Free chapter · Read without an account
Restless Hearts
Zumar Hamada
Page 16
Bayan sun gama shan ice cream, suka nufi mota Alya kuwa tun da suka fara tafiya ta jingina kanta a kujerar baya sai bacci Nawaf ya É—an waiwayo ya kalleta murmushi ya bayyana a fuskarsa ya rage sautin rediyon da ke kunne,Nadira ta lura Duk duniya Akwai mutum É—aya da har yanzu take iya lafa masa zuciyarsa Ayla
Ta ɗan gyara zamanta a hankali ta ce,Nawaf zan yi maka tambaya and please be honest with me Ya ci gaba da tuƙi ba tare da ya waigo ba ,Ina jinki go on
Nadira ta haÉ—iye yawu ,da gaske babu wata mace a rayuwarka?ya juyawa yayi ya kalle Nadira tayi nare nare da ido Kamar zatayi kuka ,babu kowa nadira ,Jin amsar sa yasa ta saki wata boyayyar ajiyar zuciya
To amma me yasa kake treating Dina Kamar trash ?sam bani da wani mahimanci a Wajan ka ,Baka cin abincina,ka raba makwanci dani why Nawaf
Nadira…Wasu abubuwa suna canzawa da lokaci ,Numfashinta ya tsaya Kana nufin ka daina sona kenan ?Ya yi shiru Kafin ya ce Ban ce ba ,saurin katse shi tayi to me kake nufi?Ya sauke ajiyar zuciya ,Ban san yadda zan bayyana miki ba ,a bar maganar ta ishe ni haka ,Baki ta zunburo ya juya ta kallon window Wani irin baƙin ciki ya mamaye Zuciyarta ,Aƙalla… dai Ya ce babu wata Wannan kaɗai ya ɗan kwantar mata da hankali.
Bayan kusan mintuna ashirin suka isa gidansu nawaf Tun daga ƙofar shiga,zaka gane gidan yana ɗauke da alamun tsohon kuɗi Saba Ayla yayi a kafada suka doshi kofar shiga falon ,a zaune suka Sami dattijuwar Tana Karatun Quraani ,Jin sallamar su Nawaf yasa ta kai aya ta ajiye Quraanin a table din dake gefenta
Oyoyo !Jikata ta zo, Sannuku da zuwa
Hajiya Rahma kenan Mahaifiyar nawaf a hankali ya ajiye Ayla a 3 sitter har kasa shida nadira suka tsugunna suka gaishe da hajiyar dan ita Sam rayuwar abuja be sa rashin tarbiya a gidan ta ,yan mata biyu ne suka fito daga kitchen ,tahra da sumayya suma Cikin girmamawa suka gaishe dasu nawaf ,tahra ta kalli inda Ayla ke kwance ,ah lalle Yau oga anyi bacci kenan ,ay dole ma ta tashi ko kuma ku bar mana ita tunda Mun shiga weekend ,shi dai nawaf ba dan kunyar Hajia ba ya da mike tahra dan ba abinda ya tsana irin Ayla take wani waje weekend ko da kowa gidan sune ,Hajia ya ciwon kafar taki ?nadira ta matso kusa da kafar hajiar Tana massaging a hankali
“Da sauki sosai habbbity naji dadin maganin da kika kawo min Jazakillah khairan, Haba ba komai hajia Allah ya kara lafiya ,ameen ya rabbi kinyi kyau masha Allah Nadira ta yi murmushi Nagode Hajia
Hajia ta kama hannunta ya naga Kamar Kin rame ?Wannan mutumin baya ciyar da ke ne?Aa Hajia dan Zazzabi nayi kwana biyu amma Alhamduillah naji sauki yanzu
Hajia ta Kara kallon ta cikin ƙauna tace anytime you’re lonely ko kuma wanna yaron yayi tafiya ki dinga zuwa gidan nan kofa a bude take a ko da Yaushe Allah ya muku albarka gabadaya,raurau idon nadira yayi ,Allah ya sallameta tayi saar suruka ta gari Alhamduillah ,tahra da Summy suka saka nadira a tsakiya idan Ka Gansu Bazaka taba cewa suruka bace ,Anty nade gskia next week my hada picnic kwana biyu bamu dan yi chilling ba ,that’s a good idea Summy Allah ya kaimu ,amma bills on me
Nawaf yana zaune a gefe Yana kallon yadda suke zagaye da matarsa ,Ya ji daɗin ganin murmushin Nadira ,Domin duk da komai Abu ɗaya ya sani Ita ba muguwar mace ba ce Kuma yan gidansu …Suna sonta Kamar yadda take sonsu sai Wajan karfe goma suka tafi gida
Wuse 1
Direct anty zaheera Wajan tadala ta wuce ta same tana zaune a bakin gado, ta cire mayafinta, dogon gashinta ya sauka a kafaɗarta zaheera ta ƙarasa ta zauna kusa da ita Na ɗan lokaci ta zuba mata ido Yarinyar tana da kyau sosai. Fuskarta cike da natsuwa da tsantsar rashin wayo A hankali Zaheera ta kai hannu ta shafa gashinta Tadala…Na’am, Anty
Zan yi miki tambaya daya bani attention dinki ,Tadala ta gyara zamanta ,Kin san cewa Kamal yana sonki sosai ko?
