Free chapter · Read without an account
Chapter 4
by Amanarcool · SAUTIN KARSHE
Babu ɓata lokaci ya nemo mai a daidaita sahu, ya shiga ciki yana faɗin "Inna ɗakko ta, ga abin hawar nan na samo". A lokacin har an fara kiran sallar magariba, Inna ta fito ɗauke da Abida a hannunta, karɓar ta Aliyu ya yi, ya fita da ita waje, Inna ta ce "To Halima ku kula da gidan sai mun dawo" Ta yi maganar tana nufar hanyar fita daga gidan, Aliyu ya zauna riƙe da Abida da jikinta ke wata irin kakarwa, Inna ta riƙa shafa fuskarta tana karanta addu'o'i a hankali tana tofa mata. Gabaɗaya Aliyu rasa nutsuwarsa ya yi. A zuciyarsa yake tunanin ko za a karɓe su idan suka je, ko kuma za'a yi musu kallon raini ne saboda rashin kuɗi. Sun ɗan yi tafiya mai nisa kafin su ƙaraso Asibitin
Katafaren gini ne da aka yi shi cikin tsari mai kyau da ɗaukar hankali. Suna tsaya wa a harabar wurin Aliyu ya fito da sauri, Abida na rungume a jikinsa. Ba tare da ya yi tsammani ba, ya ga wata nurse ta nufo su da sauri tana faɗin "Sannunku da zuwa, meyafaru?" Ta ya musu tambayar cikin tsantsar kulawa. Aliyu ya buɗe baki zai yi magana sai dai kalmomin suka kasa fita daga bakinsa. Sai Inna ce ta ce, "Wallahi bamu san me yake damunta ba, gata nan dai numfashinta har neman ɗaukewa yake, kawai dai mun ga jikinta na ƙamewa kamar tana jijjiga".
Da sauri nurse ɗin ta karɓi Abida, ta shiga da ita ciki da hanzari.
Aliyu dai tsayawa ya yi yana bin su da kallo, ya ma rasa abin yi a tsorace yake kar a caje su kuɗi ya kasa biya.
Halin da Abida take ciki ya sa kai tsaye emergency aka wuce da ita. A reception record officer ya kalli Aliyu ya ce, "Kai ne mahaifinta?"
Jiki a sanyaye ya ce "Eh ni ne"
"Ok, ka zo zamu buɗe mata file".
Cikin sanyin jiki Aliyu ya ce "To shikenan, sai dai bamu da isasun kuɗi a hannunmu, yanzu ma jira nake yi na ji me za ku ce?".
Ya ƙare wa Aliyu kallo sannan ya ce "Ka kwantar da hankalinka. A nan ba'a buƙatar wasu kuɗaɗen a hannunku masu yawa, akwai ɓangaren da ake bayar da kulawa ta musamman, an biya kaso bakwai na abin da za a yi wa mara lafiya, kaso uku kawai za ka biya. Abin da likita ya ce za a duba, sai a saka ku a tsarin tun da na ga alamar ba ka da ƙarfi, in sha Allah za'a yi mata duk abin da ya dace".
"Kai amma kuwa na gode sosai da sosai, Ubangiji Allah ya saka wa wanda suke ɗaukar nauyin marasa lafiya da alkhairi na gode sosai "
Sai a lokacin ya ji ya samu nutsuwa. Bayan an buɗe mata file ɗin ne ya dubi Inna ya ce "Inna bari na je waje na yi sallah kin ga har lokaci ya wuce" Inna ta ce "To shikenan nima bari na yi sallar kafin su fito mu ji halin da ake ciki". Fita ya yi waje, ita kuma Inna wata nurse ce ta nuna mata inda za ta yi alwala ta yi sallah.
****
Zaune yake a cikin katafaren falonsa, sanyi Ac na ratsa shi ta ko ina, hannusa riƙe da kofi yana shan coffee a hankali yana kallon tv, kira ne ya shigo wayarsa, cikin nutsuwa ya ajiye kofin hannunsa tare da ɗaukar wayar ya kara a kunnensa. "Kar ku damu, ban samu yin magana da yaron ba, amma na bar saƙo wurin abokinsa, na san yana ganin saƙona zai neme ni, saboda tamkar uba nake a wurinsa". Shiru ya yi yana sauraren na cikin wayar, kafin ya ce "Ok to shikenan, ai baku da matsala in dai harkar kasuwanci ce yaron ya ƙware sosai". Ya yi masa sallama ya ajiye wayar, ɗaukar kofin ya yi ya ci gaba da shan coffee ɗin sa yana kallo.
*****
Hanif na kwance yaga kiran Sudais ya shigo wayarsa, kamar ba zai ɗauka ba, sai kuma ya ɗaga yana faɗin "Malam lafiya za ka dame ni da kira yanzu?".
"Naga saƙonka" Sudais ya faɗa
"To sai aka yi yaya?" Cewar Hanif don haushin Sudais ɗin yake ji.
Murmushi Sudais ya yi, saboda ya san abokin nasa a hasale yake da shi, cikin kwantar da murya ya ce "Haba mutumina, am so sorry ɗazu koda ka kira ni ba a daidai nake b..." "Kaga ni ba wani daɗin baki da za ka yi mini yanzu" Hanif ya katse shi, kafin ya ci gaba da faɗin "Ai in da sabo na saba da wannan baƙin halin naka. Yanzu dai tunda kaga saƙon dana tura maka ɗin sai ka neme shi kuyi magana domin ya tabbatar da na isar da saƙonsa" daga haka Hanif ya katse wayar yana jan tsaki.
Sudais kuwa murmushi ya yi, yana bin wayar da kallo, shi kan shi ya san Hanif na haƙuri da halinsa wasu lokutan, shi ya sa yake ƙara jin ƙaunarsa a ransa, domin samun aboki irinsa sai an tona.
****
Sai da ya yi sallar isha sannan ya dawo cikin asibitin da sauri. Tun daga bakin corridor ɗin ya hango Inna tsaye a bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da Abida, sai zarya take cikin tashin hankali da damuwa, bakinta na motsi alamar addu'a take yi. Ganin yadda ta yi zuru-zuru ya sa gaban Aliyu ya faɗi. Da sauri ya ƙarasa gare ta ya ce "Inna lafiya? Har yanzu ba su fito ba ne?".
Kai ta girgiza masa kawai kafin ta ce "Har yanzu basu fito ba".
Shiru ya yi ya jingina da bango yana jin zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, idan ya tuna yadda jikin yarinyar ya rikice gabaɗaya, sai ya ji jikinsa ya yi sanyi.
Buɗe ƙofar aka yi, wani likita ne sanye da farar coat ya fito yana cire safar hannunsa. Da sauri Aliyu da Inna suka zuba masa ido suna kallonsa. "Kai ne mahaifin yarinyar nan?".
"Eh likita" Aliyu ya faɗa da sauri.
Kallonsu likitan ya yi, yanayin fuskarsu kaɗai ya isa ya nuna irin tashin hankalin da suke ciki. Cikin nutsuwa ya ce "Biyo ni ofis". Daga haka ya yi gaba, Aliyu ya bi bayansa.
Suna isa ofis ɗin, ya zauna tare da nuna ma Aliyu kujerar zama, zama ya yi yana tsare shi da ido saboda ya matsu ya ji wane hali ƴarsa take ciki. Likitan ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce "Mun gama duba ta, tare da yi mata duk wani gwajin da ya dace, maganar gaskiya akwai matsala, yarinyarka na fama da wani ciwo ne a cikin cikinta wanda yake buƙatar aiki cikin gaggawa, idan ba haka ba kuma matsalar za ta iya ƙara tsananta. Ta samu ƙullewar hanji ne sai an yi aiki an gyara".
Wani irin jiri ne ya ɗibi Aliyu, da sauri ya jingina jikinsa da kujera yana bin likitan da kallo kamar bai gane abin da aka faɗa ba. Can kuma ya ce "Aiki fa ka ce?" .
Jinjina masa kai ya yi, sannan ya ce "Dan haka akwai buƙatar a yi mata aiki da gaggawa kar a samu matsala, yanzu za a nemo jini a ajiye". Likitan ya yi masa bayani cikin nutsuwa.
"Innalillahi wa inna ilaihim raji'un" shi ne kawai abin da Aliyu yake ta nanatawa, kafin ya ɗago yana kallon likitan da idonsa da suka canza launi, cikin dasashiyar murya ya ce "Likita aikin da za'a yi mata yana buƙatar maƙudan kuɗi ko?"
Tambayar tasa ta fito cike da tsoro da farga ba.
Tausayinsa ne ya bayyana a kan fuskar likitan. Cikin kwantar da murya ya ce
"Eh to, gaskiya da kuɗi, amma mu na da sashi na musamman, Asibiti na da gidauniya da masu hali suke saka kuɗaɗen tallafi, har da sauran hukumomin lafiya na duniya su na saka tallafinsu. So tun da yarinya ce ƙarama za ta iya shiga cikin tsarin tallafin. Kuɗin gado kawai za ku biya, da kuɗin aiki da na magani duk a ciki za a yi mata"
Aliyu ya kasa magana na ɗan wani lokaci, ya tsurawa likitan ido yana tunanin ko dai kunnuwansa ne basu ji abin da ya faɗa daidai ba. Da ƙyar ya buɗa baki ya ce "Likita kamar kyauta na ji kana faɗar za a yi aikin? Ko dai nine ban ji abin da ka faɗa daidai ba?".
Murmushi ya yi, ya ce "Eh haka na faɗa, in sha Allah za a yi mata aiki kyauta, kuma za ta samu lafiya in sha Allah, kuɗin gado kawai za ku biya". Shiru Aliyu ya yi yana tunanin dama taimakon nan da ake faɗar ana yi a asibitin nan gaskiya ne? Murya a sanyaye ya ɗago da kai yana kallon likitan ya ce "Na rasa wace kalar godiya zan yi muku, bakina ya rasa kalmomin da zai furta a matsayin nuna godiyata a gare ku. Sai dai ina fatan Ubangiji Allah ya yi muku tukwaici da gidan aljanna, Allah ya ƙara ɗaukaka darajar wannan asibitin. Muna godiya sosai da sosai".
"Amin summa Amin, yanzu ka je ku tsara yadda za a tanadi jinin da za a yi mata aikin, za a baka consent form da zaka saka hannu. A daren nan in sha Allah za a yi mata aikin"
Aliyu ya yi ta murna tare da jero musu duk addu'ar da ta zo bakinsa. Yana fita Inna ta tare shi da tambayar ya ake ciki? Me yake damunta?. Nan ya yi mata bayanin komai, abu biyu ne suka haɗe mata lokaci ɗaya, ga damuwar aikin da aka ce za a yi wa Abida, da kuma farin cikin jin za'a yi mata aikin kyauta. Ta dubi Aliyu tana faɗin "Allah mun gode maka, kaga abin da nake faɗa maka ko Gadanga? Dama an ce asibitin nan ana taimako. Ubangiji Allah ya saka musu da alkhairi, Allah ya basu ladan wannan aikin taimakon da suke yi. Ka tambaye su nawa ne kuɗin gadon, sai mu je gida a faɗi a tashi a nema" jiki a sanyaye ya amsa mata da "Amin" sannan ya ce "Inna, ina tunanin ko za ki je gida domin ki sanar da Halima halin da ake ciki, tunda sun ce a daren yau za su yi mata aikin. Ba lallai ne mu sake ganinta yau ba sai zuwa gobe, na san yanzu haka hankalinta a tashe yake". Inna ta ce "A'a ko dai kai ka tafi gida, ni ba inda zani zan zauna a nan, kai da kake namiji kai ya kamata ka tafi, in ya so gobe da safe sai ka dawo". Ba haka ya so ba, kawai dai baya son yin jayayya da Innar ne ya sa ya ce mata "To".
Wayar abokinsa ya kira, ya sanar da shi halin da ake ciki, ya nemi ya ba shi aron kuɗi, dan ya samu ya biya kuɗin gadon da aka nema.
Koda ya isa gida a tsakar gidan ya tarar da Halima da Ma'u zaune, sannu da zuwa suka yi masa, ya amsa tare da neman guri ya zauna, Halima na son tambayarsa ya jikin Abida amma ta kasa saboda fargabar abin da za ta ji. Ma'u ce ta yi ƙarfin halin cewa "Yaya ya jikin Abidar da sauƙi?".
"Eh da sauƙi, ko da na baro an shiga da ita za a yi mata aiki". Dafe ƙirji Ma'u ta yi, ta ce "Aiki kuma Yaya? Wane irin ciwo ne haka da har za a ce sai an yi mata aiki?". Kamar ya share ta sai kuma ya ce "Sun ce tana da matsalar ƙullewar hanji, wanda dole sai an yi mata aiki da gaggawa". Shiru Ma'u ta yi tana tunanin wane irin ciwo ne wannan. Halima ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba da jin cewar za a yi wa ƴarta aiki ba. Cikin karaya ta ce "To a ina za a samu kuɗin da za a biya a yi mata aiki yanzu? Duba da halin da muke ciki" ta yi tambayar cikin yanayi na damuwa. Jiki a sanyaye ya ce "Sun ce akwai wani ɓangare na tallafi da aka ware domin taimakawa marasa ƙarfi, za su saka ta a ciki, aikin kyauta za a yi mata, kuɗin gado kawai zamu biya. Yanzu sai ki haɗa mana kayan da za a buƙata mu tafi asibitin" yana gama faɗar haka ya shiga cikin ɗaki. Bin bayansa suka yi da kallo. Ma'u duk da tashin hankali da ta ga Halima a ciki, hakan bai hana ta yin ƙasa da murya ba ta ce "Aunty Halima wannan mijin naki ba ƙaramin ƙoƙari kike yi na zama da shi ba, wannan ai da mijina ne kullum sai an jimu da shi. Idan ta kama ma zamu iya bawa hammata iska....." Fitowar da ya yi ne ya sa ta yin shiru. Halima ta yi murmushin ƙarfin hali, wato a ko wane yanayi ake ciki Ma'u sai ta nuna halinta. Ya dubi Ma'u ya ce "Ke tashi ki je ki kwanta dare ya yi".
Wuƙi-wuƙi ta yi da ido tana kallon ɗakin Inna, kafin ta fara susar jiki ta ce "Yaya wai a ɗakin Inna zan kwana ni kaɗai?".
"To da a ɗakin wa za ki je ki kwana?" Ya tambaya yana haske ta da fitila. Shiru ta yi tana sunkuyar da kai.
Halima ta ce "A'a ba zai yiwu a bar ta ita kaɗai ba, sai dai mu tafi tare har da ita" bai ce ƙala ba ya ɗauki buta ya shiga makewayi.
Yana shiga Ma'u ta ce "Yanzu na ji batu, dan wallahi ba zan kwana a gidan nan ni kaɗai ba, sai dai na biku mu tafi tare". Halima ta ce "To bari ya zo na faɗa masa abin da kika ce" "Saboda kin iya munafurci ko? Ke dai ki ji da abin da yake damun ƴarku, na san yau daga ke har shi babu wanda zai yi bacci, ni kam baccina zan yi hankali kwance, dama duk damuwar da kika ga ina yi ta munafurci ce" . Ƙyale ta Halima ta yi, domin ita a yanzu tunanin halin da ƴarta take ciki take yi, ta shiga surutu sai da ta ji alamar Aliyu zai fito sannan ta tashi ta shige ɗakin Inna. Halima ta gama haɗa musu duk wani abu da za su buƙata, sannan suka rufe gidan suka tafi asibiti. A daren aka nemi jinin da za a saka mata, Inna ta ce "Aliyu ya koma gida ya kwana, saboda kar a bar gidan babu kowa" ba don ransa ya so ba ya yi musu sallama ya tafi. Ƙarfe biyu na dare, bayan jinin da aka saka mata ya ƙare, aka shigar da ita ɗakin da za a yi mata aikin. A daren nan gabaɗayan su babu wanda ya yi baccin kirki, kowa da abin da yake saƙawa a ransa, hadda Ma'u ba ta yi wani baccin kirki ba, tana farawa take farkawa. Sai wajen asuba wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da su.
Amanarcool
***