Free chapter · Read without an account

Disproval

by ZAHRAA · Zumar Hamada 🍯 🏜️


Bayan maganar Khalifa, Tadala ta daɗe a tsaye tana kallon bayansa cike da ruɗani. Sam ba ta fahimci me yake nufi ba Ta yaya ma ya san ba Mansoor take waya da shi ba? 

next day duk suka shirya zuwa kallon hawa , yauma tadala tayi kyau kamar ka saceta  VIPS seats suka samu a gidan sarki daga nan zasu dinga kallon kafin masu hawa  su tafi zaga gari 

Ga su nan Sun fito Mardiyyah ta janyo hannun Tadala suka matsa gaba kaɗan don su fi gani Da farko ta ga dawakai ne kawai chan ta hango shi   Yana kan doki, sanye cikin  shigar sarauta A wannan lokacin ba ta ga businessman ɗin Abuja ba, ba kuma Daddy ɗin da take saba gani cikin yadi ko suit ba Ta ga ɗan asalin Katsina ne mai cikar kamala da kwarjini irin na sarakuna , Mardiyyah ta kalle ta  tadala Yau Kinga Daddy a kan doki ko?

eh na gansa kuma sarautar ta masa kyau wallahi A gefe guda kuwa, Safa da Marwa sun ciro wayoyinsu suna ɗaukar hotunan Daddy ,ita ma tadala  ciro wayarta Ta ɗaga ta sama kaɗan duk camera is not clear kamar tasu twins 

click Ta ɗauki hoto daya biyu  har biyar ta  ci gaba da snapping ɗinsa murmushi  kwance a fuskarta A can kuwa  tun da Alhaji Kamal ya fito idanunsa suka sauka kan Tadala ba ƙaramin kyau ta yi ba masa ba bazin ɗin ya zauna daram a jikinta gold ɗin kuma ya ƙara fito da hasken fuskarta. Kwalliyarta ta yi mata wani irin kyau da ya sa ko daga nesa take ɗaukar numfashinsa chan kuma ya Lura Ba shi kaɗai yake kallonta ba  harda masu  waiwaya  wasu kuma idanunsu sun makale a kanta A hankali fuskarsa ta sauya  At this point Ya fara gane cewa maza ba za su ƙyale masa Mi Dahlia cikin sauƙi ba chan  ya ga wani saurayi ya matso kusa da inda take tsaye ita da Mardiyyah ,amma kuma tadala yakewa magana  Kamar har murmushi yaga mi dahlia dinsa tayi wa saurayin wani irin kishi  ne ya taso masa ji yayi gaba daya hawan ya fita a ransa


A ƙasar Saudi

(*** ga masu Neman number na )

Bayan an idar da sallar Eid, Nadira da Alya suna zaune a cikin ɗaya daga cikin manyan lounges din hotel ɗinsu, suna jiran dawowar Nawaf daga masallaci Tun ranar da suka iso ƙasar domin gudanar da Umrah, rayuwarsu ta sauya ta wata hanya da Nadira ba ta taɓa tsammani ba. Hayaniyar da ta saba mamaye gidansu ta ɓace, gardama da saɓani sun yi nisa da su, yayin da wani irin yanayi na natsuwa da kwanciyar hankali ya mamaye zaman nasu. Nawaf ya fi kasancewa tare da su fiye da da, har ma murmushin da ya daɗe bai bayyana a fuskarsa ba ya fara dawowa a hankali 

Nadira ta ɗan ɗaga kai ta kalli ƙofar lounge ɗin, kafin ta sauke ajiyar zuciya Wai me ya tsaya yi haka ne?A karon farko cikin shekaru masu yawa, zuciyarta ta ji 

wani irin salama Ashe rayuwar aure  tana da daɗi idan babu faɗa babu zargi, babu blackmail da ɗora wa juna laifi Kawai zaman lafiya ne da nutsuwar da ta daɗe tana mafarkin samu.

