ƙamshin turare mai sanyaya rai ya gauraye ko’ina. Wutar chandelier tana Haska falon 

wata kyakkyawar  yarinya ce a kasan carpet yar  kimanin shekara biyar a zaune , tana ta ƙoƙarin haɗa wani puzzle. Dogon gashinta a ɗaure cikin ponytail biyu

Nawaf yana zaune a ƙasa kusa da ita, sanye da fara  T-shirt da bakin wando ,Fuskar nan tasa mai tsauri da yawanci ke tsoratar da mutane, a yanzu cike take da murmushi.

abba , wannan ya ƙi shiga…” yarinyar ta faɗa tana turo baki Nawaf ya karɓi ɓangaren puzzle ɗin Hmm… saboda princess ɗina tana ƙoƙarin haɗa shi a inda ba gurinsa ba ne To kai ka gyara min mana 

To , Your Highness take Ya haɗa mata shi 

Yayy!  Ta rungume shi ,Nawaf ya sumbaci goshinta My smart girl 


A daidai lokacin ne suka ji sautin takalmi.

Wata kyakkyawar mace doguwa, yar gayu, sanye cikin wata doguwar silk robe ta sauko daga bene Gashinta ya sauko a kafaɗarta, fuskarta ɗauke da ɗan gajiya Tana tsaya tana kallon su Kusan minti biyu kenan 

Amma ko kallonta Nawaf bai yi ba kuma tasan yasan da zuwan ta   yarinyar ce ta ɗaga kai 

Amma!! Ta miƙe ta rungume ta 

Matar ta sumbaci kanta sannan ta sake kallon Nawaf Har yanzu kuna nan?

Nawaf bai ɗaga kai ba 

Hmm kawai yace yana danna wayarsa 

Ta ƙaraso ta zauna a kujerar kusa da su.

Na dawo tun ɗazu am so tried wallahi 

Hmm ok sani  Ta lumshe idanunta Nawaf… wannan ce amsarka? Ya ɗaga idanunsa a kanta Kina  magana ne ?murmushi mai ciwo tayi Tana kallon Nawaf Kamar ta rufe shi da duka Ya sake mayar da hankalinsa kan puzzle din da Kara daukowa 

amma duba butterfly yarinyar ta mike Tana nuwa mahaifyar tata 

Very beautiful, sweetheart yayi kyau 

ta sake kallon mijin nata ,Nawaf, yaushe rabon mu da zama muyi  hira? Yaushe rabon mu da cin abinci tare?kala be ce mata 

Sometimes I feel like I’m living with a stranger  Nawaf ya ɗan ɗago kai Bana son hayaniya da yawa kin sani ,Hayaniya? Hira da matarka ne hayaniya  yanzu?

Shiru bai amsa ba ,Amma idan tana magana… ta nuna diyarsu, kana iya zama awa biyu kana sauraronta.

A wannan karon ya ɗago ya kalleta kai tsaye

“Because she’s five shekarar ta biyar she needs my attention ,ikon Allah haka ma zaka ce ?Ya maida dubansa kan diyarsu wacce ta zauna darere Akan cinyarsa 

abba …Na’am, princess.

Tomorrow za ka kai ni ice cream?Of course anything for you princess 

Promise?Ya miƙa ƙaramin yatsansa.

Pinky promise Ta sa nata.

Matar ta zuba musu ido Wani irin abu ya soki zuciyarta 

Nawaf… ,Uhmm ,Ya amsa ba tare da kalle taba Ta sauke ajiyar zuciya kai daina  kewata ko ? Falon yayi tsit.

yarinyar ma ta ɗaga kai tana kallon su Nawaf bai amsa nan take ba ya sauke Ayla a hankali yace  Ki tafi ki ce wa nanny ta shirya ki zakiyi bacci .

Okay, abba good nyt abba ,good night amma Ta sumbaci kumatunsa ta haye sama 

Kema bacci  ya kamata ki yi it’s late.

Ya raba ta gefen ta zai wuce , a haukace ta   Kira sunan sa 

Nawaf !Ya tsaya cak 

Ta haɗiye yawu  Me ya faru da mu ne?”

Ba tare da ya waiwayo ba, cikin muryarsa mai sanyi ya ce Ban sani baYa ci gaba da tafiya Ya barta zaune ita kaɗai cikin falon…

Tana kallon bayansa har ya  ɓace,A karon farko cikin dogon lokaci…Ta ji tsoron cewa watakila ta rasa mijinta tun tuni, kawai yana  zaune ne gida ɗaya da shi. 🤭

Nadira ta bi bayansa hanzarce  Ta  tsaya a bakin ƙofa, idanunta a kansa Nawaf ya cire agogonsa ya ajiye a gefe, kamar kullum fuskarsa babu alamun abin da yake tunani.

A hankali ta ce,Nawaf… ka bani hakkina na aure.Ya ɗaga idanunsa ya kalle ta na wasu daƙiƙu, babu wanda ya yi magana.

Kin tabbata?” Ta jinjina kai.

Bai ƙara tambaya ba Ya ƙaraso kusa da ita. komai ya kasance cikin shiru mai nauyi..Sam babu Armashi Babu kallon da ya saba yi mata a shekarun farko  aurensu.

Tamkar zuciyarsa tana wani wuri daban Da komai ya lafa…Nadira ta zuba masa ido.

Ta kasa gane abin da take ji Sai kawai hawaye suka cika mata idanunta Nawaf ya lura.

Ya ɗan daure fuska  Me ya faru kuma ?

Ta girgiza kai  Chan kuma ta fashe da kuka.

Menene haka, Nawaf?.

Ba haka kake ba, abban  Ayla.

Ina mutumin da yake kallona kamar ni kaɗai ce a duniyarsa? Ina mutumin da yake hira da ni? Da yake murmushi idan yana tare da ni?”

Muryarta ta soma rawa ji yadda kake min Kamar Wanda aka mana auren dole ?

Ta share hawayenta da bayan hannunta.

“Ko ka fara neman mata  ne?Ko akwai wata macen? A daidai wannan lokacin…

Wani hoto ya fado masa a rai Wata fuska.

Wani murmushi Farida 

Ba tare da ya shirya ba, wani ɗan murmushi ya subuce masa Nadira ta tsaya cak.

“Nawaf… tuni Ya dawo hayyacinsa Amma ina ya makara Ta matso gabansa.

Nawaf, ina magana… kana murmushi?”

Numfashinta ya fara sauri.Wata ka tuna?

Bai amsa ba Hawayenta suka sake zubo.

Ta girgiza kai a hankali Kamar ta fahimci wani abu da zuciyarta ta daɗe tana tsoro.

Ashe akwai wata…

Nadira tsaye kiji Kar ka Matso tayi saurin katse shi Duk shekarun nan ina ta ƙoƙarin dawo da kai… amma ashe zuciyarka tana wani wurin?Ta nuna shi da yatsa.

Ka san me? Ka bani kunya, Nawaf. Shame on you Ya tsaya kamar mutum-mutumi.Ta share hawayenta Fuck you, Nawaf

Ta nuna masa middle finger cikin fushi da ɓacin rai Sannan ta juya Bang! Ta buga ƙofar ɗakin da ƙarfi

Shiru ya mamaye wurin Nawaf ya tsaya a inda yake A karon farko cikin dare…

Ya gane wani abu mai ban tsoro.

A duk lokacin da aka ambaci wata mace…

Fuskar Farida ce ta fara zuwa masa a rai.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol