Free chapter · Read without an account

G_D - 6

by Khadeeja Candy · GUMBAR DUTSE

***

◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦

𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️

Zaku iya Karanta GUMBAR DUTSE a Wattpad & Arewabooks @KhadeejaCandy

𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 6️⃣

Sai da ta duba ko'ina ta ga babu mai ganinta sannan ta shiga dakin saukar bakin ta tsaya a cikin duhun tana jiran isowarsa, ya saba mata a duk lokacin da ta bukaci wani abu daga gareshi, ko bata bukata ba wani lokacin ya kan cilasta mata shiga a nan ta jira har sai ya zo.

Kusan tun da ta yi wayo ta mallaki hankalin kanka take cikin wannan rayuwar da mutumen da ya rike ta a matsayin uba, ya zama gatanta, ya saka mata tsoron abubuwa da yawa a zuciyarta, shiyasa ta gagara labartawa kowa damuwar dake cinta ta aje abun a zuciyarta. 

A lokacin da tunaninta yake yaudarar shekarunta ya tsorata da mutuwa da duka ne, a yanzu kuma yana  tsorata ta ta zancen lalacewar aurenta ne, da irin kallon da mutane za su mata idan aka sani, da kuma irin hukuncin da Umma Hindu zata mata idan ta san akwai wani abu tsakaninta da mijinta. Tana tsaye a dakin tana share hawaye ya shigo, sai da ya haskata da fitila sannan ya juyar fitilar kofar waje ya aje redio bakin kofar da murya kadan saboda ko da wani ya zo yayi zaton wani abu yake a cikin dakin, ya matsa da ita can kurya ya fara taba ta, tana yi tana ture hannunsa har har dai ta hakura ta kyale shi yayi abun da zai yi ya gama, ta daura zanenta ta fito tana jin zuciyarta kamar zata fashe tsabar takaici da bakinciki.

Ta san bata isa ta shiga cikin gidan ta yi kuka ba, dan haka ta gudu ta boya bayan dakunan bakin ta zauna a gurin tana ta kuka, ta saba zama a nna ta yi kuka a duk lokacin da hakan ya faru da ita, kusan gurin ya zame mata wani gurin da take jinginawa ta zubar da hawaye, idan ta gama sai ta shiga gida, sai dai wannan lokacin kukan ya zo mata a wani yanayi na dabam, saboda bata da murya kuma bata da madafa, saboda abu kadan sai ya taba jikinta, duk wahalar da take ma yi Umma Hindu bata isa ta tunkareta da wata bukata ba, sai idan sallah ce ko biki, shi kuma ba zai bata ba sai ya bukaci wani abu daga gareta.

Saurayinta ba zamauni ba, balle ta tambayi shi kuma ita bata iya tambayar yan'uwa tana son abu ba ma balle samari, idan kuma kawayenta suka yi abu ba tare da ita ba zata ji ba dadi domin sun saba tun kuryaci komai a tare suke, bata san iya lokacin da wannan abun zai dauka yana tafiya a rayuwarta ba, bata san yadda zata samarwa kanta mafita ba. Amman idan ta yi aure wata kila komai zai wuce, dole Malam Salisu ya kyale ta wannan ya saka hankalinta ya dan kwanta, ta share hawayenta ta tashi ta shiga cikin gidan, kai tsaye gurin bachinta ta nufa ta kwanta kan shimfidarta, a nan ma wasu hawayen take har bachi ya dauketa.

Sai da rana ta fara ketowa sannan aka tashe su su yi Sallah, daman Sallah azuba basa yinta a lokacin da kowa ke yi sai rana ta yi, iyyaen ma wani lokacin suka makara balle yaran da ba komai suka sani na ibada ba, aje dai makaranta ne kawai a koyi karatu qur'ane ba kowa ya damu da na ibada ba, da zarar yarinya ta sauke ganin ake ta gama komai ko da bata gama sanin komai akan ibada da addininta ba, ko da yake karatun ma a gurin wasu yake dole wasu talla kawai suka sakawa gaba. Shiyasa wasu sukan ce kauye dauda, kauye ragga, kauye rangwamen addini.

Bayan gama sallah asuba ta dauki tsintsiya ta share gidan, ita kadai ce yarinyar da idan zata yi shara take share ko'ina na tsakar gidan, sauran yara kuma sai dai kowa ya share bangaren mahaifiyarsa, mai gidan yayi fada akan hakan har ya gaji ya hakura, domin ko kadan matansa basa da hadin kai, sai bala'in kishi da ba ni na iya kawai suka iya. Bayan ta gama ta dauki tulu ta kama hanyar rafi, wayi gari jiki da zuciya babu dadi, hakan ya saka bata da walwala, sai ta zabi tafiya rafin ita kadai ta debo ruwan ba tare da ta biyawa abokan diban ruwanta ba, Kande da Basira.

Safiya ce, mutane da yawa a lokacin suke deban ruwa kowa ya ganta sai ya ce ina Basira ko Kande sai ta yi musu alama da suna gida, a maya ta biyu ne ta gadu da Kande da Basira su za su tafi rafin ita kuma ta debo ruwan a kanta.

"Hmmm Lallai Batula ashe kin zo debo ruwa baki biya mana ba, amman mu yanzu muna fito gidanku aka ce kin zo rafi"

Kande ta fada tana tabe baki, daman ita ce bata barin a kwana komai aka yi mata sai ta yi magana. Batula ta yi murmushi kadan ta mata alama da ta yi hakuri da hannu daya, sannan ta dafa Basira dake kallonta, bata sake yin kukurin wani abu ba ta wuce ta barsu a gurin. Basira da Kande suka bita da kallo.

"Lafiya take yau?"

"Waya san mata, kin san yanzu ganin take ba daya take da mu ba saboda zata yi aure"

Kande ta fada, sai Basira ta kalleta.

"Haba dai, aiko Batula bata da wannan, bata tana nuna wani abu ba tun da aka mata auren nan, kila akwai abun da aka mata, kin san Umma Hindu ba raga mata take ba"

Kande ta tabe baki.

"Hmm ke kika ganin haka, amman ni tuni na lura Batula ta canja mana Wallahi"

"Aa, bari mu hadu anjima na tambaya ba rasa abun da ke damunta ba"

Tare suka gangara rafin suka debi ruwan suka fara na su cikon. Sai da Batula ta cika kayan Umma Hindu sannan ta aje tulun, Malam Salisu ya fito da shirinsa na fita yana ta saka mata albarka.

"Yarinyar duk ta fiku kokari a gidan nan, ga tsabta yanzu daga tashinta har ta share gidan, koda yaushe acancan da ita ba kamar ku ba, shiyasa ta samu miji ta barmu"

Ya saka hannunsa aljihu ya ciro dubu daya ya mika mata.

"Ungo, je ki yi kitso da lalle"

Batula ta kalleshi sannan ta karasa ta saka hannu biyu ta karba har tana risinawa domin tarbiyarta ce haka. Ta yi masa alama da ta gode

"Tohm Allah ya miki albarka"

Ameen, din ma alama ta yi domin babu bakin amsawa. Ta koma ta zauna tana jin haushinsa kamar yadda take jin haushin kanta. Sauran yaransa suka taso suna rokon su ma ya ba su amman ya hana su sai ma rufesu da yayi da fada, Salamatu ta ce.

"Malam kana ji da Batula"

Malam Salisu dake gyara rawaninsa ya ce.

"Ai duk ta fisu hankali da natsuwa da tarbiya ne, ita gaba daya ta fita dabam"

Altine ta karba mata.

"Uhm... Agola ka fi dan masu gida, ita dai saboda bata da baki ne da Allah kadai ya san abun da zata yi"

Batula ta kallesu kawai ta maida kanta kasa, ta san ko za su tasu su tsigeta a gidan, Umma Hindu ba zata saka baki ba saboda ita ma tana jin haushin yadda Malam Salisu yake nuna mata kulawa fiye da sauran yaranta, ba shi kadai ba har mutanen waje suna fadar Batula ta fi sauran yaranta tarbiya, hakan kuma baya mata dadi saboda duk ita ta yi musu tarbiya domin a hannunta suka girma, tana ganin dai kamar Batula ta fisu iya munafurci ne.

  Har suka ci suka shude Batula bata ce komai ba, daman ina bakin maganar balle tace ace tace, ai da Malam Salisu ya fita sannan ta tashi ta zuba dumamen da Umma ta gyara yau da kanta, ta zauna ta fara ci, loba biyu ta cire hannunta ta wanke ta aje tuwon ta shiga daki ta yi ma Umma Hindu alama da kudin da Malam Salisu ya bata ta muna kafarta da kanta.

"Kitson zaki tafi?"

Ta daga kai.

"Kawo kudin"

Batula ta mika mata, sai Umma Hindu ta cire dankwalin kanta ta duba dari biyar ta mika mata ta saka dubun a cikin kudin da suke gurin sannan ta maida dankwalin akanta.

"Dari biyar ta isheki, yaushe ma kika yi kitso, ban da shegen bariki, ke komai dai so kike ace kin fi kowa, ke kishiyarki tana cikin matsala, ko mai baki bata kai ki iya kissa ba"

Batula ta saka hannu biyu ta karba idonta na cika da kwalla domin dari biyar ba zai isa ta siye lalle kuma ta biya mai lalle da mai kitso ba, kuma bata isa ta ce a kara mata ba, ta fito dakin jiki ba kwari tana rike da tsohuwar dari biyar. Salamatu da bata gani ta yi shiru ta tabe baki.

"Ba dai dubun da aka bata ba ne kika karbe rabi? Kai Allah ka ba mu wadatar zuci, kai baka bada ba kuma an bada sai ka karba? Wannan lalacewa har ina"

Daga can cikin dakin Umma Hindu ta jefo mata mata zagi ta fito kamar zane zai fadi.

"Har gidan Idi mai nama, ko zaki zo ki kwatar mata ne? Wai ko shekaranjiya Malam be shiga tsakanina da ke akan shiga lamari ba?"

Salama ta mike tsaye tana wulgar da tsintsiyar dake hannunta.

"Ba dai gidan Ubana ba Wallahi, sai fai gidan Harisu na lambu, ubana ya fi karfin ubanki balle ke, yar iska marar mutunci ni ce daidai da ke, wai kin gagari kowa ko? Tarbiyar gidan na Lambu kike nunawa shiyasa mijinki ma baki masa biyayya, ba dan zalinci ba yaushe za a dauki kudi a bawa yarinya marainiya ki karbe ki raba biyu, shiyasa nemanki baya albarka"

"Ke da nemanki yake albarka ina neman yake? Daki babu komai sai wata shegiyar katifa kudi sai dai a dunkule a abawa malamai da bokaye, wai duk saboda a mallake malam ni kuma a kore ni, ni kuwa bana koruwa a gidan nan Wallahi, idan kika ga na bar shi to malam ya mutu, ke ko mutuwa yayi ina nan daram"

"Daman ai ba tsoronshi kike ba, shi ma yana zaune da ke ne dan dole saboda yara ko jiya ya fada min ba dan yaran nan da yanzu ya sake ki"

Altine dake surfe ta daga tabarya sama ta chabe tana dariya.

"Ahehehehehheheh ayiiiiiruuuuruuui nananye"

Larai ta leko.

"Salamatu ke ce mahaukaciya mai daukan zancen namiji, ke da aka auro ata uku ba a sake ki na sai ita da aka auro kamin ke? Ke dalla ba kanki lafiya, Hindu kam zama daram a gidan nan"

Salamatu ta gwatsaleta.

" Dalla gafara can kaza marar zuciya ga haihuwa duk shekara, ke ma ai Hindu ba raga miki take ba da kike kokarin shigar mata, duk zan iya da ku Wallahi, dan na zama kujerar tsakar gida"

Kan kace kabo gidan ya hargitse da bala'i, kamin Umma Hindu ta juyo kanta.

"Kawo dari biyar din. Dan ubaki ba za ayi lallen ba, idan akwai wanda zai kwatar miki kudin sai na gani, wai ke dole sai kin janyo min magana ko? Sai kin nunawa duniya ba ni na haife ki ba? Toh ba za'ayi lallen ba su abokan naki da suke koya miki munafurci sai ki tafi su baki kudin yar iska kawai marar mutunci"

Batula taba yarda da matsa ba domin ta san babu abin da zai hana Umma Hindu ta doketa, sai ta aje gudun nan ta fita da gudu tana hawaye. Waje ta tsaya ta share hawayen sannan ta kama hanyar gidansu kawarta Basira, ta shiga gidan kanta a kasa saboda bata son aga idonta, ta shiga dakin Maman su Basira ta zauna kan wata tsohuwar kujera da ta gama lalacewa.

" Basira yi hanzari ki fito ga Batula nan ta zo, idan kika shiga bandaki sai ki zauna kamar an aika bawa garinsu"

Innarsu Basira ta fada, tana rufe Basira ta fito rike da buta tana dariya.

"Kai Inna kina tsarguwata a gaban Batula salon ta rika tsokanata kuma kin san halinta"

Inna ta yi dariya tana kara tsokanarta, Basira ta shafe hannunta jikin zanenta sannan ta shiga dakin tana dariya, ganin hawaye a idon Batula ya daga mata hankali sai ta janyo lalulen dakin ta saki ta nufi kusa da ita ta zauna.

JAWAD POV.

Vibration din da wayarsa take non stop ya saka shi bude idonsa dan dole badan bachin ya wadace shi ba. Yayi mika ya tashi zauna sannan ya kai hannu ya dauki wayar ya duba number mai kira, picking yayi ya kara a kunnensa ya amsa da muryarsa mai amo irin ta mazan mazaje.

"Hello"

"Ku dai haka kuke takama da wulakanci kala kala? Kai ayi ta kiranka ba zaka daga ba sai ka ga dama, shi kuma ko daga wayar ma baya yi"

"Me muka yi Momy"

Ya tambaya yana mitsika idonsa.

"Me ye ma baku ba? Yaron nan na yi magana da shi ya dauko ka kai da shi ku tafi gidan kawata Hajiya Zulai ku ga yaranta amman ko daga wayata baya yi"

"Be fada min ba, kuma kwana biyun nan muna ta fama da aikin Daddy ne, kin san kuma Ariz ba shi da wani dogon hutu"

"daman duk yadda zaka yi ka kare abokinka zaka yi, ra'ayinku daya ai, shiyasa ni ban ga amfanin kira ina kawo maka kararshi ba?"

"Ayi hakuri Momy zamu gyara, amman abun be kai ayi mana auren dole ba"

"Idan ba haka aka yi muku ba ai ba za ku yi hankali ba, musamman kai da nake ganin abun duniya be dame ka ba, amman ka biyewa abokinka kuna ta shirme, lokaci fa tafiya yake baya jiran kowa"

"That's right, bari na kira shi"

Ya kashe wayar yana jin kansa na son ciwon, daman shi duk wani abun da ya shafi doguwar hira ko magana baya ciki, wannan dalilin ne ya saka shi kyamar aure, domin ya san yadda mata suke, shi yadda ma zai tafi ya tsara yarinya ko ya fada mata yana kaunarta aiki ne a gurinsa, shi kan da ace yana takara da wani gurin neman aure kuma ace da kalamai za'ayi yakin, nan da nan za a cinye shi.

Iskar bakinsa ya busar ya kwanta yana rike da wayar, sai ga wani kira ya shigo masa, har yayi tunanin ko Momynce ya sake kira sai da ya duba ya ga Ariz ne.

"Malam idan zaka yi aure ka yi aure, Momy ta kira tana min fada akanka"

"Ai ko na yi aure idan kai baka yi ba, ba tsira zaka yi ba, na lura so take ta mana auren dole shiyasa na bar mata gidan ai na tare a gidana"

Jawad ya ja gudun tsaki.

"Yanzu Daddy ya gama tambayata abubuwan daka yi a kauyen nan, shi ma fada yake me yasa baka iya samunsa ka masa bayani, laifi yake ta dora min wai na ki na koya maka yadda zaka yi rika magana, ka dawo gida amman halinka be canja ba, dan Allah ka zama mutum Jawad, wasu fa suna son bakin magana amman Allah be ba su ba, kai kuma Allah ya baka amman kana wulakanci"

ARIZ POV.

Dipppp ya ji Jawad ya kashe wayar, sai yayi murmushi kuma yaja tsaki.

"Me hali be fasa halinsa, amman zaka canja wata rana dolenka"

Ya aje mug din dake hannunsa ya kai hannu ya dauki remote ya kashe laraban da watsowa a tv, sannan ya dauki jacket dinsa da car key ya sauka kasa da sassarfa sai kamshi yake zubawa, kana ganinsa ka ga matashin saurayi mai jini a jika kuma kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa. Sai da ya fara yi ma motar key sannan ya nufi gate ya bude ya fita da motar ya dawo ya rufe gate din, ya shiga motar a ransa yana raya dole ya nemo mai gadi saboda budewa da kuma rufe gate din nan. Ya koma motar sa tare da yin sama da gilashinsa ya ja motar sannan ya kai hannu ya kunna kida ya kure volume daman shi gwanin shan waka ne, duk wani abu da ya danganci nishadi yana ciki, wannan ne ya banbanta ta shi da Jawad.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol