Free chapter · Read without an account

G_D - 7

by Khadeeja Candy · GUMBAR DUTSE

***

◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦

𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️

Zaku iya Karanta GUMBAR DUTSE a Wattpad & Arewabooks @KhadeejaCandy

𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 7️⃣

Assalamu alaikum.

Fatan kowa yana lafiya.

Na san kun yi missing din Gumbar Dutse.

Na shiga rububin Exam ne kwana biyu, shiyasa na aje komai sai a yanzu da na gama hankali ya kwanta🥰

____________

"Lafiya Batula? Me ya faru?"

Ya tambaya murya kasa kasa saboda bata son mamanta ta ji, ita da Kande sun saba ganin damuwa a fuskar Batula, wani abun ko bata fada musu ba sun sani, amman ganin kukanta ba kasafai ba, sai idan Umma Hindu ta mata duka a gabansu ne tsabanin haka ita da Kande ba za su iya bada shaidar cewar Batula na zuwa gurinsu da wata damuwa tana kuka kamar yadda ta gani a yau ba.

Batula ta sauko kasa ta zauna tana kuka sosai irin kukan da ace tana da murya za a iya jinta har makota, tun tana yi da hawaye har numfashinta ya fara rawa saboda tsabar kuka, tana da damuwar abubuwa da yawa da bata san ta ina zata nemi mafitarsu ba, bata ma san ta ina zata fara fadarsu ba. Ana ganin kamar bata damu da wani abun da ake mata ba, ko an ganin kamar bata da wayo, tana jin komai saboda ita ma mutum ce. Hawayen da take ne ya saka Basira ta fara kuka ita ma ba tare da sanin dalilin kukanta ba.

"Dan Allah ki fada min me ya faru? Tun da kika zo kike ta kuka Batula? Baki taba haka ba, me aka yi miki? Ko wani ne ya mutu?"

Batula ta girgza kai, ta yi mata alama da littafi da abun rubutu, Basira ta tashi ta dauko jakarta ta makaranta da biro ta aje mata. Sai da Batula ta kama biron ta dora shi akan littafi sai kuma ta gargadin da Malam Salisu yake yawan yi mata, ta fara hararo abubuwan da yake fada mata za su faru idan ta tona masa asiri, sai ta kalli Basira ta share hawayenta ta yi girgiza mata kai tana murmushi.

"Ki rubuta mana"

Ta girgiza kai hawaye na sauko mata, alamar ba zata rubuta ba.

"Mu ukun nan kawayen juna ne Batula, idan ma baki son kowa ya sani Wallahi ba zan fada ba, Kande ma na san ba zata fada ba, yadda kika zo da damuwa haka idan baki fada min ba ai zaki saka ni a tunani ne"

Batula ta mike tsaye rike da littafin da biron ta yi ma Basira alama da ta biyo bayanta. Basira ta saka Hijab dinta ta bi bayan Batula tana fadawa Mamanta.

"Na tafi na yi rakiyar Batula"

"To ki dawo da wuri, ga surfe nan yana jiranki"

"Tohm ba zan dade ba"

Ta amsa sannan ta fice, da suka fita ne Batula ta kama hannunta ta rike wata zuciyar na raya mata karta fada wata zuciyar na fada mata ta fada ko dan ta samu mafita da sassauci a cikin ranta.

"Ina kike son muje?"

"Rafi"

Ta rubuta saboda ta san idan rana ta take babu mutane a rafin kuma gurin ne mai fadi za su iya zama su yi hirarsu babu wanda zai ji su.

" Tohm zo mu tafi gidansu Kande mu kirata"

A tare suka dauki hanya ba su karasa gidansu Kanden ba suka ci karo da ita a hanya.

"Gidanku za mu je mu kira ki"

"Me akan lallen ne? Inna na tsaya jiran ta ba ni kudin, kin san ni ba irin Batula bace da saurayinta aiko mata kawai zai yi"

Ta yi maganar da zolaya tana kallon Batula da idonta ya kumbura saboda kuka.

"Ba wannan ba, zo muje tafi"

"Mu yi me da rana haka ba kitson zamu je ba?"

"Akwai abun da yake damun Batula za mu tafi mu yi magana a can"

Tun kam su isa Kande take ta tambaya amman Batula bata fada musu komai ba sai da suka isa rafin suka samu guri suka zaune nesa da ruwa kuma nesa da hanya ta inda wani ba zai boya ya sauraresu ba.

"Me ya faru Batula? Umma Hindu ce ta yi wani abu?"

Batula ta yi shiru idonta na cika da wani hawayen sannan ta rubuta musu.

"Zaman gidan ne ya fara isata, bana jindadi gurin kowa"

Cikin damuwa Basira ta kalleta.

"Ya zaki yi wannan Umma HINDU sai hakuri, kuma ke ai Allah yayi miki arzikin samun miji Batula, kin kusa aurenki ki yi tafiyarki, ni na san In Shaa Allahu aurenki ba zai wuce shekarar nan ba"

"Yanzu dai me ya faru? Me ta yi miki?"

Kande ta tambaya, Batula ta kallesu tana jin natsuwa da aminci a tare da su, ta san ba za su fadawa kowa matsalar ba amman duk da haka sai da ta roki su rufa mata asiri a rubuce.

"Haba baki yarda da mu ba ne wai? Babu wanda zai ji, kuma waye ma be san abun da Umma Hindu take miki ba na cutarwa da nuna banbanci, ai ba sabon abu ba ne"

Cewar Basira.

"Wannan karon ba matsalar Umma Hindu ba ce kadai Basira, har da Baba"

Suka kalli juna ita da Kande bayan sun karanta abun da Batula ta rubuta musu.

"Shi ma ya bi bayanta ne ko yaya? Me yayi miki?"

Su biyun suka hada baki gurin tambaya, a nan ma sai da ta share hawayenta sannan ta rubuta musu.

"Yace idan na fada ba zai sake daukar dawainiyata ba, kuma ba zan taba aure ba, kuma kun san Umma Hindu ba zata kyale ni ba, dan Allah karku fadawa kowa"

Basira ta karata sannan ta kalleta ta daga mata.

" Babu wanda zai ji na miki alkawari"

"Na gaji da zaman gidan ne, saboda babu sanyi ta ko'ina, sai ta gurin Baba, shi ma yana daga min kafa ne saboda yana son ya rika mu'amala da ni kamar matarsa ne, yana min abubuwan da bana so"

"Innalillahi Wa'inna Ilaihirra'un, me yake miki Batula? Kar dai....?"

Kande ta tambaya bata karasa ba tana zaro ido. Batula ta ji kunya da bakinciki sun lullubeta, bata san lokacin da wani kukan ya zo mata ba. Kamin ta gama rubuta musu abun da ba zata iya fada ba takardar da jike da hawayenta.

"Kusan duk lokacin da zan tafi da bukatar wani abu a gurin Baba, shi ma sai ya bukaci wani abu daga gareni, kudin da kitson da kunshin da na tambaya jiya be ba ni ba sai da ya sai da ya taba jiki"

"Subhanallahi yaushe wannan abun ya fara Batula"

"Wallahi tun ina karama, ni dai kawai na girma na ganni a ciki, a can baya bana mantawa yana tsorata ni da wuka da kuma Umma Hindu yace duk na fada mata sai ya yanka ni ya fede kamar yadda ake yi ma rago, ita kuma Umma Hindu zata gasa ni ko ta soya saboda ba raga min take ba, ko da na fara wayo abun ya zame min kamar jiki, ko da yaushe idan ina da bukatar abu zai ce sai ya taba ni, wani kokacin ma ko ban bukaci komai ba shi yake neman taba ni"

"Amman Batula ai kina da wayo yanzu, idan a can baya kin biye yanzu za ki iya fada"

Basira ta fada tana dafata. Batula ta rubuta mata.

"Yace idan na fada babu wanda zai aure ni, kuma babu wanda zai yarda da ni, kuma Umma Hindu ba zata bar ni ba, zan zama bar kyama abar tsegumi a sa'anina, ban san ya zan yi ba, idan ina son wani abu Umma Hindu bata min, babu wanda yake min sai shi, ko dukana take shi kadai yake tare min, yau ma bayan ya ba ni kudin ta karbe bata bar min ko naira ba, kuma ni nake mata wahala, kullum nice mai cika mata kayanta da ruwa, ni ce shara ni ce talla, wani lokacin har da girki, amman bana jindadinta ko kadan, abu kadan ta rika ce min munafuka, sai duka da zagi"

Cikin kuka Basira ta karashe karanta rubutun.

"Tohm Batula ki gudu mana, ki koma gurin dangin mahaifinki"

"Idan na tafi me zan fada musu? Umma Hindu tana cutar da ni? Matar da ta rike ni tun ina karama har girma? Ai ba za su yarda ba, kuma kin san ba zan taba fadar abun da Baba yake min ba, kuma idan na gudu Umma Hindu ko Baba za su iya cewa ba za su min komai na aure ba, su ma can ban sani ba ko za su min, kuma idan na fada abun da Baba yake min ai ba zan taba aure ba, kuma bana iya magana Basira ba kowa zai so mace kamar ni ba"

Ta rubuta musu. Kande ta ce

"Matsalar ma shi wannan Musa ba zama yake a garin ba, ai da sai ya fito ku yi aure kawai"

Basira ta kwantar da  Batula dake kuka jikinta ita ma tana kukan.

"Kuma matsalar ma shi ne Mai Garin balle ace za a kai masa kara, ni kaina na kulle na rasa me zance, Batula ki yi taka tsantsan kar ya lalata miki rayuwa, Wallahi duk wanda ya ji wannan abun ba zai fahimce ki ba, kuma za ayi ta miki kallon yar iska, musamman a kauyen nan da abun gulma baya musu kadan"

Batula ta tashi zaune da sauri tana girgiza kai sannan ta dauki littafin ta rubuta

"Kun min alkawarin ba za su fadawa kowa ba, dan Allah Basira, Kande karku fadawa kowa"

"Babu wanda zai ji In Shaa Allahu, amman Batula haka abun nan zai cigaba da tafiya? Kar abun ya wuce guri ki yi ciki"

Batula ta girgiza kai da sauri tana hawaye.

"Ni ina ganin kawai ki fadawa Musa tun da shi zaki aura, hakan zai saka ya tausaya miki kuma zai yi hanzari ya shirya ayi komai a kare cikin lokaci"

Nan ma Batula ta girgiza kai da sauri, ta hade hannayenta tana rokonsu wata zuciyar na tambayar miyasa ta fada musu ma tun farko.

" Ai tun da shi ne zai aureta be kamata ya san komai ba, mu bar wannan maganar a tsakaninsu kawai mu taya ta da addu'a"

Basira ta fada, domin sam bata gamsu da shawarar da Kande ta kawo ba cewar a fadawa mijin da zai aureta ba.

"Zan daina zuwa masa da kowace bukata, balle har ya samu damar nema wani abu ni ma a gareni"

Ta mika musu takardar bayan ta rubuta. Basira ta daga kai.

" Eh haka yayi kuma ko an aika ki gurinsa karki je kawai ki rika samu hanya kina guduwa"

Ta daga kai, ba dan tana da tabbacin zata iya haka ba, domin bata isa Umma Hindu ta aike tace ba zata je ba ko kuma ta yi mata hanya hanya.

"Lallen ma zamu bari sai wani lokacin mu yi, saboda ban da kudi yanzu da sai na biya miki"

Basira ta fada, sai Kande ta kalleta cikin rashin jindadi.

"Ko kuma dai mu yi ita sai ta bari sai idan Musa zai dawo tukuna"

Batula ta sauke kai kasa tana jin babu dadi ko kadan bata son ta ga an wareta ba ayi komai a tare da ita ba.

"Aa ni dai na fasa, ke dai idan kinji zaki iya kije ayi miki, ku tashi mu tafi kar rana ta kara budewa"

Basira ta fada tana mikewa tsaye ta kade jikinta daga jar kasar da ta taba mata tufafi, Batula ma ta kade jikinta ta gangara rafin ta wanke fuskarta sannan ta dawo suka jera suka fara tafiya a tare.

JAWAD POV.

Bandaki ya shiga ya wanke fuskarsa ya wanke bakinsa sannan ya fito ya dauki tawul ya goge fuskarsa, ya nufi kofar dakin ya bude ya fita.

"Ina kwana Gwaggo"

Ya aiko mata da gaisuwa tun gabanin ya karasa saukowa Stairs din. Sai ta kalleshi bakinta cike da goro, ta kai hannu ta rage redio dake gefenta.

"Lafiya kalau, yau kuma sunan da yara suke min ka tuno? Saraki sai yanzu ka tashi"

Yayi murmushi ya kalli redio ya kalli tv dake kunne sannan ya kalli dinning.

"Kin karya?"

"Eh saboda ka dawo ai sun kawo min abinci da wuri yau"

Ya sake yin murmushi kadai, sannan ya nufi kofar fita falon.

"Bari na je na karya"

"Tohm a dawo lafiya, jikan Gwaggo"

Ya fice yana taba wuyansa da yake jin kamar yana son masa ciwo. Sai da ya fita daga bamgaren mahaifiyarsa gaba daya yayi yar tafiya sanna ya isa bangaren Hajja Yelwa. Tura kofar falon yayi ya shiga, be saba sallama ba dan haka be yi ba kai tsaye ya nufi dinning area domin yin abun da ya kawo shi. Tsaye ya samu Hajja Yelwa dankwalinta a kafada dayan hannunta a kanta tana tsosawa a hankali, bakinta kunshe da murmushin da ya bayyan a hakoranta biyu na makka.

"My Son, an shigo"

"Ina kwana"

"lafiya kalau"

Ta amsa sannan ta ja masa kujera a kusa da Ayla.

"Yanzu nake cewa Ayla zan shiga bangaren na duba ko lafiya har yanzu baka shigo ka karya ba, yaran duk fita babu kowa a gidan"

Murmushi kawai yayi domin baya son dogon zancen, shi ma kuma dan kar tace be amsa mata ba ne. Ayla ta dube shi.

"Ina kwana"

Ya daga kai ba tare da ya kalleta ba, sannan ya zauna a kujerar dake facing din wanda Hajja Yelwa ta ja masa. Ya kai hannunsa ya bude warmers din yana duba me da me aka shirya musu as breakfast. Sanin Jawad ya tsani gashi ya saka Hajja Yelwa ta cire dankwalin daga kafadarta ta daura a kanta, ta zauna a kujerar da so ya zaune be mata hakan ba.

Ayla ta mike tsaye ta zari tissue tana goge bakinta.

"Har kin koshi?"

"Eh yau da wuri nake son tafiya bana son na yi latti"

"Tohm Allah ya tsare, aikin na ku ne sai ku, wanda zai auri irinku ma sai yayi hakuri"

Ayla ta yi murmushi.

"Kai Adda Yelwa, toh daman auren Nurse ai sai mai tsananin rabo, kuma ni na fi sha'awar auren mai irin aiki kin ga mun huta ba complain"

"Ayla nan zaki bar plates din? Kina kallo dai yau babu kowa a gidan nan sai ni, ni zan kai miki plates din gurin wankewa?"

Ta yamusa fuska.

"Adda Yelwa gaskiya, ya kamata a dauko mana mai aiki, dan kai plate din nan dan wanke wanke goge goge sai ta rage mana mu huta"

"Na ji, ni ma ai na fiku bukatar mai aikin, kamin mu same ta ai sai ki dauke wannan ko"

Haka ta dauke plate din ba dan ranta ya so ba. Ta nufi kitchen ta aje ta fito, Hajja Yelwa ta yi murmushi tana binta da kallo har ta bar gurin, sannan ta maida dubanta durin Jawad da ko kallon inda suke be yi ba cin abincinsa kawai yake.

"Ya gajiyar jiya? Alhaji ya sakaku abun da ba ku saba ba, ai Dawood ya ce dama shi Alhaji ya saka domin shi irin abubuwan nan suna burge shi, kuma shi ne ba shi da wata rikakkiyar sana'a ko aiki a yanzu, kai kuma ai ba ma tsarinka ba ne, domin baka saba da irin wannan wahalar ba, kuma tsarin abin da ka koya be hada hanya da gurin ba"

Jawad be dago ba balle ya furta wani abu, daman kuma ta san halin ɗan nata ba son magana yake ba, sai a amsa magana goma be maida daya ba, ba dan kuma be ji ba sai dan maganar tana masa wahala. Ta yi shiru na san lokaci sai kuma ya murza hannayenta kamar mai shafa ma.

"My Son, daman ina son na sake maka magana akan Gwaggo, kasan zaman tare sai hakuri musamman da tsofaffi, wani lokacin duk yadda kake kokarin kyautata musu kake son a zauna lafiya, sai ka ga ba shi suke hangowa ba, ni dai ina iya bakin kokarina gurin kyautata mata, domin ita uwa ce a gurina, ko ba dan komai ba, Gwaggo ta isa haihuwata balle kuma da alaka, yana daga cikin dalilin da ya saka a duk lokacin da tace zata koma gida nake hanawa ina ganinta a nan ai muna jin sanyi, gashi yar Daughter ma zuwa take gidanta kamin ta shigo nan sai ta fara shiga can, idan babu ita gidan ai ba zai yi dadi ba, dawowarka ta yi min dadi, saboda na san ba zaka bari Gwaggo ta bar gidan nan ba, zaka taya ni wannan yakin, amman dan Allah ka rika lusar da ita wasu abubuwan, zo mu zauna zo mu saba ne dole ana yin ba daidai ba, musamman ma yaran nan da ba son aiki suke ba, shiyasa nake ta fafutukar neman mai aiki wasu abubuwa za su mana sauki"

Nan ma dai be ce komai ba sai cin abincinsa yake, Hajja Yelwa kuma bata fasa fada masa yadda zai rarrashi Kakarsa.

"Kai kanka sai ka yi hakuri, kasan tsofin nan sai an kai zuciya nesa"

Ya aje fork din hannunsa ya zari tissue ya goge bakinsa.

"Akwai abun da kake bukata a dafa maka da rana nan? Tuwo zan girka musu yau na san kai kuma ba son tuwo kake ba, me kake son ka ci?"

"Zan ci abinci a waje"

Ya mike tsaye.

"Aa ni fa bana son kana cin abinci a waje, sam ba zan lamunci wannan ba, ko aure ka yi matarka ta kasa girka maka abinci ka zo gidanku ka ci amman ban da cin abinci a waje ba zan yarda da wannan ba"

Ya dan yi shiru for few seconds.

"Fruit salad with pepper chicken"

"Yauwa dan albarka, zan girka maka da yardar Allah, ita dai Gwaggo na san daman tana son tuwo musamman miyar kuka, saboda ita zan yi miyar"

Ya fice dinning din ba tare da yace komai ba, Hajja Yelwa ta kashe ido tana binsa da kallo zuciyarta na kuna.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol