Free chapter · Read without an account
Chapter 8
by Amanarcool · SAUTIN KARSHE
Ko da Ma'u ta dawo daga makaranta a tsakar gida ta tarar da Halima riƙe da buta ta fito daga banɗaki, tsayuwa ta yi tana kallonta kafin ta ce "Aunty Halima lafiya dai na gan ki a haka kamar wadda ba ta da lafiya?" .
Halima ta ce "Ba na jin daɗi ne Ma'u".
Cikin damuwa ta ce "Ashsha subhanallah! Ubangiji Allah ya ba ki lafiya ya sa kaffara ne, sannu Aunty, bari na je ɗaki na canza kaya sai na zo na ɗora mana girki". Halima ta kalle tana murmushi, saboda ta lura yau masu mutuncin ne a kusa, wani lokacin Ma'u na da nutsuwa da sanin ya kamata, sai dai duk lokacin da ƴan balaja'u suke saman kanta za ta aikata abin da ko ɗan shekaru goma ba zai aikata ba, ta ce "Ai na yi girki tun ɗazu na kammala".
Ma'u ta ce "Duk da ba ki da lafiyar? To shikenan" daga haka ta shiga ɗakin Inna, Halima kuma ta wuce na ta ɗakin. Kasancewar tana fashin sallah ne ya sa tana cire uniform ɗinta, ta zuba abinci ta ci, tana kammala cin abincin ta kwanta saboda wani irin bacci da take ji, har ta kwanta ta ɗaga kai ta kalli tsohon agogon bangon dake cikin ɗakin, 2:37, ta ce "Kai lokaci ya tafi har haka? Ko da na so in yi bacci sosai ashe lokacin zuwa islamiyya ya yi? To duk da haka gaskiya sai na yi baccin nan". Daga haka ɓingire ta fara bacci.
****
"Mammy"
"Na'am Zahran Mammy".
"Mammy don Allah ki saka baki Yaya Sudais ya auri Aunty Ilham, wallahi tana matuƙar sonsa, ki duba duk da sharenta da yake yi ba ƙaramin so take yi masa ba, ɗazu ta kira ni tana kuka wai za'a haɗa ta aure da ɗan abokin Uncle, ba ƙara min tausayi ta bani ba. Please Mammy ki yi wani abin mana, ai ke ce mahaifiyarsa kin isa ki tursasashi ya yi abin da kike so".
Mammy ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ni kaina Ilham na bani tausayi Zahra, Sudais ɗin ne na rasa yadda zan yi da shi, ko jiya sai da na yi masa zancen nan amma fafur ya ƙi".
"Haba Mammy, ki takura masa mana, wallahi ba ki ji kukan da take yi ɗazu ba, kamar ranta zai fita".
Mammy ta ce "Kashh, Zahra ai ba'a yi wa namiji dole wajen auren mace. Duk da na san idan na yi masa dole ɗin zai amince, amma ina duba makomar auren ne, ya zamansu zai kasance? Kar aje can Ilham ta kasa samun farin ciki a gurinsa, kin san halin Yayan naki da baƙar kafiya". Shiru Zahra ta yi ta zuba mata ido.
"Lafiya kike kallona?".
"To Mammy me zan yi in ban kalle ki ba? Ni gabaɗaya a cikin damuwa nake, haddai dana ji za'a haɗa ta aure da wani".
"Kina ta zancen za'a haɗa ta aure da wani, to ai ni ban san da zancen ba, Uncle ɗinku bai sanar dani ba, kuma ba na tunanin su Sudais ma sun san da zancen".
Zahra ta ce "Mammy Yaya Sudais ya sani, Aunty Ilham ta sanar da shi". "To shikenan koma dai ya ne, sai na ji daga bakin Ulcer tukuna zan yarda".
"Allah Sarki Aunty Ilham". Zahra ta faɗa tana yin tagumi, Mammy dai ba ta sake kula ta ba ta ci gaba da sabgogenta.
****
Ƙarfe huɗu da rabi Sudais ya fito daga office ɗinsa, bayan ya shiga motarsa yana ƙoƙarin kunna ta ne ya ji kira ya shigo wayarsa, duba wa ya yi ya ga Alhaji Sardauna ne, cikin natsuwa ya ɗaga kiran ta yi da yin sallama, can cikin wayar Sardauna ya amsa yana faɗin "Alhaji Adam, ina fatan dai ban takura maka ba?".
Sudais ya ce "A'a babu komai kar ka damu".
Sardauna ya ce "Ma sha Allah, da ma na kira ka ne in yi maka godiya, na ji daɗin yadda ka karɓi mutanen dana kawo maka hannu bibbiyu, Allah ya taimaka ya baku Sa'a a kan dukkan abin da kuka saka a gaba. Sai dai kuma akwai wani jan hankali da zan yi maka. Duk da cewar na san mutanen basu da matsalar komai, domin na daɗe ina hulɗa da su ban taɓa kama su da wani abu na ha'ince ba ko cin amana, amma ina son ka da ka yi saurin sakin jiki da su, kasan halin rayuwa, ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, ka bari har ka ga kamun ludayinsu". Sudais ya jinjina kai kamar yana gabansa ya ce "To shikenan, ina godiya sosai da kulawa, in sha Allah zan kiyaye, nagode Allah ya ƙara girma". Sardauna ya amsa da "Amin" yana faɗin "Ina yi muku fatan alkhairi"
"Muna godiya sosai" Sudais ya ce tare da yi masa sallama ya ajiye wayar, tada motar ya yi ya bar kamfanin gabaɗaya.
****
Ko da Ma'u ta tashi daga bacci idonta ne ya sauka a kan agogon ɗakin, waro ido ta yi ganin ƙarfe biyar. Da sauri ta dafe ƙirji tana faɗin "Na shiga uku ni Ma'u, Allah ya sa Yaya bai dawo ba". Da sauri ta fita waje domin ta tambayi Halima, sai dai tana fita ta ga Aliyu zaune a tsakar gidan zaune a kan tabarma yana cin abinci, Halima na zaune a gefensa, juyawa ta yi za ta koma ciki ta ji ya ce "Ke". Cikinta ne ya yi wani irin ƙugi, ta juya tana kallonsa cikin sanyi murya ta ce "Na'am Yaya?".
"Me kike yi a ɗaki tun ɗazu? Kalli gidan nan yadda ya yi datti, kin san ita ba ta jin daɗi me ya sa ba ki gyara shi ba?". Ajiyar zuciya ta sauke, saboda ta yi zaton zai yi mata magana ne akan rashin zuwanta islamiyya, ta ce "Na ɗan kwanta ne shi ne bacci ya ɗauke ni, da yake nima bana jin daɗi, amma yanzu zan gyara". Bai sake bi ta kanta ba, yana gama cin abincinsa ya tashi zai fita, Jamila ce ta shigo gidan da sallamarta, Ma'u ta amsa tana binta da kallo, cikin lanƙwashe murya Jamila ta gaishe da Aliyu, amsa mata ya yi ba tare da ya kalle ta ba ya bar gidan. Yana fita Ma'u ta tuntsure da dariya tana faɗin "Shegiya Jamila, amma wallahi ba ki da kirki, yanzu a gaban matarsa kike lanƙwashe masa murya haka?". Jamila ba ta kula Ma'u ba ta mayar da kallonta ga Halima da ta yi shiru tana kallonsu, ta ce "Aunty Halima ina yini, ya gida? Ashe kuma Abida ba ta da lafiya? Ubangiji Allah ya ba ta lafiya". Ta yi maganar a jere, murmushin yaƙe Halima ta yi ta ce "Lafiya ƙalau Alhamdulillah, Amin ya hayyu ya ƙayyum".
"Kuma kika amsa mata Aunty? Mijinki fa take son aura kuma kin sani? Taf ai wallahi da ni ce tuni na haɗa mata jini da majina".
Dariya Halima ta yi ta ce "Ai babu komai, ta zo mu zauna, tunda ba a kaina za ta zauna ba, kuma kowa da halinsa ake zama da shi, sannan kuma kin ga ai ƙawarki ce".
Ma'u ta ce "Anya kina son Yayana kuwa? Ke yanzu ko irin ɗan kishin nan da ake ji ba ki ji ba? To ai shikenan ba damuwa, ƙawata ke kam Allah ya yi dake, sai ki yi ƙoƙarin janyo hankalinsa zuwa gare ki don kin san Yayan nawa mai capacity ne". Ta yi maganar tana jan hannun Jamila suka shiga ɗaki. Halima ji ta yi wani abu mai zafi ya tokare mata a ƙirji, runtse idonta ta yi tana ambaton sunan Allah. Da ƙyar ta ji abin ya lafa mata a hankali ta tashi ta shige ɗakinta.
"Ma'u ni za ki dizga a gaban kishiyata?" Jamila ta yi maganar tana ɗaure fuska don ba ƙara min haushi Ma'un ta ba ta ba.
Kallonta Ma'u ta yi, ta sake tuntsurewa da dariya ta ce "Amma Jamila akwai ki da ƙarfin hali, wato har ta zama kishiyarki kenan? Nifa kin san babu ruwana gaskiya nake faɗa, komai mutum zai ji ba ruwana, idan na tashi yin maganata".
"To amma sai ki tozarta ni a gabanta? Yanzu matar nan in da masifaffiya ce ta ce za ta dake ni kenan ba za ki tare mini ba?".
Ma'u ta ce "A'a Jamila ƙarya haram, a kan me zan tare miki? Bayan ke kika zo har gidanta kina yi wa mijinta ƴar murya. Ai naɗe hannayena zan yi in koma gefe ina kwasar dariya". Takwaici ne ya ƙule Jamila, wani irin kishin Halima ta riƙa ji a ranta, zuwan da ta yi da niyar su je duba jikin Abida ne, amma kishin da take ji ya sa ta ji ba za ta iya zuwa ba, ba ta wani daɗe a gidan ba ta tafi saboda ba ƙaramin ƙular da ita Ma'u ta yi ba. Duk yadda kake da Ma'u matuƙar taga kana son mijin wata to ka shiga uku a gurinta.
*****
Bayan kwana biyar da yi wa Abida aiki, Alhamdulillah an fara ganin sauƙi sosai a gurinta, domin kuwa yanzu har hira ake yi da ita. Masu zuwa dubiya na ta sintirin zuwa ciki hadda Jamila. Duk ɗan uwan da ya zo sai Inna ta bashi labarin taimakon da aka yi musu a asibitin, nan jama'a suka ƙara yaba aikin alkhairin da ake gudanarwa a asibitin. Wani ɗan uwan Inna da take bashi labari ya ce "Ai wannan asibitin ba tun yanzu take irin wannan taimakon ba, an daɗe ana yinsa, kusan shekaru ashirin da suka wuce, lokacin ma ba ta bunƙasa kamar haka ba" Inna ta ce "Allah Sarki, wannan bawan Allah, Allah ne zai biya su". Ya ce "Haka ne, a cikin masu kuɗinmu da ana samun masu taimako kamar su Alhaji Sardauna ai da an ji sauƙin abubuwa da yawa, bayan fa wannan asibitin hadda gidan marayu ya buɗe domin tallafawa marayu da marasa galihu".
Inna ta ce "Bawan Allah, Allah ya biya shi da gidan aljanna, ni na daɗe ina jin labarinsa amma ban taɓa tunanin haka abin yake ba". Nan ɗan uwanta ya shiga zayyano mata irin taimakon da Alhaji Sardauna yake yi wa al'umma, ba tun yanzu ba. Inna sai addu'a take yi masa da fatan alkhairi.
****
Sudais ne zaune tare da lauyoyinsa da wasu daga cikin ma'aikatan kamfaninsa. Sai Alhaji Hali, da Alhaji Badaru, bayan sun gama gaisawa, cikin nutsuwa Alhaji Hali ya fara magana "Ba tare da ɓata lokaci ba zan fara bayani akan abin da ya tara mu a nan. Da farko dai ni da aminina mun yi nazari sosai game da harkar gine-ginen gidaje, mun fahimci akwai alkhairi sosai a ɓangaren harkar ginen gidaje na zamani, especially idan suka kasance masu sauƙin farashi, to a irin babban birni kamar Abuja ba ƙaramar riba za'a samu ba, sannan kuma za'a samu customers sosai. Saboda haka muke son kafa wani babban aikin ginen gidaje a ƙarƙashin haɗin gwiwar wannan kamfanin".
Shiru Sudais ya yi, cikin nutsuwa ya fara duba file ɗin dake gabansa, wanda komai da aka shirya yana ciki. Bayan ya gama duba file ɗin, ya ɗago ya dube su ya ce "Ma sha Allah, yanzu ya tsarin aikin zai kasance?".
Alhaji Badaru ya gyara zamansa ya ɗora da faɗin "Mun shirya tsarin aiki ne bisa matakai guda uku, mataki na farko shi ne, zamu saye filaye a guraren da muka san zai yi saurin jawo hankalin al'umma, idan muka fara da sayen filaye, mun fara kafa tushe mai ƙarfi kafin mu faɗaɗa aikin. Mataki na biyu zamu fara gina rukunin gidaje na zamani masu ɗaukar hankali. Za mu yi amfani da ƙwararrun ma'aikatan gini, waƴanda za su yi aiki cikin tsari mai kyau da zai dace da farashin da za'a yi amfani da shi". Ya kai ƙarshen maganar yana nuna hotunan tsarin gine-gine da aka tsara, ya ɗora da cewa "Za'a fara da ƙananun gine-gine, kafin daga baya idan muka ga abin na tafiya cikin tsari sai a faɗaɗa shi. Ina ga idan muka bi wannan tsarin zai ba mu damar juya kuɗaɗe cikin sauƙi, kuma a samu riba mai yawa, mataki na uku shi ne yadda za'a sayar da su, bayar da gidajen ga customers, tare da tsarin biyan kuɗin cikin sauƙi. Daga nan idan mun samu yadda muke buƙata za a ci gaba da faɗaɗa aikin zuwa wasu yankuna. Sannan za mu buɗa office ɗin kula da customers, domin tabbatar da cewa duk wanda aka karɓi kuɗinsa tare da yi masa alƙawari an cika".
Sudais ya jinjina kai, ya ce "Tsarin ya yi kyau, kuma wannan kamfanin ya amince da wannan tsarin da kuka zo da shi, sai dai ina so a kula da kyau, domin a tabbatar cewa komai na tafiya cikin tsari da cikakken bincike".
Alhaji Badaru ya ce "In sha Allah komai zai tafi yadda ya kamata". Daga nan aka ci gaba da tattauna yadda abubuwan za su wakana, bayan an gama aka yi yarjejeniya da rubuce-rubucen da za'ayi kowanne ɓangare suka saka hannu, tare da ware adadin kuɗin da za'a yi haɗin gwiwar da su, bayan komai ya kammala ne aka sallami kowa ya tafi. Sudais na tashi daga kamfani kai tsaye gida ya nufa.
Amanarcool
***