Ba da jimawa ba ƙofar lounge ɗin ta buɗe, Nawaf ya shigo cikin takunsa na natsuwa. Sanye yake da farar jallabiya  wadda ta ƙara fito da kwarjininsa, yayin da a hannunsa yake riƙe da wasu ƙananan ledoji.  Alya na  hango shi ta miƙe da gudu tana faɗin, abba  Murmushi ya bayyana a fuskar Nawaf, irin murmushin da ya kan yi ne kawai idan yana tare da Alya. Princess…ya faɗa yana buɗe ɗaya daga cikin ledar ya miƙa mata ga eid gift dinki Mine?ta tambaya cikin zumuɗi 

 yes princess   Ayla tace thank you abba ,you’re the best i love you 

Nadira ta ci gaba da kallonsu   ta yi kewar wannan Nawaf ɗin… Nawaf mai fara’a

 ya sake ɗauko wata ledar ya miƙa mata ga naki  

nadira ta ɗan zaro ido cikin mamaki Ni?Ya ɗan gyada kai kawai 

 ta karɓa, ta buɗe ledar cikin natsuwa. Tasbaha ce mai  kyau sai favorite turaren ta  sai agogo mai kyau daga gani zaiyi tsada ba kadan ba , Ta daɗe tana kallonsu kafin ta ɗaga idanunta gare Nagode Zauji Bai ce komai ba sai ɗan jinjina kai da ya yi, shiru sukayi nadira ta rasa wace hirar zata ja nawaf dashi

Abba dazu da kana addua mai kake cewa Ayla ta katse shirun 

Tambayar ta sanya Nawaf yin shiru na wasu daƙiƙu. Kamar wanda yake nazarin amsar da zai bayar, daga bisani ya sauke numfashi a hankali ya ce, Na roƙi Allah Ya ba ni natsuwa Nadira ta ɗan ɗago kai ta kalle shi Ko kaɗan ba wannan amsar ta zata ba, Alya kuwa ta yi dariya cikin rashin damuwa irin ta yara 

Shi ke nan abba Allah zai ba ka

Allahumma ameen princess 

Sai dai duk da natsuwar da yake ƙoƙarin samu, zuciyarsa ba ta gama hutawa ba. Akwai wani abu da yake nema amma ya kasa fassara shi Wani gibi da yake ji a ransa ba tare da ya san me yake nufi ba. Cikin wannan tunani ne, ba tare da ya shirya ba, wata fuska ta faɗo masa Farida as usual 

Ya tuna yadda take dariya cikin walwala, yadda idanunta ke cika da rai idan tana magana  Nan take ya buɗe idanunsa da sauri, ya gyara zamansa kamar wanda aka tashe daga mafarki  Nadira ta lura da sauyin da ya samu, ta kalle shi cikin damuwa ta tambaya, lafiya?

Ya juyo da sauri, ya ce lafiya lau

Sai dai a cikin zuciyarsa, tambaya ɗaya ce ta ci gaba da yawo gashi dai yana  cikin Haramin Makkah yana ƙoƙarin kusantar Ubangijinsa… me ya sa har yanzu wata fuska guda ɗaya take ci gaba da dawowa cikin tunaninsa?


gaba ɗaya iyalan gidan suka hallara a babban falon Hajiya, inda aka saba zama bayan irin waɗannan rana ku na musamman ana ta ba  juna labarin abin da ya faru dazu a Hawan Sallah, yayin da Hajiya ke ba jikokinta  labarin yarintar ta ,tana haɗa su da barkwanci har ta sa manya da ƙanana dariya lokaci guda.

Suna cikin wannan yanayi ne ɗaya daga cikin masu aikin gidan ya shigo falon bayan ya yi sallama cikin ladabi Hajiya ta ɗago kai ta amsa sannan ta ce, “Lafiya saminu? saminu ya ɗan sunkuyar da kansa kafin ya ce Hajiya… akwai wani saurayi a waje  Ya ce yana son yin magana da Wai buzuwa ”Ya nuna inda Tadala take zaune

Falon ya yi tsit na ɗan lokaci Tadala ta ɗaga kanta cikin mamaki  ta Nuna ƙirjinta da yatsa kamar mai tambayar kanta ko ita yake nufi. Ni?

