Free chapter · Read without an account
A Place To Belong
Daddy kayi shiru ?did You really love her?
Tambayar ta fito ne cikin natsuwa, amma ta sauka a zuciyar Alhaji Kamal kamar an jefa dutse a cikin ruwa
Yeah i love her, daddy ya amsa a sanyaye
Khalifa ya lumshe idanunsa ,A karon farko…Mahaifinsa ya amsa masa ba tare da kaucewa ba, ya zuba wa mahaifinsa ido, kamar yana nazarin fuskarsa A hankali ya ce Wow…ya ɗan yi murmushi Ban taɓa tunanin zan ji wannan daga bakinka ba Daddy
Alhaji kamal ya yi ɗan murmushi mai cike da kasala Ni ma ban taɓa tunanin zan faɗa wa kowa ba banda zaheera ,Wani ɗan shiru ya sake ratsawa tsakaninsu Khalifa ya matso kaɗan
Dad…
Na’am?
Ka san me?
Daddy ya ɗaga gira Khalifa ya yi murmushi I’m actually happy for you
Ji yayi Kamar bai ji daidai ba, Daddy ya ɗan tsuke fuska Happy for me? Khalifa ya jinjina kai Ya ɗan yi shiru kafin ya ci gaba ,Tun ina ƙarami, ban taɓa ganin ka zauna ka yi tunanin kanka ba,Komai rayuwarka mu ne
Kullum kana aiki, kana neman kuÉ—i, kana gina mana rayuwa, kana gyara matsalolinmu,ban San menene babu ba a rayuwa ban taba Neman Abu ban samu ba all thanks to you Kai ne backbone É—in wannan family.
Idanun Daddy suka É—an canza ya zama very emotional
Khalifa ya ci gaba ,Ka kasance komai a gare mu,Saboda haka… idan akwai wani abu da zai sa ka yi farin ciki, me zai hana?ya ƙara da cewa,I’m in support,One hundred percent Wani irin abu ya motsa a zuciyar Alhaji Kamal A rayuwarsa…Ya saba da yadda ake bashi girma ya saba da yabo Amma bai taɓa tsammanin ɗansa zai tsaya gabansa ya ce masa ya cancanci farin ciki ba
Ya kau da kansa kaÉ—an Idanunsa suka É—an yi ja ,Khalifa ya lura da hakan
Dad…?are you ok?
Daddy ya yi murmushi kaÉ—an ya É—aga hannu ya shafa kafaÉ—ar É—ansa Na gode, Khalifa
Wallahi ban san cewa jin wannan daga gare ka zai yi min daÉ—i haka ba ,Khalifa ya yi murmushi Amma kafin ya kara magana, Daddy ya sake kallonsa
Khalifa…
Na’am, Dad?
Let this between us for now kar Ka fadawa kowa pls ?Har yanzu… ba official ba ne Ina kan shawo kanta ne Ya ɗan yi murmushi mai cike da kunya Ban san me take tunani a kaina ba Ban ma san ko hakan zai yiwu ba
Khalifa ya yi shiru Ya ga mahaifinsa kamar wani matashi ne da yake tsoron kar a ƙi shi
murmushi ya suɓuce masa
Okay, Dad bazan fada ba
Daddy ya nuna shi da yatsa
Da gaske nake kar ka fada ,Khalifa ya yi dariya I won’t say a word ya ɗan karkatar da kai ,But I hope it works out for you Allah yasa ta Amince maka
Wani murmushi wanda ya daÉ—e bai yi irinsa ba, ya bayyana a fuskar Alhaji Kamal
Sun iso gida lafiya idan khalifa ya shige gida ya bar daddy a mota
A yau abubuwa biyu ne suka taɓa zuciyarsaNa farko, waya da iyayen Tadala ,Na biyu kuma…Kalaman Khalifa.
I’m in support. One hundred percent.
Wani irin natsuwa ya ji a ƙirjinsa
Shekaru da shekaru yana rayuwa domin kowa sai kansa Kullum cikin neman kuÉ—i, kula da iyali, da magance matsalolin mutane. A yau ne karon farko wani ya tsaya ya ce masa Ka cancanci farin ciki
Wayarsa ta yi ƙara Message ne daga Tadala
Assalamu alaikum Daddy.
Ina godiya sosai da hidima ,Wallahi ban san ta ina zan fara ba. Uma, Papa da Moussa Sun ga sako kuma sun yi maka addu’a ,kuma nagode sosai da kayan sallah da ka kawo min ,Duk da Sun yi yawa sosai Allah Ya saka maka da alkhairi, Ya ƙara maka lafiya da arziki
Nagode sosai, Daddy
ya yi shiru Ya sake karanta message ɗin murmushi ya suɓuce masa Yana mamakin yadda message kaɗan zai iya saka mutum jin wani irin daɗi Ya ɗaga kansa ya kalli saman motar Million biyu da kayan sallah kawai na yi mata… amma ita ta mayar da su kamar na ba ta duniya.
Reply ya mata Kamar haka
Wa alaikumus salam, Mi Dahlia
Abin da na yi ba komai ba ne Iyayen ki ay nawa ne, kuma duk mai taimakon iyalinsa yana taimakon kansa ne Allah Ya sanya alkhairi a rayuwarku gaba É—aya.
Ki yi huta lafiya queen Kuma ki ci abinci sosai
Ya danna send Bayan wasu daƙiƙu…Wayar ta sake haske
Insha Allah Daddy Nagode sosai
Allah Ya saka maka da aljanna
A karon nan…Ya yi dariya Dariya mai sauti kaɗan Ya ajiye wayar a ƙirjinsa
Ya Allah…a rayuwarsa bai taɓa roƙon Allah kan mace ba Amma yau…Ya samu kansa yana addu’a Ya Allah… idan alkhairi ce a gare ni, ka sauƙaƙa mini lamarinta ,idan kuma ba alkhairi ba ce… ka cire min sonta daga zuciyata ba tare da na cutar da ita ba.
A can gidan Zaheera…Tadala ma ta ajiye wayarta bayan ta ga amsar Daddy.
Ta sake karanta Iyayen ki iyaye ne…
Ki ci abinci sosai ,ki huta lafiya queen
Ba tare da ta sani ba…murmushi ya bayyana a fuskarta Ta ɗaga idonta ta kalli ledodin kayan sallah da ke jere
Har yanzu abin kamar mafarki yake ,sauke numfashi Sannan ta miƙe Ta ɗauro alwala ,Ta shimfiɗa sallayarta Ta yi raka’o’i biyu Bayan ta gama
ta É—aga hannayenta sama.
Ya Allah…Idanunta suka cika da ƙwalla
Na gode maka da ni’imomin da ka yi mini Ya rabbi Ka ba iyayena lafiya Ka yalwata musu rayuwa ,Ya rabb Ka saka wa Alhaji Kamal da alkhairi saboda farin cikin da ya saka iyayena ,Ya Allah… ban san abin da ke gaba ba Ban san wanda yake alkhairi a gare ni ba Ka zaɓa mini mafi alkhairi Ka ba ni miji na gari mai tsoranka ,Wanda zai so ni, ya girmama ni, ya kuma zama alkhairi a gare ni da iyayen da addini Ba ta ambaci sunan kowa ba ta shafa adduar
Kwanaki uku kacal suka rage zuwa Sallah Gaba ɗaya Gidadon Katsina ya shiga wani sabon yanayi An fara shirye shiryen zuwa Katsina Domin duk shekara…A gidan Hajiya Khadija, mahaifiyar Alhaji Kamal, ake yin Eid ,Tun safe masu aiki suke kaiwa da kawowa Ana fitar da akwatuna Ana haɗa kayan yara ,Ana lissafa kayan Sallah Falon Umma cika da ledoji A ɓangaren Falmata ma haka ,Hatta Sadiya ta fito da sababbin kaya tana ta tantance abin da za ta tafi da shi Gaba ɗaya gidan ya koma cikin hayaniya
, Tadala na zaune a ɗakinta tana haɗa ’yan kayanta kaɗan, taji knocking
Sadiya ce hannunta rike da leda
Mami…” kece ina yini ?
Sadiya ta amsa sannan ta zauna a gefen gadon ,Tadala, ki yi haƙuri.
Tadala ta ɗan ruɗe Haƙuri kuma, Mami?”
Sadiya ta sauke numfashi
ban samu lokacin zuwa miki sayen kayan Sallah ba,Kin ga yadda gida ya cika da hidimomi
tadala ta yi saurin girgiza kai ,Laa Babu komai wallahi
Yauwa toh ga kayan last Sallah na da na taɓa sawa sau ɗaya zuwa biyu Har yanzu suna da kyau Na ce bari in ba ki su ,Tadala ta karɓi ledar ,kawai sai ta tuna laces, super, bazin, takalma da veils ɗin da Daddy ya saya mata ta hannun Anty Zaheera.
Ta É—an yi murmushi Nagode sosai, Allah ya kara arziki da wadata .
Sadiya ta jinjina kai ,ameen
Kuma maganar tafiyar Katsina Ina ganin gara ki yi Sallah a Zaria wajen Mama ,tunda gabadaya kaf dinmu katsina zamu
Tadala ta ɗaga kai da sauri “Zaria?
Sadiya ta tsuke fuska ,Kin ga ba ki daɗe da zuwa gidan nan ba ,Har yanzu ba ki saba da kowa ba ,Ni kuma ba na son ki ji babu daɗi idan muka je can “Kuma…” Ta yi kamar tana neman kalma “Kin san halin yaran gidan nan Musamman Kuna da Zahra
Bana son wani ya ji uncomfortable saboda an tafi da ke Katsina ,tadala ta zuba wa Sadiya ido, a zahiri, kalaman sun É—an soke zuciyarta Amma kuma ya kamata ace tun tuni ta saba da irin waÉ—annan wariyar dake nuna mata a gidan gidadon katsina
ta sauke numfashi a hankali, Duk inda kuka ga ya fi dacewa da ni, a nan zan yi Sallah,
Sadiya ta ci gaba da kallontayarinyar ba ta da hayaniya ko gardama
Zan kira Mama in sanar da ita ,Ta miƙe tsaye Kuma ki shirya Za a kai ki can gobe
Bayan fitar sadiya Ta kalli ledar da ke hannunta Ba ta damu da zuwa Katsina ko Zaria ba Abin da ya fi damunta shi ne…
Ashe har dai har yanzu ita ba cikakkiyar ’yar gidan ba ce
Bayan laaasar a babban falon Gidadon katsina umma , Falmata da Sadiya ne zaune suna duba abubuwan da aka daddy ya aiko na tafia katsina
A lokacin ne suka ji sallamar Anty Zaheera Ana biye da ita da manyan ledoji Masha Allah! Har kun gama shiri kenan ?”Ta faɗa tana zama
bayan an gama gaishe gaishe anty zaheera ta dubi sadiya
Ga kayan sallar Tadala ,idon Sadiya suka sauka kan ledodin ,Na Tadala?
Eh An gama dinka su duka Na ce tun da Sallah ta kusa, bari in yi wa yarinyar nan kayan sallah
Falmata ta yi murmushiAllah ya saka da alkhairi Sannu da kokari
Zaheera ta amsa a dakile
Dr Mariya ta ce Ah lalle tadala tayi saar uwar daki Zaheera ta jinjina kai ,yake sadiya tayi ta dinga wa zaheera godiya Sabida su dr
Sadiya Ina Tadala?
Tana É—akinta, ta amsa a ciki ciki
To, kira ta ta zo ta ga kayanta Itama ta gama shirin tafiya katsina da wuri
Sadiya ta yi shiru na ɗan lokaci Kana ta ce Anty… ai ba da ita zamu tafi Katsina ba Zaheera ta ɗaga kai a hankali Ban gane ba? na yi tunanin za ta yi Sallah a Zaria har na Kira maman ma
Zaheera ta zuba wa Sadiya ido.
Wa ya yanke hukuncin hakan ?uhmmm Ni… nice naga Kamar hakan yafi Dacewa I don’t want the kids to be uncomfortable ne kuma Kinga bata saba da kowa ba
shine kawai reason dinki sadiya ?anyways idan bata saba da yaran gidan nan ba ta saba da mardiyya ,kinga dama kakarsu tana umarah a gidan hajiya duk zamuyi sallah
on the other hand sadiya kina nufin haka za a bar yarinyar nan ita kaÉ—ai a Zaria, mu kuma mu tafi Katsina gaba É—ayanmu ?Sadiya ta gyara zamanta Ba wai haka ba ne, Anty Na dai ga kamar ba ta saba da family É—in ba
ta yaya za ta saba idan kullum ana ware ta? Sallah fa ta family ce Ba a ware mutane a irin wannan lokaci kuma na sha fada miki sadiya Tadala is officially a family member sabida haka, ina ba ki umarni Tadala za ta tafi Katsina tare da mu Za ta yi Sallah tare da family É—inta mu kenan
To, Anty sadiya ta amsa a sanyaye
kira mini Tadala ,Ina son in ga ko dinkin ya yi mata ,And also falmata duk ku tara min yaran gidan duk Ina da magana dasu ,Ba tare da musu ba, aka shiga kiran su Ba da daɗewa ba, yaran duk suka hallara sai daga ƙarshe Kuna ta shigo tana tafiya cikin isa kamar kullum
Tadala kuwa tana zaune a gefen kujera, idanunta suna bin kowa cikin natsuwa Bayan yaran Sun gama gaishe ta Anty Zaheera ta É—aga kai ta kalli Kuna
Maimuna
Kuna ta É—ago kai
Na’am, mommy
Kamal ya ba ni labarin abin da kika yi wa cousin din Sadiya Tadala kwanakin baya ,Kuna ta É—an kalli Sadiya da sauri Zaheera ta ci gaba Yanzu na ba da umarni za a tafi Katsina tare da ita
zaheera ta ɗan matso gaba Wallahi, wallahi, kin ji na rantse, ko kallon banza kika sake yi mata… Ta nuna ta da yatsa
Ba Marinki zan yi ba… Zane ki zan yi da bulala ,kuna ta Zaro ido
Ba ruwana da kin kai shekara ashirin da uku Ta sake nuna ta Kina jina?
Kuna ta haÉ—iye yawu
Eh… mommy
Eh me ?
Ina jinki, mommy
Good
Ta jingina da kujera.
My eyes are on you a Katsina Duk movies ɗinki ina kallo, so don’t try me ,Kuna ta yi saurin jinjina kai,kowa shakkar anty zaheera yake no nonsense woman ce kuma tasan tsaf zata aika abinda tace na zane ta ,sauran yaran ma ta ja masu kunne
Zaheera ta juya wajen Tadala ,Ki kai kayan sallar ki É—aki Ta nuna ledodin ,Ki sa su a cikin akwatinki Ki adana su da kyau Tunda Kema ba wanda ya nuna miki nasa
Nagode anty Zaheera Allah ya Kara arziki
A lokacin ne idanun Zaheera suka yi yawo a falon Ta lura da wani abu Yanmatan gidan kaf dinsu sunyi kunshi (lalle ).
Ta sake kallon matan gidan suma duk sunyi idanunta suka dawo kan Tadala Ba kunshi
Ta É—aga kai ta kalli Sadiya.
Sadiya
Na’am, Anty.
Anya Tadala jininki ce? Cousin É—inki ce?
A tsorace sadiya ta dago Meya faru, Anty?
Yanzu, tsakaninki da Allah, yaran ki da sauran yaran gidan nan duk sun yi kunshin Sallah… Ta nuna Tadala.
Banda ita Ta sake kallon matan
Har kuma matan gidan? Ta juya wajen Umma Dr, har da ke? Umma ta É—an yi shiru.
Zaheera ta girgiza kai Ku ji tsoron Allah
Kina ji na Tadala Gobe da sassafe, tunda flight É—in rana ne zan turo mai lalle ta zo ta miki kunshi kafin mu tafi Katsina.
Idanun Tadala suka É—an cika da kwalla
Ta jinjina kai Nagode, Anty Ta yi ƙasa da murya Allah ya ƙara girma
Zaheera ta yi murmushi Amin Sannan ta juya ta kalli Sadiya Idan ba za ki iya riƙe ta kamar su Safa ba…Ki ba ni ita... Ta dawo gidana ,Kafin wani ya sake magana…
Fuuu ,Anty Zaheera ta miƙe tsaye, ta gyara mayafinta, sannan ta fice daga falon tana mita, I hate bullies you all are bullies wallahi
wani mugun kallo sadiya tabi tadala dashi ,umma ta mike cikin habaici tace
mutum ya debo ruwan dafa kansa,
mtswwww sadiya taja dogon tsaki
biyoni tadala ta fada cikin fusata
Suna shiga dakin ta janyo tadala da Karfi ,ke kika cewa zaheera ban miki kayan sallah ba ?kin sa tazo cikin kishiyoyina tana ta fada min maganganu ?
wallahil azeem ban fada mata ba Yau throughout bamuyi waya da ita ba ,kwanaki dai da naje tasa an dauki measurement dina tadala ta fada a sanyaye
to nidai ba ruwanki da dangin mijina ki gama karatun daya kawo ki kara gaba