Ta sunkuyar da kanta kasa Jin Kalmar da fito daga bakin Zaheera,ke fa? Kina son sa?
Shiru Tadala tayi ta ci gaba da kallon yatsunta ,Ina jinki bude baki kiyi magana
Uhmm Nidai gaskiya Anty ……shiru tayi ta kasa karasa maganar ,Ki faɗi abin da ke ranki ,Ba zan yi miki hukunci ba
Tadala ta haɗiye yawu ,Gaskiya… ban sani ba, Anty ,Zaheera ta ɗan ɗaga gira ,Ba ki sani ba?tadala ta gyada kai tace ni dai be taɓa yi mini wani abu mara kyau ba. Kullum yana magana da ni cikin mutunci… yana kula da ni… idan yana magana da ni sai na ji… Sai Kiji me tadala ?Tadala ta rufe fuskarta da tafin hannunta cikin kunya ,Ban sani ba Anty Zaheera ta yi murmushi amma Anty da ace ba mijin Anty sadiya bane Wataƙila… da na fi sonsa Shiru ya mamaye ɗakin Zaheera ta kasa magana ,kawai ta zuba mata ido Wani irin tausayin su duka biyun ya mamaye zuciyarta ,ta kalli yarinyar
Ta tuna yadda Kamal ya zo gidan nan cikin dare saboda kawai ba zai iya jure kwanaki biyu ba,ta tuna idanunsa lokacin da yake kallon Tadala ,Sannan ga wannan yarinyar wacce ta fama da kuruciya da kuma rudani
Ta matsa kusa da Tadala, ta rungume ta tadala ta jingina kanta a kafaÉ—arta Kina jina ko?
Eh , Anty inaji
Kada ki takura kanki Kada ki tilasta zuciyarki , Ki yawaita addu’a Ta ɗan ɗaga kanta ta kalli fuskarta ,Ki ce, Ya Allah, idan akwai alheri a cikin wannan lamari, Ka sauƙaƙa shi Idan kuma babu alheri, Ka fitar da ni daga cikinsa cikin sauƙi
Tadala ta jinjina kai to Anty Nagode sosai
Kuma ki yi addu’ar Allah Ya kawo sauƙi idan maganar fito fili ,me zai faru Anty ?Ke yarinya ce har yanzu Idan mutane suka ji labarin babban mutum kamar Kamal yana son yarinya kyakkyawa kamar ke, mutane za su yi magana. Wasu za su fahimta, wasu ba za su fahimta ba ,zaku samu challenges sosai most especially a Wajan sadiya Saboda haka, ki roƙi Allah Ya zabi muku mafi alheri, kuma Ya kare ku daga duk wani abu da zai cutar da ku. Gabanta ya fadi har ta hango tijarar da anty sadiya zata mata inda maganar nan ta fito ,Zaheera ta dade Tana bata shawarwari irin ta ya da uwa kuma sosai Tadala ta amfani
Life camp
Suna dawowa gida nadira ta shige daki bacci take ji sosai ,nawaf yayi wa Ayla wanka ya canza mata kaya dan Sun dawo Sun tarar nanny har tayi bacci
Balcony ya Koma yana dan danne danne a cikin laptop dinsa gabadaya tunaninsa yana kan Farida,Shigarta ta mutunci Yadda ta yi saurin kauda kai Da kuma yadda ta kalle shi Kamar tana son samun amsa a fuskar sa abinda ya fara birge shi da ita shine ajinta ,yadda ta nuna Kamar bata San shi ba
ta cire tuta ,a yadda yan matan yanzu suke da rawar kai ya tabbata da wata ce sai ta masa magana not minding bashi kadai ta gani ba .ya É—auki waya Ya duba lokaci 11:45pm ba tare da tunanin koma ba Ya fita
Zuwa Club
Club
Farida tana backstage Sanye da costume ɗin aikinta Amma hankalinta ba ya jikinta ta tunanin Shin yana da mata ne? Idan yana da aure me yasa yake zuwa kallon rawar ta??Muryar Manager taji ,Pinky , you’re next Ta fito stage Haske ya sauka a kanta.
Ta fara rawa idanunta suka sauka a kan wani teburi Nawaf Yana zaune Idanunsa na kanta Kamar kullum ,sai dai Yau Ba ta yi farin cikin ganinsa ba ,Sabida tambayar dake cin ranta tun safe
Haske yana ci gaba da haskaka stage Kiɗa yana tashi Mutane suna tafi Amma…Farida kamar ba ta jin komai ,Idanunta suna kan mutum ɗaya ,shima yana kallonta Ba tare da ya kauda kai ba Wani irin abu ya tsaya mata a maƙoshi Me yasa yake kallonta haka?Me yasa duk lokacin da yake kallonta…sai ta ji kamar ita kaɗai yake gani a wurin?Kiɗan ya tsaya tafi na tashi ,ta yi ƙaramar sunkuyawa kamar yadda ta saba Sannan ta juya ta koma backstage zuciyarta tana bugawa Saboda ta san abu ɗaya zai biyo ta
Backstage
Ta isa gaban mirror Ta zauna Ta cire earrings É—inta a hankali knocking taji Ba tare da ta juyo ba ta san shi ne dan kamshin sa ya mamaye dakin
Kin yi kuskure sau uku yau ,Farida ta É—aga kai cikin mamaki ,wai kuskure kenan ?
Wajan rawa Kin rasa beat sau uku ,Uhmm Ashe ka Lura ?shiru yayi bece komai ba ,Dama tasan bazai amsa ,wacce na ganku tare dazu ?nawaf ya dan daure fuska me yasa kike tambaya it’s my personal life ,dan Jim farida tayi yarinyar tayi kama da kai she is your daughter? Yeah she’s my daughter,shikenan ta faru ta kare farida ta ayyana a ranta ,murmushi yake tayi ,masha Allah she’s beautiful Allah ya mata albarka
Ameen ya rabbi Nagode ,let’s go ,da Kamar bazata shi ba chan kuma tabi bayansa
zShiru ba magana Haka suka karasa gidan ,Ya zauna a sofa, ya jingina kansa idanunsa a rufe ,Farida ta tsaya tana kallonsa Tun daga club É—in yau Akwai wani abu a tattare da shi ,kamar hankalinsa yana wani wuri daban A hankali ta cire takalmanta ta zauna kusa da shi.
Mr. Silent… Bai buɗe ido ba ,be amsa ba ,Ta yi murmushi kaɗan ka manta ina nan ne?
Ya buɗe idanunsa a hankali Ya kalleta I’m sorry ,Yau kaine ke cewa sorry ? Wani ƙaramin murmushi ya kusan subuce masa
Farida ta ƙara matsowa kusa dashi ta jingina kanta a kafaɗarsa ,Ka gaji ne?
Yeah Maybe kona dame ka? Sometimes… mutum baya buƙatar wanda zai yi masa tambayoyi Yana buƙatar wanda zai zauna kusa da shi kawai Nawaf ya ci gaba da kallonta,wata irin nutsuwa ce a cikin muryarta Relax oky ? Gyada mata kayi
Ka san wani abu?Ban taɓa ganin ka cikin damuwa haka ba,ganin bashi da niyar maganar farida ta mike ,shikenan Bari na tafi so that Ka Sami enough time nayi tunanin ta fada ta mikewa tare da murguda mishi baki A karo na farkon tun zuwan su
Wani ƙaramin murmushi ya bayyana a fuskar Nawaf Farida ta zaro ido ,Oh my God
Ya kalleta da mamaki menene ? Ka yi murmushi ,Ban yi ba ya fada a dake wallahi kayi guess what ?Murmushi yana maka kyau sosai… kamar na ɗauki picture ,Mutane suna da dimples, wasu suna da idanu masu kyau… kai kuma murmushinka ne rare species Sai dai a kama shi da camera ,Wani ɗan murmushi ya sake subuce masa Farida ta saki ihu kaɗan There! Ka sake yi yeeeeey
Ya girgiza kai You’re strange ga surutu Kamar Ayla ,zama tayi a cinyarsa ƙoƙarin ceton duniya ne Saboda idan ka dinga murmushi haka… mutane za su daina jin tsoronka A karon farko tun da suka bar club
Nawaf ya saki wata ƙaramar dariya Yeee ! Ya yi dariya ma Ya girgiza kai yana kallonta she’s so childish ,taga dan farida ta canza salon wasan duk wata kwarewarta sai da gwada shi Yau ,gabadaya ta susuta nawaf Kamar ba shine muskilin da take fama dashi yayi magana ba Tana mugun Jin dadin yadda take da makamin yakar nawaf a shimfida
na fara sabawa da jikin ki hope Ni kadai kk gani farida ? Dan Jim farida tayi ,Kai zaka ba kanka amsa kasan yadda Ka fara jina ay
Tana so ta tambaye shi me yake fadawa matarsa ya kwana a waje sai kuma taga ya mugun tsare gida
Rabbatul bait ke ta Kira tun dazu
A nitse ya dauki wayar yayi shiru
farida na lefe na gefensa
Duk da ba speaker yasa ba tana jiyo muryar matar
Nawaf ina kaje ?
Na tashi Shan ruwa na duba garage ba motar Ka ?for how long kake kwana a waje ban sani ba ?
Sai yanzu kika Lura kenan ? Yayi Murmushin takaici Nawaf Wallahi wallahi Zan kashe duk wacce kake tunanin Ka samu
Bazaka hadani da wata mace ba am warning you nawaf
Nawa kk biya sadakina nadira ?
Nawaf na fada maka i can be dangerous don’t try me
Be Bari ta karasa zancen ba kit ya kashe wayar