Eh, ke Ya ce sunansa Hamid 

Da jin sunan, Tadala ta ɗan yi tunani shine dazu yake ta naci ta bashi number taki daga karshe ya tambaye ta a ina take cikin kosawa tace masa gidan su gidadon katsina 

Hajiya ta jinjina kai cikin natsuwa To ki je ki ji abin da yake son faɗa fadimatu 

Tadala ta ji gabanta ya faɗi Ba ta san dalilin ba, amma kafin ta miƙe sai da idanunta suka nemi Daddy Kamar tana son ganin wani abu a fuskarsa

Sai dai Alhaji Kamal bai ko ɗago ya kalleta ba ,yana  kallon wani gefe kamar baya falon 

Jeki mana Fadimatu Hajiya ta sake maimaitawa cikin tausasasshiyar murya.

Da ƙyar Tadala ta miƙe daga inda take zaune ,Khalifa shi ma ya miƙe ba tare da wata-wata ba ,zan raka ta, ganin ba Wanda ya hanashi ,msuka fita tare 

A harabar gidan kuwa Hamid yana tsaye cikin wani yadi mai tsada 

fuskarsa cike da ladabi yana  hango su ya yi saurin yin sallama

suka amsa masa Ya ɗan yi shiru kamar wanda yake tattara ƙarfin guiwar fara magana sannan ya ce A gaskiya… na zo ne neman izini ne  Khalifa yace Izinin me?”and please introduce yourself 

Hamid ya gyara tsayuwarsa, sannan idanunsa suka sauka kan Tadala na ɗan lokaci kafin ya ce suna Abdulhamid SKB Ina aiki ne a CBN Na ga wannan baiwar Allah yau wajen Hawan Sallah, shysa na biyo ta gida kamar yadda addini ya hallarta ,na zo in sanar da iyayenta  cewa ina da niyyar neman aurenta  .maganar ta saukawar Tadala kamar daga sama  ta kasa cewa uffan

Khalifa yayi gyaran muryar yace mungode Allah Ya saka da alkhairi amma ka yi haƙuri… a riga an yi mata 

miji Hamid ya tsaya na ɗan lokaci yana kallonsa Oh…kawai ya iya faɗa kafin ya sauke numfashi ya ce, Allah Ya sa alkhairi..All the best 

Khalifa ya amsa Hamid ya sake yi musu sallama cikin mutunci, sannan ya juya ya tafi.

yana fita Tadala ta juyo tana kallon Khalifa cikin mamaki An yi min miji?ta tambaya fuskarta cike da ruɗani wani Mijin?

Khalifa ya yi murmushi irin nasa mai cike da sirri Mu koma ciki Anty tadala ya juya ya fara tafiya ba tare da ya amsa tambayar ba 

suna shiga  falon Hajiya ta ɗago kai tana kallonsu Kun dawo? Me yake so? Khalifa ya zauna cikin natsuwa kafin ya ce Ya zo ne yana wai  ya nemi auren Fadimatun ki

To me ka ce masa?Na gaya masa an yi mata miji Nan take Hajiya ta mayar da kallonta kan Tadala Fadimatu… da gaske ne?kafin Tadala ta samu damar buɗe baki Sadiya ta yi saurin cewa, Akwai wani daga Nijar da zai aiko manya nan ba da jimawa ba Ana cikin maganar ne sun dade tare 

Hajiya ta yi shiru na ɗan lokaci tana nazarin maganar kafin daga bisani ta ce c

To tunda ba a kai ga maganar ba, bai kamata a kori yaron nan haka ba Mace ai allura ce cikin ruwa… Kalmar ta sauka cikin falon kamar ba ta da wani nauyi, amma ga mutum ɗaya ta bugi zuciyarsa  Alhaji Kamal  Ya sauke idanunsa ƙasa yana jin tamkar an danne masa zuciyarsa A karon farko, wani irin tsoro ya shiga ransa… tsoron da bai taɓa jin irinsa ba. Domin ya fahimci abin da Hajiya ke nufi. Tadala kyakkyawa ce, yarinya ce, kuma idan ya ci gaba da shiru yana jiran lokaci ya wuce zaa kasa shi 

Bayan an watse daga falon Hajiya kowa ya nufi ɗakinsa A Alhaji Kamal bai motsa ba Yana tsaye a harabar falon idanunsa a lumshe,kalmar Hajiya tana ci gaba da maimaituwa a kansa zaheera na gefe tana chatting da mijinta 

Zaheera 

Ta juya ta kalle shi Na’am?”Ya yi shiru na wasu daƙiƙu ya ce Zan faɗa wa Hajiya Zaheera ta ɗan zaro ido Yanzu?

Ya gyada kai Eh ta sauke numfashi Mu je 

Suka sami Hajiya a ɗakinta Tana zaune a gefen gado Al-Qur’an a hannunta  Suratul Mulk take karantawa ,Ba su ce komai ba 

Har ta kai aya ta ƙarshe 

Ta yi addu’a Ta shafa a fuskarta sanna ta ɗago kai Yan biyuna… me ya kawo ku da dare haka? Da alama akwai magana Zaheera ta kalli Kamal

 dik sun  rasa inda zasu fara 

Hajiya…“Na’am?

Kamal zai ƙara aure ,Hajiya ta yi murmushi Masha Allah Ta kalli Kamal  Allah Ya sa albarka A ina ka samo matar?Zaheera ta haɗiye yawu sanna tace Tadala ce Kusan daƙiƙa goma Ba wanda ya motsa Hajiya ta zuba musu ido Ta sake kallon Kamal 

Kalma daya ta furta Ban amince ba

Me?Zaheera ta faɗa a hankali Hajiya ta rufe Al-Qur’an ɗinta Ta ajiye shi a gefenta Sannan ta ce Ban amince ba Ta nuna musu ƙofa ku fitar min  daki bacci zanyi  mamaki ya bayyana a fuskar zaheera

Ba ta taɓa ganin Hajiya ta yanke hukunci cikin sauri haka ba  Ta matsa kusa Hajiya, ki saurare mu mana Hajiya ta girgiza kai Ba fa zan amince ba ana barin halal dan  kunya.

 Kamal ya ɗago kai muryarsa na rawa yace Hajiya Dan Allah ki taimaka idanun Hajiya suka ɗan canza Amma ta yi shiru Wallahi Muryarsa ta sarƙe yace Ba zan iya rayuwa babu ita ba dan Allah hajiya ,Zaheera ta juya da sauri ta kalle shi Twin ɗinta roƙo yake yi Ta maida kallonta ga Hajiya Hajiya ki taimake shi Wallahi yana sonta ,Hajiya dan Allah 

 ku fita zaheera Zan kwanta ba Wanda yayi motsi a cikin su 

Ta sake maimaitawa Na ce ku fita dan kaniyarku 

Sum-sum suka fita  zaheera ta kalli kamal Ka haƙura kenan Twin?

Bai amsa ba  kawai ya ɗaga kai Ya kalleta kawai sai Ya fara tafiya Kamal tsaya mana Kamal, cak  ya tsaya Amma bai waiwayo ba Zaheera ta sha gabansa  Ta ɗago ta kalli fuskarsa  Gabanta ya faɗi A hankali ta ce Kuka kake? Da sauri ya juya fuskarsa gefe “A’a.

Muryarsa ta fito a sarƙe 

good night twin ya fada yana kokarin tafiya 

good night kar hakan yasa jikin ka yayi sanyi fight for your woman kamal and ka goge hawayen Kafin su karasa zubuwa


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol