Free chapter · Read without an account

G_D - 15

by Khadeeja Candy · GUMBAR DUTSE

***

◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦

𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️

Turaren wuta kike nema? Ko kuma na jiki? Humra kike nufi ko kambasa spray? Ke na tuna turaren set kike so? Ko kuma dai ke zaki zaba da kanki? Au oil perfume wai? Ke ni kamshin turaren ya rikita ni, bana fahimta wane kuke so daga ciki, iyakar abun da zan iya shaida shi ne, kamshi mai kwantar da zuciya da sanyaya ruhi, ya kwantar da hankali. Ya Salam🤦🏻‍♀️kina son kamshi baki nemi yar fillo Collections ba? To me kika yi? 😳 Haba ai da sauranki shiyasa na ji dan tsami tsami🫢

Tana da turaruka kala kala, iri iri, masu kamshi da tashin kai, ga sauki ga mutuntuka, karku bari wannan damar ta wuce ku, chat her ***

𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 1️⃣5️⃣

"Babu inda zan je zaman yayana zan yi"

Malam Salisu ya nuna ta hannunsa.

"Zaman yaya na me? Na jefar da yayan nawa ne? Ko kuma na bar miki ragamarsu ne? Ni zan rike yayana yaro ko ɗaya ba zaki tafi da shu ba"

"Wannan abun be yi dadi ba, sam baka yi tunani ba Malam, idan Batula ta aikata abu sai ka hukuntata amman miye laifin Hindu a ciki?"

Cewar Inna. Larai ta kebe baki.

"Ke Inna yanzu ai duk wannan ya kau, tun da aure ya kare ai babu sauran zance"

Umma Hindu ta nufi Larai cike da masifa tana son kai mata duka.

"Uban waye ya sako bakinki a ciki, tsohuwar munafuka, har baya ga dangi, ai ke baki zo ba sai da komai na malam ya kare, kuma ina tafi arziki zai bar gidan nan domin ni na zo da abuna"

Har ta bude baki zata yi magana Malam SALISU ya daga mata hannu alamar ta yi shiru, sannan ya dubi Inna ya ce

"Dan Allah ki sakata gaba ki tafi da ita, bana son wata rigima ko tashin hankali"

"Tohmm Salisu yanxu abu har ya kai haka? Ka sake ni ba ba zaka bar ni na tafi da kafata har kana fadar Yayata ta saka ni gaba, sai kace wata annoba? Karka manta akwai yaya a tsakaninmu, kuma ni na rufa maka asiri ka samu abun da ka samu yau"

Taja huci ta sauke.

"Ba gidan ka, garin nan ma yau ba zan kwana ba, daman aure ya kawo ni kuma aure ya kare, sai na nuna maka ni yar halak ce"

Ta shiga dakin ta fara hada kayanta, yaranta nata kuka wasu na zagin Batula harda yi mata Allah ya isa. Tufafinta kawai ta hada dman sauran kayan sai daga baya a dawo a dauka wasu kuma sai dai ta bar ba yara.

Musa da kawunsa suka fice rai babu dadi, Inna kuma ta shiga dakin gurin taya Umma Hindu hada kayanta.

"Za zo ki hado kayanki ko kuma sai ni zan hado miki? Shegiya hasararriya, haihuwar jaraba, daman ke baki taba zuwa da alheri ba, tun da kike hannuna har yau ban taba cin amfaninki ba sai hasara da nake yi, yau dai kin yi nasarar kashe min aure, kin saka makiya na farinciki da dariya ai sai ki zuba ruwa kasa ki sha"

Batula ta dago jikinta daga na Basira, ta rarrafa saboda bata kuzarin mikewa tsaye, tana isa bakin kofar dakin Ramatu da lawusa yayan Umma Hindu suka rufe Batula da duka, Inna ma ta kama musu, kan kace me bakinta da fuskarta sun kumbura, Basira ma da ta shiga domin raba fadan aka hada har da ita suka yi ta duka. Duka suka mata sosai saboda babu wanda zai tare mata, babu wanda zai ce su bari, matan gidan daman ba cetonta suke ba idan Umma Hindu na dukanta balle kuma yanzu da kowa yake mata kallon mai laifi.

Lawusa ta kwaso jakar Bango ta jefowa Batula.

"Ga kayanki nan kar ma ki shigo dakin nan tun da ba na Ubanki ba ne, saboda Umma ba ita ta haife ki ba shiyasa kika mata haka ko? Baba ma haka saboda kina ganin ba Ubanki ba ne ko?"

Umma Hindu ta nufi kayan ta dauko ta wulgasu cikin ɗakinta.

"Ke ba zata dauki komai ba ma, ai duk abun da zata dauka a gidan nan ta same shi kuma saboda ni, toh Wallahi ba zata tafi da komai ba, tashi mu tafi munafuka"

Inna ta ce.

"Hindu da hakuri kika yi sai gobe, yamma ta yi yanzu, sai ki tafi ido na ganin ido"

"A'a wallahi yau zan bar garin nan, ai kara yanzu, ke kika ganin zan iya kwana na tashi da abun kunya?"

Daker Batula ta iya mikewa tsaye ta jingina da ginin kofar dakin tana kokarin tsada hawayen da basu shiryawa hakan ba a yanzu, Basira ta matsa kusa da ita.

"Bari na je na yi magana da Innarmu idan ta yarda sai ki zauna a gidanmu, Wallahi idan kika bita wuya zaki sha da wulakanci"

Ita dai Batula bata iya cewa komai ba, sai sharar hawaye take, da ta ji kafufuwanta kamar ba za su dauketa ba sai ta tsuguna kasa tana ta kallon gidan da mutanen cikinta, yanzu barin gidan zata yi, zata bar garin gaba daya, kawayenta masoyinta yan'uwa da mutanen da ta sani duk zata bar su ta koma wani garin da bata saba ba, ta koma cikin wasu mutanen da bata saba mu'amala da su ba, zata koma inda kowa zai mata kallon yar iska kuma yar kashin aure, tsanar da Umma Hindu take mata zata karu yanzu, duk akan laifin da bata aikata ba...

"Zaki tashi mu kama hanya ko sai na ci ubanki"

Ta zabura tana dawowa daga duniyar tunanin data tafi ta daga kai ta kalli Umma Hindu, ta mike tsaye ta juya ta kalli dakin Umma Hindu gefen inda take kwana, sannan ta kalli tufafinta da aka jefar a cikin dakin, bata gama bawa idanuwanta abinci ba, Inna ta kama hannunta da karfi ta janyota kamar wata marar galihu suka nufi kofar fita, Umma Hindu sai bace bace take tana son ta samu mai cewa wani abu a cikin matan gidan, sai dai bata samu hakan ba domin Malam Salisu ya gargadesu kamin ya fita, kuma suna jin maganar, tsabanin ita da ko yace kar a aikata abu sai ta aikata sai dai a mutu.

Da suka fito waje gidan ne, makota suka fara lekowa suna kallonta, wadanda take aminta da su kuma suka fito a guje ana jaje, sai a lokacin da fashe da kukan bakinciki tana jin kewar gidan da mutanen garin da bata bari ba, kaso mai yawa daga kawaye da mutanen arziki da suke tayata jaje suna ta tsinewa Batula albarka da Allah wadai, kadan ne kawai ba su dora mata laifi ba. Haka Umma Hindu ta fito unguwar tana kuka mutanenta ma suna kuka, babu yadda ba'ayi ba ta kwana garin amman ta nace akan ba zata kwana, daman haka take idan ta kafe a abu babu wanda ya isa ta canja ra'ayinta, wannan ma yana daga cikin abun da yake batawa Malam Salisu rai a zamantakewarsu.

Achaba daya suka hau, ita da Batula da babu mayafi a tare da ita balle talkamin da bata saba sakawa ba, a gurin mutanen karkara, hawan achaba mutum biyu ba wani abu bane balle kuma Umma Hindu da fitar da kudi ba abu mai sauki ba ne a gareta, musamman yau da take cikin bakinciki da bacin rai.

Suna kan Achaba Umma Hindu na labartawa mai Achaɓan abun da ya faru, a yanayin yadda yake amsa mata ya nuna be yarda da abun da ake ta fada ba, domin shi ma ya ji labari ne bayan ya dawo daga gurin kasuwancinsa. Sai maimaita yake adai yi bincike, abu ne da yake a bayyana ga mutanen garin kusan kowa ya san halin kowa, daman haka rayuwar karkara take shiyasa ko bako ya shigo sai anji labari ko kuma an gane ba dan garin ba ne kusan kowa ya san kowa.

Kamin ya kai tashar da zai saukesu, su samu motar kauyen Sabau, Umma Hindu ta bukaci ya saukesu a hanya.

"A nan Kuma? Ku zaku fasa ne? Domin dai gaskiya abu ne mai wahala a samu motar Sabau a yanxu, saboda yamma ta yi sosai, sai idan wani mai chaba za ku samu ya kai ku, su kuma tsada suke mota ta fi arha"

"Eh shiyasa ai na sauka a nan, achaba zan hau ba sai na isa cikin tasha ba"

Ta amsa masa, sai ya sauka gefen titin mai cike da turbaya, suka sauka Umma Hindu ta dauko kudi ta mika masa sai ya girgiza kai.

"Aa ba zan karba ba, Allah dai ya kaiku lafiya ya sawwake, Batula Allah yayi miki mafita"

Ya tsaya da nufin tsada musu mai achaba da zai dauke su, nan ma Umma Hindu ta hana shi ta yi masa godiya, sai yayi musu sallama ya juya ya koma unguwar da ya fito, sai da ya yi nisa ya bace musu da gani sannan Umma Hindu ta dubi Batula cike da mugun bakinciki da takaici.

"Ba zaki min bakinciki ba, kuma na daɗaɗa miki, yadda kika kunsa min bakinciki haka zan dama miki shi kuma dole ki shanye, ba zan biya miki kudin abun hawa ba zuwa Sabau, ko dai ki koma can gurin yan iskan samarinki su baki kudin achaba ko kuma ki kama hanyar garin tun yanzu kamin dare yayi miki, dan Allah ba zan biya miki kudin mota ba, shawara ta rage ga mai shiga rijiya"

Batula ta daga kai ta kalli Umma Hindu tana jin zuciyarta kamar zata rabe gida biyu, sai kuma ta sauke kanta kasa, daga Rorau inda suke zuwa kauyen Sabau tafiya ce mai nisa ta awa biyu akan abun hawa, idan tace zata tafi yaushe zata isa? Gashi yamma ta yi? Kamar yadda ba zata iya komawa cikin garin ta roki kudin abun hawa ba, idan ma ta koma gurin waye zata taje ta tambaya? Wa zai kula ta?

Tsoron tafiya ita kadai a garin da bata gama sanin hanyarsa a kafa ba ya saka ta riko hijabin Umma Hindu ta girgiza mata, tana rokon kar ta tafi ta barta.

"Ai wallahi komai zaki yi ba zan tafi da ke ba, kinji ma na rantse"

Ta buge mata hannu ta cigaba da tafiyarta. A halin da Batula take a yanzu bata saka ran wani zai yarda ya taimaka mata, sai wanda be san me ya faru ba, ba dan komai ba sai dan gudu ace suna tare, ita kanta bata shirya karbar taimakon kowa ba, kar ayi amfani da hakan ace daman halinta wanda ya kaita ga halaka. Amman ya zata yi? Ta kama hanyar garin da ta san idan ta yi nisa sai ta sake tambayar ina zata bi? Garin iyaye da kakanninta ne, sai dai bata saba tafiya garin a kafa ba, gashi idan ta bata bata babu bakin tambaya ko yi ma kowa bayani, tun da be zama lallai ace kowa ya isa tsaya ta rubuta masa bukatarta a masa ba, waya sani ko wadanda zata hadu da su ba su iya ma karatun ba.

Bata gama tunanin mafita ba, zuciyarta ta yanke mata shawarar tafiya, a haka idan wani abun ya same ta a hanya, bata ki ba ko da kuwa mutuwa ce, a halin yanzu kam ta gaji da rayuwa, gashi kuma bata yi mafarkin hango farinciki nan kusa ba.

Tana tafe tana tuntube, saboda hankalinta baya jikinta tunanin na neman zauta duniyarta, ashe Umma Hindu zata iya mata hakan? Ko da ace da gaske ta aikata anya ta cancanci danyen hukunci da kyama ga wulakanci a gurin mutanen da take ganin kamar ba za su iya juya mata baya ba? Laifin zina ya kai a kasa yi mata uzuri, tsayawa bincike a gano gaskiya? Hakan yana nufin bata da gata ga kowa kenan?

Yanzu idan ma ta tafi can wane irin hukuncin zata fuskanta? Su din za su biyewa mutane ne ko kuma za su fahimce ta?

Idanuwanta suka cika da zafafan hawaye masu zafi, bata taba yi ma kanta sha'awar mutuwa ba sai a yau, kamar yadda bata taba tsanar kanta ba sai a yau. Tana tafe tana share hawaye, kowa ya ganta ya san ba lafiya ba, ga fuska a kumbure ga hawayen dake ta zubo mata tana sharewa, wasu su tambaye ta lafiya take kuka wasu kuma ido ne na su, ita dai bata amsawa kowa ciki har da wanda ya rike hannunta yana son jin ba'asi sai ta janye ta cigaba da tafiyarta bata bawa kowa amsa ba.

Abu ne sabo a gurinta, tafiya garin Sabau a kafa, mutane suka je wasu saboda makon biyan kudin abun hawa wasu kuma saboda sabo, domin an san mutanen karkara ta tafiya a kafa matukar ba garin da ya ke da nisa ba ne sosai, har ta fara tunanin ko dai ta hau abun hawa idan ta isa ta karbi kudin gurin yan'uwan mahaifiyarta da suke can? To kuma idan ta tarar da Umma Hindu ta bata a gurinsu fa? Bakar kaza idan ta riga kowa shiga akurki bata barin kowa ya shiga, Inji hausa.

Tana tafe gajiya na kara sauko mata, zazzabi na rufeta, ga zuciyarta na mata nauyi, kanta kamar zai fashe, ta raba hanya ta fara tafiya ana ta kiraye kirayen sallah magariba, da ta gaji da tafiyar sai ta raba gefen hanyar cikin kasa ta zauna ta saitin da take iya hangen inda ta fito sai kuka ya zame mata sabo ya zame mata sabo saboda bakinciki barin garin da a cikinsa ta girma a cikinsa take komai nata...

Ta kwanta a gurin tana jin wani irin kishin ruwa, makoshinta ya bushe, gaba daya ta rasa ina zata saka kanta, ta rasa me zata yi, idan ta ce zata tafi garin a kafa ma ba zata iya ba, idan kuma ta koma cikin garin Rorau gurin wa zata koma.? Da zaman ya gagara mata dadi ne ta kwanta a gurin tana jin wani bachin wahala yana kokarin sace ta, ita da shi suka yi ta kokawa har yayi nasara akanta..

Can cikin bachin ta ji an tallafota sai ta farka ta tashi zaune, da ta duba sai ta ganta cikin wani gida na kasa, ga wata mata a kusa da ita tana ta kallonta, ga kofin ruwa na silver a gefen matar, Matar da Batula bata waye ta ba, ta dauko kofin dake cike da ruwa ta kara matsawa kusa da Batula ta ta kai mata kofin a baki, Batula ta fara shan ruwa mai sanyi jikinta har rawa yake saboda kishin da take ji, sai da ra sanye ruwan gaba daya, sannan matar ta aje kofin ta saka hannayenta biyu ta tallafi fuskar Batula tana share mata hawayen da sai a lokacin ta san da wanzuwarsu.

Ta share mata hawayen tana ta kallonta fuskarta cike da tausayawa, can kuma ta sake ta, ta mike tsaye sai Batula ta yi hanzari riko zanenta, matar ta juyo ta sake duba Batula.

"Wacece ke?"

For the first time ta ji ta iya furta haka. Ta ti hanzarin kai hannu ta taba makoshinta, Matar bata ce mata komai ba ta juya zata cigaba da tafiya sai Batula ta sake yunkurin magana.

"Wacece ke? Ban gane ki ba, ban san ki ba"

Ta furta tana kallon kamanin matar da suka yi kama da ita sosai, banbanci kawai matar ita babban mace ce Batula kuma yarinya ce. Anan ma bata ce mata komai ba ta nufi hanyar fita daga gidan ta fice Batula nata kallonta...

Firgigit ta farko daga nauyayyen bachin da ya dauke ta, da sauri ta taba bakinta ta taba makoshinta, sai ta yi yunkurin yin magana amman ta kasa muryarta ta ki ta fita, a nan ta gane mafarki ne ta yi ba zahiri ba ne, amman wacece matar da ta gani? Bata taba ganin mahaifiyarta domin ko da ta yi wayo bata yi shi da uwa ko uba ba, to wacece wannan domin ta yi kama da wasu daga cikin dangin mahaifiyarta, kuma ta yi kama da ita, sai dai bata taba saninta ba.

Daga farkawarta bachin da tunani ta ji wani abu sabo a yau da bata taba jin irinsa ba, ta tsinci kanta a cikin wani yanayi na kewa, kewar uwa, asalin uwa mahaifiya, wanda sabon abu ne yau a gurinta, ta bata fuska sosai hawaye na sauko mata...

©️ Khadeeja Candy ✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.