Free chapter · Read without an account
G_D - 3
***
◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦
𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️
Zaku iya Karanta GUMBAR DUTSE a Wattpad & Arewabooks @KhadeejaCandy
𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 3️⃣
Hannayensa ya zuba aljihu yana ta kallon mutanen karkarar, ganin rawar dandali mai kama da taron kasuwa wani abu ne sabo a gurinsa, kusan tun da yayi wayo ya mallaki hankalin kansa be taba zuwa karkara ba, be rayu da mutanen karkara ba.
Yadda suke tafiyar da rayuwarsu mu'alamarsu da yadda suke karrama baki abun ya burge shi matuka, ba su da wutar nepa ,ba su hanya mai kyau da abinci kamar birni, ba su da gine gine na zamani kamar Abuja ko Kano, amman a haka suna rayuwarsu cikin farinciki, wannan ma wani sabon karatu ne a gurinsa.
A lokacin da idonsa ya sake sauka akan Batula sai ya kasa kauda fuska, a ganin da yayi mata daga dazun zuwa yanzu da dare nan, ya fahimce abubuwa uku akanta, tana da son nishadi tana da far'a kuma tana da kyau.
Yana da dayan abubuwan da take da su wato kyau, amman ya rasa nishadi ya rasa yadda zai koyi zama da mutane ko sakewa a cikinsu, ya rasa yadda zai yi ya koyi surutu ko iya bada labari. Ita ta rasa baki amman bata yarda ta rasa nishadi da far'a ba, shi kuma yana da bakin amman magana tana masa wahala, kamar yadda far'a ta juya masa baya, ba kasafai ake ganin murmushinsa ba ko da kuwa yana a yanayin farinciki ne, sai idan ta kai ta kawo yake murmushi, dariyarsa kuma mahaifiyarsa ce kadai take iya bada labarinta, tun bayan da ta bar duniya Jawad be sake samun wani farincikin ba.
Bata yarda nakasa ta saka damuwa ba, bata yarda nakasa ta hana ta farinciki ba, bata yarda ta zama dabam da sauran mutane ba, bata yarda nakasa ta hanata karatu ba, hakan ya burgeshi, yana son jajirtattun mutane masu kokarin ganin sun yi nasara a rayuwa kamar yadda shi ma yayi. Ya daga kansa sama ya kalli sararin samaniya, hatta iskar karkara dabam take ko'ina a sake iska na kadawa kana gaanin fadin sama, idan ka sauke kai kuma kana hango wasu gidaje ko garuruwan da suke kusa. Ya lumshe ido yana maida numfashi a hankali, yana jin ina ma ace lokacin da mahaifiyarsa ta rayu a kauyen yana da wayo, ta fada masa a kauye ta yi rayuwa a nan ta girma, akan je kauye da shi, amman ba zai iya wasu abubuwan ba. Wayarsa ta yi vibration ya bude idon ya ciro wayar ya duba mai kiran, kamin ya amsa ya kara a kunne.
"Kaka"
"Jawadi, kana lafiya?"
"ina lafiya Kaka"
"baka kira ni ba tun da ka tafi, kuma dare yayi baka dawo ba, na ga suna rufe gate din"
"A nan za mu kwana sai gobe zan dawo"
"Allah ya tsare, ya kawo lafiya ka ga a cooler da aka zuba min abinci yau? Saboda ta ga baka nan, daman na fada maka dawowarka ne ya saka take min abun kirki, bata da mutunci ko kadan"
"Zan dawo ai Kaka"
"Tohm a dawo lafiya, Allah ya maka albarka ya baka mata ta gari"
" Ameen"
Ya kashe wayar ya sauke, sannan ya kalli Ariz da ya iso gurin waya cikin bacin rai, sai da ya gama wayar sannan ya kalli Jawad yana jan tsaki ya ce.
"Wai gilas din window na aka fasa"
Jawad ya sake dubansa da alamar tambayar ta ya haka ta faru.
"Yaran makota na ne, jiya ma kamin na fito sai da suka min barna, idan na koma sai na nuna musu ban da mutunci, na gane idan ka shiga sabuwar unguwa idan baka nuna musu jan wuya ba ne kai sai su raina maka wayo, na san duk ba zai wuce laifin wannan yarinyar ba, sam bata ita tsawatar da kanenta"
Ya karasa da kwafa. Jawad ya maida dubansa gurin dandalin ya acigaba da bawa idanuwansa abinci. Ariz ma kallon yake yana fadawa Jawad wasu abubuwan da be sani ba.
"Kai yarinyar can kamar ita ce muka gani dazun"
Jawad ya daga kai alamar eh.
"Me take siyarwa a can?"
Jawad ya kalleshi yana daga fadunsa alamar ta ina zai sani bayan shi ma tsaye yake tare da shi. Ariz ya gangara ya sauka kan dutun da suke daman hanyar ta kan tudu ne ake gangarawa a sauka dandalin, yana isa gurin idon mutane ya dawo kansa daman wasu sun hango shi tun a lokacin da suke tsaye, wasu kuma a yanzu ne suke ganinsa, kana ganin yanayinsa kyaun tufafinsa da kalarsa ka san dan birni ne ba dan garin ba. Da ya sauka yayi ta kallon abubuwan da suke gurin ne yana tambayar wasu abubuwa da farashinsu ba dan ya siya ba.
Batula na ganinsa ta daina rawa ta zauna ta rike bahon kulinta tana ta kallonsa har ya iso inda take, suna hada ido ta daga masa hannu ta washe hakora.
"Me kike siyarwa"
Ya tambaya yana mata alama da hannu domin be yi zaton tana ji ba. Ta nuna kullinta ta dauka ta mika masa, be karba sai ya ce ta aje.
"Ina yayanka"
Ta hada hannu biyu yatsa da yatsa ta nuna babban ta tambaya, ai ba zata manta da wanda ya bata kudi ba, sai kuma ta yi sa'a Ariz ya fahimce tambayarta.
"Yayana? Ba yayana ba ne, dan'uwana ne"
Ya juya ya nuna mata inda Jawad yake tsaye, sai ta tara hannunta a goshinta tana tare hasken wutar karar dake tashi domin ta samu damar hango shi da kyau, sai farin watan daya haska garin ya taimaka mata gurin hango shi. Ta daga masa hannu hakoranta a bude amman shi be dago mata ba, yana can tsaye a natse yana kallonta.
Batula ta kalli Ariz ta janye bahonta ta rubuta masa a kasa.
"Ka ce ya siye kuli kuli akwai dad'i sosai, tun da yana da kudi"
Ariz ya karanta sannan yayi dariya ya juyo ya kalli Jawad ya juya ya kalli Batula, yayi mata alama da ta tafi ta kai masa, sai ta lake fada bata yarda ta tafi ba. A ransa ya ce 'Ai ya fiki iya shege'. Sai da Ariz ya gama zaga gurin ya kalli abun da zai gani ya gaisa da wasu sannan ya koma gurin da Jawad yake tsaye yana jiran ya dawo su tafi, domin abun da shi ba zai iya ba ne. Kusan sai da aka fara watsewa a dandalin sannan Batula ta doro bahon kulinta ta nufo gida tana tafe tana hawaye, ta san dole yau za'ayi mata dukan da take tsoro domin tun da ta fita bata dawo ba saboda bata dawo ba saboda bata siyar ba, gashi kuma dare yayi still bata siyar ba. Sai da ta isa kusa da gidansu sannan ta fara sanɗa tana leken kofar gidan hango mota fake a bangaren da baki suke sauka ya saka ta mamaki, domin bata san an yi baki a gidan ba, kuma ba kasafai ake baki masu mota ba.
Karasawa ta yi gurin motar ta nan ta hango Ariz da ke kwance yana taba waya, Jawad kuma yana zaune yana kallonta, domin ya lura da lokacin da iso gurin motar dauke da baho akai, ta bude baki alamar mamaki ashe bakin ma a gidansu za su sauka, sai a yanzu take tambayar kanta da kuma mamakin sake ganinsu da ta yi a dandali dazun. Ta sake daga ma Jawad hannu nan ma be mayar mata ba, daman gaishe da mutane ba halinsa ba ne balle ita da take karama. Tana hango Malam Salisu ya nufo inda suke kan babur ta gudu ta boya da dayan gefen motar ta sauke bahon kanta.
Kusa da su ya faka babur dinsa ya sauka wani matashin yaro da ke bayansa ya karasa inda suke ya aje musu ledar lemun zaki, Mai Gari ya karasa ya zauna a gurin ya gaisa da su, yana fadin.
"Ba nepa garin ba zai muku dadin zama ba, sai ku da muka saba"
"Ba laifi akwai iska sosai a nan waje ai"
Ariz ya fada, Jawad kam tun da suka gaisa da Mai Garin be sake cewa komai ba daman shi ba gwanin hira ba ne, da Ariz yayi ta magana har yake fada musu ya kira Daddy dazun sun gaisa, har suka ci suka cinye Jawad be tofa komai ba, mai gari yayi musu sallama ya tashi ya shiga cikin gidan tare da babban ɗansa. Sai a lokacin Batula ta fito daga gurin da ta boya ta nufi kofar gidan ta leka sai kuma ta dawo tana jin tsoron shiga ciki.
Jawad na kallonta, Ariz da sai a lokacin ya ganta ya ce
"Me kuma take yi a nan?"
Ta sake yunkurin shiga gidan sai kuma ta dawo baya ta tsaya kana ganinta ka san a tsorace take. Ariz ya kunna haske wayarsa ya haska ta sai ta juyo a fisgice, ya haska kansa ta yadda zata ganshi yayi mata alama da ta zo. Sai ta bar kofar gidan ta iso inda suke tana yi tana kallon gidan kar wani ya fito ya ganta.
"Me kike a nan"
Ta rubuta mata cikin wayarsa ta karanta ba tare da ta karbi wayar ba, sai ta nuna kanta ta nuna gidan, alamar gidansu ne.
"To miyasa kike tsoron shiga?"
Ta masa alama da duka ta nuna kulin dake gefenta fuska a takure kamar ba ita ba.
"Idan baki siyar ba dokanki za'ayi"
Yana rubuta yana fada tun kamin ta duba wayar ta daga masa kai domin ta ji me ya ce. Jawad ya kalli kulin ya kalleta be fahimci zancen na idan bata siyar ba za a doke ta, domin a kasar da ya zauna ba a taure hakkin yara haka. Tana ganin haske fitila ta tashi da sauri ta boya a gefen motar, ta yi zaton ko wani zai fito ne kar ace an ganta gurin baki tana damunsu laifinta ya karu.
Mikewa Jawad yayi tsaye ya isa gurin motar ya saka hannunsa aljihu ya ciro key ya matsa ya bude bayan motar ya dauki bahon kulin dake kusa da inda take duke ya watsa kullin a bayan motarsa ya rufe a take hankalin Batula ya tashi sai da ta ga ya saka nufi motar ya bude driver seat ya dauko kudi ya saka mata a cikin robar sannan hankalinta ya kwanta.
A take fuskarta ta cika da murmushi sai ta duka kasa tana masa godiya kudin da ya bata har yayi yawa.
Tana ta kallonsa fuskarta da murmushi har yaje ya zauna, sannan ta mike tsaye tana jindadi, Ariz yayi mata alama da ta zo sai ta tafi ya daga lemun da mai gari ya kawo musu ya saka mata guda hudu a roban, ta bude baki tana zaro ido, tare da girgiza kai alamar aa ta saka hannu ta cire lemun a robarta ta aje a gurin, ta dauki daya ta bude gyalen dake kumkurunta ta daure lemun ta daura a jikinta sannan ta musu godiya tana murmushi ta tashi ta shiga tana tafiya tana waigensu a ranta sai mamaki take yadda suke bata kudi, da alama dai garin da suka zo akwai kudi sosai alamu ya nuna wannan dayan be san darajar kudi ba.
"Allah sarki, yarinya mai hankali irin wannan rayuwar ke lalata yaya mata, ace dan baka siyar da sana'a ba za a dokeka, kai rayuwar kauye bata yi ba"
Ariz ya fada, Jawad dai sai kallon kofar gidan yake kamar ya san za'a fito, babu jimawa kuwa sai ga Mai Garin ya fito da kansa yana rike da hannu Batula dayan hannunta kuma a fuskarta ta rufe tana kuka. Mai Garin ya karaso inda suke zaune
"Ranka ya dade kai ka siye kuli ka bata kudi mai yawa haka"
Ya tambaye Ariz ganin kamar shi ne mai sakewa yayi magana.
"Eh Jawad ne ya siya, lafiya Allah yasa ba dukanta aka yi ba?"
"Tace ku suka siya amman dai kara ana tambayawa kasan zamani yanzu, ba wuya yara sun lalace dole sai da sa'ido"
"Eh haka yana da kyau ai, amman duk da haka Malam a dan rika daga musu kafa kan talla kar ace dole sai sun siyar za su dawo gida"
"Ai ni ban ma san bata gidan da dare ba sai yanzu da ta shigo, ina! Ai da tuni na aika an nemota, yarinya ba uwa ba uba idan ba mu kula da ita ba wa zai kula da ita? Ba Eh ba Aa idan zaka kwantar da ita a nan ka yanka ba zata iya ihu a kawo mata dauki ba, kuka wannan Batula ba zata iya yi ba, wasu ma zaka ga ana jin sautinsu, idan suna kuka ko gunguni amman ita sam bata komai, ni ne nake rike da ita a karkashina ake mata komai, amman tana ji duk abun da za a fada mayawa ce bata iyawa, a haka na saka ta makaranta har ta yi wayo, haka take yawo ba talkami mun yi mun yi ta ki sauya hali"
Ya ba su labarin ne saboda su yaba ma kokarinsa.
"Allah Sarki, ashe tana ji"
Ariz ya fada cikin tausayi, Jawad kan kallonta kawai yake kamin ya kalli kafafuwanta da Malam Salisu ke haskawa, ya dora daga inda ya tsaya na yadda yake kula da ita da tarewa idan za a duketa, sannan ya musu sallama ya juya yana rike da hannunta suka koma ciki.
"Kai Allah ya baka bakin amman magana sai ka ga dama kake yi, ga wasu na nema"
Jawad be amsa zolayar da Ariz yake masa ba ya mike tsaye.
"Sai da safe"
Ya nufi motar da be rufe ba ya shiga cikin ya kwantar da kujerar. A motar Jawad ya kwana Ariz kuma ya shiga dakin bakin ya kwanta a katifar da aka ba shi, sai da dare ya fara rabawa sosai sannan Jawad ya hango mazan gari wasu duk sun fito a bakin gidansu sun yi shimfida sun kwanta, a nan kowa ya kwana har safe.
Tare da jama'ar garin suka yi Sallah Asuba, sannan suka dawo dakin a tare a nan ma Ariz bachi ya sake komawa even though ba dadin bachin yake ji ba saboda akwai banbanci wannan dakin da dakin da ya saba kwana.
Jawad kuma ya zauna yana ta lasa wayarsa har 7am ta yi sannan aka shigo musu da koko da kuma ruwan tea da madarar siyarwa sai suga da buredi da milo guda biyu sai cup, wanda aka aiko ta fada musu kosai sai zuwa anjima idan mai siyarwa ta fito za'a kawo musu.
Babu abun da suka taba ciki, abincin jiya ma babu wanda ya ci balle, tare suka fito dakin suka aika aka kira musu mai garin ya fito rike da rediyo da babbar riga sai hulla dake sanye a kansa.
"Ranku shidade kun fito ne? An tashi lahiya ya kwanan gajiya"
"Alhamdullah"
Duk suka amsa sannan Ariz ya fada masa za su kama hanya yanzu, duk yadda ta so su tsaya su karya a nan ba su yarda ba, kuma ba su karbi komai daga kyautar da yayi musu ba na kayan amfanin gona, sai dai sun masa alheri sosai sannan suka shiga motar bayan sun masa sallama.
"A fadawa Batula mun tafi"
"Tohm ranka ta dade, ta tafi rafi debo ruwa, mun gode sosai"
Ya rufe musu motar, yana fada musu dayar hanyar da zata fi musu saukin isa cikin gari. Jawad yaja suka kama hanya, ta hanyar da suka ga Batula a jiya gurin rafin nan ta gurin Jawad ya bi da ya kusa isa gurin sai ya sauke gilashin motar ya rage gudu, yana ta kallon hanyar da bi lokacin da yake neman ruwa, da ya kawo gurin sai ya tsaya ya kasa wucewa kamar yana jiran wani. Ariz ya kalleshi sannan ya kai hannu ya danna horn din motar har sau uku, Jawad ya kalleshi sai kuma ya ja motar ya cigaba da tukin a hankali. Sai da suka fara nisa sannan Batula ta iso gurin daman akwai dan tafiya kadan tsakanin koramar da kuma hanyar da motocin suke wucewa.
Ba su ganta ba, amman ita ta hango motarsu bata damu da rashin ganinta da ba su ba ta daga hannu tana musu bye bye, a ranta tana addu'ar Allah ya kaisu lafiya, domin su ne baki na uku da aka yi a gidansu suka nuna mata kulawa sosai kuma suka mata alheri mai tsoka. Ta bi motar da kallo tana murmushi har ta daina hangosu sannan ta juya ta koma inda ta bar tulunta ta lemun da take tsaka da barewa a lokacin da ta jiyo odar mota, zuciyarta ta raya mata su ne.
"Su ne ko?"
Ta dagawa Kande kai, sannan ta yi mata alama da sun tafi.
"Garin shegen shige shigenki dai wata rana sai kin hadu da masu yankan kai sun tafi dake gashi baki da baki balle ki yi ihu, har wani daukar kudi ake ana baki kina karba ke mayyar kudi"
Batula ta saki baki tana kallon kawarta Kande, kamin ta kai hannu ta karbi ragowar lemun da take mika mata.
"Na sha rabi, dauki tulunki mu tafi"
Ta bare ta ka baki sannan ta dauki tulun ta dora a kai suka kama hanya suna tafe tana sha har ta shanye kamin ta isa gida.
Sai da Jawad ya sauke Ariz a sabon gidansa da ya koma sannan ya wuce family house dinsu.